*وإذا ذكر الله وحده اشمأزت قلوب الذين لا يؤمنون بالأخرة، وإذا ذكر الذين من دونه إذا هم يستبشرون*
```Idan ka duba Tafsirin 'kummy, wani jibgegen malamin Addinin shi'anci ne, a karkashin wannan Ayar wai sai yace ta sauka ne akan wane da wane! A akidar shi'anci idan sukace wane da wane, toh suna nufin Abubakar da umar, ko kuma suce Na farko da na biyu shima duk ma'anar daya ce! Toh amma a wannan suna nufin Abubakar da umar!
Toh amma ga fassarar ayar kafin muyi nisa
"Idan aka ambaci sunan Allah shi kadai, sai zukatan wadanda basuyi imani da ranar lahira ba su firgita, amma idan aka ambaci sunan wanin Allah(gumakansu ko waliyyai ko Wani Abun bauta) sai surinka fara'a suna jin dadi saboda wannan Albishir Na fadin sunayen"
Idan mai karatu zai iya daure wa ya duba littafan tafsirai Na manyan malaman musulunci insha Allahu zai samu cikakken bayani, amma ga Wani bayani daga littafan tafsiri guda biyu! أيسر التفاسر تأليف أبي بكر جابر الجزائري، صفوت التفاسير تأليف محمد علي الصا بوني
Sukace wannan ayar tana magana akan halin mushirikai ne, idan aka fadi sunan Allah saboda duhun jahilci da bata dake tare dasu sai su rinka bayyana fushi suna damuwa, amma idan aka ambaci sunan gumakansu ko waliyyai ko wani Wanda suke bauta mawa sai kagansu suna farin ciki da jin dadi.
Toh komin hassadarka sai ka yarda da cewa Abubakar ba mushiriki bane! Duk Wanda kuma yace Abubakar mushiriki ne, wallahi sunanshi kafiri, da Nassin kur'ani, domin Abubakar da Nasarar Allah yake tafiya a cikin Al'amurransa.
Allah ka kara mana son sahabban Annabi Muhammad s.a.w kamar yadda kace ka yadda dasu. Allah ka kaskantar da duk mai Akeedar zagin sahabban Annabinka.```
Copyright©
Hashim Surajo Uba Tsamiya
Http://hashim141473.mywapblog.com
No comments:
Post a Comment