Monday, 2 January 2017

TAIMAMA DA HUKUNCE- HUKUNCENTA

TAIMAMA DA HUKUNCE-
HUKUNCENTA

Matashiya: Hakika Allah mai girma da daukaka
ya shar'anta tsarkaka daga hadasin da yake
karami ko babba kafin gabatar da sallah,
wannan tsarkaka kuma bata yiwa sai da ruwa
mai tsarki mai tsarkakewa, gabatar da wannan
tsarki da kuma rowan da aka ambata shine
abinda yake wajibi muddin akwai dama, sai dai
akan sami wasu lokuta da ake rasa rowan
kwatakwata ko kuma ga ruwan amma idan aka
yi alwala da shi ko wanka za'a rasa wanda za'a
sha, koma yin anfani da rowan zai haifar da
wasu cututtuka da dai sauran wasu dalilai
shar'antattu da zasu hana amfani da ruwan to
akan haka aka shar'anta Taimama domin
sawwakewa al'umma, da kuma dauke dukkan
wata damuwa akan hakan.
Mecece Taimama?: Taimama itace; Shafar
fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi
kebantacce.
Kenan ba kowacce shafar fuska da hannu ne
yake zama taimama ba, sannan kuma ba a
kowanne wuri ake yi ba, sannan ba yadda aka
ga dama ake yi ba.
Tabbatuwar Taimama: Taimama ta tabbata
daga haske na Alkur'ani da kuma Hadisan
ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allan su
tabbata a gareshi- kana da ijima'in malamai.
Tabbatuwarta A Kur'ani : Allah ya yi bayanini
shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai
girma a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma
Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu
kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato
aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki yana
cewa:
''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani! Idan
kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku
da kuma hannayanku zuwa gwiwar hannu, ku
kuma shafi kawunanku kuma ku (wanke)
kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance
masu janaba to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan
kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan
tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan
gida, ko kuma kun taba mata (janaba) baku sami
ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki
sai ku sahfi fuskokinku da kuma hannayanku
daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun
kunci ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku
kuma domin ya cika ni'imarsa a gareku domin ku
gode masa. (Ma'idah, aya ta:6).
Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi
hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake
karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan
tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi
taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da
manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar,
Allah muna gode maka, akan wannan ni'ima.
Tabbatuwar Taimama A Hadisi : Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare
shi- yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba
wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana
sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira
tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta
zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani
mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to
ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda
yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''.
Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521.
Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin
ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan
al'ummar gatan da bai yiwa wata al'ummaba, a
ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta
zama wurin sallah, al'ummomi da suka gabata
basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu,
amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka
kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an
sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi
tsarki da ita kamar yadda bayanai suka gabata
a baya akan istijmari, sannan kuma zaka yi
taimama da ita kamar yadda ake kawo bayani a
yanzu haka.
Taimama matsayine na musamman da wannan
al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya
taimama ga wata al'ummaba kafin wannan
al'ummar domin yalwatawa ga wannan
al'ummar.
I jima'i: Malamai duk sun yi ijima'i akan
tabbatuwar taimama.
Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a
shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan
abinda kasan ba'a yi said a ruwa to ana yi da
taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani
da dai sauransu.
Taimama Tana Tsayawa Matsayin A Lokuta
Kamar: Kenan anan za'a lissafo abubuwan da
suke sawa a yi taimama, domin kada kabar
sallah ta wuce maka kace ai baka sami ruwa
bane wannan ba zai sa ka sami sassauci ba
domin sabo da hakan aka shar'anta taimama,
wadannan wurare sune kamar haka:
1. Rashin Ruwa: Kasan cewa suna cikin tafiya
ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun
nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba,
to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su
bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai
su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a
cikin su akwai masu janaba, ko matan da
al'adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar
da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko
da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi
addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane
shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da
sauki a gareka.
2. Ruwan Ba Zai Isaba: Idan kuma a tare da ku
akwai ruwan amma kuna da matukar mukata
domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi
za ku ba dabbobi ko shi kuke sawa a injin mota
ta yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe
ku wadancan bukatuba, asalima za'a iya
tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa
to amma miyagun namun dajine a wurin ko
kuma matattarar barayine wurin to anan fa
hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa,
saboda haka wadanda suke dashi kadan domin
bukatunsu sai su sha su yi taimama.
3. Cuta: Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta
a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin
warkewa, sai ka yi taimama.
4. Rashin Motsi: Idan ya zamana yana fama da
rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai
iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar
kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko
babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya
yi taimama.
5. Sanyi : Idan yana matukar jin tsoron sanyi
idan ya yi anfani da ruwa, kuma ga shi yana son
yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami
abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya
yi taimama.
Wadannan bayanan suna nuna mana cewa
rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba
zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin
warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da
aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici
shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya
to abu na farko da zai ajiye shine sallah, inda
zaka je gai dashi kace ya yi sallah kuwa sai ka
ga ana kallonka ana nuna maka halin da yake
ciki kamar kai baka da tausayi, inda kuma zaka
dan shafa masa dari ko dari biyu sai ya miko
hannu, Allah Ya sawwake.
Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai
bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a
barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba.
Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa
kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa
akan bandejin ko karan dorin to sai ya yi
alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba
sai ya wankeba.
Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya
zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan
kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi
bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi
sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo
matsanancin rashin lafiya day a shafi gabban
alwala ko taimama darasine mai zaman kansa,
a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-
daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin
cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya
kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan
taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa
da alkhairi.
Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake
doron kasa kamar inda yake; rairayi ko
jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko
ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.
Siffar Taimama: Yadda ake gabatar da taimama
shine; zaka wara yatsun hannayanka biyu ne sai
ka buga a kasa, sannan sai ya shafi fuskassa
da cikin tafikan hannunsa, sai kuma ya shafi
hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), zai yi ko
kari ya tabbata ya game ko'ina na fuskarsa a
lokacin da yake shafar kar ya manta da
karkashin gemu da kuma hannayansa, idan yana
da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko
ina, idan lokacin da ya shafo kasar kwai yayi ko
kura sai ya karkade, ba'ace dole sai mutum ya
sa kasa a fuskarsa ba.
Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau
biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun
kuma ya shafi hannuwa zuwa gwiwar hannu.
Za'a ko yi yadda ake taimamane da sauran
ibadu a gaban malamai, karantawa anan kadai
ba zata wadatarba, su kuma malamai su ji
tsoron Allah su koyawa al'umma wadannan
ayyuka a'aikace, sawa'un makarantun
islamiyyune ko malaman da suke koyar da
darussan addinin musulunci a cikin jami'o'i ko a
kwalejojin ilimi, ko kuma malamai da suke
karantarwa a cikin masallatai, kada ka taba jin
dan ka karantar da baki kowa ya gane, a'a sai
ka yi a aikace, kada ka manta sai da ma'aikin
Allah ya koyawa sahabbansa wadannan ayyuka
a aikace, ka ko san idan saurin ganewane sun
fika sun fi daliban da kake koyarwa.
Abundake Bata Taimama; Taimama tana baci
da duk abinda yake bata alwala babbane ko
karami, kamar tusa fitsari…. Fitar maniyyi, jinin
al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi
taimama ya gushe to taimama ta gushe.
Wanda ya rasa ruwa kuma ya rasa kasar da
zai yi taimama akanta, ko kuma ya kai wani
halin dab a zai iya taba ruwaba ko kasa to shi
wannan zai yi sallar ne a yadda ya sami kansa,
ba tare da alwala ko taimama ba, domin Allah
bai dorawa rai sai abinda zata iya.
Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar
farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan
taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi
sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi
kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama
to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar,
domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa
idan bai samu ba to sai ya yi taimama.
Idan mutum ana binshi wadansu salloli da ya
manta da su to ya samu ya sallacesu da
taimama guda.
Kammalawa: wannan kadan kenan daga cikin
abubuwan da suka shafi taimama da fatan sun
wadatar, kuma za'a koma ga malamai.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.

No comments: