Saturday, 7 December 2019

004 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 004_

🔸 *ADDU'AH A LOKACIN DA KA FARKA DAGA BARCI A TSAKAR DARE*

Hadisi yazo daga Ubbadah bn Samit (R.A), Manzon Allah S.A.W yace: "Duk Wanda ya farka a tsakar dare, ya fadi: *_((LAA ILAHA ILALLAHU, WAHDAHU LAA SHARIKALAHU, LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU, WAHUWA ALAA KULLI SHAI'IN QADEER. ALHAMDULILLAHI, WASUBUHANALLAHI, WALLAHU AKBAR, WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI, bayan wannan sai kace: RABBIG FIRLEE, ko kayi addu'ah a lokacin Allah zai karba maka, idan kuma kayi alwala kayi sallah(Nafila) an karba maka sallarka))._*
[Bukhari 1154]

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

003 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 003_

🔸 *KABBARA DA TASBIHI A LOKACIN KWANCIYA BARCI*

Daga Aliyu bn Abi Dalib(R.A), Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da Fadima(R.A.H) ta nemi a bata wacce zata rika yi mata hidima sai Manzon Allah (S.A.W) yace: "Shin bazan nuna maku wani alkhairin da yafi wannan ba(Mai hidima)? Idan ku kayi nufin kwanciya ko idan kun kwanta, kuyi *KABBARA Sau 34, SUBHANALLAHI sau 33, ALHAMDULILLAHI sau 33.* Wannan shi yafi alkhairi gareku sama da Mai yi maku hidima."

SAI MUN HADU A FITOWA NA GABA INSHA ALLAHU

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

002 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 002_

🔸 *KARANTA SURATUL IKHLAAS DA FALAQI DA NASI KAFIN KWANCIYA BARCI*

Daga Aisha (R.A) tace: Manzon Allah (S A.W) ya kasance idan yazo ma kwancinsa a kowane dare yana hada hannuwanshi, sannan ya karanta a cikin hannayen *SURATUL IKHLAAS da FALAQI da NASI,* sannan sai ya shafe jikinsa gwargwadon iko, yana fara daga kan shi da fuska, da abin da ya rage na sauran jiki, yana aikata haka sau uku. *[Bukhari 5017]*

SAI MUN HADU A FITOWA NA GABA INSHA ALLAHU

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

001 KARATUN HADISI...

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHIKE KAWO ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DAGA ZAUREN: *MU KYAUTATA NIYYA*

_Fitowa Na farko 001_

🔸 *KWANCIYA BARCI DA ALWALA*

Manzon Allah (S.A.W) yace ma Barra' bn Aazib(R.A): "Idan kayi nufin zuwa ma kwancinka, kayi alwala irin alwala da kake idan za kayi sallah, sannan ka kwanta da bangaren jikin ka na dama... *[Bukhari 6311, Muslim 6882]*

*Fa'ida:* Idan ka kwana da alwala mala'iku zasu Rika nema maka gafara a wurin Allah har zuwa safiya

DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A TUNTUBI WADANNAN NUMBERS:
+2348064734911
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

Tuesday, 3 December 2019

001 LADUBBAN MUSULMI A LOKACIN SANYI

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

*LADUBBAN MUSULMI A LOKACIN SANYI*

_001_

*ﺑﺴﻢ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ*

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Wanda yake jujjuya yanayi yanda yaso, Wanda cikin hakan akwai ayoyi da izina, yabo da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Lokacin sanyi lokaci ne mai falala da mumini ke iya ribatarsa wajen neman yardar Allah, hakika magabata sun kasance suna bushara da murna da zuwansa

ﻗﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ:

) ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻏﻨﻴﻤﺔ ﺍﻟﻌﺎﺑﺪﻳﻦ )
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : )ﻣﺮﺣﺒﺎً ﺑﺎﻟﺸﺘﺎﺀ ﺗﺘﻨﺰﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺒﺮﻛﺔ ﻭﻳﻄﻮﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻟﻠﻘﻴﺎﻡ ، ﻭﻳﻘﺼﺮ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻟﻠﺼﻴﺎﻡ).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺒﺼﺮﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ) ﻧﻌﻢ ﺯﻣﺎﻥ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻟﻴﻠﻪ ﻃﻮﻳﻞ ﻳﻘﻮﻣﻪ ، ﻭﻧﻬﺎﺭﻩ ﻗﺼﻴﺮ ﻳﺼﻮﻣﻪ ).

Akwai ladduba da *HUKUNCE-HUKUNCE* daya kamata mu kiyaye daga cikinsu akwai:

1: *RIBATARSA DA IBADU MUSAMMAN AZUMI,*

yazo a hadisi Wanda malamai sukayi sabani kan ingancinsa, sai dai ya tabbata daga Abu huraira, '' ﺍﻟﻐﻨﻴﻤﺔ ﺍﻟﺒﺎﺭﺩﺓ ﺍﻟﺼﻮﻡ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ''
*Ganima mai sauki azumi lokacin sanyi*.

babu shaka yin azumi a lokacin sanyi garabasa ne saboda abubuwa kamar haka:

A: Gajartar yini da raguwarsa.

B: Rashin zafin rana.

C: Saukin qishirwa.

2: *KIYAYE SHAN RUWA:*
Wannan abin nema ne a likitance, Saboda yin sakaci da shan ruwa yana janyo Rashin lafiya, Bincike na lafiya, ya nuna cewa sakaci da shan ruwa a lokacin sanyi yana janyo mutuwa lokaci daya, saboda idan mutum yabar shan ruwa zuciyarsa zata tsaya daga aiki.

Don haka masu Kula da lafiya suna bada shawarar shan ruwa kafin bacci da bayan tashi daga bacci, da lokacin cin abinci.

3: *AMFANI DA RUWAN ZAFI WAJEN WANKA DA TSAFTACE JIKI*
  Domin ba jarumta bane yin Amfani da ruwa me tsananin sanyi lokacin sanyi domin yana iya janyo ma mutum Rashin lafiya, Addini yazo da kare lafiya da rayuwar mutum.

Allah yace:

[ ﻭﻻ ﺗﻠﻘﻮﺍ ﺑﺄﻳﺪﻳﻜﻢ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺘﻬﻠﻜﺔ]☆
Kuma yace
[ ﻭﻻ ﺗﻘﺘﻠﻮﺍ ﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺎﻥ ﺑﻜﻢ ﺭﺣﻴﻤﺎ]☆

Yazo a hadisi cewa wasu sahabbai sunyi fatawa ga wani dan-uwansu da janaba ta sameshi, lokacin sanyi.
Kuma suna matafiya, kuma bashida lafiya.
Dayayi wanka da ruwan sanyi sai ya mutu, da suka dawo suka fadawa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sai yace:

*[ﻗﺘﻠﻮﻩ ﻗﺘﻠﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻻ ﺳﺄﻟﻮﺍ ﺣﻴﻦ ﺟﻬﻠﻮﺍ ﻓﺎﻧﻤﺎ ﺷﻔﺎﺀ ﺍﻟﻌﻲ ﺍﻟﺴﺆﺍﻝ ]*

4: *KYAUTATA ALWALA DA CIKATA, KOMAI TSANANIN SANYI,*
Saboda hadisin da Muslim ya rawaito:
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ'' ﺃﻻ ﺃﺩﻟﻜﻢ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻳﻤﺤﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻭﻳﺮﻓﻊ ﺑﻪ ﺍﻟﺪﺭﺟﺎﺕ: ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﺑﻠﻰ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺎﻝ: ﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ، ﻭﻛﺜﺮﺓ ﺍﻟﺨﻄﺎ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ ﻭﺍﻧﺘﻈﺎﺭ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺼﻼﺓ، ﻓﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ ﻓﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ '' ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:  *" Shin bazan fada muku abinda Allah yake shafe kurakurai dashi ba, kuma yake daga darajoji dashi.*
*Suke eh ya Manzon Allah.*
*Sai yace:*
*CIKA ALWALA TARE DA SAMUN ABABEN DA ZASU SA KIN HAKAN.........................*

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﻣﺴﻠﻢ:

ﻭﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﺇﺗﻤﺎﻣﻪ ، ﻭﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ ﺗﻜﻮﻥ ﺑﺸﺪﺓ ﺍﻟﺒﺮﺩ ﻭﺃﻟﻢ ﺍﻟﺠﺴﻢ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ. ﺍﻧﺘﻬﻰ .

5: *KIYAYE SALLAR ASUBA CIKIN JAM'I*
  Hadisai dayawa sunzo suna tsoratarwa kan Rashin halartar asuba da isha a jam'i, Har manzon allah yace sune sukafi nauyi ga munafukai, kayi kokari ya kai bawan allah ka ceci kanka daga fadawa gungun munafukai da barin sallar asuba lokacin sanyi domin bakasan sanda mutuwa zatazo maka ba, Hakanan hadisai sunzo suna bushara ga masu kiyeye sallar asuba a lokacinta cikin jam'i, malamai sukace wadannan hadisai sun kunshi kusan busharori goma ga masu kiyayeta.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU

DOMIN SHIGA GROUP DIN:
*MU KYAUTATA NIYYA*
+2349030201868

https://fb.me/abbansinan

Saturday, 23 November 2019

020 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MU KYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa na Ashirin 020_

Gabatarwa: *Farida bintu salis*

*FASALI NA BIYU*

*CIKI NA ZAMANIN HAILA DA GWARGODONSA.*

Zance acikin wannan fasalin yana da matsayi guda 2.

*MATSAYI NA FARKO:*  A cikin shekarun da haila take zuwa acikin su.

*MATSAYI NA BIYU:*  A cikin lokacin Haila.

Amma shekarun da haila tafi rinjaye acikinsu MATSAYI NA FARKO shine: tsakanin
shekara 12 Zuwa shekara 50, amma ana samu sau da yawa mace tana yin haila a kafin
haka ko bayan haka gwargodon halinta da tasowarta da kuma tsufanta. Lallai malamai
sunyi sa6ani akan shin shekarun da haila take zuwa aciki suna da iyaka da aka ayyana ta
yadda mace ba zatayi haila gabanninsu ba ko bayansu. Kuma shin jinin da yake zuwa ga
mace a gabanninsu ko bayansu jinin haila ne ko na cuta? Malamai sunyi sa6ani acikin
wannan.
Darimiy yace: Bayan ya kawo sabanin: dukkan wadannan kuskure ne awajena domai a
baki dayan wannan yana komawa ne izuwa samuwar jinin, duk jinin da ya samu a kowani
hali da shekaru, ya wajaba a sanya shi a matsayin haila. Wallahu a'alamu. (Al-majmu'u
sharhil Muhazzab 1/336)
Wannan abunda Darimiy ya fada shine daidai, kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn
Taimiyyah. Wato duk sanda mace taga haila to ita mai haila ce koda bata cika shekara 9
ba ko kuma ta wuce shekara 50. Wannan kuwa saboda ALLAH da Manzonsa (SAW) sun
rataya hukuncin haila ne bisa suwarsa. Kuma ALLAH da Manzonsa (SAW) basu iyakance
wasu ayyanannun shekaru ba game da wannan ya wajaba komawa zuwa sumuwar jinin
wanda aka rataya hukunce hukunce a kansa. Iyakance shi da ayyanannun shekaru yana
buqatar dalili daga Qur'an ko sunnah. Gashi kuwa babu dalili akan haka.
Amma MATSAYI NA BIYU: Shine gwargodon Haila wato gwargodon zamaninta, haqiqa
malamai sunyi sa6ani mai yawa a kusan zantuka guda 6 koma 7.
Ibnul Munzir Yace: "wata jama'a tace: babu wata iyaka ta kwanaki ga mafi qarancin Haila
ko mafi yawanta"sai nace: wannan magana kamar maganar Darimiy ce wacce ta gabata,
haka kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah kuma shine dai dai domin qur'ani
da sunnah da kuma abunda ake gani yau da gobe, sun nuna hakan.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU

https://fb.me/abbansinan

Thursday, 21 November 2019

019 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha Tara  19_

LITTAFI: *JININ DABI'A GA MATA.*

WALLAFAR: *SHEIKH MUHAMMAD SALIH AL'UTHAYMEEN.*

FASSARAR: *UTHMAN MUSA GABARI*

GABATARWA: *FARIDAH BINTU SALIS(Bintus~sunnah)*

*MA'ANAR JININ HAILA DA HIKIMARSA!!!*

HAILA AYAREN LARABCI: shine kwararar abu da kuma gudanarsa.

A SHARI'A: shine jini da yake faruwa ga mace na dabi'a ba tare da wani sababi ba acikin
wasu sanannun lokuta.
Shine jini na dabi'a ( mai zubowa) ba tare da wani sababi na rashin lafiya ba ko rauni ko zubewar ciki ko haihuwa ba.
Saboda cewa shi jinine na dabi'a don haka yana sabawa gwargodon halin mace da yanayin tasowarta da tsufanta, saboda haka mata suna sassa6awa a cikinsa, sassabawa
mabanbanta na zahiri.

*HIKIMA A CIKINSA:*  yayin da dan tayi(yaro) ya kasance acikin mahaifiyarsa bazai yuwu ya
ringa yin kalaci da irin abunda mutum na wajen ciki yake yin kalaci dashi ba. Kuma bazai
yuwu ga wanda yafi kowa tausayinsa ba ya iya sadar da kalaci gare shi (ta kowace hanya
ba) saboda haka sai ALLAH (SWT) ya sanya jijiyoyin jini acikin mace wanda ta hanyar sune dan tayin(yaron) da yake cikin mahaifiyarsa zai dinga yin kalaci acikin mahaifiyarsa ta hanyar cibiya, jinin zai dinga shiga ta jijiyoyin d'an cikin yayi kalaci dashi. Tsarki ya tabbata ga ALLAH mafi kyawun masu halitta.
Wannan shine hikimar wannan saboda haka idan mace ta dauki ciki sai haila ta yanke mata sai 'yan kadan ne ke yin Haila idan suna da ciki, haka kuma masu shayarwa kadan ne ake samun wacce take yin Haila a cikinsu, musamman a farkon lokacin
shayarwa.

A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU.


DOMIN SHIGA GROUPS DIN: *MU KYAUTATA NIYYA* NA MAZA KO NA MATA SAI A AYI MAGANA TA WHATSAPP NUMBER:
+2348064734911

https://fb.me/abbansinan