HUKUNCIN JININ AL'ADA
( JININ HAILA)
Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su
tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban
shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jerin hukunce
hukuncen jinin al'ada wanda ake kira jinin haila
wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu
kawo hukunce hukuncen jinin biki (wato jinin
haihuwa.
Muhimmanci: yana da matukar muhimmanci
sanin hukunce hukunce jinin al'ada, muhimancin
bawai ya tsaya ga mata bane kadai a'a harda
maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na
zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada,
misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko
dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta
bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a
sakinta ba kuma a saduwa da ita, sannan ga
yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta
yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku
(al'ada uku) kafin akace ta kammala idda
sannan ai maganar sabon aure, to idan tana
al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan
sai bayan shekara daya da rabi za'a fara
maganar aure, shi yasa muka ce sanin hukunce
hukuncen wannan jinni ba wai ya rataya ga
mata bane kadai har da maza.
Menene Jinin Al'ada: Jinin al'ada jinine da yake
fita da karan kansa daka gaban macan da a
al'dance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce
kwanaki goma sha-biyarba.
Wannan shi ake nufii da jinin al'ada, da akace
'jinine da yake fita da kansa' kenan idan ya
zamana ba da kansa ya fitaba kamar ace
cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinni
ya balle mata to wannan bai zama jinin
al'adaba.
Da akace 'Ta gaba' kenan idan ya fita ta
dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin
al'adaba. Da akace 'Wacce a al'adance zata iya
daukar ciki' kenan idan ya fita daga wacce a
al'adance ba zata iya daukar cikiba sabo da
yarinta ko girma to wannan shima bai zama
jinin al'adaba.
Amma da aka ce 'Ba tare da ya wuce kwanaki
goma sha-biyarba' kenan idan ya wuce kwanaki
sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba.
Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin
al'adaba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau
kansuba za su yi sallah domin jinin ciwone sai a
nemi magani, Allah ya sawwake.
Mafi Karancinsa: Malamai sun karawa juna sani
kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa
shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan
ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.
Mafi Yawansa: Mafi yawan kwanakin jinin al'ada
shine kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya
wuce haka to bai zama jinin al'adaba muddin ba
ciki take da shiba.
Mata Dangane Da Al'ada: anan mu sani mata
suna da halaye biyar musamman idan muka yi
la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya
zo na al'adane ko bana al'ada bane, kamar
haka:
1. Kasa da shekara tara: Idan jinni ya zowa
yarinyar da take kasa da shekara tara to
malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada
bane, jinin ciwone sai a nemi magani.
2. Tara Zuwa Sama: Idan zamana jinin ya zo ne
ga wacce ta cika she kara tara zuwa zamanta
budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi
kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin
na al'adane ko na ciwo. Kada mu sha'afa
yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da
hutu da wahala suna tasiri.
3. Budurci Zuwa Sheka 50: Idan jinni ya zo
daga lokacin da ta zama mudurwa zuwa
shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun
tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.
4. Daga 50 - 69: Idan jini ya zowa mace a
tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara
hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai
sukace za'a tambayi kwararrun mata da likitoci
domin sanin wannan jinin na ciwone ko na
al'ada.
5. Daga 70: Idan jini ya zo bayan mace ta cika
shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai
sukace wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane.
Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin
abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce
hukunce akansu, kuma ana ginine akan tsarin
kalandar musulunci, wadannan bayanai na
karkasuwar mata har zuwa gida buyar kamar
yadda ya gabata haka malam Adawi ya kawo a
cikin littafinsa 'Hashiyatul Adawi' , Allah ya ji
kansa da gafara.
Ina dada jadda cewa yanayin abin ci da da
abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri
matuka, dukkan abinda ba'a mahimtaba
dangane da yana yin zuwan jinni ko daukewarsa
yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi
tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi
bayan da cewa yanada alaka da hukunce
hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce
miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da
aka saka zata iya kammala idda akasa da
watanni uku.
Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama
shine zuwansa na farko sannan ya tabbata
cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga,
dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau
kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta bata
lada idan kuma ta bari samari suna
jagwalgwalata ita za'a rubutawa zunubi, ba
wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara
yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka
wanda ta sha.
Tabbatuwar Jinin Al'ada: Shifa abinda ya
shafi jinin al'ada al'amari da Allah madaukain
sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai
girma, Allah yana cewa:
''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada,
Kace: Shidinnan cutane, ku ninci (saduwa da)
mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai
sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka
(suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya
umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba
kuma yana son masu tsarkaka'' . Bakara, ayata:
222.
Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan)
Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan
Adam'' . Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane
ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine
wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci
a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane
ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya
amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan
labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin
Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci
itaciyar.
Shifa jinin al'ada kada amanta jinine da yake
fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu,
Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya
zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin
mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da
mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da
karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya
zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga
mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada.
Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi
nono jaririn yana sha amatsayin abin ci, shi
yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa
kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata
da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya
kasance ba inda zaii je to shine sai ya taru a
mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake
fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko
bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan –
kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah-
gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.
Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari
ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin
al'ada, kashi na farko; itace wacce ta fara,
kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai
kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga
bayanansu kamar haka;
1. Wacce Ta Fara: Ita wacce ta fara al'ada ya
zama yinta na yanzu shi ne ganin al'adarta na
farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata
zuba idone ta ga kwanaki nawa zauka kafin ya
yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-
biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya
doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'adaba,
kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara
sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa
kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama
(Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake
cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu
mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su
tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi
yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko
makamantan haka, wata babbar macece amma
bata san menene jinin al'adaba ita dai kawai
tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu
kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.
2. Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta
saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku
a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi
al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai
ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima
kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta
wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki
sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farko
kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar
karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira
wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da
tsayayyun kwanaki.
Ita wacce ta saba wato wacce take da
sanannun kwanakin al'ada to wadannan
kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan
kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai
ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada,
amma idan kwanakin suka cika al'adar kuma
bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka
zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki
shabiyar su cika, misali idan al'adarta kwanaki
biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki
biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron
daukewar sun zama takwas kenan, idan ya
dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke
ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin
sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara
uku sun zama sha-hudu idan bai daukeba sai ta
kara kwana daaya, ya zama goma sha-biyar
kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya
dauke ko bai daukeba domin kwanakin al'ada
makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma
sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan
shi jinin al'ada sunanshi jinin cuta (Istihala) sai
a nemi magani.
Adukkan wadancan kare-karen kwanaki da
aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na
saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin
hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi
jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga
wacce ta fara da wacce ta saba.
3. Mai Juna-biyu (Mai ciki): Galibin mata masu
juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar
mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga
al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita .
Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu to ida
cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin
al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan
kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata
iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da
biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan
ana da juna biyu kuma aka ga jini.
Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata
wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke
bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda
zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta
natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo
sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware
kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki
domin da hakane zata cika kwanakinta na
al'ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta
farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta
hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a
ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da
ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana
biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita
ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu
al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki
takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da
dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine
kenan, ba na dane ya dawaoba.
Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jinin
al'ada ya dauke akwai alama da shara'a ta
sanya domin ya zama shine manuniya akan
cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun
kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin
kantane, sune kamar haka:
1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine
mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin
gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a
tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata
al'adarta ta dauke.
2. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai
laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace
ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta
kammala.
Wadannan alamomi su suke nuna daukewar
al'adar mace, idan mace bata taba ganin
al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin
bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba
sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta
saba ganice sai ta ga bushewar gaba to
malamai sukace zata zata dan saurara kadan
domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai
ga fitar zababban lokacin sallah ba.
A dunkuledai kowanne daya daga cikin
wadannan abubuwa guda biyu yana nuna
samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci
gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata
sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da
ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin
ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma
zata yi sallaba, da dai sauransu.
Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-
diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta
damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama
matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma
idan a karshen jinine to wannan ba komai,
Ummu Atiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: ((Mun
kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da
diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani
abune)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i,
Hadisi Na: 368 , Ibnu Majah Hadisi Na: 647,
Darimi Hadisi Na: 865.
Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin
da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar
asuba, amma ba'ace tat shi cikin dareba domin
ta duba.
Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta
ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da
la'asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga
tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi
sallar magariba da lisha.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai-al'adaba:
Anan za'a lissafa abubuwan da basu halatta
mai al'ada ta yi su ba ko ayi mata ba,
wadannan abubuwane guda goma:
1. Sallah: Bai halatta mai al'ada ta yi sallaba
farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yi ba'akarba
ba sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta
kammala al'adar ba zata rama sallolinba.
2. Saki: Baya halatta matar da take al'ada a
saketa, wannan ya sabawa karantarwar
musulunci, saboda haka koda yana son ya
saketa to ya bari sai ta kammala al'ada kafin
ya sadu da ita sai ya saketa, amma idan ya
saketa tana jinin al'adar to sakin ya yi amma
za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai
kai ukuba.
3. Dawafi: Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin
Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda
maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da
kwanan mina dana muzdalifa da jifa da
Labbaika, da daidai sauransu.
4. Zama A Masallaci: mai al'adah ba zata
zauna a cikin masallaciba, domin sauraron
karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.
5. Azumi: Bai halatta mai al'ada ta yi azumi na
farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba,
saboda haka zata lissafa azumin da ta sha
bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba'a ajiye
azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo,
amma dazaran ta zo to dazaran ba azumi,
dazaran bata zoba to dazaran akwai azumi, ko
da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to
biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.
6. Taba Alkur'ani: mai al'ada bata taba
kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita
bata da tsarki, amma wannan bay a hana idan
ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa
wuri.
7. Karatun Alkur'ani: mai al'ada bata karanta
Alkur'ani, duddacewa wadansu malamai suna
ganin ya halatta ta karantashi da ka domin kada
ta manta sabanin dauka.
8. Saduwa: Bai halattaba saduwa da mace
tana al'ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu
da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa
Allahba asalima ta yi biyayyane ga reshi, bai
halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai
al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki,
kenan koda al'adar ta dauke amma batayi
wankaba to bai halatta a sadu da itaba. Ya
halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin
matarsa alokacin da take al'ada bayan ta yi
kunzugu inbanda daga cikbiyarta zugwiwarta
wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke
kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta
taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.
9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al'ada tana
tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.
10. Wajabta Wanka: Al'ada tana wajabta wanka,
wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar
ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.
Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan
tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah ya yi mana
jagora ya karba mana ayyukammu.
Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka
gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al'ada
bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba,
kuma lalle idan aka kallaci yadda ake sakaci
tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi
wannan al'amari to lalle abin yanada ban tsoro.
Anan gaba abinda zai biyo baya shine hukuncin
jinin biki wato jinin haihuwa.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja, Nijeriya.
No comments:
Post a Comment