Thursday, 12 December 2019

TASBIHIN MAMU IDAN LIMAN YA KARANTA SURATUL A'ALA A CIKIN SALLAH

📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚
*KO YANA HALASTA MAMU YAYI TASBIHI A LOKACIN DA LIMAN YA KARANTA SURATUL A'ALA A CIKIN SALLAH???*
📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚

Rubutawa: *Abu Hussain, Abdulhameed As-safrawy*

Fassarawa: *ABU-SINAN ATS~TSAMAWY*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su kara tabbata ga farin jekada, Annabi Muhammad S.AW, da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka:

Bayan tambaya da mutane suka yawaita akan wannan matsalar naga ya dace in fassara wannan amsa da babban Malami ABU HUSSAIN ya ba wani Wanda yayi mashi irin wannan tambayar amsa a 04/09/2011 kusan shekaru tara kenan da suka gabata.
Kai tsaye ga hujjojin da malam ya kawo akan halascin hakan Daga bakin magabata
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

*IMAMUS SUYUDY (RH) A CIKIN*
الدر المنثور
Ya kawo hadisi Wanda imamu Ahmad da Abu daud da ibn Murdawaihy da imamul Baihaqy a cikin سنن nashi, Daga ibn Abbas(R.A): Manzon Allah s.a.w ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka Abdurrazak ya fitar a Musnad nashi, da ibn Abi Shaibah, da Abd bn Humaid, da ibn jarir, Daga ibn Abbas: ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka ibn Abi Shaibah da Abd bn Humaid sun fitar Daga Aliyu bn Abi Dalib (R.A) ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى sai yace: سبحان ربي الأعلى Alhali yana cikin Sallah, sai aka tambayeshi: shin anyi kari ne a cikin Qur'ani? Sai yace: A'a, mun kasance ana umurtarmu da fadar hakan, sai muke fada.

Haka Sa'eed bn Mansur da Abi Shaibah da Abd bn Humaid da Imamul Munzary sun fitar Daga  Abi Musa Al-Ash'ary(R.A) cewa Abi Musa Al-Ash'ary ya karanta سبح اسم ربك الأعلى a sallar Juma'ah sai yace: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Sa'eed bn Mansur da Abd bn Humaid da ibn Jarir da ibnul Munzary da imamul Hakim(kuma ya inganta) Daga Sa'eed bn Jubair yace: Naji Ibn Umar yana karanta: سبح اسم ربك الأعلى sai yace: سبحان ربي الأعلى sai yace: wannan itace Qira'ar Ubayyu ibn Ka'ab

Haka ibn Abi Shaibah da Abd bn Humaid Daga Abdullahi bn Zubair, cewa: Abdullahi bn Zubair ya karanta سبح اسم ربك الأعلى sai yace سبحان ربي الأعلى Alhali yana cikin Sallah.
Haka Nan Abd bn Humaid ya fitar da wani hadisin Daga Dhahhak cewa: yana karanta SURATUL A'ALA, Sannan yana cewa duk Wanda ya karanta ta ya fadi: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Abd bn Humaid ya fitar Daga Qatada, yace: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta SURATUL A'ALA yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Haka Nan Ibn Abi Shaibah ya fitar daga Umar, ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa سبحان ربي الأعلى

Ibn Katheer a cikin Tafsirinsa yake cewa:
Imamu Ahmad yace, Waqee' ya bashi labari, Isra'il ya bashi labari, Daga Abi Ishaq, Daga Muslim Al-bad'een, Daga Sa'eed bn Jubair, Daga ibn Abbas: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Ibn jarir Ad-dabary(R.H) yace: ibn Humaid ya bani labari, Hakam ya bani labari, Daga Anbasah, Daga Abi Ishaq Al-hamdany: Ibn Abbas ya kasance idan ya karanta: سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى
Haka idan ya karanta: لا أقسم بيوم القيامة idan ya Kai karshen ta أليس ذلك بقادر على أن يحيي الموتى
Sai yace: سبحانك وبلى

Bayan wadannan akwai wasu manyan malaman musulunci da dama da suka kasance suna aikata wannan Sunnah

Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albany(R.H) a cikin Sahih Abi daud(4/39)
Daga ibn Abbas: Manzon Allah S.A.W ya kasance idan ya karanta سبح اسم ربك الأعلى yana cewa: سبحان ربي الأعلى

Albany yace: Hadisi ne ingantacce, imamul Hakim ma ya inganta shi akan sharadin Buhari da Muslim.

Da wannan zamu fahimci kenan ba laifi bane don liman ya karanta SURATUL A'ALA mamu suyi Tasbihin da ya tabbata, kamar yadda hadisi ya tabbata akan hakan Daga bakin Manzon Allah S.A.W , kuma sahabbai suka kasance suna aikata wannan Sunnah.

Allah ya kara fahimtar damu sunnar Annabi Muhammad S.A.W, ya bamu ikon aiki da ita.

*Hashim Siraj Uba Ats~tsamawy (ABU-SINAN)*
+2349030201868

15/04/1441H
12/12/2019

https://fb.me/abbansinan

Saturday, 7 December 2019

010 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 010_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *SALLAH RAKA'A BIYU BAYAN ALWALA*

Manzon Allah S.A.W yace: *_((Duk Wanda yayi alwala irin wannan alwalar tawa, sannan yayi sallah raka'a biyu ba kayi tunanin komai ban cikin zuciyarka, an gafarta mashi abunda ya gabatar na zunubinshi))._*
[Bukhari 539, Muslim 159: Daga Humraan maula Uthman R.A]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

009 KARATUN HADISI

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 009_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *TAKAITA RUWA*

*_Daga Anas (R.A) yace: ((Manzon Allah S.A.W ya kasance yana wanka da sa'i daya ko mudu  5, yana alwala da mudu daya))._*
[Bukhari 737, Muslim 201]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

008 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 008_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *KALMAR SHAHADA BAYAN KAMMALA ALWALA*

Daga Umar Dan khaddab(R.A) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: *_((BABU WANI  DAYA DAGA CIKIN KU DA ZAIYI ALWALA, YA KYAUTATA ALWALAR, Sannan yace: ASH-HADU ANLAA ILAHA ILALLAHU, WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WARASULUHU, face sai an bude mashi kofofin aljanna guda takwasz ya shiga ta inda yake so))._*
[Muslim 553]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

007 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 007_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

006 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 006_

*SUNNONIN ALWALA*

🔸 *KUSKURAR BAKI DA SHAQA RUWA A 'DIBA GUDA*

Daga Abdullahi bn zaid(R.A), Manzon Allah S.A.W yace: *(( KUSKURAR BAKI DA SHAQA RUWA ANA YI NE A 'DIBA GUDA))*
[Bukhari 555]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

005 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 005_

🔸 *ADDU'AH A LOKACIN TASHI DAGA BARCI*

*الحمدلله الذي أحيانا بعد ما أماتنا، وإليها النشور*

*_ALHAMDULILLA I-LLAZI AHYÃNA BA'ADA MA AMÃTANA WA'ILAIHIN-NUSH UR._*

[Bukhari 6312]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan