Monday, 22 May 2017

AZUMIN WATAN RAMADHANA

🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉
*AZUMIN WATAN RAMADANA*
🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇🍉🍇

*بسم الله الرحمن الرحيم*

_Rubutawa;_ *HASHIM SURAJO UBA(ABU SINÃN)*

```ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU.

  Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t shi kadai Wanda yayi mana umurni da azumtar ramadana, tsira da amincin Allah su tabbata ga farin jekada, Annabi Muhammad s.a.w Wanda ya koya mana yadda zamu gabatar da ibadar azumi da sauran ibadoji.

Bayan haka;

FALALAR WATAN RAMADANA DA AZUMI A CIKIN WATAN.

Manzon Allah s.a.w yace; "idan ramadana ya shigo, ana bude kofofin sama, ana kulle kofofin jahannama, ana daure shaidanu.
A wani hadisin kuwa manzon Allah s.a.w cewa yayi" Dukkan wani aiki da dan Adam zaiyi, ana lunka aikin da lada goma irinsa, idan a ramadana ne, ana lunkashi zuwa lunki (700), sai Allah mai girma da daukaka yace ;  banda azumi, domin azumi nawa ne, kuma ni zan sakawa Wanda yayi shi, yabar matarshi da abubuwan da yakeso, da abinci, da abin sha saboda ni, mai azumi Nada farin ciki biyu, farin ciki lokacin buda baki (shan ruwa) da farin ciki lokacin haduwarshi da Allah, yamin/warin bakin mai azumi yafi turaren almiski kamshi a wurin Allah.[Bukhari da Muslim]

ABUBUWAN DA SUKA WAJABA GAREKA A RAMADANA

Ya dan uwa

Kasani cewa Allah ya wajabta mana azumi domin mu bauta masa dashi, sannan kuma ya kasance cewa azuminka ya zamto karbabbe mai amfani.
Dole ne ka kiyaye wadannan abubuwan da zasu zo domin samun cikakkar lada;

1- kiyaye sallah; Da yawa daga cikin masu azumi suna wasa da sallah, bayan kuwa cewa tana daga cikin gimshikan addini, barinta kuma yana kai mutum ga kafurci.

2- Dole ka kasance mai kyawawan dabi'u; Dole ne mu tsoraci kafurci da zagin addini, da aikata muna nan dabi'u a cikin mutane, kafirci yana fitar da musulmi daga addini.

3- Dole ne mu kiyaye halshenmu da sukar juna.
 
Manzon Allah s.a.w yana cewa; "idan dayanku yana azumi, to kada ya fadi maganganun da basu dace ba, idan wani ya zageka ko ya nemi yayi fada da kai, sai kace mashi ni azumi Nike, ni azumi Nike.

4- Ka nisanci zuwa wurin da ake aikata barna! Ko kallon fina-finai na banza, domin hakan zai kai ga bata azuminka.

5- Ka yawaita sadaka ga makusantanka da mabukata, da ziyartar yan uwanka.

6- Ka yawaita zikiri da karatun Qur'ani da saurararshi, da bibiyar ma'anoninsa, da aiki da abinda yake karantarwa, sannan da zuwa masallatai domin daukar darussa masu amfani, kamar sauraran tafsirai, yin ittikafi a masallaci idan goman karshe na ramadana suka kama.

7- karanta takardu akan azumi, domin sanin hukunce- hukuncen da suka shafi azumi, ta yarda zakasan cewa cin abinci ko abin sha da mantuwa baya karya azumi, kasan cewa ita janaba wacce ta sameka da daddare bata hana ka daukar azumi da sauransu.

LADUBBAN DA SUKA SHAFI AZUMI.

1- kiyaye halshe; Manzon Allah s.a.w yace; "Duk Wanda bai bar zancen karya ba, da aiki da zancen karya, Allah baya da bukatar barin cinsa ko shansa.

2- BUDA BAKI DA SAHUR DA ADDU'AH.

Manzon Allah s.a.w yace; "idan dayanku zaiyi buda baki, to ya fara da dabino domin akwai albarka a ciki, idan bai samu dabino ba toh sai yayi da ruwa, domin suna tsalkakewa.
Manzon Allah s.a.w ya kasance idan zaiyi buda baki yana fadar;
ذهب الظمأ، وابتلت العروق، وثبت الأجر، إن شاء الله.

Ma'ana: "YUNWA TA TAFI, GABOBI SUN DAI DAI TA, LADA TA TABBATA DA YARDAR ALLAH".
Manzon Allah s.a.w yace; "mutane baza su gushe suna samun alkhairi ba matukar suna gaggauta buda baki.

Anan dole mu gujewa muna nan akeedun shi'ah wadanda basa shan ruwa sai duhu ya shigo sosai, suna kafa hujja da ayar Qur'ani dake cikin suratul bakara, inda Allah s.w.t yake cewa; "...sannan Ku cika azumi zuwa dare. Wanman magana malamai sunyi bayanin me ake nufi tun da dadewa, mai Neman Karin bayani ya duba tafsirin "Aisarat-tafaseer, na jabir jaza'iry."

