YADDA AKE WANKAN
TSARKI
Matashiya: Bayanda bayanai suka gabata akan
abubuwan da suke wajabta wanka, ayanzu za
mu kawo bayani akan yadda ake gabatar da
waken da izinin Allah.
Da farko dai mu sani shi wannan wanka
amanace daga cikin tarin amanar dake tsakanin
bawa da mahaliccinsa, saboda haka ya zama
wajibi ka kiyaye wannan amanar, kuma ka
himmatu da sanin hukunce hukuncen wannan
wanka, domin ka gabatar da shi a yadda
musulunci ya tsara, abinda ya rikice maka sai
ka yi tambaya, kada kace wai kunya zata
hanaka, jin kunya a irin wadannan al'amurra
abune da musulunci bai yarda da shiba, kuma
wani nau'ne na tsoro da shaidan yake tsoratar
da mutane da shi, kuma ya sanyawa mutum
kasalar da ba zai iya gudanar da cikakken
addiniba. Al'amarin hukunce-hukuncen tsarki
al'amarine mai girman gaske, sakaci a cikin
wannan lamari yana da matukar hadari, domin
kada ka manta hukunce-hukunce sallah ya
ratayune fa da tsarki wacce kuma sallar nan
itace ginshikin addini.
Farillan Wanka: Ka/Ki sani shi wankan tsarki
yana da farillai da kuma sunnoni dama
mustahabbai, amfanin saninsu shine domin duk
abinda yake farillane sai baka yi shi to wankan
bai yiba, amma idan sunnah ka bari wankan ya
yi saidai ka rage lada. Su farillan guda biyarne;
(1) Niyya: Abinda ake nufi shine ka kudurce a
zuciyarka/ki yanzu hakannan wankan janaba
zaka yi ko zaki yi, ko kuma na daukewar al'ada
ko biki…', wannan itace niyya, ba wadansu
abubuwa ake karantawaba, niyya kuma tana da
matukar muhimmanci, ai kaga shi yasa ta zo a
farko.
(2) Game Jiki Da Ruwa: Ana so ka tabbatar ko
ina a jikinka ya sami ruwa, kada ka manta da
dukkan mahadar gaba.
(3) Cuccudawa: Ka tabbata ka cuccuda ka
gurza ko ina da gwargwadon hali, kada ka
manta da kasan hammata da dukkan matse-
matsi…'.
(4) Tsefe Gashi: Ka tabbata ruwa ya shiga ko
ina a cikin gashin kanka ko kanki, Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
yana cewa: ''Karkashi ko wanne gashi akwai
janaba, ku wanke gashi, ku kuma tsaftace jiki'' .
Abudaud, 248, Tirmizi: 106, Ibnu Maja: 597.
(5) Yi Lokaci Guda: Wannan shi ake nufi
'Muwalat' ma'ana idan ka fara to kada wani abu
ya katseka sai ka kammala.
Wadannan sune farillai ka tabbata sun cika a
duk lokacin da kake wanka, kada ka manta shi
wankan tsarki anayin shine da ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa ken an banda mai sabulu. Ka
samu idan kana da janaba kuma kanason ka yi
wankan tsarki da kuma wankan zuwa wurin aiki
ko kasuwa da sauransu, sai ka fara gabatar da
wankan tsarki tukunna, idan ka gama sai ka sa
sabulu ka ci gaba da wankanka.
Siiffar Wankan Janaba: Da farko za ka yi niyya
a zuciyarka (kamar yadda bayani ya gabata).
Sannan ka ce: Bismillah , sai ka wanke
hannayanka biyu sau uku, sai kuma ka wanke
gabanta (al'aura), hannun dama na zuba ruwa
na hagu yana wankewa, sannan sai ka goge
hannun naka a bango, sai ka gabatar da
cikakkiyar alwala, sannan sai ka kamfaci ruwa
ka zuba a kanka domin ka kosar da gashin
kanka zaka yi hakanne sau uku. Sannan sai ka
dibi ruwa ka kwarara a jikinka kana cuccudawa
domin rowan ya kai ko ina, Shikenan ka gama.
Kana da dama ka wuce zuwa sallah kai tsaye
batare da ka yi alwalaba, sai dai idan wani abu
cikin abubuwan da suke karya alwala ya faru.
Kada ka manta koda kana cikin wanka
alwalarka ta karye wankanka nanan ba abinda
ya sameshi, sai idan kana so ka yi sallah to sai
ka yi alwala.
Banbanci Janaba Da Al'ada: Anan ana so ki
gane wankan janaba da wankan daukewar jinin
al'ada ko biki duk iri dayane, inda suka
banbanta kadanne. Wuri na farko: Niyya, domin
da ita ake banbace ibada da ibada kamar
wannan da muke Magana kai. A wankan janaba
mace ba sai ta kwance kitson ta ba domin
hakan zai zama akwai wahalarwa sai ya wajaba
ta tabbata ruwa ya shiga asalin tushan gashin
kai, amma a wankan daukewar al'ada ko na biki
ya halatta ta kwance kitson dake kanata, amma
ba wajibi bane, a dai tabbata ruwa ya shiga ko
ina wannan kuma ya shafi maza kamar yadda
ya shafi mata, akwai maza masu yawan gemu
da suma to dolene a tabbata ruwa ya kai ga
asalin tushan gashi, a cuccuda ko ina da ina,
idan mutum yana sanye da zobe ya tabbata
ruwa ya shiga karkashin zoben, akyautata
wanka a kuma karanta ruwa. Allah ya sa mu
dace.
Idan mace al'adarta ta dauke kuma ga
wankan janaba akanta, to wanka guda za ta yi
sai ta gwama niyyar kamar yadda wadansu
malamai suka fada, domin wankan janaba dana
al'ada duka wajibine kuma komai nasu
dayane…'.
Idan mutum yana da janaba kuma ga wankan
juma'a, to anan ya samu ya shgar da wankan
juma'a cikin na janaba, ba wai ya shigar da na
janaba cikin na juma'aba, domin na janaba
wajine, amma na juma'a ba wajibibane a mafi
yawan maganganun malamai.
Idan ka yi wankan janaba sai kuma ka manta
baka yi alwalaba wankanka ya yi, kuma ka
samu ka yi sallah ko da baka yi alwalaba
muddin ba wani abun da ke karya alwala da ya
faru, domin alwalar ta shiga wanka duk inda
zaka wanke a alwala ka wanke shi a wanka,
kuma kamar yadda alwala take wajibi kafin
sallah haka wanka yake wajibi ga mai janaba.
Amma idan mutum ya yi wankan juma'a to
sai ya yi alwala kafin sallah.
Ya hallata miji da mata su yi wankan janaba
tare, kamar yadda aka ruwaito daga daya daga
matan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi- yana yi.
Ka samu ka jinkirta wanka amma sai ka yi
alwala domin alwalar na rage kaifin janaba,
kuma tana kara kuzari idan za'a sake saduwa.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka
gabata ya bayyana a fili yadda addinin
musulunci ya kula da tsarkaka da kuma lafiya,
domin janaba bakaramin al'amari bace, saboda
haka aka shar'anta wanka, kuma aka kawo
siffar wankan daki-daki domin ka fahimci a
musulunci ba'a yin abu da ka, fatammu shine
Allah ya karba mana kurakurai kuma ya gafarta
mana, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.
No comments:
Post a Comment