FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA
#MATSAYIN_TAUHIDI_GA_RAYUWAR_MUSULMI
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
BAYAN mukaddimah........
Yan uwa musulmi masu albarka kamar yadda kuka gani kan abunda khudbar mu zata yi magana, Yan uwa hakika shi tauhidi shine rayuwar bawan Allah kacokan..
Yan uwa musulmi hakika hakika Allah madaukakin sarki ya halicce mu baki daya dan mu bauta mashi, Babban dalilin halittar mu baki daya shine dan yin bauta ga Allah ga Allah mahallici.
Allah madaukakin sarki ya halicce mu kuma yabamu umarnin bauta mashi, A cikin suratul zariyat Allah madaukakin sarki na cewa "BAN HALICCI MUTUN DA ALJANI BA SAI DAN SU BAUTA MANI"
Bautar Allah ga kowane mutun da aljani dole ne kuma wajibi ne, Mafi girman abun bukata ga bawan Allah shine kadaita Allah ba tare da sanya mashi kishiya ba a ko ina..
Hakika cikin imaninka da tauhidinka dole ne sai kazama mai furtawa da kaskantar da kai da kwadayin rahamar sa da tsoron azabar sa, Da kuma kasancewa mai sujjada gareshi da cikakken tsoron sa!!
Yan uwa musulmi masu albarka hakika domin kara tabbatar da tauhidi Allah ya wajabta mana karanta suratul fatiha a cikin kowace sallah da zamu yi, A ciki muke cewa "IYAKA NA ABUDU WA'IKA NAS TA'IM"
IDAN HAR BAWA YAKI YIN BAUTA GA ALLAH HAKIKA YAYI ASARAR DUNIYA DA LAHIRA!!! 😨😨😨
Yan uwa musulmi hakika Allah ya aiko mazannin shi baki daya domin su tabbatar da tauhidi da musulunci a kasa, Kuma Allah ya aiko littafan baki daya dan tabbatar dan tauhidi a kasa '
ALLAH madaukakin sarki ya fada cikin suratul nahli cewa "WALLAHI MUN AIKOWA KOWACE AL' UMMAH DA MANZO DOMIN SU BAUTA MA ALLAH KUMA SU KAFURCEWA DAGUTU"
Yan uwa musulmi hakika wannan ayar kadan ce daga cikin ayoyin dake tabbatar da dole ne yin bauta ga Allah da kuma kare yin tauhidi.
Yan uwa musulmi masu albarka lallai da tauhidi ne rayuwa ke natsuwa kuma ta samu kwanciyar hankali, Hakika idan rayuwa ta kasance babu tauhidi a cikin ta tabbas dabba ta fishi,
Duk wanda keda tauhidi to hakika shi rayayyene, Idan kuma baida tauhidi komai mulkin sa da duk wani gata nashi to matacce ne.
Allah madaukakin sarki yana cewa cikin suratul an'am cewa "WANDA YA KASANCE MATACCE MUKE RAYASHI MU SANYA MASHI HASKE"
hakama Allah madaukakin sarki na cewa "KU KARBA KIRAN ALLAH DA MANZO IDAN AN KIRAKU GA RAYUWA (TAUHIDI)
Yan uwa musulmi wallahi duk wanda baisan Allah ba baida banbanci da dabbah, Har ma dabba tafi shi domin kuwa ita dabba babu wani hisabi da za'a yi masu.
Idan har muka yi imani lallai ALLAH zai samar mana da jindadi, Allah yana fada cikin suratul nur cewa "ALLAH YAYI ALKAWARI IDAN KUKAYI IMANI DA AIKI NA KWARAI ZAMU KHALIFANTAR DAKU DA SHARADIN KUN KADAITA ALLAH"
kafurcewa Allah lallai shine babban jigon samun zaman lafiya mai dorewa.
Riko da tauhidi shine jigo na samuwar arziki, Allah madaukakin sarki na cewa "DUK WANDA YAYI IMANI DA ALLAH YA AIKATA AIKIN KWARAI ZAMU AZURTASHI"
Arziki na nufin wadatar zuci, Koda kaga kafuri da kudi da dukiya zaka same shi babu kwanciyar hankali da natsuwa.
Amma idan kana da cikakken imani da Allah zaka ji natsuwa da wadata koda baka da kudi 😀
Yan uwa musulmi masu albarka hakika Riko da tauhidi na kawo natsuwa daga shaidanu,Bai yiwuwa shaidani ya tsaya idan ake gudanar da tauhidi.
Duk inda ake kiran sallah shaidan yakan tsere da gudu, Har sai an gama sannan idan za'ayi ikama haka, Saboda a cikin kiran sallah da ikama akwai tauhidi a cikin su.
Hakama ayatul kursiyu aya ce mai girman gaske, Wanda duk ya karanta ta kafin ya kwanta Allah zai turo mala'iku su rika gadin shi wannan duk dalilin tauhidin dake ciki ne.
Yan uwa musulmi hakika Riko da tauhidi yana kawo kariya tsakanin ka da mushrikai, Domin ALLAH madaukakin sarki yace "LALLAI ALLAH NA BADA KARIYA GA MASU IMANI" duk wani kokarin mushrikai nan cutar Allah bazai bari ba domin yayi alkawarin kariyar.
Yan uwa musulmi dole ne tunatar da muminai game da abunda ya shafi tauhidi domin kamar yadda muka fada shine ginshikin rayuwa,
Hakika tunatar da muminai game da imani yana da muhimmancin gaske domin zai zaburar da sabunta masu imanin su, Domin Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "IMANI KAMAR RIGA NE"
wato kenan yana tsufa idan har ba'a sabunta shi.
Yan musulmi akwai wasu musulmi dasu ke matukar adawa da maganar da shafi tauhidi, Domin wai su a ganin su tsanantawane yin maganar tauhidi, kawai abar kowa yayi yadda yake so...
To shi musulunci ba haka yake ba, Yana da tsari kuma da zarar anyi nisa cikin kaucewa tsarin sa to za'a iya halaka!!
Yazama wajibi kuma dole ga kowane musulmi yasan tauhidan nan guda 4 - Rububiya
-Qulihiya
-As-mau wassifat
-Risalah
Dole a sansu tare da sanin matsayin kowane daga cikin su.
Ta sanin su zai sa mu kaucewa duk abunda zai kange daga Allah, kamar shirka da Allah!!!
Domin kamr yadda muka sani shirka da Allah na warware ibadu sa imani baki daya.
Yin shirka ko duba ko bugun kasa da zuwa wurin bokaye na warware imani, Domin Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Duk wanda yaje wurin boka ko mai duba kuma ya gasgata abunda ya fada mashi to ya kafurta abunda aka saukar wa Annabi Muhammadu sallal lahu alaihi wassalam (Al'qurani mai tsarki)
Duk abunda kake nema ka tuna Allah ne ke badawa tun kafin a hallicce ka a rubuta duk abunda zai zama naka.,
Basai kaje wurin wani kazami ba mushriki, Ya raba ka da imanin ka ya raba ka da kudin ka.
Yan uwa musulmi mu kara tunawa fa lallai ALLAH ya hallicce mu ne dan kadai mu bauta mashi.
Idan har Zamu yi hakuri da talauci da rashi dole ne muyi hakuri da yawan yiwa Allah ibada domin akwai ranar sakamako.
Tun daga aure, sutura abinci gida mota abokan ta, Da duk wani abu na bukatar rayuwar mu basu kai muhimmancin tauhidi ba.
Yan uwa musulmi masu albarka idan muka diba yadda rayuwa ba chan ba chan babu tauhidi wata rana sai mutuwa tazo ta riska shikenan!! 😨😵😷
Allah ya tabbatar da tauhidi a zukatan mu ya yafe mana yayi mana rahama, Ya ubangiji ka yafe mana kurakuren mu ya kare daga hassada da kyashi da jin zafi da gulma da annamimanci da karya da ciwo da kuturta da makanta da kurumta da sauran ciwuka.
Ya ubangiji ka zaunar damu lafiya ka biya bukatun mu na alkhairi ka gafarta wa mamatan mu, Allah kayi salati da tasleemi ga Shugaban mu Annabi Muhammadu da iyalinsa da sahabban sa da dukkan mataimakan sa da sahabban sa yardaddu baki daya har zuwa ranar sakamako.
Ameen ya rabb.
©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 24-Rabi'ul akheer {4}-1439
Friday 12-January - 2018 AB