Manzon Allah s.a.w yace"kuyi sahur, domin a cikin yin sahur akwai albarka."

Manzon Allah s.a.w yace"Duk Wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatan kwacin ladarsa, ba tare da an rage komai daga ciki ba.

3-  DAGA CIKIN FA'IDOJIN AZUMI

   Duk Wanda yayi azumin ramadana, yana mai imani da Neman lada, an gafarta mashi abunda ya gabata na zunubbansa.

Duk Wanda yayi tsayuwar ramadana, yana mai imani da Neman lada, an gafarta mashi zunubbansa.(ma'ana: tsayuwar tarawihi da kiyamul-laili.)

4- WADANDA AKA YIWA RANGWAMEN AZUMI.

   *Marar lafiya da matafiyi, zasu ranka saboda fadar Allah s.w.t cewa;"Wanda ya kasance a cikinku marar lafiya ko akan hanyar tafiya, zai ranka azumin a kwanakin sauran watanni."
Amma marar lafiya Wanda ba'asa ran warkewa a kusa, toh sai ya rinka ciyar da talaka daya a kowace rana.

* Mai haila, da jinin haihuwa zasu aje azumi, saboda fadar ummuna Aisha R.A; "mun kasance ana umurtanmu da ranka azumi, amma ba'a umurtanmu da ranka sallah.[Bukhari da Muslim].

* Dattijo da dattijiya, wadanda sun tsufa sosai basa iya daukar azumi toh zasu ciyar da talaka daya a kowace rana.

* Mace mai ciki da mai shayarwa idan sunji tsoron rayukansu, toh zasu aje azumi sannan su ranka kawai, amma idan suna jin tsoron yayansu ne kawai, toh zasu ranka kuma su ciyar.

5- ABUBUWAN DAKE BATA AZUMI.

Abubuwan dake bata azumi sun kasu gida biyu:
Na farko; Abunda ke bata azumi Wanda ke wajabta rankawa kawai;

* Cin abinci ko abinsha da gangan.

* Yin amai da gan gan, saboda fadar annabi Muhammad s.a.w cewa: " Duk Wanda yayi amai, toh zai ranka azumi.[Hakim ya ruwaito]

* Mace mai haila da mai haihuwa, koda sauran mintuna kadan ayi buda baki tazo musu, toh zasu ranka azumin.

* Istimna'i(masturbation) wasa da al'aura da hannunka har maniyyi ya fito shima yana bata azumi kuma sai ka ranka.

Abu na biyu dake bata azumi kuma yake wajabta ranko da kaffara shine JIMA'I, akan maganar malamai kaffarar shine yanta baiwa ko azumin kwana sittin(60) a Jere.

6- ABUBUWAN DA BASU BATA AZUMI

* Cin abinci ko abinsha da mantuwa, ko da kuskure ko da tilasci! Babu ranko kuma babu kaffara, saboda fadar manzon Allah s.a.w cewa"Wanda ya manta yana azumi ya ci ko ya sha toh ya cika azuminsa, Allah ne ya ciyar dashi kuma ya shayar dashi.[Bukhari da Muslim]

* Amai ba dagan gan ba.

* Yin aswaki a kowane lokaci ko brush da sauransu.

* Dandana abinci da sharadin kada ka bari ya wuce maka.

* Sumbantar matarka, da sharadin kada akai ga aikata jima'i. Saboda manzon Allah s.a.w ya kasance yana sumbantar Aisha alhali yana azumi[Bukhari da Muslim].

* Cirewar hakori, ko zubar jini daga baki ko hanci.

* idan Alfijir ya keto alhali abunsha na hannunka, kada ka aje har sai ka biya bukatarka.

*jinkirta wankan janaba ko haila ko na haihuwa daga dare zuwa hudowar alfijir. Abunda yafi shine ayi gaugawar yi kafin sallar asuba.

Muna rokon Allah ya amfanar damu da abunda muka rubuta, Allah yasa munyi domin Neman yardar shi, Allah ya sanya ibadojin da zamu gabatar a ramadana su zamo karbabbu, kuma su zamo sanadiyyar tsira garemu duniya da lahira. Inda mukayi kuskure Allah ya shefeshi daga idanun masu karatu ya fahimtar dasu tare damu gabaki daya. Allah ya doramu akan tafarki madaidaici.

WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.

COPYRIGHT©
Hashim Surajo Uba(ABU SINÃN)```

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abbansinaan.blogspot.com

http://abbansinan.wordpress.com

http://shababusunnahtsafe.blogspot.com

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

atstsamawy@gmail.com

+2348064734911
+2348064734911

No comments: