Wednesday, 5 April 2017

لا إله إلا الله

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*BAYANIN MA'ANAR LAA'ILAHA IL-LALLAHU!!!*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*_001_*

_Rubutawa:_ *Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)*

*بسم الله الرحمن الر حيم*

*الحمد لله رب العالمين، وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين.*

```Da farko ya kamata musan cewa ita wannan Kalmar itace ke rabewa tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba!
Wannan Kalmar akan ta aka aiko dukkan Annabawa!
Itace Kalmar dake tabbatar da tsoron Allah na hakika!
Itace igiyar nan mai karfi, wacce duk Wanda ya riketa zata kaishi Aljanna!

Abin lura: Wannan Kalmar ba fadarta a baki ko da halshe tare da jahiltar ma'anarta ke sanya musuluncinka ya inganta ba!

Domin kuwa munafukai suna fadarta a bakunansu, amma kuma Allah yace" suna chan kasan wuta" a suratun nisa'i aya ta 145, tare da cewa suna Sallah suna sadaka, watakila har wurin wa'azi suna halarta.

Abunda ya kamata ga duk wanda ya fadeta, toh ya san ma'anarta har a zuciya ya kudurceta(ma'anarta, sharuddanta, falalarta, da abunda ta kunsa na tauhidi da akeeda) dole ne kaso Kalmar, kaso mai son Kalmar, dole ne ka yaki duk mai adawa da Kalmar ko mai saba mata.

Ita Kalmar LAA'ILAHA- IL-LALLAH! korewa ne da kuma tabbatarwa. Kore ilahantaka ga duk wani wanda ba Allah ba! Koda kuwa Manzo ne, ko Annabi, ko Mala'ika, ko wani mutumin kirki, ko gausi ko waliyyi koma Waye!  Tare da tabbatar da ilahantaka ga Allah shi kadai.

Na daga cikin mas'alolin jahiliyya wanda Annabi Muhammad s.a.w ya saba musu; Bautar mutanen kwarai ta Hanyar Neman biyan bukatunsu da nufin su nema musu ceto a wurin Allah, saboda zatonsu akan cewa Allah na son hakan. Kamar yadda Allah s.w.t yake cewa;
*ويعبدون من دون الله ما لا يضرهم ولا ينفعهم ويقولون هؤلاء شفعؤنا عند الله.* {يونس ١٨}

Ma'ana: "Suna bautar wani wanda ba Allah ba, Wanda bai iya cutar dasu, kuma bai iya amfanar dasu, har ma zakuji suna fada cewa wadancan sune masu cetonmu a wurin Allah"

Wannan ayar in muka lura zatayi aiki ga masu Dariku da yan shi'ah! Saboda suma zakuji suna fadar irin wadannan kalmomin, bari ma, wani lokaci nasu sunfi muni da hadari.

Muna rokon Allah s.w.t ya tabbatar damu akan tauhidi da akeeda Allah ka kara mana Ikhlasi.

Wannan mukaddima ce, amma bayanin zaizo a fitowa ta gaba insha Allahu.

Copyright©
Hashim Suraj Uba Tsamiya(ABU SINÃN)
08064734911```

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

Thursday, 30 March 2017

QARYA ADON YAN SHI'AH

*'KARYA ADDININ YAN SHI'AH!!!*
**

**

**
```Don haka ne ibn Taimiyya a cikin minhajis-sunnah 1/59 yake cewa; Malamai ma'abota ilimi sunyi ittafaki(sun hadu) akan hakaitowa da ruwayoyi da isnadi akan cewa yan Shi'ah(Rafidhawa) makaryata ne na gaske, kuma karya a wajensu dadadden abune ba wai yau suka fara ba.
Haka shima ABU HATIM-ARRAZY yake cewa naji yunus ibn Abdul-a'ala yana cewa; Ash-hab ibn Abdul-aziz  yace: An tambayi IMAMU MALIK akan yan shi'ah? Sai IMAMU MALIK yace; kada kuyi magana dasu! Kada Ku  ruwaito magana ko wani Abu da zai amfani Al'umma daga garesu! Domin su makaryata ne.

Wannan kuwa kowa na iya gasgata hakan a wannan zamani da muke ciki

((YAA KU WADANDA SUKAYI IMANI, KU KARE KAWUNANKU DA IYALANKU DAGA WUTA! WACCE MAKAMASHINTA MUTANE DA DUWATSU))

Allah ka  kare musulmai daga makirci da sharrin yan Shi'ah a duk inda suke```

Copyright©
*Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINÃN)*
📞08064734911☎

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

QARYA ADON YAN SHI'AH

*'KARYA ADDININ YAN SHI'AH!!!*
**

**

**
```Don haka ne ibn Taimiyya a cikin minhajis-sunnah 1/59 yake cewa; Malamai ma'abota ilimi sunyi ittafaki(sun hadu) akan hakaitowa da ruwayoyi da isnadi akan cewa yan Shi'ah(Rafidhawa) makaryata ne na gaske, kuma karya a wajensu dadadden abune ba wai yau suka fara ba.
Haka shima ABU HATIM-ARRAZY yake cewa naji yunus ibn Abdul-a'ala yana cewa; Ash-hab ibn Abdul-aziz  yace: An tambayi IMAMU MALIK akan yan shi'ah? Sai IMAMU MALIK yace; kada kuyi magana dasu! Kada Ku  ruwaito magana ko wani Abu da zai amfani Al'umma daga garesu! Domin su makaryata ne.

Wannan kuwa kowa na iya gasgata hakan a wannan zamani da muke ciki

((YAA KU WADANDA SUKAYI IMANI, KU KARE KAWUNANKU DA IYALANKU DAGA WUTA! WACCE MAKAMASHINTA MUTANE DA DUWATSU))

Allah ka  kare musulmai daga makirci da sharrin yan Shi'ah a duk inda suke```

Copyright©
*Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINÃN)*
📞08064734911☎

http://abbansinan.WordPress.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abusinan.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

Wednesday, 29 March 2017

WATAN RAJAB

```WATAN RAJAB

Watan da yan bidi'ah ke sheke ayarsu da rudar jahillai akan azumtar watan gaba daya ko kuma wasu kwanaki na cikin watan.
Irin wannan lokaci ya shigo ace bamu Dan shafa Kansu ba munyi kuskure.
Saboda haka Ku sauraremu bayanan Malamai zaizo akan watan Rajab da bidi'o'in da yan bidi'ah suka kirkira akan watan.

Kudai cigaba da kasance da ABBAN SINAAN a shafukan Sada zumunta na Facebook;
Hashim surajo uba Tsamiya.
Watsapp;
08064734911```

http://abbansinan.WordPress.com
http://hashimtsamiya.blogspot.com
http://abusinan.blogspot.com
atstsamawy@gmail.com

Friday, 24 March 2017

YAR JAMI'AH

```YAR JAMI'AH!

MEYE ILLAR DAKE SANYA WASU MAZA (MUSAMMAN GAYU DA KANANAN USTAZAI) CEWA BASA IYA AUREN YAR JAMI'AH???

WACECE YAR JAMI'AH???

MEYE BAMBANCI DAKE TSAKANIN YAR JAMI'AH DA YAR SAKANDARE KO WACCE BA TAYI BOKO BA???

HMMMMM

Wannan sune tambayoyin da Wata baiwar Allah YAR JAMI'AH tayi man, kuma ta nemi na bata Amsa.

Sai dai na bata hakuri zuwa wani lokaci kadan,bayan mun kare exams zanyi nazari sossai sannan na bata amsoshin tambayar ta.

Need ur prayer exam mode actvt

ABBAN SINAN(Hashim Surajo Uba Tsamiya)```

Http://abusinan.mywapblog.com
http://hashimtsamiya.mywapblog.com

Monday, 13 March 2017

PRAYER

Assalamu alaikum warahmatullah.

Dear brother and sister's,
I need your prayer bcos our examination commence on Monday insha Allah. So dat your prayer is very considerable to me.

ABU~SINAN
Hashim Surajo Uba Tsamiya Tsafe

Thursday, 9 March 2017

SHI'ANCI

*وإذا ذكر الله وحده اشمأزت قلوب الذين لا يؤمنون بالأخرة، وإذا ذكر الذين من دونه إذا هم يستبشرون*

```Idan ka duba Tafsirin 'kummy, wani jibgegen malamin Addinin shi'anci ne, a karkashin wannan Ayar wai sai yace ta sauka ne akan wane da wane! A akidar shi'anci idan sukace wane da wane, toh suna nufin Abubakar da umar, ko kuma suce Na farko da na biyu shima duk ma'anar daya ce! Toh amma a wannan suna nufin Abubakar da umar!
Toh amma ga fassarar ayar kafin muyi nisa
"Idan aka ambaci sunan Allah shi kadai, sai zukatan wadanda basuyi imani da ranar lahira ba su firgita, amma idan aka ambaci sunan wanin Allah(gumakansu ko waliyyai ko Wani Abun bauta) sai surinka fara'a suna jin dadi saboda wannan Albishir Na fadin sunayen"

Idan mai karatu zai iya daure wa ya duba littafan tafsirai Na manyan malaman musulunci insha Allahu zai samu cikakken bayani, amma ga Wani bayani daga littafan tafsiri guda biyu! أيسر التفاسر تأليف أبي بكر جابر الجزائري،   صفوت التفاسير تأليف محمد علي الصا بوني 
Sukace wannan ayar tana magana akan halin mushirikai ne, idan aka fadi sunan Allah saboda duhun jahilci da bata dake tare dasu  sai su rinka bayyana fushi suna damuwa, amma idan aka ambaci sunan gumakansu ko waliyyai ko wani Wanda suke bauta mawa sai kagansu suna farin ciki da jin dadi.
Toh komin hassadarka sai ka yarda da cewa Abubakar ba mushiriki bane! Duk Wanda kuma yace Abubakar mushiriki ne, wallahi sunanshi kafiri, da Nassin kur'ani, domin Abubakar da Nasarar Allah yake tafiya a cikin Al'amurransa.

Allah ka kara mana son sahabban Annabi Muhammad s.a.w kamar yadda kace ka yadda dasu. Allah ka kaskantar da duk mai Akeedar zagin sahabban Annabinka.```

Copyright©
Hashim Surajo Uba Tsamiya
Http://hashim141473.mywapblog.com