KURAKURAI A KIRAN SALLAH
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ ﺍَﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺍَﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ
Gabatarwa:
Dasunan Allah maiyawan rahama
maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su kara
tabbata ga fiyayyan halittar Allah, manzan tsira
Annabi Muhammad da Iyalan Sa da Sahabban
Sa baki daya da wadanda suka bi bayansu da
kyautatawa izuwa ranar sakamako, amin.
Bayan haka, hakika wannan bita da 'yan
uwa suka shirya a Shirin Hasken-Musulunci
anan Minna, fadar Jahar Neja ayau (Alhamis: 4,
ga Ramadan 1432 daidai da 4, Agusta 2011)
lallai tana da matukar muhimmanci musamman
a irin wannan lokaci, wanda yake a fili take irin
gudun mawar da ladanai suke bayarwa a cikin
al'umma baki daya.
Wannan matashiya da zamu tattauna a
kanta maitaken "Kura-Kuran da ake samu a
kiran sallah'' muna fatan ta zama wani abune
da za mu yiwa juna gyara, don gyara kayanka
bai zama sauke mu raba ba, kuma muna so a
wannan haduwa ya zana an magance wadannan
kura-kurai duddacewa ba su ke nanba, amma
har idan muka gane cewa akwai kurakuran
kuma muka dauki hanyoyin gyara to zamu sami
taimakon Allah akai, Allah ya yi mana jagora
amin.
A cikin wadannan kurakurai akwai
wadanda su ke da alaka da maikiran sallah,
akwai kuma wadanda suke da alaka da
ma'anonin kiran sallah ta yadda idan ma'anar ta
canza sai ta maida shi ba kuma kiran sallah ba.
Sannan akwai wadanda suke da alaka da
al'umma baki daya, lalle wanan yana nuna mana
cewa matsayin ladaini a cikin al'umma ba
karamin matsayi bane, muna rokon Allah da
sunayan kyawawa da siffofin sa madaukaka ya
yima jagora amin.
A yanzu za'a dan lissafa wasu daga ciki,
ayi kuma dan karin haske sannan abada
shawarwari.
Akwai wadansu abubuwa da zasu shiga
cikin kura kuran da ake samu a kiran sallah,
kamar:
1. Rashin Kiran Sallah A Farkon Lokacinta:
Kamar yadda malamai suka zayyana bayana a
littafai cewar kiran sallah shi ne: Sanar da
mutane shigar lokacin sallah. Kuma kamar aka
sani kowacce sallah tanada lokacinta kuma
gashi malam ya kara mana bayi ya kuma fito
mana da lokatan fili, wanda rashin kiran sallah a
farkon lokacin ta ya haifar da angama kiran
sallah sai a tada ikama, wanda anasone
tsakanin kiran sallah da tada ikama a sami
tazara ta yadda mara alwala zai yi alwala,
wanda sai ya yi tsarki ya je ya yi tsarki, anan
kenan zamu gane yana daga cikin manyan
ayyukan ladan da lokacin sallah ya yi ya kita
domin ya sanar da al'umma shigar lokacinta.
Babbancin kiran sallah da ikama shine:
Kiran sallah sanar da mutane shigar lokacin
sallah (Ladani kuma shi ya kamata ya fi kowa
tantance lokutan sallah), ita kuma ikama: sanar
da wadanda ke cikin masallaci anfara sallah.
2. Rashin Tantance Lokaci: Ladani ya sani shi
ne mutum na farko da yafi kowa sanin canjin
lokaci da yadda yake karuwa da kuma yadda
yake raguwa, kuma idan zai yi anfani da agogo
kada ya dogara da agogo daya, ya zamana yana
dasu uku ko hudu, rashin wannan wadansu
ladanan suke kiran sallah tsakaddare ko dab da
magariba idan hadari ya rufe rana.
Ladanifa ya sani sallolin mutane da
azuminsu suna ratayene a wuyanshi, miliyoyin
mutane basa shanruwa ko su dakatar da sahur
sai ladan ya kira sallah.
3. Rashin Tsayawa A Koyi Kiran Sallah: wannan
yana daga cikin manyan matsalolin da ake
samu, ta yadda inda za'a kowa ya fadi malamin
da ya koya masa kiran sallah to da anyi zuffa.
Hakan ya haifar da kowa yake yin yadda ya ga
dama, wasuma ka ji da yarukansu suke yi ba da
larabciba.
4. Rashin Tantacce Ladanai A Masallaci:
wannan yasa kowa ya zama ladani, wanda yake
wannan kuwa kuskure ne, wannan baihana a
sami ladanai a masallaci gudaba, su zama biyu
ko uku ko dai gwargwadon abida ya sawwaka
amma tsayyayu, wannan zai sa asan cewa
ladani wane yana kiran sallar asubahine kafin
alfijiri ya keto amma ladani wane sai bayan
alfijiri, kamar yadda ya kasance tsakanin Bilal
da Ibnu ummi maktum Allah ya kara musu
yarda.
5. Rashin Sanin Ma'anonin Kiran Sallah:
wannan ya haifar da abubuwa masu yawa, da
basa cikin addini, misali: Ladani ya kammala
kiran sallah sai yace 'Ayi alwala, a jaddada' inda
yasan ma'anar
ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍَﻟﺼَّﻼَﺓِ، ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍَﻟْﻔَﻼَﺡِ
Hayya alas Swalah, Hayya alal Falah da bai fadi
waccar maganarba.
6. Rashin Kula Da Ladubban Sallah: wannan ya
sa sai kaka ladani yana kiran sallah amma sai
kaga kamar yana wani abu da bashi da alaka da
addini, wani lokacin sai ya yi kamar ya juyawa
alkibla baya.
7. Kura kurai a lafuzza : ana samun kurakurai
masu tarin yawa a lafuzzan kiran sallah.
Wadannan kurakurai sun kashi kashi biyu.
(a) Kuskure mai canza ma'ana: irin wadannan
kura-kurai suna fitar da shi daga kiran sallah
kwatakwata ya zama wani abu daban, misali:
ﺍَﻟﻠﻪُ ﺃَﻛْﺒَﺮُ – ﺃَﻛْﺒَﺎﺭُ
(b) Kuskure na bata lafuzza: wanda yake fitar
da shi daga duniyar larabci, misali:
ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ
Shawarwari:
A takaitaccen wanna jawabi da kuma wadannan
abubuwa dana gani ina bada shwara kamar
haka:
1. Bayar da mintina bayan kiran sallah kafin
tayar da sallah, wannan ko zai tabbatane idan
ankira kowacce sallah a farkon lokacin. Misali
Azahar minti 20 la'asar minti 15 magariba minti
10 lisha minti 15 asuba minti 20.
2. Ladani ya zama yana da agogo kamar uku
banda na wayarshi, kuma ba zaije kiran sallah
ba sai ya duba su duka.
3. Aiki da dukkan abubuwan da aka gabatar a
wannan bita.
4. Gyara inda duk mutum ya ji yana da kuskure.
5. Isar da wadannan bayanai ga wadanda basu
zo wannan bita ba.
6. Ladanai su samara da wata haduwa da zasu
dinga yi lokaci lokaci domin tuntubar juna koda
ko za'a fara a matakin unguwa unguwa ne.
7. Ci gaba da shirya irin wannan bitar lokaci
bayan lokaci
8. Koyon kiran sallah baki da baki daga wurin
malamai masana.
Allah ya gafartamana ya kuma ya fe mana,
Allah ya karbi ayyukammu amin summa amin.
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ
ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar Neja Nijeriya.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. MU KOYI IBADA A SAUKAKE
Sunday, 1 January 2017
KURAKURAI A KIRAN SALLAH
ZAGIN AISHA R.A
*ZAGIN AISHA RADHIYALLAHU ANHAA!!!*
*_Imamu Malik RH yace; "Duk Wanda ya zagi Aisha a kashe shi. Sai aka ce mashi saboda me za'a kashe shi? Sai yace; Duk Wanda ya jefe ta(cewa tayi zina) kamar ya sabama (karyata) Qur'ani ne"._*
```Wannan kuma haka yake, hukuncin duk matsiyacin da ya zagi ummuna Aisha, hukuncinsa kisa kuma dole mu yakeshi.
Haka Qur'ani yace uwarmu ce, duk Wanda bai yarda ummuna Aisha uwarsa bace, toh munsan uwarsa ba ta wuce HAAWUYA, Allah ya tsare uwar mutum ta zama HAAWUYA```
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINAAN)_*
DARIQA
BABBAN DALILIN DA YASA HADIN KAI YAKE WANZUWA TSAKANIN SHI'AH DA DARIQU SHINE; SU YAN SHI'AH BASU ZAGIN TIJJANI DA INYASSI DA SAURAN YAN CUWA-CUWAN WALIYYAI!
SU KUMA A AQEEDARSU INDAI BAZAKA ZAGI JIKAN MANZO(TIJJANI) BA! TOH KO KA ZAGI KAKAN(ANNABI MUHAMMAD S.A.W) KO KAYI MASHI KARYA, KO KA ZAGI ABOKAN SHI, KO KA ZAGI MATANSHI, TOH KAI ABOKIN TAFIYA NE!
WANNAN JAHILCI NAKU YAN DARIQU YAYI YAWA! YA KAMATA KUSAN ME KUKEYI!
KUFA KUKE YABA ABOKAN ANNABI A WURIN MAULIDI! AMMA KUMA SABODA ZINDIQANCI IDAN YAN SHI'AH SUN GAYYACEKU NASU MAULIDIN SAI SU ZAGI ABUBAKAR SU ZAGI UMAR SU ZAGI AISHA SU ZAGI HAFSAT, KUNA ZAUNE SAMAN KUJERU DON KAWAI SUN KAWO MAKU JUICE DA LEMU DA SWAN SANNAN BASU TABA TIJJANI DA INYASSI BA! WANNAN ZINDIQANCI YAYI YAWA, YA KAMA KU FARKA DAGA SUMAR DA KUKAYI!
ALLAH YA TSARE MANA IMANINMU.
ABBAN SINAAN
Hashim Surajo Uba Tsamiya
MASJID ABI HURAIRAH TSAFE
🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌
MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE
*NABIYYUR RAHMAH*
*_MASJID ABI HURAIRAH YAR YARA TSAFE_*
*JERANGIYAR KARATUTTUKAN NABIYYUR RAHMAN.
WANDA MALAM SANI LIMAN TSAFE, (LIMAMIN ABU HURAIRA AREA 2. TSAFE) YA GABATAR A' MASALLACIN ABU HURAIRA YAR'YARA TSAFE, AN SAUKE LITTAFIN CIKIN CASSET ARBA'IN DA (48) ALLAH YA BIYA MALAM AMIN.
Darasi Na 01Nabiyyulrahmah by Malam Sani Liman tsafe
http://darulfikr.com/s/12024
Darasi Na 02 Nabiyyulrahmah
http://darulfikr.com/s/12025
Darasi Na 03 Nabiyyulrahmah
http://darulfikr.com/s/12026
Darasi Na 04NabiyylRahmah
http://darulfikr.com/s/12027
Darasi Na 05NabiyyulRahmah
http://darulfikr.com/s/12028
Darasi Na 06 Nabiyyulrahmah
http://darulfikr.com/s/12029
Darasi Na 10 Nabiyul Rahmah
http://darulfikr.com/s/12032
Darasi Na 12 NabiyulRaham by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12030
Darasi Na 13 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12031
Darasi Na 14 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12034
Darasi Na 15 NabiyulRahmah By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12033
Darasi Na 16 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12035
Darasi Na 17 NabiylRahmah
http://darulfikr.com/s/12036
Darasi Na 17 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12037
Darasi Na 19 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12038
Darasi Na 20 NabiylRahma by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12039
Darasi Na 21 NabiyulRahmah By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12040
Darasi Na 22 Nabiyulahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12041
Darasi Na 23 Nabiyulahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhuraiah
http://darulfikr.com/s/12042
Darasi Na 24 NabiyulRahmah ByMal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12043
Darasi Na 25 NabiyulRahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12044
Darasi Na 26 NabiyulRahmah By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12045
Darasi Na 29 NabiyulRahmah
http://darulfikr.com/s/12049
Darasi Na 30 NabiyulRahma
http://darulfikr.com/s/12046
Darasi Na 31 NabiyulRahma by Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/12047
Darasi Na 32 NabiyuRahmah By Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12050
Darasi Na 39 NabiylRahamah by Mal Sani Liman Tsafe
http://darulfikr.com/s/12053
Darasi Na 40 Nabiyul Rahmah by Mal Sani Liman Tsafe Abuhurairah
http://darulfikr.com/s/12054
Darasi Na 42 NabiulRahma By Mal Sani Liman
http://darulfikr.com/s/12055
Darasi Na 47 NabiyuRama by Malam Sani Liman
http://darulfikr.com/s/12060
Darasi Na 48 NabiyulRahmah By Malam Sani Liman
http://darulfikr.com/s/12061
MUQABALA
*NEW UPDATES 10/08/2016*
*MUQABALA!!!*
Muqabala tsakanin Wani mai suna *TIJJANIYYA INYASSIYYA* account dinshi Na facebook! Tare da number shi: *08094652545*
Sai abokin muqabalar fitinannen yaron nan ta yadda suke cewa wato *HASHIM SURAJO UBA TSAMIYA* da number shi: *08064734911*
Wannan muqabala ta biyo bayan cika bakin da suke yi a shafin sadarwa na Facebook, sai naga ya dace in kirashi domin muyi magana, Na kuma dauki audio domin mutane suyi hukunci da Kansu.
Muqabalar ta farko mai tsawon 01:28:55
👇👇👇👇👇👇
http://kiwi6.com/file/e0gfczbnen
A lokacin da ya gudu sai Na kara kiranshi mukayi mintuna 11:27secs,
👇👇👇👇👇👇👇
http://kiwi6.com/file/50bcae4l2e
sai karshen mai tsawon mintuna 11:39secs
👇👇👇👇👇👇👇👇
http://kiwi6.com/file/50bcae4l2e
Malam yi hukunci da kanka domin fahimtar Wanda ke kan qur'ani da hadisi.
Hashim Surajo Uba Tsamiya
Http://hashim141473.mywapblog.com
Wednesday, 7 December 2016
IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA MAULIDI BA, HASALI YAYI FADA DA ITA...
🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*_IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA BIDI'AR MAULIDI BA, HASALI MA YAYI FA'DA DA ITA_*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_001 Fitowa Na daya_
_Rubutawa:_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
بسم الله الر حمن الر حيم
```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga Wanda babu wani Annabi bayansa, tare da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka;
Nayi nufin yin wannan rubutu ne saboda Wata 'karya dake yawo a kafofin sadarwa na zamani(social medias) akan cewa ibn taimiyya yace Maulidi halas ne, har ma yace akwai lada ga Wanda yayi. Maganar wacce suke sama mata gindin zama a cikin littafin shehin Malamin mai suna((I'KTIDA'UL SIRA'DUL MUSTAQEEM)).
Kafin bada amsa ga maganar ya kamata masu karatu kusan cewa Malamai ba ma'asumai bane! Suna dai dai suna kuskure.
Amma ga wata magana ta ibn Taimiyya akan maulidi;```
قال ابن تيمية-رحمه الله- ((فإن هذا [يعنى الإحتفال بالمولد] لم يفعله السلف مع قيام المقتضى له وعدم المانع منه، ولو كان هذا خير محضا أو راجحا لكان السلف رضي الله عنهم أحق به منا، فإنهم كانوا أشد محبة لرسول الله صلى الله عليه وسلم وتعظيما له منا، وهم على الخير أحرص، وإنما كمال محبته ةتعظيمه في متابعته، وطاعته واتباع أمره، وإحياء سنته باطنا وظاهرا، ونشر ما بعث به، والجهاد على ذلك بالقلب واليد واللسان، فإن هذه هي طريقة السابقين الأولين من المهاجرين والأنصار والذين اتبعوهم بإحسان...)) {اقتضاء صراط المستقيم ص ٣٥٠ دار ابن الهثيم}
_Ma'ana;_ *_"Ibn Taimiyya -Allah yayi masa Rahama- a cikin littafinsa [Iktida'ul siradul mustakim] yana cewa; Lallai wannan (Bukin maulidi) magabata basu aikatashi ba tare da suna da damar yin hakan kuma babu abunda zai hanasu, da wani aikin Alkhairi ne babba ko kuma mafi rinjaye da magabata-Allah ya yarda dasu- su sukafi cancanta su aikatashi fiye damu, domin sun fimu son Annabi Muhammad Tsira da Aminci SU tabbata a gareshi da girmamashi kuma sun fi mu kwadayi ga Alkhairi, to amma abin da ke cikakken so da girmamawa ga Annabi shine bin sunnarsa, da yi masa biyayya da bin umurninsa da rayar da sunnarsa a boye da bayyane da kuma watsa abin da aka aikoshi dashi da kuma yin kokarin yadashi da Alkalami da hannu da kuma halshe, kuma wannan shine tafarkin wadanda suka gabacemu daga cikin muhajiruna da Ansar da wadanda suka bisu da kyautatawa._* [Iktida'u siradul mustakim shafi na 350]
```wannan shine abin da sheikhul Islam Allah yayi masa rahama ya fada game da bukin maulidi, kuma wannan karara yake cewa bidi'ah ne daga cikin bidi'o'i, Wanda yasa dole muyi yaki dashi.
Sai dai yan bidi'ah saboda son rai da son zuciya sun bar wannan magana dake nuna cewa maulidi bidi'ah ne, sunyi riko da Abinda yayi dai dai da son rayuwarsu, kamar yadda dama wannan shine Al'adarsu Qur'an ma yayi bayani a cikin suratul [Ali imran aya ta 7] daman su mutane ne masu son shubuha.
Su kuwa Ahlis Sunnah ba haka suke ba. Imamul wa'ki'i ibn jarrah yake cewa;```
((أهل السنة يكتبون مالهم وما عليهم، وأهل الأهواء يكتبون مالهم)).
[ذم الكلام للهروي ٣٣٨]
_Ma'ana;_ *_"Ahlus sunnah suna rubuta abinda yake hujja a garesu da Wanda yake hujja akansu, amma masu bin son zuciya (YAN BIDI'AH) suna rubuta abinda yake hujja garesu kawai._* [Zammul kalam 338]
```wannan rubutu zai zamo shimfida na warware wannan shubuha, fitowa ta gaba zanyi bayani akan maganar da ibn taimiyya ya fada wanda yan bidi'ah suke ganin cewa hujja ne garesu.
Allah ya karemu daga bin son zuciya da watsi da sunnar Manzon Allah, Allah ya tabbatar da dugaduganmu akan bin sunnah da aiki da sunnah.```
Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
📞08064734911
Http://hashimtsamiya.blogspot.com
atstsamawy@gmail.com
KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KO YANA HALASTA YIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W KO WANI DAGA CIKIN MAGABATA...!!!???*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
_Fitowa ta biyu (002)_
_Rubutawa;_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
*Godiya ta tabbata ga Allah Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah s.a.w da mutanen gidansa da sahabbansa da duk Wanda yabi tafarkinsa da kyautatawa har tashin kiyama.*
_Bayan haka;_
_Nayi rubutu mai irin wannan take Wanda nace fitowa na gaba yana nan zuwa, to kuma insha Allahu zan cigaba da bada hujja akan haramcin Maulidi da kuma zamanshi bidi'ah abar kyama. Manzon Allah s.a.w ya kasance idan zaiyi huduba bayan ya godewa Allah, ya nemi taimakonshi da gafararshi daga karshe sai yace;_
(( أما بعد، فإن خير الحديث كتاب الله وخير الهدي هدي محمد صلى الله عليه وسلم وشر الأمور محدثاتها وكل بدعة ضلالة)).
_Ma'ana;_ *_"Bayan haka; Lallai fiyayyen zance shine littafin Allah, kuma fiyayyar shiriya ita ce shiriyar Muhammad s.a.w, kuma mafi sharrin al'amurra sune wadanda aka kirkiro, kuma dukkan bidi'ah bata ce"_* [Muslim ya ruwaito]
```Bayan wannan; yana daga cikin abunda yasa Malamai suka kyamaci bidi'ar Maulidi; bayan zamanshi bidi'ah, akwai haduwa mata da maza da wake wake da amfani da kayan kid'a (Badujala, piano,...) Da shaye shayen abubuwan dake sa maye, da wasu sharrance sharrance, wani lokaci Abunda yafi wadancan yana faruwa, wato shirka da Allah, ta hanyar wuce gona da iri wajen yabon Manzon Allah s.a.w ko waninsa kamar; Tijjani, Inyassi, jelani, Mahadi, Hussain, yaa Ali, ko waliyi na wheelbarrow. Za kaga ana Addu'ah ana Neman agajinsu da taimakonsu ko fadar cewa Annabi Muhammad s.a.w yasan gaibi ko wani daga cikin waliyyai, wadannan abubuwa duk zaka samu suna faruwa a wajen Maulidi. Shi kuwa Annabin Rahama s.a.w cewa yayi;```
((إياكم والغلو في الدين، فإنما أهلك من كان قبلكم الغلو في الدين)).
_Ma'ana;_ *_"Ku kiyayi yin shishshigi a cikin Addini, saboda babu wani Abu Wanda ya hallaka wadanda suka gabace ku face shishshigi a cikin addini._*
A wani Hadisin Manzon Allah s.a.w cewa yayi;
((لاتطروني كما أطرت النصاري ابن مريم إنما أنا عبد فقولوا: عبدالله ورسوله))
_Ma'ana;_ *_"Kada Ku zurfafa wajen yabo gareni kamar yadda kiristoci suka zurfafa wajen yabo ga Dan Maryam(Annabi isah) ni bawa ne kawai, saboda haka kuce; bawan Allah kuma manzon Allah._* [Bukhari ya ruwaito]
```Abin mamaki shine zaka samu da yawa daga cikin mutane suna kokari wajen halartar wadannan tarurrukan na bidi'ah, kuma suna kare masu yinsu, amma kuma sai kaga basa halartar wuraren Neman ilimi, Inda za'a nuna maka yadda zakabi Allah da Manzonsa ba inda za'a nuna maka falalar karya ta waliyyan karya ba. Babu shakka wannan yana daga cikin raunin imani da kuma karancin basira, kuma yana nuna cewa tsatsa ta rufe zukatansu ta nau'o'in zunubai da sabon Allah.
Allah ya karemu daga fadawa cikin shirka da bidi'ah da bata.
SUNNAH SAK
BIDI'AH SAM
MAULIDI SAM SAM SAN SAM SAM
Wa'ka:
DA MAULIDI NE ALAMAR SON MANZO
DAN FODIO DA BA ZAYA CE MAR BIDI'AH BA.```
Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*
📞08064734911📞
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya
Http://hashimtsamiya.blogspot.com
atstsamawy@gmail.com