ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. MU KOYI IBADA A SAUKAKE
Saturday, 2 December 2017
MAGANAR IMAM AHMAD BN HAMBAL AKAN DAIDAITUWAR ALLAH A SAMA
Monday, 27 November 2017
HALASCIN SALLAH DA TAKALMI A MUSULUNCI
```HALASCIN SALLAH DA TAKALMI
Hadisi ya tabbata cewa An tamabayi Anas bn
Malik "shin ko Manzon Allah s.a.w ya kasance
yana SALLAH da Takalminshi???" Sai ya amsa
musu da cewa Ehhh.
Sahihul bukhari [1/494]
A wani Hadisin Annabi Muhammad s.a.w cewa
yayi" Ku saba ma yahudawa, domin su basu
SALLAH da Takalminsu ko huffinsu.
[Abu daud da ibn hibban suka fitar, imamush-
shaukany yace; babu wani abu na suka a cikin
wannan hadisin, domin sabawa yahudawa abune
Wanda shari'ah tayi umurni da hakan a wurare da
dama.]
Amma fa ba wai munce wajibi bane!!!, A'a
Sunnah ce ta Annabi Muhammad s.a.w kuma
Malamai sunce mustahabbi ne yin SALLAH da
takalmi.
Kada wani yace ABU SINAAN yace wajibi ne!!!
Amma ya kamata ka Dan raya wannan sunnar
koda sau daya ne, amma fa kada kaje masallacin
anguwarku Wanda basu san da wannan sunnar
ba kace zakayi musu SALLAH da takalmi!!! Idan
sukayo waje da kai toh laifinka ne kuma kai ka
janyo!!!
Allah ya tabbatar damu akan Sunnah.
ABU SINAN
Hashim Siraj Uba Tsamiya```
KISHIN MATA
.
*MACE BA'A TABA YI MATA KISHIYA*
*TA KIRKI*
1● In ka auro *USTAZIYA,* tace:
Munafukan gari, Allah a baki,
sharri a zuci, in ko ka auro 'yar
gayu tace ta fitsare kafa, ba tada
kamun kai.
2● In ka auro *MAI KYAU* tace
kyalkyal banza, ka auro mara
kyau tace an cuce ka.
3● In ka auro *FARA* tace Sadaka
Yalla ko Hasken Ambi, in baka ce
tace Bayan Tukunya.
4● Ka auro daga *DANGINTA* tace
kana son bata zumunta, in kaje
wani gun tace Tsintattar Mage.
5● Ka auro *yar makota,* tace
wadda ta gama sanin sirrimmu?,
in kaje nesa tace baa san asalinta
ba.
6● In ka auro *Babba,* tace an
kwaso kwashi kwaraf, in ko
karama tace girma ya fadi.
7● In ka auro *KAWARTA* tace duk
matan duniya?, don cin fuska da
cin amana?, in ko ka auri 'yar
aikin gidan, tace Tir !, wai iyakar
wulakanci ke nan, kuma baka da
taste.
8● Ka auro *YAR MANYA* tace: Kuda
wajen kwadayi akan mutu, in
'yar talakawa ka auro tace: Allazi
Wahidin, Allah baku mu samu.
9● In ka auri *YAR AMININ KA* tace:
Tsohon Banza, yau Baba ya koma
Bobo, in ko abokiyar aikinka a
ofis ka auro, sai tace: Abin boye
ya fito fili.
10● In ka auro mai *ABIN HANNUNTA*, ( wato Business woman) tace: Kano Jiddah
ko 'yar Dubai, in ko ba mai sana'a
bace, tace an kwaso cima zaune.
11● In ka auro *YAR MALAMAI* tace
asirce ka aka yi ba yinka bane, in
ko 'yar bata da karatu, sai tace
gidansu ko sallah baa iya ba.
12● In ka auro daga *DANGINKA*
tace ana son a hade kai a ware
ta, in kuwa bazawara ka auro, sai
tace: In kaga godiya da sirdi, to
wani ta kayar kuma wani mai
gigi zata sake kayarwa..........
_
Yaushe kenan zaa auro kishiya ta
kirki?
_
WAI ME YA SA mata basa SON
KISHIYA NE?
Monday, 2 October 2017
FACEBOOK SECURITY
YAYA ZAN KARE FACEBOOK ACCOUNT DINA
DAGA BLOCKIN KO HACKERS??
Daga Dan uwa: Basheer Journalist Sharfadi Kano.
Assalamu Alaikum warahmatullah,
Kamar yadda muka tattauna jiya kan wadannan
matsalolin da suke faruwa na yunkurin yin awon
gaba da rayukan facebook, to cikin ikon Allah
yau zamu tattauna ne akan wancan take da na
bayar a sama, inda zan kawokadan daga
abubuwan da ya kamata mu sani kuma mu
kiyaye game da account din mu, sai a biyo mu,
1. Yana da kyau ka dinga canja password din ka
akalla bayan sati daya (1) zuwa sati biyu,
sannan wajen canjawar a guji sanya 123456 ko
sunan ka, ko kuma lambar wayarka, sunan
budurwar ka, ko unguwar ka, a’a yana da kyau ka
sanya harufa da kuma lambobi, kai harma da
symbols kamar @”-+, sannan kada ka yarda ka
sanar da wani wannan password din naka,
Sannan a kula kada kayi amfani da password
guda daya a dukkan abubuwanka misali a Email
dinka da kuma facebook din ka da sauran abinda
kake budewa duk su zama iri daya domin hakan
zai baiwa wasu damar yin awon gaba da account
dinka,
2. sanya Karin email akan account dinka a kalla
ina bada shawarar kayi adding email kamar guda
uku (3) akan account dinka kaga kana da
cikakken iko akan account dinka duk wani motsi
ko wani yunkuri da akayi kai tsaye zaka gani,
Sannan a setting na email din ka mayar dashi
babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai “only
me” a yaren facebook,
3. Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki
kana samun sakonni acikin ta da yawan mu
lambobin da muka bude facebook dasu mun rasa
layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar
daga kan fb din mu canza ta da lambar da muke
da ita a yanzu, rashin yin hakan zai bamu
matsala don haka idan kasan ka rasa layin ka to
ka canza lambar layin ka na yanzu domin ka
cigaba da samun sakonnin facebook,
4. Ka sanya “Login Approval” a account din ka
yadda zaka sanya shine ka bi wannan hanyar
kaje :Home -> Account Settings -> Security ->
Login Notification sai ka mai da shi “Enable”
Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na
account din ka sannan idan zakayi login dole sai
an turo maka da code ko kuma kayi approving ta
wayarka idan android ce, sannan anan bangaren
zaka iya samar da “code generator” ta yadda
zaka samar da wani code wanda kai ka dai ne ka
sanshi idan kazo yin login bayan password to shi
ma zaka saka shi,
5. Sannan zaka iya zabar wasu amintattu daga
friend dinka kamar Grantor kenan ka sanya su,
suma zasu iya baiwa account din ka kariya,
6. Ka samar da tsayayyiyar browser da kake
hawa facebook, kada ka zama yau ka ari wayar
wancan ka hau gobe ka ari ta wancan, sannan a
daina yin saving din password a browser saboda
zaka iya yadda wayar ka, ko kuma a dauke maka
ita, mu samman a wannan lokacin da ake yawan
kwace kaga wani zai iya hawa, sannan facebook
zasu iya yi maka blocking saboda yawan yin
hakan,
7. Ka dinga yin log out duk sanda ka hau idan
zaka sauka,
8. Kada ka baiwa wani ko wata bayanan ka na
yin login a account din ka ko wani web site,
9. Kayi tunani kafin ka danna link, zaka ga ance
ka danna link, to ka fara yin tunani kafin ka
shiga, misali ace ka danna kaga abinda zai faru
ko makamantan hakan, ko idan ka shiga sai kaga
ance ka saka password dinka to duk irin wannan
sai a kiyaye,
10. Kayi login a www.facebook.com ka wai
www.fb.com kada kayi login a facebook ta kan
wani site daban ba wannan ba, ko application
wanda ba ingantacce ba,
11. Ka dinga yin updating din browser din ka ko
application din ka,
12. ka dina installing anti virus a wayar ka ko a
computer da kake amfani da ita,
13. ka daina yawan tura Requesting ko yawan
yin accepting ka kula wajen karbar wanda baka
san shi ba, yana da kyau ka duba propile din sa
kafin kayi accepting din sa,
14. Ka daina yawan yin sharing na wani link da
baka tantance shi ba,
15. ka daina hade facebook account dinka da ko
wane shafukan internet, zaka ga da yawa daga
website ana yin register din su ta facebook mai
makon kayi da email sai kayi da facebook shima
wannan ya kamata ayi tunani sosai kafin
aiwatarwa,
16. Kada ka yi wani psoting wanda ya sabawa
wadansu to idan suka yi ta yin reporting din sag
a facebook su ma zasu yi blockin din account din
ka,
Bara na dakata anan naga rubutun zaiyi tsayi da
yawa,
Naku: Basheer Journalist Sharfadi
Domin bada shawara ko Karin haske za’a iya
tuntuba ta a:
www.facebook.com/journalistsharfadi
Phone: 09035830253
Email: bjournalist55
# BasheerSharfadi #Facebook # SocialMedia
Saturday, 15 July 2017
MEYASA BA'A AMSA ADDU'OINMU???
*MEYASA MUKE ADDU'AH, AMMA SAI MUGA KAMAR BA'A KARBA MANA???*
```An tambayi Ibrahim bn Adham(RH) akan cewa meya samemu ne, muna Addu'ah amma ba'a karba mana??
Sai yace: Zukatanku sun mutu da Abubuwa takwas(8).
NA FARKO; Munsan Allah, amma ba muyi mashi biyayya(ma'ana; munsan hakkin Allah, amma bamu gabatar mashi da hakkinshi).
NA BIYU; Muna karanta Alkur'ani, amma bamu aiki dashi(ma'ana: Bamu aiki da iyakokin da Allah ya gindaya a cikin Qur'anin).
NA UKU: Munce munason Manzon Allah (Salallahu alaihi wasallam), amma sai muka yi mashi tawaye, muka kiyin amfani da sunnar shi.
NA HUDU: Munsan cewa Shaidan makiyinmu ne, amma sai muka sakar mashi akala muna binshi.(Muna yi mashi biyayya wajen sabon Allah).
NA BIYAR: Munsan cewa Aljanna gaskiya ce, amma bamu aiki domin mu shigeta.
NA SHIDA: Munsan cewa wuta gaskiya ce, amma bamu guje mata.
NA BAKWAI: Mun wayi gari mun shagaltu da aiboban(harkokin) mutane, mu kuma mun bar namu aiboban(harkokin).
NA TAKWAS: Kun binne mataccinku, amma Baku lura da kuma wataran za'a binneku.
NA TARA: Mun ce, muna tsoron mutuwa, amma ba muyi mata tanadi ba.
NA GOMA: Muna cinye ni'imomin Allah, Amma bamu gode mashi(muna cinye abincin Allah, abin shan Allah, da sauran ni'imomi amma mun kasa gode mashi).
Wadannan da wasunsu sune dalillan dake sa muke rokon Allah sai Allah ya kyalemu da dabararmu.
Yaa Allah ka bamu ikon gode maka.
Yaa Allah ka karo mana ni'imominka ta hanyar da muka sani da wacce bamu sani ba.```
HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
+2348064734911
+2349030201868
SHAFUKAN SADA ZUMUNTA DOMIN BIBIYARMU.
atstsamawy@gmail.com
hashimusurajo5@gmail.com
I G @ abbansinan
http://hashimtsamiya.blogspot.com/
http://abbansinaan.blogspot.com/
http://shababusunnahtsafe.blogspot.com/
http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com/
https://mobile.facebook/hashimusurajo.tsamiya/
Saturday, 1 July 2017
MUHADARA MAI TAKEN; AMFANI DA KUMA ILLOLIN SOCIAL MEDIA
*MUHADARA MAI TAKEN; AMFANI DA KUMA ILLOLIN SOCIAL MEDIA*
Muhadara mai taken amfani da kuma illolin social media a cikin al'umma wacce kwamitin matasa na *SHABABU AHLISSUNNAH WALJAMA'AH SUKA SHIRYA DOMIN GORON SALLAH,* muhadarar wacce *USTAZ MUSA S LAWAL(Abu salih Ibn salih)* ya gabatar a masallacin *UTHMAN BIN AFFAN TSAFE,*
Wallahi akwai abubuwan da ya kamata mu amfana dasu kwarai da gaske a cikin wannan muhadara.
Kai dai kawai shiga link dake kasa domin saukewa a wayanka.
👇👇👇👇👇👇👇👇
*Amfani da illolin social media by Ustaz musa s lawal Tsafe*
http://darulfikr.com/s/24715
Allah ya sakawa Malam da Alkhairi akan wannan lecture da yayi mana.
darulfikr.com takuce domin yada Sunnah a koda yaushe.
Copyright©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya
+2348064734911
+2349030201868
Monday, 26 June 2017
2017 RAMADAN TAFSEER
*2017 COMPLETE RAMADAN TAFSEER*
COMPLETE 2017 RAMADAN TAFSEER DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA ABU HURAIRA AREA II TSAFE.
wanda Malam Sani Liman Tsafe (ABI HURAIRA) yake gabatarwa a Area II Tsafe, jahar Zamfara Nigeria.
Shiga links dake kasa Domin saukewa Cikin sauki ka saurara Cikin kyakykyawan Sauti.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
01 Ramadan Tafseer 1438Ah Suratul Nisa i By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24378
02 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24379
03 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24380
04 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24381
05 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Sani LimanTsafe
http://darulfikr.com/s/24382
08 Ramadan Tafseer Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24383
09 Ramadan Tafseer Akan Hukunce Hukunce Mata Na Dare By Mal San Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24384
10 Ramadan Tafseer Na Dare By Abu-Hurairah Tsafe
http://darulfikr.com/s/24385
11 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24386
12 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24387
14 Ramadan Tafseer 1438 Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24388
15 Ramadan Tafseer Na Dare Suratul Ma ida By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24389
16 Ramadan Tafseer 1438 Na Dare By Mal SaniLiman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24390
17 Ramadan Tafseer Na Dare 1438 By Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/24391
19 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24392
20 Ramadan Tafseer 1438 Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24393
21 Ramadan Tafseer 1438Ah Na Dare By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/24394
Kasance do darulfikr.com a koda yaushe domin samun karatuttukan maluman sunnah.
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*
http://masjiduabihurairatsafe.blogspot.com