Tuesday, 7 May 2019

03 BARKA DA SHAN RUWA

🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*BARKA DA SHAN RUWA*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉

_003_

8⃣ *KO YANA HALASTA IN DOGARA GA KIRAN SALLAH DA AKE YADAWA A GIDAJEN RADIO A WURIN YIN BUDA BAKI KO SHIGAR ALFIJIR?*

_AMSA_

Yana halasta, musamman idan an tabbatar kafafen masu inganci ne a wurin ayyukansu, ko kuma  musulmi ke jagorantarsu, wannan itace fatawar *SHEIKH MUHAMMAD BN UTHAIMIN RAHIMAHULLAH*

9⃣ *MINENE HUKUNCIN SAHUR GA WANDA YAYI NUFIN YIN AZUMI?*

_AMSA_

Yin sahur mustahabbi ne kamar yadda *sheikh muhammad bn salih al-uthaimin RAHIMAHULLAH* ya tabbatar da hakan, kamar yadda yake sunnah ne yin sahur din a daya bisa ukun karshen dare, saboda fadar *ZAID BN THABIT (RA)* _"MUNYI SAHUR TARE DA MANZON ALLAH S.A.W, SAI MUKA TASHI DOMIN MUYI SALLAH, SAI AKA TAMBAYI ZAID, NA WANE TAZARA TSAKANIN KIRAN SALLAH DA SAHUR? SAI YACE: KAMAR KWATANKWACIN KA KARANTA AYA HAMSIN(50)."_ [Bukhari da muslim]

Da kuma fadar manzon Allah s.a.w cewa: _"AL'UMMATA BA ZASU GUSHE SUNA SAMUN ALKHAIRI BA MATUKAR SUNA GAGGAUTA BUDA BAKI, SUNA JINKIRTA SAHUR"_ [Imamu Ahmad ya ruwaito]

🔟 *DAME AKE SON MAI AZUMI YAYI BUDA BAKI?*

_AMSA_

Anason fara buda baki da *DABINO,* idan bai samu ba sai ya fara da *RUWA* Dalili akan haka shine hadisin da yazo daga salman bn Aamir (RA) yace, Manzon Allah s.a.w yace: _"idan dayanku ya kasance yana azumi yayi buda baki da *DABINO,* Idan bai samu ba sai yayi da *RUWA,* Saboda su ruwa tsarkakakku ne"._ [Maruwaita biyar suka ruwaito shi ] thirmidhi yace hadisi ne HASAN SAHIH



*ALLAHUMMA TAQABBAL SIYAMANA* 👏👏👏👏

#ABU_SINAN
+2348064734911

Monday, 6 May 2019

02 BARKA DA SHAN RUWA

🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*BARKA DA SHAN RUWA*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉

_002_

4⃣  *MINENE HUKUNCIN AZUMIN RAMADAN?*

_AMSA_

Azumin ramadan farilla ne, Allah s.w.t ya farlantashi ga bayinshi, Qur'ani da  sunnah da ijma'i duk sun tabbatar da hakan, Qur'ani shine fadar Allah s.w.t : *_"YAA KU WADANDA SUKAYI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI, KAMAR YADDA AKA WAJABTAMA WADANDA SUKA GABACEKU, DOMIN KU SAMU TSORON ALLAH"_*
A sunnah kuma shine, bukhari ya ruwaito hadisi da muslim a cikin sahihan littafansu, daga Abdullahi dan umar r.a, Manzon Allah s.a.w yace: *_"AN GINA MUSULUNCI AKAN GINSHIKAI BIYAR, KALMAR SHAHADA, TSAYAR DA SALLAH, BADA ZAKKAH, AIKIN HAJJI, AZUMIN RAMADAN"_*
duk wanda yayi inkarin farlancinshi yayi ridda

5⃣ *MINENE SHARADIN YIN AZUMI?*

_AMSA_

Azumi na wajabta ga dukkanin musulmi, baligi, mai hankali, mai lafiyar da zai iya yin azumin

6⃣ *YAUSHE ZAN KUDURCE NIYYAR YIN AZUMIN RAMADAN?*

_AMSA_

wajibi ne ka kudurce niyyar yin azumin ramadana kafin fitowar alfijr, idan bakayi niyyar yin azumi ba sai bayan alfjr ya fito, azuminka baiyi ba, amma a azumin nafila ya inganta zaka iya yin niyya da rana tsaka, saboda hadisin aisha r.a dake nuni akan hakan.

7⃣ *ZAN IYA YIN NIYYA GUDA DAYA A RAMADANA BAKI DAYA?*

_AMSA_

Abunda yake dai dai shine niyya a farkon watan ta wadar har zuwa karshe, babu bukatuwar chanja niyya a kowane dare, kuma ita niyya ba'a furuci da ita, muhallinta shine zuciya.

#ABU_SINAN
+2348064734911

01BARKA DA SHAN RUWA

🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*_BARKA DA SHAN RUWA_*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉

_001_

1⃣ *MI KE TABBATAR DA SHIGAR WATAN RAMADAN???*

*_AMSA_*

Yana tabbatuwa da abubuwa guda biyu;

*_Na farko:_* cikar watan sha'aban kwana talatin

*_Na biyu:_* Ganin jinjirin watan Ramadan

2⃣ *MENENE HUKUNCIN WANDA YAGA JINJIRIN WATAN RAMADAN SHI KADAI 👌 AMMA BA'A KARBI SHAIDARSHI BA???*

*_AMSA_*

Ba zaiyi azumi ba sai tare da mutane, saboda hadisin da yazo a jaami'ut-thirmidhi da waninsa, Manzon Allah s.a.w yace: "azuminku ranar da kuke azumi(ranar da kowa ya fara)"

3⃣ *MUTUM NAWA NE ZA'A IYA KARBAR SHAIDARSU TA GANIN JINJIRIN WATAN RAMADAN???*

*_AMSA:_*

Za'a Karbi shaidar mutum daya zuwa sama, saboda hadisin da imamu Abu daud da waninsa suka ruwaito, Abdullahi Dan Umar (RA) yace; "Mutane sunga wata, sai naje na fadawa Manzon Allah s.a.w cewa ni naga wata, sai Annabi s.a.w yayi azumi, kuma ya umurci mutane da suyi azumi, imamut tirmidhi yace: ma'abota ilimi suna aiki da wannan karantarwa.

*FADAKARWA*

_Amma a wurin fitar watan Ramadan sai da shaidar mutane biyu ake ajiye azumi, kuma malamai basuyi sabani akan wannan ba._

#ABU_SINAN
+2348064734911