HUKUNCIN JININ
ISTIHALA ( JININ CIWO)
Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su
tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban
shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jinin istihala wato
jinin ciwo, saboda baya amsa jinin al'ada wato
jinin haila haka kuma ba amsa sunan jinin biki
wato jinin haihuwa kenan, wato kenen shi
wannan jinin ba jinin al'ada bane ba kuma jinin
haihuwa bane saboda haka baya dauke da
hukunce-hukuncensu, baya hana sallah da
azumi da saduwa kamar yadda wadancan suke
hanawa.
Matashiya: Domin yin kandagarki yana da
matukar kyau da tsari mace ta lura da abubuwa
kamar haka:
(1) Launin Jininta: Ta yi kokari ta gane launin
jininta na al'ada wanne kala yake zuwa mata
'Baki ne ko Ja'.
(2) Lokacin Zuwa: Shin al'adarta tana zuwa
mata ne a farkon wata ko tsakiyarsa ko karshe.
(3) Kwanakinsa: Kuma ta kiyaye kwanaki nawa
yake zuwa mata a duk lokacin da take al'ada.
(4) Shinshina: Wato yanayinsa yana da karnine
ko wari.
Dukkanin wadannan abubuwa ana bukatar ta
gane su kuma ta fahimcesu tun lokaci da take
lafiya, -Allah ya sawwake – domin idan jini ya ci
gaba da zuwa saboda ciwo da wadannancan
bayanai za'a yi aiki domin a gano mata
kwanakin jininta na al'ada da kuma kwanakin da
suke na rashin lafiya.
Jinin Istihala : Shine ballewar jini ba'a
lokacinsaba, ta wata jijiya da ake kira 'Azil' .
Al'amari mai jinin Istihala al'amarine mai
rikitarwa domin yadda jinin al'ada yake kama da
jinin istihala, to idan jinin ya kasance yana zuba
a koda yaushe ko mafi yawancin lokaci to a irin
wannan lokaci me zata yi la'akari da shi a
matsayin al'ada me kuma zata yi la'akari da shi
a matsayin jinin istihala ta yadda ba zatabar
azumi da sallah ba saboda shi? Domin mai jinin
istihala ana mata hukunci mata masu tsarkine,
kada a manta ya kandauki mace tsawan
shekaru ko watanni ba al'amarine da za'a yi
wasa da shi ba. La'akari da wannan bayani lalle
mace mai jinin istihala tanada yanayi guda uku:
Yanayi Na Farko: Ya kasance dama tanada
lissafin tsarin al'adarta kafin wannan ciwo na
zubar jini ya sameta, kamar ace dama ta
kasance kafin jinin istihala tana al'adane tsawan
kwanaki biyar ko takwas missali a farkon wata
ko a tsakiya kuma ta san adadin lokacin, to
wannan zata zauna ne a matsayin mai al'ada
gwargwadon yadda ta saba, sai ta bar sallah da
azumi domin a wannan lokacin ana mata
hukuncin mace mai jinin al'ada, idan al'adar ta
dauke (Kwanakin da ta kaddarasu cewa sune na
al'adar) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah, sai
ya zama jinin da ya ci gaba da zuwa jinin
istihalane ba jinin al'adaba, kamar yadda
Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi) yace ma Ummu Habiba '' Ki
zauna gwargwadon da al'adarki take zuwa,
sannan sai ki yi wanka ki kuma yi sallah'' , Muslim
334, hakanan kuma Ma'aikin Allah (Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi) ya fadawa
Fatima diyar Abu Hubaish cewa : ''Ai wannan
wata jijiyace, ba al'ada bace idan lokacin al'adarki
ya iso sai ki bar sallah'' Bukhari 228 , Muslim
333 .
Yanayi Na Biyu: Idan ya zama bata da wani
yanayi sananne saidai jinin nata ana
banbanceshi yana dauke da siffar jinin al'ada,
kamar ya kasance baki ko mai kauri ko ya
kasance yana da wata shinshina amma sauran
baya kama da siffar jinin al'ada, kamar ya
kasance jaa amma bashi da shisshina kuma
bashi da kauri, to a irin wannan yanayi za ta yi
la'akari da jinin da yake dauke da siffar jinin
al'ada a matsayin jinin al'ada sai ta bar sallah
da azumi…' sai kuma ta yi la'akari da wanda ba
shiba jinin ciwone bana al'adaba, sannan sai ta
yi wanka idan wannan jinin da yake dauke da
siffar jinin al'adar ya dauke, daga nan kuma sai
ayi mata hukuncin mace mai tsarki, kenan sai
ta ci gaba da sallah da azumi…' ko dako jinni na
zuba, kamar yadda Ma'aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya fadawa
Fatima diyar Abi Hubaish:
'' Idan ya kasance jinin al'ada, shifa jinine baki
akasanshi, to sai ki dakatar da sallah, idan kuma
dayanne sai ki yi alwala ki yi sallah'' . Abu Daud
286, Nasa'I,220, Ibnu Hibban 1348.
Yanayi Na Uku: Idan ya kasance bata da wani
abu da take gane jinin al'ada da shi, kuma babu
wata siffa da take banbance jinin al'ada da
wanda ba na al'adaba, to anan zata yi la'akarine
da mafi yawan kwanakin al'ada a kowanne wata
wato kwanaki shida ko bakwai, domin wadannan
kwanakin sune mafi yawan kwanakin da mata
suke al'ada, wannan ko saboda hadisin
Hamnatu diyar Jahash Ma'aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi:
'' Abin sani kawai wannan (Jinin ciwon)
wani zungurine daga shaidan, saboda haka sai ki
yi al'adarki kwana shida ko kwanaki bakwai,
sannan sai ki yi wanka, idan kika tsarkaka sai ki
yi sallah kwanaki ashirin da hudu ko ashirin da
uku, kuma ki yi azumi ki yi sallah, yin haka ya
isarmiki, haka za ki dinga yi kamar yadda mata
suke al'ada'' . Tirmizi: 128, Abu Daud: 287, Ibnu
Majah: 627.
Atakaice: Idan aka yi la'akari da bayan da
suka gabata za mu fahimci cewa; mai yanayi
tabbatacce zata yi anfani da wannan yanayin
ne, wacce take abinda take banbance al'ada da
jinin da ba na al'adaba za ta yi anfanine da
wannan, amma wacce bata da wata alama to
za ta yi al'ada kwanaki shida ko bakwai.
Abinda kan mai jinin istihala (jiwo): Dudda
cewa a hukumce mace mai jinin istihala wato
jinin ciwo macece mai tsarki dudda cewa jinni
na tare da ita alokaci, saboda haka za ta yi lura
da abubuwa kamar haka:
1. Ya zama wajibi ta yi wankan daukewar jinin
al'ada bayan wucewar kwanakin da aka yi
la'akari da su a matsayin jinin al'ada.
2. Za ta wanke gabanta domin gusar da abinda
ya fita alokacin kowacce sallah.
3. Za ta sanya auduga ko makamancinta a
gabanta domin hana shi diga kasa, wato zata yi
kunzugu kenan.
4. Za ta dinga yin al'awala a kowacce sallah,
kenan ba zata yi salloli biyu da al'awala dayaba,
saidai idan ramuwace, Allah kadai shine masani.
Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka
gabata ya bayyana a fili yadda musulunci ya
kula sosai kan abinda ya shafi hukunce-hukunce
jinin dake samun mata, kama daga jinin al'ada
jinin biki har zuwa wannan jinni na istihala wato
jinin ciwo, kuma wannan yana nuna
muhimmancin al'ummar muslmi su tashi tsaye
domin sanin wannan al'amari musammanma
mata, kuma daga nana za mu dasa aya akan
abinda ya shafi tsarki za kuma mu shiga abinda
ya sahafi Sallah da izinin Allah.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja, Nijeriya.