KURAKURAI A KIRAN SALLAH
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ ﺍَﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺍَﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ
Gabatarwa:
Dasunan Allah maiyawan rahama
maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su kara
tabbata ga fiyayyan halittar Allah, manzan tsira
Annabi Muhammad da Iyalan Sa da Sahabban
Sa baki daya da wadanda suka bi bayansu da
kyautatawa izuwa ranar sakamako, amin.
Bayan haka, hakika wannan bita da 'yan
uwa suka shirya a Shirin Hasken-Musulunci
anan Minna, fadar Jahar Neja ayau (Alhamis: 4,
ga Ramadan 1432 daidai da 4, Agusta 2011)
lallai tana da matukar muhimmanci musamman
a irin wannan lokaci, wanda yake a fili take irin
gudun mawar da ladanai suke bayarwa a cikin
al'umma baki daya.
Wannan matashiya da zamu tattauna a
kanta maitaken "Kura-Kuran da ake samu a
kiran sallah'' muna fatan ta zama wani abune
da za mu yiwa juna gyara, don gyara kayanka
bai zama sauke mu raba ba, kuma muna so a
wannan haduwa ya zana an magance wadannan
kura-kurai duddacewa ba su ke nanba, amma
har idan muka gane cewa akwai kurakuran
kuma muka dauki hanyoyin gyara to zamu sami
taimakon Allah akai, Allah ya yi mana jagora
amin.
A cikin wadannan kurakurai akwai
wadanda su ke da alaka da maikiran sallah,
akwai kuma wadanda suke da alaka da
ma'anonin kiran sallah ta yadda idan ma'anar ta
canza sai ta maida shi ba kuma kiran sallah ba.
Sannan akwai wadanda suke da alaka da
al'umma baki daya, lalle wanan yana nuna mana
cewa matsayin ladaini a cikin al'umma ba
karamin matsayi bane, muna rokon Allah da
sunayan kyawawa da siffofin sa madaukaka ya
yima jagora amin.
A yanzu za'a dan lissafa wasu daga ciki,
ayi kuma dan karin haske sannan abada
shawarwari.
Akwai wadansu abubuwa da zasu shiga
cikin kura kuran da ake samu a kiran sallah,
kamar:
1. Rashin Kiran Sallah A Farkon Lokacinta:
Kamar yadda malamai suka zayyana bayana a
littafai cewar kiran sallah shi ne: Sanar da
mutane shigar lokacin sallah. Kuma kamar aka
sani kowacce sallah tanada lokacinta kuma
gashi malam ya kara mana bayi ya kuma fito
mana da lokatan fili, wanda rashin kiran sallah a
farkon lokacin ta ya haifar da angama kiran
sallah sai a tada ikama, wanda anasone
tsakanin kiran sallah da tada ikama a sami
tazara ta yadda mara alwala zai yi alwala,
wanda sai ya yi tsarki ya je ya yi tsarki, anan
kenan zamu gane yana daga cikin manyan
ayyukan ladan da lokacin sallah ya yi ya kita
domin ya sanar da al'umma shigar lokacinta.
Babbancin kiran sallah da ikama shine:
Kiran sallah sanar da mutane shigar lokacin
sallah (Ladani kuma shi ya kamata ya fi kowa
tantance lokutan sallah), ita kuma ikama: sanar
da wadanda ke cikin masallaci anfara sallah.
2. Rashin Tantance Lokaci: Ladani ya sani shi
ne mutum na farko da yafi kowa sanin canjin
lokaci da yadda yake karuwa da kuma yadda
yake raguwa, kuma idan zai yi anfani da agogo
kada ya dogara da agogo daya, ya zamana yana
dasu uku ko hudu, rashin wannan wadansu
ladanan suke kiran sallah tsakaddare ko dab da
magariba idan hadari ya rufe rana.
Ladanifa ya sani sallolin mutane da
azuminsu suna ratayene a wuyanshi, miliyoyin
mutane basa shanruwa ko su dakatar da sahur
sai ladan ya kira sallah.
3. Rashin Tsayawa A Koyi Kiran Sallah: wannan
yana daga cikin manyan matsalolin da ake
samu, ta yadda inda za'a kowa ya fadi malamin
da ya koya masa kiran sallah to da anyi zuffa.
Hakan ya haifar da kowa yake yin yadda ya ga
dama, wasuma ka ji da yarukansu suke yi ba da
larabciba.
4. Rashin Tantacce Ladanai A Masallaci:
wannan yasa kowa ya zama ladani, wanda yake
wannan kuwa kuskure ne, wannan baihana a
sami ladanai a masallaci gudaba, su zama biyu
ko uku ko dai gwargwadon abida ya sawwaka
amma tsayyayu, wannan zai sa asan cewa
ladani wane yana kiran sallar asubahine kafin
alfijiri ya keto amma ladani wane sai bayan
alfijiri, kamar yadda ya kasance tsakanin Bilal
da Ibnu ummi maktum Allah ya kara musu
yarda.
5. Rashin Sanin Ma'anonin Kiran Sallah:
wannan ya haifar da abubuwa masu yawa, da
basa cikin addini, misali: Ladani ya kammala
kiran sallah sai yace 'Ayi alwala, a jaddada' inda
yasan ma'anar
ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍَﻟﺼَّﻼَﺓِ، ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍَﻟْﻔَﻼَﺡِ
Hayya alas Swalah, Hayya alal Falah da bai fadi
waccar maganarba.
6. Rashin Kula Da Ladubban Sallah: wannan ya
sa sai kaka ladani yana kiran sallah amma sai
kaga kamar yana wani abu da bashi da alaka da
addini, wani lokacin sai ya yi kamar ya juyawa
alkibla baya.
7. Kura kurai a lafuzza : ana samun kurakurai
masu tarin yawa a lafuzzan kiran sallah.
Wadannan kurakurai sun kashi kashi biyu.
(a) Kuskure mai canza ma'ana: irin wadannan
kura-kurai suna fitar da shi daga kiran sallah
kwatakwata ya zama wani abu daban, misali:
ﺍَﻟﻠﻪُ ﺃَﻛْﺒَﺮُ – ﺃَﻛْﺒَﺎﺭُ
(b) Kuskure na bata lafuzza: wanda yake fitar
da shi daga duniyar larabci, misali:
ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ
Shawarwari:
A takaitaccen wanna jawabi da kuma wadannan
abubuwa dana gani ina bada shwara kamar
haka:
1. Bayar da mintina bayan kiran sallah kafin
tayar da sallah, wannan ko zai tabbatane idan
ankira kowacce sallah a farkon lokacin. Misali
Azahar minti 20 la'asar minti 15 magariba minti
10 lisha minti 15 asuba minti 20.
2. Ladani ya zama yana da agogo kamar uku
banda na wayarshi, kuma ba zaije kiran sallah
ba sai ya duba su duka.
3. Aiki da dukkan abubuwan da aka gabatar a
wannan bita.
4. Gyara inda duk mutum ya ji yana da kuskure.
5. Isar da wadannan bayanai ga wadanda basu
zo wannan bita ba.
6. Ladanai su samara da wata haduwa da zasu
dinga yi lokaci lokaci domin tuntubar juna koda
ko za'a fara a matakin unguwa unguwa ne.
7. Ci gaba da shirya irin wannan bitar lokaci
bayan lokaci
8. Koyon kiran sallah baki da baki daga wurin
malamai masana.
Allah ya gafartamana ya kuma ya fe mana,
Allah ya karbi ayyukammu amin summa amin.
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ
ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar Neja Nijeriya.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. MU KOYI IBADA A SAUKAKE
Sunday, 1 January 2017
KURAKURAI A KIRAN SALLAH
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment