Wednesday, 26 October 2022

02 NASIHAR BARKA DA SAFIYA

*NASIHAR BARKA DA SAFIYA 002*

*_(Nine Yusuf wannan kuma ɗan uwana ne)_*

Wannan maganar Annabin Allah Yusuf (Alaihissalam) ce, a lokacin da yayi maganar shine shugaban ƙasar Misira kuma taskar arzikin ƙasar na akan ikonsa...

Tare da haka, bai juya baya ya kalli matsayinsa ko muƙamin da yake akai ba, sai ya ambaci sunansa tsurar shi ba tare da wani laƙabi ba, domin wanda yake da zuciya mai girma, da ɗabi'u maɗaukaka baya juyawa ya kalli wani matsayi na mulki ko kuɗi ko yayi alfahari ya riƙa ɗagãwa da hakan a cikin mutane.

Dr. Hussein Al~feefy
_____________________________

Ni(Abu Sinan) nace, naji a cikin wani karatu da Fadhilatush-Sheikh Dr. Swalih bn Abdillah bn Hamd Al-Osaimi (H) aka tambaye shi cewa: meyasa kake ambatar sunan su Ibn Taimiyya da Ibnul Qayyim gãya ba tare da laƙabin Sheikh, ko Al-allama ko Ustaz da sauransu ba?

Sai ya da amsa da cewa: Wanda Allah ya ɗaukaka baya buƙatar wata ɗaukakar mutane, yace Abubakar Siddiq, ko Aliyu ko Abu Huraira (Radiyallahu Anhum) ka taɓa jin za'a kira su an ce Al-allama Abu Huraira? Ko Fadhilatush-Sheikh Aliyu Bn Abi Ɗalib? Yace sun wuce wannan matsayin, don haka ne ma aka samu wasu daga cikin magabata suna kyamatar wannan laƙubban.
___________________________

Amma yau Ɗalibin da bai gama zama a harkar ilimi ba idan zaka kira sunan shi kai tsaye sai yaga ka ƙasƙanta shi saboda rashin ikhlasi a cikin ayyuka.

Allah ya ganar damu ya bamu ikon yin ibada domin shi


© *AbbanSinan Tsamiya*
01 Rabi'u Thani, 1444AH
27 October, 2022

01NASIHAR BARKA DA SAFIYA

*NASIHAR BARKA DA ASUBA*

Idan wani yazo wurin ka domin ka taimake shi akan bukatarsa, toh fa kaine mai amfanuwa da hakan, domin Allah SWT shine yayi maka ni'ima, ya buɗe maka ƙofar Alkhairi.
A wannan lokacin kyautatawar da za kayi mashi kanka ne zaka kyautata ma; Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Idan kun kyautata, toh kanku kuka kyautatamawa) a wani wuri kuma yace: (Ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka)

Allah ya bamu abinda zamu taimaki wanda yazo nema a wurin mu🤲

 ©Dr. Hussein Al-feefy

Fassarar:
*AbbanSinan Tsamiya*
30 Rabi'u Awwal 1444AH
26th October, 2022

Tuesday, 13 September 2022

LADUBBAN TAMBAYA

*FA'IDA*

Ya kamata ɗalibi yayi riko da ƙa'idodi huɗu yayin tambayar Malami:

 1. Kayi tunani akan abinda zaka tambaya, duk wanda ya munana manufar tambayarsa, za'a haramta mashi albarkar ilimi, da amfaninsa saboda mummunar manufarsa.

 2. Kula akan abinda kake tambaya akansa, kada kayi tambaya sai abinda zai amfanar.

 3. Kula da halin da Sheikh yake ciki a lokacin tambayar, kada ka tambayi Malami a yanayin da baya cikin natsuwa ko baya cikin jin daɗi.


 4. Mai tambaya ya natsu akan yadda zai gabatar da tambayarsa, ya tabbata ya fitar da ita a hanya mai kyau yadda za'a fahimta.


Na cirato na kuma fassara daga Littafin تعظيم العلم na Masoyina *Fadhilatush-Sheikh Al-allama Dr. Swalih bn Abdillah bn Hamad Al-Osaimi (Hafizahullah)*


© Mai Fassara
*Abban Sinan*
16/02/1444AH
13/09/2022

Thursday, 29 July 2021

002 ‏FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ‎ﷺ

FARIN JEKADA, ANNABI MUHAMMAD ﷺ

Fitowa ta biyu 002

Manzon Allah ﷺ yana da wasu haƙƙoƙi masu tarin yawa da ba za'a iya ƙirge su ba, waɗanda suka zama wajibi mu kula dasu kwarai da gaske.
Ga kaɗan daga cikin su:

1. IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ

Ma'anar imani da Manzon Allah ﷺ kamar yadda wasu daga cikin Malamai suka faɗa shine: 
a) Gasgata shi a cikin duk abinda ya faɗa ko ya bada labari
b) Yi Mashi biyayya a cikin dukkan komai
c) Bin Shari'ar Manzon Allah ﷺ
Don haka ne ma wasu daga cikin Malamai suka ce gasgata Manzon Allah ﷺ yana ɗaukar abubuwa guda biyu:
NA FARKO: Tabbatar da AnnabtarSa ﷺ da gasgata Shi akan duk abinda ya isar daga Ubangijin Shi SWT, da kuma yadda cewa Wannan ya keɓanci Manzon Allah ﷺ ne kawai (Ma'ana: babu wani Annabi da zai zo da irin wannan a bayan Shi ﷺ

NA BIYU: Gasgata Shi ﷺ a cikin abinda yazo dashi, ka yarda cewa yazo dashi ne daga wurin Allah SWT, sannan kuma wajibi ne a bishi.

Wajibi ne a Gasgata Manzon Allah ﷺ a cikin dukkan abinda ya bada labari daga Allah SWT, Na abubuwan da suke na Gaibu ne, Labarin Wuta da Aljanna, Labarin tanadin Sakamako mai kyau ga wanda ya kyautata aiki, da mummunan sakamako Ga wanda ya ɓata aikinsa, Labarin Azabar ƙabari da kuma Ni'imomin dake cikin shi, da dukkanin wani abu da Manzon Allah ﷺ ya bada labari dole ne a Gasgata Shi ﷺ.
Allah Maɗaukakin sarki yana cewa:
وَمَا يَنطِقُ عَنِ الۡهَوَىٰ، إِنۡ هُوَ إِلاَّ وَحۡيُُ يُوحَىٰ
Ma'ana:
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
(MaganarSa ﷺ) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

Zamu dakata a nan Saboda kada Rubutun yayi Tsayi, a fitowa ta gaba zamuyi Magana akan: ABUBUWAN DAKE WARWARE IMANI DA MANZON ALLAH ﷺ Allah ya ɗora mu akan Tafarki na gaskiya har ƙarshen Rayuwar mu, Allah ya kare Addinmu na Musulunci daga Makircin yahudu da Nasara🤲 yaa Allah ka rugurguza duk masu taɓa ƙima da mutuncin Manzon Allah ﷺ a duk inda suke, yaa Allah da wanda akayi yaji daɗi, da wanda yayi, da wanda yana da ikon magana amma yayi shiru Saboda kada arna suce mashi mai tsats-tsauran ra'ayin addini, yaa Ubangiji duk ka tozarta su a nan duniya da gobe ƙiyama🤲 yaa Ubangiji ka ƙara mana Son Annabi Muhammad ﷺ🤲 kasa mu mutu muna masu bin shiriyar Annabi Muhammad ﷺ


✍️ Hashim Sirajo Uba Ats-tsamawy Tsafe
atstsamawy@gmail.com
18/12/1442AH
28/07/2021

01 ‏FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ‎ﷺ

FARIN JEKADA, ANNABI MUHAMMAD ﷺ 

Fitowa ta Farko 001

KO KASAN MA’NAR MUHAMMADUR RASULULLAHI ﷺ ?

Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda ya haɗa Sunan shi da sunan Manzon sa a wajen kalmar Shahada.

Tsira da Aminci su tabbata ga Manzonsa wanda ya fayyace mana ma’anar kalmar shahada ga ayyukansa.

Ma’anar ka shaida MUHAMMADU Manzon Allah ne, shine yin furuci a ɓoye da bayanne, cewa lallai Annabi Muhammad ﷺ bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne zuwa ga mutane baki daya, da kuma aiki da abun da wannan kalmar ke ɗauke da shi.

Ya kamata kai Ɗan uwa Musulmi kasani cewa kalmar MUHAMMADURRASULULLAH ﷺ 
tana da ma’ana da rukunnai da sharuɗɗa, da kuma abun da ta hukunta. Ga yadda ma’anar take:

Yiwa Manzon Allah ﷺ ɗa’a a cikin abinda yayi umurni, gasgata shi a cikin abinda ya bada labari, nisantar abinda ya hana ko ya tsoratar, ba’a bautar Allah, bautar kuma ta samu karɓuwa face yadda Manzon Allah ﷺ 
ya tsara (ya shar’anta).
Dole ne mai faɗar Muhammadur Rasululahi ﷺ 
 yayi aiki da waɗannan bayanai, domin faɗar hakan da harshe kawai ba zai wadatar ba.

RUKUNAN MUHAMMADUR RASULULLAHI ﷺ 
 GUDA BIYU (2) NE:

RUKUNI NA FARKO: 
SHINE ZAMAN SHI BAWAN ALLAH:
 Zaman shi bawan Allah yana kore zurfafawa gareshi. Kamar yadda hadisin da Bukhari ya ruwaito yana cewa "Kada ku ɗagani kamar yadda nasara suka ɗaga ISA DAN MARYAM (A.S) Ni bawan Allah ne kuma Manzonsa ne.”
Ma’anar bawan Allah shine: mutum ne wanda aka halitta daga cikin halittar Allah yana gudana a gareshi abin da yake gudana ga mutane kamar yadda Allah SWT ke faɗa cewa: - “Kace masu lallai ni mutum ne irinku (Suratul Kahfi 109). Cewa da wasu keyi Manzon Allah ﷺ  ba mutum bane wannan zurfafawa ne, da kuma nakkasa shi. Masu faɗar wannan sun can-can-ci a hukunta su.

RUKUNI NA BIYU: SHINE MANZON ALLAH (S.A.W): - Ma’anar Manzon Allah ﷺ 
shine wanda aka aiko ga wasu ko kuma ga mutane baki ɗaya don kira ga Allah. Shi Mai bushara ne mai gargadi.

SHARUDDAN MUHAMMAD RASULULLAH ﷺ 
 GUDA SHIDA (6) NE:

1. Furuci da ManzancinSa da kudiri a cikin zuciya.

2. Bin Manzon Allah ﷺ da aiki da abunda yazo da shi na gaskiya, da barin abun daya hana na ɓarna.
3. Gasgata abin da ya bada labari na gaibu daya wuce da kuma mai zuwa.

4. Son Manzon Allah ﷺ fiye da kanka da dukiyarka da uwayenka da sauran mutane baki daya.

5. Gabatar da zancen shi akan zancen ko wane mutum da kuma aiki da sunnar Shi ﷺ 

6. Bashi kariya daga kowace nakasa da kuma kare sunnar shi iya karfinka.

ABINDA KALMAR TAKE HUKUNTAWA SHINE:

Yi mashi Ɗa’a, gasgatashi, barin abin da ba sunnar Shi bane, (kamar bidi’o’i da ƙage-ƙage)ﷺ 

FADAKARWA

A karshe muna kira ga ‘yan uwa Musulmi su sani cewa Allah bai karɓar duk wani aiki face sai ya cika sharuɗɗa guda biyu (2).

IKHLASI: - Shine yin aiki don Allah

MUTABA’A: - Bin Manzon Allah ﷺ 
sau da kafa a cikin duk abinda zaka gabatar, kamar yadda bayanai suka gabata.

Daga karshe muna roƙon Allah (S.W.T) ya aza mu kan bin Sunnar Manzon Allah ﷺ  kuma ya kashemu a kanta Amin.

Rubutawa
Abu Sinan, Hashim Sirajo Uba Ats-tsamawy Tsafe
17/12/1442AH
27/07/2021

Tuesday, 30 March 2021

05 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA BIYAR (005) DA NA SHIDDA (006)

📒ABU NA BIYAR: SUNNAH NE DANGIN MAMACI DA MAKWABTAN SA SUYI ABINCIN DA KOSAR DA IYALAN MAMACI SU AIKA MASU📒

📌1.Yana daga cikin karantarwar Annabi Muhammad SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM domin tausaya ga iyalan mamaci, dangin sa da makwabtan sa su aika masu abincin da zai Kosar da su. Saboda Hadithin Abdullahi bin Ja'afar da yake cewa: lokacin da labarin mutuwar mahaifin mu (Ja'afar) ya zo, sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM yace: "KUYI ABINCI DON IYALAN GIDAN JA'AFAR (ku aika masu) HAKIKA ABIN DAKE SHAGALTAR DA SU YA ZO MASU". [Abu Dawud da Tirmiziy da bin Majah suka ruwaito sa kuma Hadithi ne ingantacce].

🖋️Haka kuma Imam As-Shafi'iy a cikin littafin sa AL-UMM yana cewa: "INA SO GA DANGI DA MAKWABTAN MAMACI SUYIWA IYALAN MAMACI ABINCI DA ZAI KOSAR DASU A YINI DA DAREN DA YA RASSU, DOMIN SUNNAH NE KUMA YANA DAGA CIKIN AYUKKAN MUTANEN KIRKI A GABANIN MU (Sahabbai da Tabi'ai) DA MA NA BAYAN MU (sauran mabiyan Sunnar Annabi). A karshe sai ya kawo Hadithin Abdullahi bin ja'afar da ya gabata.

📒ABU NA SHIDDA:MUSTAHABBANCIN SHAFA KAN MARAYA DA TAUSAYA MASA📒

📌1. Mustahabbi ne shafa kan maraya da girmama sa, saboda Hadithin Abdullahi bin Ja'afar da yake cewa:.....Manzon Allah ya wuce mu yana kan dabba ni da Qathm da Ubaidullah bin Abbas, sai yace ku miko man shi (wannan yaro) sai aka mika ni ya dora ni a gabansa, sai yacewa Qathm ku miko man shi, sai aka mika masa shi, sai ya dora sa a bayan sa...... a duk lokacin da ya shafi kaina sai yace: "YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA". [Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito sa kuma Hadithi ne ingantacce].

Wannan shine abinda Sunnar Annabi Muhammad SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM ta tabbatar dangane da ta'aziyya.

Wallahu a'alamu bissawab.

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

04 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA HUDU (004)

📒ABU NA HUDU: ABUBUWA UKU DA YA KAMATA A NISANTA A LOKACIN MUTUWA📒

Ya kamata a nisanci al'amurra uku da matane ke yawan yi lokacin da aka yi mutuwa.

📌1. Tururuwar mutane wurin shiga gidan da akayi mutuwa, bai dace ba mutane su dinga shiga gidajen da aka yi mutuwa alhali basu da hurumin shiga gidan da sunan yiwa mata ta'aziyya.

📌2. Taruwa a wani kebantaccen wuri domin karbar gaisuwa (ta'aziyya), kamar Masallaci ko gida ko Makabarta. Musamman yanzu wuraren karbar gaisuwa ya dauki wani sabon salo, wani lokaci kaga kamar buki ake yi an kawo rumfuna da kujeri sai abinci ake kawowa kala-kala, wani lokaci kuma ya zama wurin sharholiya da shaci fadi da giba da aibanta shugabanni da Yan siyasa da masu kudi harma da malaman addini. Kai abin bai tsaya nan ba wasu sun mayar da wurin karbar gaisuwa wani dandalin siyasa da rabawa matasa zauna gari banza kudade.

📌3. Abinci da iyalan mamaci ke tanada domin tarbon masu zuwa ta'aziyya, dalili akan haka shine: Hadithin Abdullahi Albajaliy yace: mu (Sahabbai) "MUN DAUKI TARUWA DON KARBAR GAISUWA (ta'aziyya) DA TANADIN ABINCI DON MASU TA'AZIYYA A MATSAYIN NIYAHAH (wato kururuwa ko kukan mutuwa). [Ahmad da bin Majah suka ruwaito sa, Imam An-Nawawiy ya inganta shi]

🖋️Haka kuma Imam An-Nawawiy a cikin littafin sa AL-MAJMU' sharhin MUHAZZAB na Shayhin Malami Shayraziy cewa yayi: " AMMA ZAMA DOMIN TA'AZIYYA IMAM AS-SAFI'IY DA SHAYRAZIY SUN NASSANTA KARHANCIN SA(kyamar sa)" abinda yake nufi sun karhanta taruwar iyalan mamaci a gida domin mai son yayi masu ta'aziyya ya same su yayi masu ta'aziyya, dai dai abin da ya kamata su tafi wajen bukatun su (na yau da kullum), duk wanda ya ya hadu dasu yayi masu ta'aziyya. Kuma babu bambanci wajen karhanta wannan zama tsakanin maza da mata.

🖋️Abinda Imam An-Nawawiy ya fada yana cikin littafin Imam As-shafi'iy: AL-UMM 1/248, ga kuma abinda yake cewa a cikin littafin: "INA KYAMAR TARON KARBAR TA'AZIYYA KODA BABU KUKA DOMIN YANA SABANTA BAKIN CIKI DA KALLAFA WAHALHALU NA KASHIN DUKIYA".

🖋️Shi kuma bin Humam ya nassanta karhancin a cikin littafin sa SHARHUL HIDAYAH 1/473, kuma yace: BIDI'AH CE MAI MUNI" kuma wannan shine mazhabar Hanabila kamar yadda yake cikin AL-INSWAF 2/565.

Kuma abinda kowa ya sani ne kamar yadda bayani ya gabata wurin karbar gaisuwa ya zama wurin fira, giba, kallon mata, labarin Yan siyasa, Yan kwallo, shugabanni, masu kudi da dai sauran su. Wanda hankali lafiyayye ba zai yarda da wannan ba balantana Shari'ah.

Wallahu a'alamu bissawab

Mu hadu a darasi na biyar (005)insha'allah

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz Juma'at Mosque Bungudu)