Monday, 22 May 2017

DABI'UN MAGABATA A CIKIN WATAN RAMADHANA

🍌🍌🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍌🍌
*DABI'UN MAGABATA A CIKIN WATAN RAMADANA*
🍇🍇🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍇🍇

_Rubutawa;_ *Hashim Ibn Surajo Ibn Uba(ABU SINÃN)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

```Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda yayi umurni da azumtar watan ramadana, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w, Wanda ya koya mana yanda zamu gabatar da azumin.

Bayan haka;

Magabata suna da wasu dabi'u da ayuka da zantuka a cikin ramadana, watan ramadana shine watan da Allah s.w.t ke cewa; "watan ramadana Wanda q cikinshi ne aka saukar da Qurani, domin shiriya ga mutane, da kuma bayanai game da shiriyar....[bakara 185]

Magabata na kwarai suna da ayukan da suke aikatawa a ramadana  fiye da sauran watanni.  Daga cikin magabatan akwai;
*IMAMU MALIK IBN ANAS(imamu darul hijra) ya kasance baya dakatar da karatuka a masallacin Annabi Muhammad s.a.w sai a ramadana, domin yana shagaltuwa da karatun Qurani ne kawai.

*SUFYANUS-THAURY R.H; ya kasance idan Ramadana ya shigo, yana barin dukkan wasu ibadodi, yana shagaltuwa da tilawar Qur'ani.

* MUHAMMAD IBN ISMA'IL AL-BUKHARI(mai sahihul-bukhari): ya kasance a cikin duk yini daya yana sauke Qur'ani, yana tsayuwar tarawihi acikin kwana uku na tqrawihin yana sauke Quran.

*SA'ID IBN JUBAIR: ya kasance yana saukar Qur'an a duk kwana biyu.

* ABU AWANAH yace; naga IMAMU QATADA yana karantar da Qur'an a watan ramadana.

*IMAMU QATADA; ya kasance yana saukar Qur'ani a duk bayan kwana bakwai, idan ramadana ya shigo yana sauka duk kwana uku, idan kwanaki goma na karshe suka shigo yana saukewa a kowane dare.

*RABEEY IBN SULAIMAN(Dalibin imamush-shafi'i) R.H yana cewa; imamush-shafi'i ya kasance yana saukar Qur'ani a ramadana sau sittin (60)[kowace rana sau biyu] a kowane wata yana sauka sau talatin(30) bayan ramadana.

    Kiyamul-laili aikin Annabi Muhammad s.a.w da sahabbansa ne, Aisha R.A take cewa; "kada kubar tsayuwar dare, domin Manzon Allah s.a.w bai taba barinta ba, idan baya lafiya yana yi a zaune.

* Umar Ibn khaddab R.A ya kasance yana sallar dare dai dai gwargwado, idan dare ya raba, said ya tayar da iyalansa domin yin sallar, yana cewa SALLAH! SALLAH!! SALLAH!!! Sannan sai ya karanto aya ta 132 dake cikin suratu Daha, inda Allah madaukakin sarki yake cewa; "Ka umurci iyalanka da yin SALLAH ka kwadaitar dasu akanta, bamu tambayarka wani arziki mine masu azurtaka....

  Wannan shine dabi'un magabata na kwarai a watan ramadana, to mu ya halinmu yake a wannan wata mai albarka???

* Abdullahi Ibn umar(Allah ya kara masu yarda) ya kasance yana yin azumi ba ya buda baki(shan ruwa) sai tare da talakawa, ya kasance idan yana cin abinci sai wani mabukaci yazo ya tambaya sai ya tashi daga abincin ya mika masa, ya wuce da azumi ba tare da yayi sahur ba.

  Wadannan sune magabata na kwarai, kuzo Mani da irinsu a wannan zamanin yã Ku masu da'awar salafiyya da Sunnah!?

*YUNUS IBN YAZEED yake cewa; IBN SHIHAB AZ-ZUHURY ya kasance idan ramadana ya shigo yana cewa; "Wannan watan Qur'ani ne, da kuma ciyar da abinci".

* HAMMAD IBN ABI SULAIMAN ya kasance yana ciyar da mutum dari biyar(500) a watan ramadana. Ya kasance kuma yana ba kowane dayansu dirhami Dari(100).

  Yã yan uwa na masu daraja ya kamata mu kwatanta rabin abunda magabatanmu na kwarai suka aikata na ayukan alkhairi, kada mu shagaltu da abunda bazai amfanemu ba, daga baya mu koma da na sani! Allah madaukakin sarki yana cewa;"ومن أعرض عن ذكري فإن له معيشة ضنكا ونحشره يوم القيامة أعمى، قال رب لم حشرتني أعمى وقد كنت بصيرا، قال كذلك أتتك آياتنا فنسيتها وكذلك اليوم تنسى، وكذلك نجزي من أسرف ولم يؤمن بآيات ربه، ولعذاب الآخرة أشد وأبقى.

Allah yq karemu.

WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.



COPYRIGHT©
Hashim Ibn Surajo Ibn Uba(ABU SINÃN)```

atstsamawy@gmail.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

http://abbansinaan.blogspot.com

http://abbansinan.WordPress.com

http://shababusunnahtsafe.mywapblog.com

http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com

+2348064734911
+2349030201868

No comments: