Monday, 5 December 2016

ANYA KUNASON HUSSAINI???

*ANYA KUNASON HUSSAINI???*

```gaskiya wannan munafunci ne karara!
Shin wai goma ga Wata aka kashe Hussain ko Ashirin ga Wata???

Anya kunason shahada???

Anya kunason Hussaini???

Tsoron me ya hanaku fitowa a ranar goma ga Wata sai yau ashirin ga Wata???

Ko kuna tsoron Ayi fatahu Tsafe ne???

Meyasa kukayi shi tun da safe, sabanin lokuttan baya sai anyi la'asar???

Kunji kunya! Kunji kunya!! Kunji kunya!!!

Allah ya kyauta```

ALHAMDULILLAH.

*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!*

```A madadin kwamitin SHABABU AHLIS SUNNAH WALJAMA'AH TSAFE, muna farin cikin sanar daku cewa Mai gida kuma babban malaminmu, patron na wannan kwamiti, wato Sheikh Musa s lawal Tsafe (Abu salih ibn salih) ya samu nasarar lashe jarabawar karo karatu a jami'ar musulunci dake jamhuriyar Niger(digiri na biyu), muna taya Malam da sauran Abokanshi guda hudu murnar lashe wannan jarabawar.  Allah yasa ayo karatu mai amfani Wanda za'azo a cigaba da kwarara manashi a kwakwalenmu har sai mun fara tunbudinshi.

Hashim Surajo Uba Tsamiya ```

SUWAYE AKA KASHE TARE DA HUSSAINI A CIKIN AHLUL BAITI ALLAH YA YARDA DASU.???

*SUWAYE AKA KASHE TARE DA HUSSAINI A CIKIN AHLUL BAITI ALLAH YA YARDA DASU???*

*من قتل مع الحسين من أهل البيت رضي الله عنهم؟؟؟*

*_Yana daga cikin Abunda zakuji yan shi'ah na fada cewa suna son Ahlul baiti! Toh amma Sayyidina Hussain shikadai ne Ahlul baiti??? Sauran Yayan sayyidina Aliyu su ba Ahlul baiti bane???_*

```yana daga cikin soyayyar sayidina Aliyu ga khalifofin da suka gaba ce shi, sanya ma yayanshi sunayensu. Duk Wanda ya sanya ma dan shi sunanka soyayya ne yasa hakan ko gaba???
Daga cikin sunayen yayan sayyidina Aliyu da kuma yayan Hassan ibn Aliyu ibn Abi dalib wadanda aka kashe tare da Hussaini akwai;
√ Abubakar ibn Aliyu ibn Abi dalib! An kasheshi tare da Hussaini a karbala'a. Kai Dan shi'ah ka duba wannan littafi domin ka ganewa idonka; (Muntahal Amãl,1/528) zaka samu cikakken bayani.

√ Umar ibn Aliyu ibn Abi dalib! Shima ya samu shahada a Karbala'a tare da Sayyidina Hussaini. Ka duba littafin (kashful gummah, 1/440)

√ Usman ibn Aliyu ibn  Abi dalib! Shima ya zama shaheedi a karbala'a ka duba littafin (muntahal Amãl, 1/526-527)

Daga cikin wadanda suka samu shahada a Karbala'a akwai yayan sayyidina Hassan ibn Aliyu ibn Abi dalib, daga ciki akwai;

√ Abubakar ibn Hassan ibn Aliyu ibn Abi dalib! Ka duba cikin(Al-irshãd shafi na 186-248 ko kashful gumma, 1/575-580).

√ Umar ibn Hassan ibn Aliyu ibn Abi dalib! Shima Allah ya bashi shahada a karbala'a. Ka duba cikin(Mazãlimu Ahlul baiti, 254 ko i'ilamul wara, 112).

  Wadannan duk suna cikin Ahlul baiti Rasulul-llah, amma da yake Addinin shi'anci an ginashi ne akan karya da yaudara da siyasa. Sai kaji suna Ambaton sunan Hussaini kadai a matsayin Wanda ya samu shahada a Karbala'a. Saboda gabarsu da kiyayyarsu da masu wadannan sunaye!

Kurtugin shi'ah na Tsafe ina mai tabbatar maka cewa; matukar zaka rika gaba da Abubakar! Toh sai ka chanja sunan Uba!
Allah yayi mana tsari da jahilcin yan shi'ah da suke fama dashi, jahillan cikinsu kuma Allah ya cetosu.```

Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya_*

SUNNAH NE YIN SALLAH DA TAKALMI

🔈🔉🔊🔈🔉🔊🔈
*SUNNAH NE YIN SALLAH DA TAKALMI, DAGA GROUPS DIN MUKYAUTATA NIYYA!!!*
📣📣📣📣📣📣📣

*Rubutawa:* *_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAN)_*

*Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna Neman gafararSa, muna Neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, Wanda Allah ya shiryar babu mai iya batar dashi Wanda kuma ya batar babu mai iya shiryar dashi, kuma ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma ina shaidawa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, yabo da godiya sun tabbata ga fiyayyen halitta Wanda  yace Wanda yayi mashi da'a Dan Aljanna ne, Wanda ya saba mashi Dan wuta ne!*
_Bayan haka:_

*وعن أبى سعيد رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "إذا جاء أحدكم المسجد، فلينظر، فإن رأى فى نعليه أذى أو قذرا فليمسحه، وليصل فيهما.*
(أخرجه أبو داود، وصححه ابن خزيمة).

```Hadisi ya tabbata daga Abi sa'id(R.A) yace, Annabi Muhammad s.a.w yace: idan dayanku yayi Nufin zuwa Masallaci to ya duba idan yaga datti ko Wata 'kazanta a takalminshi, to ya goge sannan yayi SALLAH a cikinsu.```

Yan uwa mu lura, Manzon Allah s.a.w cewa yayi: *MU DUBA IDAN MUKA GA WANI DATTI KO KAZANTA MU GOGE MUYI SALLAH A CIKINSU!*  kuma hadisi ingantacce Wanda Abu daud ya fitar a cikin littafinshi kuma ibn khuzaima ya ingantashi. Imamu Nasirudden bn Albany ya ingantashi.
*Imamu Ahmad(imamu Ahlis sunnah waljama'ah) yake cewa: " من رد حديث رسول الله صلى الله عليه وسلم فهو شفا هلكة*
```Ma'ana: Duk Wanda za'ace ga Hadisi ingantacce amma ya tsaya jayayya yana son raddi ga Hadisin, imamu Ahmad yace yana gefen Halaka!

Ma'abota cewa ba'a SALLAH da takalmi ko zaku bamu hujjarku???``` 

*ABU SINAN* ```na jiran yaji rubabbun hujjojinku. Domin yasan inda kuka dogara.```

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINAAN)_*

Http://Hashim141473.mywapblog.com

ANNABI MUHAMMAD S.A.W BAISAN GAIBU BA...!!! 001

*ANNABI MUHAMMAD S.A.W BAI SAN GAIBU BA...!!!*

*_Fitowa ta daya(01)_*

*_DAGA; Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINAAN)_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*

  ```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda baya da Abokin tarayya. Tsira da Amincin Allah SU tabbata ga farin jekada   Wanda babu wani Annabi bayansa,Annabi Muhammad s.a.w tare da jama'ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka; Nayi nufin yin wannan takaitaccen rubutu saboda ganin yadda wasu yan bidi'ah ke cusa ma kananan yara Akeedar cewa Annabi yasan gaibu a makarantunsu Na Zawuyya da sauran Majami'oinsu.
Zan takaitu insha Allahu akan Qur'ani da hadisai ingantattu, saboda kada in kawo maganar wani malami na sunnah wani kuma ya kawo man ta Inyass ko wani shehi!
Ga wasu daga cikin Ayoyin Qur'ani dake nuna cewa Annabi baisan gaibu ba.```

*وعنده مفاتح الغيب لايعلمها إلا هو...*
_Ma'ana;_ *_kuma A wajenshi(Allah) makullan gaibu suke babu Wanda ya sansu sai shi(Allah)_*

*A wani wurin kuma Allah S.W.T cewa yayi;*
*_قل لايعلم من في السماوات والأرض الغيب إلا الله، وما يشعرون أيان يبعثون_*

_Ma'ana;_ ```Kace(yã kai Annabi Muhammad s.a.w) babu Wanda yasan gaibu a sama ko a kasa sai Allah, kuma basu San yaushe ne za'a tashesu ba(bayan mutuwa).```

*Idan kuma muka leka a suratu lukman aya ta karshe Allah S.W.T cewa yayi;*
*_إن الله عنده علم الساعة وينزل الغيث ويعلم ما فى الأرحم، وما تدرى نفس ماذ تكسب غدا، وما تدرى نفس بأي أرض تموت، إن الله عليم خبير_*
_Ma'ana;_ *_Lallai a wurin Allah ne Ilimin sa'a yake(Tashin kiyama) kuma shine ke saukar da girgije, kuma yasan Abunda ke cikin mahaifa, kuma babu Wata Rai da tasan Abunda zata Aikata a gobe ko Anjima, babu Wanda yasan a wace kasa ko a wane gari zai  mutu. Lallai Allah masani ne kuma mai bada labari ne._*

```Wadanan Ayoyi da na kawo dukkansu idan ka duba Tafsiran manyan Malamai wadan da ba son Rai a zuciyarsu, zaka samu sunyi cikakken bayani karara, babu boye boye ko shaci fadi, zaka samu babu Wanda ya kawo cewa Annabi yasan Gaibu.
Idan muka dawo a cikin hadissai kuwa, ga hadisi na biyu dake cikin AR'BA'UNA HADITH, Wanda tun bamu da wayo ake karantar damu shi, Hadisin Sayyidina Umar R.A Wanda imamu Muslim ya ruwaito, Lokacin da Mala'ika jibril lokacin da yake yima Annabi Muhammad s.a.w Tambayoyi, daga karshe yake tambayar shi;``` 
*فأخبرني عن الساعة: قال: ما المسئول عنها بأعلم من السائل....*
_Ma'ana;_ *_ka bani Labarin sa'a(Tashin kiyama)? Sai Annabi Muhammad s.a.w yace; Ai Wanda aka tambaya baifi Wanda yayi Tambayar sani ba._*
``` Shin idan  manzon Allah s.a.w yasan gaibu meyasa bai fada masa Ranar da za'ayi tashin kiyama ba???
Daga karshe inason in fadawa yan uwa cewa; Maganar gaskiya Annabi Muhammad s.a.w bai San gaibi ba sai Allah ya sanar dashi ta fuskar wahayi, amma kafin Allah yayi masa wahayi bai sani ba.

  Allah s.w.t Nike Roko da ya karemu da bin son zukatanmu, ya bamu ikon yin koyi da farin jekada Annabi Muhammad s.a.w a dukkanin Rayuwarmu.

Sai mun hadu a fitowa Na biyu insha Allahu```

Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)_*

Shiga link dake kasa mu hadu a Facebook
https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya

IYAYENMU NE

*_ALLAH S.W.T YACE; MATAN ANNABI IYAYENMU NE!*_

      *_Amma shi Dan shi'ah yace ba uwayenshi bane yana zaginsu, sai mukace duk Wanda yace ba iyayenshi bane toh mu munsan uwarshi, uwarshi itace hãwuyah, (wuta)_*

```ABU SINAAN```

ANNABI MUHAMMAD S.A.W BAISAN GAIBI BA...!!!

🎙🎙🎙🎙🎙🎙🎙
*ANNABI MUHAMMAD S.A.W BAISAN GAIBU BA...!!!*🎤🎤🎤🎤🎤🎤

*_Fitowa ta biyu(02)_*

*Daga; Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINAAN)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya sanar da Dan Adam Abunda bai sani ba, tsira da Amincin Allah su tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w tare da iyalan gidansa da sahabbansa da duk Wanda yabi hanyarsu da kyautatawa har zuwa ranar da kudi da yaya basu da amfani sai Wanda yaje ma Allah da zuciya mai tsoronshi da mika wuya gareshi.*

*_Bayan haka_*

```Nayi rubutu Mai irin wannan taken a sama sai wasu yan bidi'ah da wadanda basu fahimci addini ba suka yo Mani chaa, sai naga dacewar na kara haskaka ma Al'umma domin kowa ya kara gane inda aka nufa.

Da farko dai Menene Ma'anar gaibu???

     Ita dai Kalmar gaibu kalma ce ta larabci, wadda take hawa akan duk abunda ya boyewa sanin mutum, duk abinda tunanin mai tunani ko hankalin mai hankali bazai iya riskarsa ba to shi ake cewa gaibu. Misali; Sanin yaushe zaka mutu, sanin Abinda zai sami rayuwarka a nan gaba, da sanin ranar tashin Kiyama duk suna daga cikin Misalan gaibu. (Nemi rubutun Abokin da'awa a fagen Media Malam Awaisu Al'araby fagge Wanda yayi a 28/04/2015 domin Karin bayani.)
Idan ka fahimci ma'anar gaibu, toh sai mu leka Qur'ani domin mu warware matsalar.
A cikin Qur'ani Allah S.W.T yake cewa;```
*يسئلك الناس عن الساعة، قل إنما علمها عند الله، وما يدريك لعل الساعة تكون قريبا.*
_Ma'ana;_ *_suna tambayarka(Annabi Muhammad s.a.w) akan lokaci(Tashin kiyama), sai Allah yace, kace saninta(Tashin kiyama) yana wurin Allah kadai. Kuma meya sanar dakai watakila ta kasance kusa._*

   ```Wannan ayar koda ace ita kadai aka saukar akan ilimin gaibu to tabbas ta isa hujja akan wadancan yan bidi'ar, abunda mutane basu fahimta ba akan wannan lamarin shine, su yan bidi'ah suna son fakewa da guzuma domin Harbin karsana, idan su ka yarda Almajiransu suka gane cewa Annabi Muhammad s.a.w baisan gaibu ba, sai Wanda Allah ya sanar dashi,idan kuma Allah ya sanar dashi ya tashi daga gaibu zuwa wahayi, toh idan suka fahimci wannan toh zasu gane cewa Ashe wadancan waliyyan na bugi yaudararsu sukeyi, domin sunce Sunsan gaibu, hujjarsu ta cewa haka saboda saboda tijjani da inyass duk jikokin Annabi ne, toh tunda Annabi yasan gaibu toh toh toh ai ai ai shi kuma jikane, saboda haka dole mu haska ma Al'umma domin su fahimci ina gaskiyar take.
  Wata ayar kuma Allah S.W.T cewa yayi;```
*ولا أقول لكم عندى خزائن الله ولا أعلم الغيب...*

_Ma'ana:_ *_(Allah ne da kanshi ya cewa Annabi Muhammad s.a.w ya fadawa mutane cewa) Ban ce muku Taskokin Allah a hannuna suke ba, sannan kuma bansan gaibu ba._*

   ```To anan Abunda zance shine duk Wanda ya fahimci ma'anar gaibu wacce muka ambata a farkon rubutu, to zai fahimci cewa Manzon Allah s.a.w baisan gaibu ba,sai Wanda Allah ya sanar dashi, idan kuma Allah ya sanar dashi ya tashi daga gaibu zuwa wahayi, Allah ya kara fahimtar damu gaskiya ya bamu ikon binta.
Toh yanzu bari mu leka cikin hadisi.```
 
*Hadisi ya tabbata daga ummuna Aisha R.A akan cewa Annabi baisan gaibu ba.*
*عن عائشة رضي الله عنها قالت؛ من حدثك أن محمدا صلى الله عليه وسلم رأى ربه فقد كذب وهو يقول(لاتدركه ألابصار)، ومن حدثك أنه يعلم الغيب فقد كذب وهو يقول لايعلم الغيب إلا الله*

_Ma'ana:_ *_Nana Aisha tace "duk Wanda yace maka Annabi Muhammad s.a.w yaga Allah toh karya yakeyi, sannan duk Wanda yace maka Annabi yasan gaibu to karya yakeyi, domin shi din yana cewa babu Wanda yasan gaibu sai Allah._*[Bukhari 7380,6945, Muslim 457,287]

   ```Toh yan uwa kunji zancen Nana Aisha matar Manzon Allah s.a.w wacce take kusa dashi a koda yaushe, Masu karyata Ahlis sunnah akan wannan zancen to me zakuce akan zancen Nana Aisha??? Nasan indai ka yarda Nana Aisha uwar muminai ce to baza ka karyata taba, domin indai kai mumini ne to uwarka ce, idan kace ba uwarka bace sai muce toh ai munsan wacece uwarka, eh itace hãwuya, Allah ya kyauta. Bari na dakata a nan idan bukatuwar fitowa na uku ta taso, toh a matsayinmu na dalibai zamu kara cewa wani Abu.
Allah ka jikan sheikhul Islam Muhammad ibn Abdulwahab, a cikin Littafinsa kashfus shubuhãt yake cewa;```
*والعامي من الموحدين يغلب ألفا من علماء هؤلاء المشركين، كما قال تعال؛(وإن جندنا لهم الغلبون) [الصافات ١٧٣]*

_Ma'ana;_ *_Mai karamin sani(ilimi) cikin masu kadaita Allah yana rinjayar mutum dubu cikin mushirikan Malaman bidi'ah, kamar yadda Allah yace; Rundunar Allah sune Masu yin nasara. Rundunar Allah sune masu yin nasara da hujja Qur'ani da hadisi, haka kuma suke yin nasara da harshensu._*

```Allah ya tabbatar damu akan sunnar Annabi Muhammad s.a.w ya dawwamar damu a cikin aiki da ita Amiin.```

https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya

Copyright©
*Hashim Surajo Uba Tsamiya*
📞08064734911📞