Thursday, 30 January 2020

005 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*

_005_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

✅ *CIGABA DA BAYANI AKAN SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.*

11. *NISAN WURIN ZAMA DA KUMA KASALAR ZUWA ZIYARA*
Akwai daga cikin mutane wadanda idan gidan su ko garin su yana nesa sai a dinga jin kasalar zuwa ziyartarsu, wanda wannan sai ya nisantasu da yan'uwansu.
Nisan wuri bai kamata ba ya zama dalili na yanke zumunta, musamman wannan zamanin da ake da hanyoyin sadarwa daban daban, Allah ya bamu ikon kulawa da zumunta.

12. *MAKWABTAKA A TSAKANIN YAN UWA*
Da yawa Makwabtaka tana gadar da yankewar zumunta a tsakanin yan'uwa. Umar Dan khaddab yace ku umurci yan'uwanku su dinga ziyartar yan'uwansu amma kada suyi makwabtaka da juna a gidajensu, sannan sau dayawa kusanci a tsakanin gidajen yan'uwa yana haifar da sashen wasu matsaloli wadanda suke haifar da fada a tsakanin 'ya'yansu wanda wannan yakan zarce har zuwa ga iyayensu sai wannan ya haifar da gaba da yanke zumunci a tsakaninsu.

13. *KARANCIN KAUDA KAI DA HAKURI A KANSU:*
Sashen wasu mutane suna da karancin kauda kai da kuma hakuri akan abin da yan'uwansu suka yi masu. Wasu yan'uwan da an samu sabani tsakaninsu ko wani kuskure da ya afku sai su yanke zumunta, su kaurace ma yan'uwansu.

14. *HASSADA:*
   Akwai daga cikin yan’uwa wanda Allah yake azirtawa da ilimi ko wani babban matsayi ko dukiya mai yawa sai ka same shi yana yima yan'uwansa hidima yana kyautata ma su, sannan ka samu sashen yan'uwansa suna nuna masa hassada da kiyayya da haifar da rikici tsakanin shi da su, suna cewa duk abin da yake yi masu ba domin Allah yake yi ba.

15. *YAWAN WASA:*
Lallai yawan wasa (da sunan wai abokin wasa) yana haifar da mummunan abu a tsakanin yan'uwa domin wani yana iya fadar kalma mai muni ga dan'uwansa ba tare da ya kula da hadarinta ba agare shi, wannan sai ya gadar da kiyayya da gaba a tsakaninsu a sanadiyyar wannan Kalmar.

16. *ANNAMIMANCI DA KARBAR GULMA:*
Akwai da yawa daga cikin yan'uwa wadanda dabi'arsu shine yawo da annamimanci a tsakanin yan'uwa domin su kawo rabuwar kai da gurbata tsakanin yan’uwa wanda wannan yana gadar da yanke zumunta, sai dai abu mafi muni shine karbar gulma da yadda da ita shi ke haifar da yankewar zumunta.

17. *SHAGALTUWA DA DUNIYA:* Shagaltuwa da duniya da son yawan tara abin duniya yana hana mutun sadar da zumunta, da kuma samun lokacin ziyartar yan'uwansa da nuna soyayyar shi zuwa gare su.

18. *MIYAGUN HALAYE NA MATAR SHI:*
Wasu daga cikin mutane ana jarabtarsu da muguwar mata mai mummunan dabi’a mai yawan sukar yan'uwansa, bata son yayi mu’amala da yan'uwansa ko wasu, tana dogewa wajan ganin ta raba shi da yan'uwansa tana hana shi ziyartarsu, da sadar da zumunta zuwa garesu, idan yan uwan sa suka ziyarceshi sai tayi ta fushi tana murtike fuska. Bugu da kari akwai mazajen da suke mika ragamar zumuncinsu ga matarsu sai wanda ta yarda dashi yake sadarmawa, wanda bata yarda da shi ba sai ya yanke ma sa.

19. *MANTAWA DA WASU YAN'UWA A LOKACIN WALIMA KO WATA HIDIMA:*            Hakika wani daga cikin yan'uwa yakan shirya walima ko wata hidima ya gayyaci yan'uwansa sai ya manta da wani ko wasu, sai su da ba’a gayyata ba su munana masa zato, su nuna kamar an wulakantasu an zabi wasu wadanda suka fisu, wannan  nasa ya kaurace masu da yanke zumunta a tsakaninsu.
Wadannan sune  kadan daga cikin abubuwan dake janyo kauracewa juna da kuma yanke zumunta. Ya kamata a basu kulawa ta musamman da hattara da fadawa cikinsu.

A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI *ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA*

DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*

#ABBAN_SINAN

https://fb.me/abbansinan

No comments: