🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_003_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *HADARIN DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA*
Hakika Allah (SWT) da manzonsa (SAW) sun tsoratar dangane da hadarin yanke zumunci, suka sanya matsayin yanke zumunci dai dai da Fasadi/barna a bayan kasa.
Allah (SWT) yace to shin kuna fatan idan kun juya daga (umarnin) zakuyi barna a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntarku? Wadannan sune wadanda Allah ya la'anesu, kuma ya kurmantar dasu, kuma ya makantar da ganinsu. *(Suratu Muhammad 22-23)*
An karbo hadisi daga Aisha (R) manzon Allah (SAW) yace zumunta tana rataye da al’arshin Allah. Tana cewa wanda ya sadar dani Allah ya sadar dashi, wanda ya yanke ni Allah ya yankeshi *(Muslim 2555)*
An karbo daga MUD’IM (R) manzon Allah (SWA) yace mai yanke zumunta baya shiga Aljanna *(Muslim 2556)*
Haka nan kuma, an karbo daga Abubakrata, Manzon Allah yace, Babu wani laifi daya can-canta Allah ya gaggauta ma ma'abocin sa uquba tun anan duniya tare da cewa yayi mashi tanadin uqubar a lahira kamar wanda ya yanke zumunta da kuma azzalimi *(Bukhari adabul mufrad 67)*
An karbo daga Abu Huraira; lallai wani mutum yace ya manzon Allah lallai ni ina da yan'uwa kuma ina sadar da zumuntarsu amman suna yanke mani, ina kyautata masu amma suna munana mani, ina yin hakuri dasu amma suna jahiltata? Sai Annabi yace, idan har ka kasance kamar yadda ka fada to lallai kamar kana zuba masu toka ce mai zafi, Allah ba zai gushe ba yana taimakonka akansu matukar ka dauwwama akan haka *(Muslim 2558)* Ma’ana: kamar kana ciyar dasu toka mai zafi saboda abin da suke haduwa dashi na laifi.
Haka nan kuma an karbo daga Abdullahi ibn Amru binul As, Manzon Allah (SAW) yace, bai zama mai sadar da zumunta ba wanda yake so aranka mashi, sai dai mai sadar da zumunta shine wanda idan an yanke mashi, shi yana sadarwa *(Bukhari 541)*
An karbo daga salmanu ibn Amir, Manzon Allah yace, yin sadaka ga miskinai sadakace kamar sauran sadakoki, amma yin sadaka ga dan'uwa tana da darajoji biyu (2) ladar sadaka da kuma ladar sadar da zumunci *(Abu Dawud 2555 da Tirmidhi 658)*
An karbo daga Abu Hurairah yace, lokacin da wannan ayar ta sauka,,, kayi gargadi ga yan'uwanka makusanta, Annabi (SAW) ya kira Quraishawa, suka hadu gaba dayansu, yayi musu wa’azi gaba dayansu kuma yayi ma dai-dai kunsu yace ya Fatima ki tsamar da kanki daga wuta, lallai ni bani wadatar daku a wurin Allah da komai sai dai lallai kuna da wata zumunta da sannu zan sadar da ita *(Muslim)*
ANAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI *SABUBBAN DAKE JANYO YANKE ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868
DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
No comments:
Post a Comment