🍌🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍌
*YA YA ZAMU FUSKANCI RAMADANA???*
🍇🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍇
_Rubutawa:_ *Hashim Ibn Siraj Ibn Uba{ABU SINÃN}*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda ya wajabta mana yin azumin watan ramadana, Tsira da amincin Allah su tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w Wanda ya koya mana yadda zamu gabatar da azumin ramadana.
Bayan haka;
Allah s.w.t yana fada a cikin suratul bakara aya ta 185 cewa;" watan ramadana Wanda a cikinsa ne aka saukar da Qur'ani domin shiriya ga mutane da kuma bayyanar da shiriyar....."
Ya yan uwa
Allah s.w.t ya kebance watan ramadana da kebantattun abubuwa masu yawa akan waninsa. Daga cikin abubuwan akwai;
* Fadar manzon Allah s.a.w cewa: warin bakin mai azumi, yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.
* Mala'iku na nemawa mai azumi gafara har zuwa lokacin da zaiyi buda baki.
* Ana tsare shaidanu a cikin Ramadana.
* Ana bude kofofin aljanna, ana rufe kofofin wuta.
* A cikin Ramadana ne Daren lailatul kadri yake, wadda tafi wata dubu Alkhairi.
* Allah na gafartawa mai azumi a karshen daren ramadana.
Ya yan uwa
Da wane irin abu zamu tarbi ramadana? Da wasannin banza??? Ko da zuwa kallon kwallo??? Ko da kallon fina finai???
Muna neman Allah ya tsaremu da aikata daya daga cikinsu a wannan wata mai albarka.
Shi bawan Allah na kwarai yana fuskantar ramadana da tuba zuwa ga Allah, yana mika lokuttanshi gaba daya domin yin ayukan kwarai, bawan Allah na kwarai shine mai rokon Allah akan ya karba masa ibadojinsa da addu'oinsa.
1- AZUMI
Manzon Allah s.a.w yana cewa; "Dukkan wani aiki da mutum zai yi, yana da ladar goma irinsa, amma ga azumi ana lunka aikin zuwa lunki dari bakwai(700). Allah mai girma da daukaka yace; banda azumi! Azumi nawa ne, kuma ni zan sakawa masu azumi,(ma'ana babu Wanda yasan adadin ladar mai azumi sai Allah) sun bar abubuwan da suke sha'awa da kauna, sun bar abinci da abin sha saboda ni, mai azumi nada farin ciki biyu, farin ciki lokacin buda baki(shan ruwa), da kuma farin ciki lokacin haduwarsa da ubangijinshi. Warin/yamin bakin mai azumi yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.[Bukhari da Muslim]
Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda ya azumci ramadana, yana mai imani, da kwadayin Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubbanshi.[Bukhari da Muslim]
2- SALLAR TARAWIHI/KIYAMUL-LAILI.
Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda yayi tsayuwa a ramadana, yana mai kwadayin Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubanshi.[Bukhari da Muslim]
3- SADAKA
Manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kowa sadaka a Ramadana da waninsa, manzon Allah kyautarsa tafi iskan dake kadawa yawa, domin tana game kowa da kowa. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana cewa; "Mafificiyar sadaka, itace wacce akayi a cikin Ramadana.
4- CIYAR DA ABINCI
Akwai alkhairai kwarai da gaske a cikin ciyar da abinci, a Ramadana ne ko waninsa. Kamar yadda Allah s.w.t ya ambata siffofin mutanen kirki a cikin suratul insãn aya ta 8-12 saboda suna ciyar da abinci tare da zukatansu na cikin jin dadi da walwala lokacin da suke ciyarwar.
Magabata na kwarai sun kasance suna ciyar da abinci a ramadana kwarai da gaske, manzon Allah s.a.w yana cewa; "yã Ku mutane Ku watsa sallama, Ku ciyar da abinci, Ku sadar da zumunta, kutashi lokacin da mutane ke barci domin kuyi sallah, zaku shiga aljanna da aminci.[imamu Ahmad ya ruwaito da tirmidhi, Albany ya ingantashi].
Manzon Allah s. a.w yace: "Duk Wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatan kwacin ladarsa, ba tare da anrage mashi komai ba.[imamu Ahmad ya fitar, da nasa'i, Albany ya ingantashi.
5- NEMAN LAILATUL-KADRI.
Allah madaukakin sarki yana cewa: "Lallai mu muka saukar dashi (Qur'ani) a daren daraja, wa ya sanar dakai me ake cewa daren daraja, daren daraja yafi Alkhairi fiye da wata dubu.
Manzon Allah s. a.w yace; "Duk Wanda yayi tsayuwar daren lailatul-kadri, yana mai imani da kwadayin Neman lada, an gafarta mashi zunubbansa.[Bukhari da Muslim]
Lailatul-kadari ana nemanta a daren 21,23,25,27 ko 29. Hadisi ya tabbata daga ummuna Aisha R.A tacewa manzon Allah s.a.w idan na dace da daren lailatul-kadari me zan fada? Sai yace mata kice; اللهم إنك عفو،تحب العفو،فعف أني
Ma'ana; "yã Allah kai mai yafiya ne, kanason masu yafiya, ka yafe mani.[Ahmad ya ruwaito da tirmidhi, Albany ya ingantashi].
6- YAWAITA ZIKIRI DA ADDU'AH DA ISTIGFARI.
Ya yan uwa
Kwanakin watan ramadana masu tsada ne, mu daure mu ribacesu da yawaita zikiri da addu'ah, musamman a kebantattun lokuta na amsar addu'ah. Daga cikin lokuttan akwai;
* Lokacin da mai azumi zaiyi buda baki, ba'a maida addu'ah a wannan lokacin.
* Daya bisa ukun dare, lokacin da Allah s.w.t yake saukowa yana cewa: "ina mai rokona in amsa mashi, ina mai neman gafara in gafarta mashi.
Daga karshe ina kwadaitar damu akan mu tsaya mu ribaci wannan wata mai albarka kafin ya wuce! Idan ya wuce bamu da tabbacin zamu kara riskarshi.
Allah ya tabbatar damu akan aikata abubuwan da suka dace da sunnah a cikin wannan wata mai albarka.
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
COPYRIGHT©
Hashim ibn Surajo ibn Uba(ABU SINÃN)
ATS~TSAMAWY```
atstsamawy@gmail.com
http://hashimtsamiya.mywapblog.com
http://abbansinaan.mywapblog.com
http://abbansinan.WordPress.com
http://shababusunnahtsafe.mywapblog.com
http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com
https://free.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
+2348064734911
+2349030201868
No comments:
Post a Comment