Thursday, 9 March 2017

ALHAMDULILLAH.

*ALHAMDULILLAH!*

*Allah ya saka ma _MALAM NURA ALIYU TSAMIYA_*  ```Malam ya kasance a duk lokacin da za'a fara wa'azi na kwamitin da'awah ya na wani jawabi inda yake cewa; "A duk lokacin da kaji za'a fara wa'azi kira'ar Qur'ani na tashi, toh Alama ce da ke nuna cewa za'ayi wa'azin musulunci!  Bude taro da kide kide ko wake-wake alama ce dake ta Addinin kirista! Mai kokwanto ya bari ranar lahadi yaje church yaji da me suke budewa!"
Toh wa'azin Malam ya fara tasiri ga daliban waliyyin baro na Tsafe! Duk da cewa farko kide kide a kasa, amma kafin OGA ya fara jawabi sai naji Ankira wani domin bude jawabin ko ba'a lura ba, da karatun Qur'ani.
Toh adai cigaba da wannan fadakarwar MALAM NURA, insha Allahu sai gaskiyar ta ida bayyana.```

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya_*

No comments: