HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.
DARASI NA HUDU (004)
📒ABU NA HUDU: ABUBUWA UKU DA YA KAMATA A NISANTA A LOKACIN MUTUWA📒
Ya kamata a nisanci al'amurra uku da matane ke yawan yi lokacin da aka yi mutuwa.
📌1. Tururuwar mutane wurin shiga gidan da akayi mutuwa, bai dace ba mutane su dinga shiga gidajen da aka yi mutuwa alhali basu da hurumin shiga gidan da sunan yiwa mata ta'aziyya.
📌2. Taruwa a wani kebantaccen wuri domin karbar gaisuwa (ta'aziyya), kamar Masallaci ko gida ko Makabarta. Musamman yanzu wuraren karbar gaisuwa ya dauki wani sabon salo, wani lokaci kaga kamar buki ake yi an kawo rumfuna da kujeri sai abinci ake kawowa kala-kala, wani lokaci kuma ya zama wurin sharholiya da shaci fadi da giba da aibanta shugabanni da Yan siyasa da masu kudi harma da malaman addini. Kai abin bai tsaya nan ba wasu sun mayar da wurin karbar gaisuwa wani dandalin siyasa da rabawa matasa zauna gari banza kudade.
📌3. Abinci da iyalan mamaci ke tanada domin tarbon masu zuwa ta'aziyya, dalili akan haka shine: Hadithin Abdullahi Albajaliy yace: mu (Sahabbai) "MUN DAUKI TARUWA DON KARBAR GAISUWA (ta'aziyya) DA TANADIN ABINCI DON MASU TA'AZIYYA A MATSAYIN NIYAHAH (wato kururuwa ko kukan mutuwa). [Ahmad da bin Majah suka ruwaito sa, Imam An-Nawawiy ya inganta shi]
🖋️Haka kuma Imam An-Nawawiy a cikin littafin sa AL-MAJMU' sharhin MUHAZZAB na Shayhin Malami Shayraziy cewa yayi: " AMMA ZAMA DOMIN TA'AZIYYA IMAM AS-SAFI'IY DA SHAYRAZIY SUN NASSANTA KARHANCIN SA(kyamar sa)" abinda yake nufi sun karhanta taruwar iyalan mamaci a gida domin mai son yayi masu ta'aziyya ya same su yayi masu ta'aziyya, dai dai abin da ya kamata su tafi wajen bukatun su (na yau da kullum), duk wanda ya ya hadu dasu yayi masu ta'aziyya. Kuma babu bambanci wajen karhanta wannan zama tsakanin maza da mata.
🖋️Abinda Imam An-Nawawiy ya fada yana cikin littafin Imam As-shafi'iy: AL-UMM 1/248, ga kuma abinda yake cewa a cikin littafin: "INA KYAMAR TARON KARBAR TA'AZIYYA KODA BABU KUKA DOMIN YANA SABANTA BAKIN CIKI DA KALLAFA WAHALHALU NA KASHIN DUKIYA".
🖋️Shi kuma bin Humam ya nassanta karhancin a cikin littafin sa SHARHUL HIDAYAH 1/473, kuma yace: BIDI'AH CE MAI MUNI" kuma wannan shine mazhabar Hanabila kamar yadda yake cikin AL-INSWAF 2/565.
Kuma abinda kowa ya sani ne kamar yadda bayani ya gabata wurin karbar gaisuwa ya zama wurin fira, giba, kallon mata, labarin Yan siyasa, Yan kwallo, shugabanni, masu kudi da dai sauran su. Wanda hankali lafiyayye ba zai yarda da wannan ba balantana Shari'ah.
Wallahu a'alamu bissawab
Mu hadu a darasi na biyar (005)insha'allah
✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz Juma'at Mosque Bungudu)
No comments:
Post a Comment