Ibrahim Jalo Jalingo
BA MAZHABA BA CE LAIFI MAZHABANCI SHI NE LAIFI:
Ba mazhaba ba ce laifi a'a mazhabanci shi ne laifi, ma'anar mazhabanci shi ne: nassin Annabi mai
tsira da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan kai ka ki yin aiki da
shi wannan nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa abin da ke rubuce cikin mazhabarka.
Ba kungiya ba ce laifi a'a kungiyanci shi ne laifi, ma'anar kungiyanci shi ne: nassin Annabi mai tsira
da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan kai ka ki yin aiki da
wannan nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa wata ka'ida da kungiyarka ta shata wa kanta.
Allah muke roko da Ya tausaya mana Ya cusa son Annabi mai tsira da amincin Allah, da son fifita
maganarsa a kan maganar kowa cikin zukatanmu. Ameen.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. MU KOYI IBADA A SAUKAKE
Thursday, 9 March 2017
Dr jalo
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment