Sunday, 1 January 2017

HUKUNCE HUKUNCEN ALWALA

HUKUNCE-HUKUNCEN
ALWALA

Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman kanta
wacce Allah madaukakin sarki ya sahar'antata
kafin gabatar da wadansu ibadu musammamma
sallah, mutum yana samun cikakken ladan
alwala idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin
sarki ya saukar da hukunce-hukuncen alwala a
cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan
kuka ta shi za ku yi sallah to ku wanke
fuskokinku da hannayanku zuwa gwiwar hannu
ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa
idan sawu (idan kafa)…'' Suratu Ma'ida, aya ta: 6.
Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin
alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi anwanke ko
kuma anshafa, sannan kuma ayar ta iya kance
ko wanne mahalli, sannan kuma Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
ya bayyana siffar yadda alwalar take da
maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake
gamsasshan bayani.
Ka sani lalle ita wannan alwala tanada falala da
kuma sharudda da kuma farillai sannan tana da
sunnoni da kuma mustahabbai, sharuddannan
da farillai tabbas a tabbata ansame alokacin
gabatar da alwala iya gwargwado domin da
sune alwala zata zama karbabbiya, amma su
sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne ta
inda matsayinsu bai kai matsayin sharuddai da
farillaiba.
Falalar Alwala: Dudda cewa alwala wajibice
wannan kadai ya isheta samun matsayi a
musulunci domin dukkan abinda akace farillane
to wannan matsayi ne me zaman kansa, bayan
hadisi na 62 a cikin Muwadda'u Malik yana
cewa: '' An karbo daga Abdullahi As-Sunaabihi,
lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi yace:
''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi
kuskurar baki dukkanin laifukan dake bakin sun
fice, idan kuma ya face laifukan (Day a shaka)
sun fice, to idan kuma ya wanke fuskarsa
laifukan da ke fuskar ta sa sun fice, har wadanda
ke karkashi girar shi, idan ya wanke hannayansa
laifukan dake hannayansa sun fice, har wadanda
ke karkashi faratansa (jam'in farce), to idan
kuma ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun
fice har wadandake kunnuwansa, to idan kuma
ya wanke kafafuwansa duk laifukan dake
kafafuwan nasa sun fice, har wadanda ke
karkashi farcen kafafun nashi. Sannan kuma
tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya zama wani
karine da yake da shi''.
Lalle wannan bakamar falala bace da alwala
take da shi, domin mai alwala zai kasance yana
kammala alwala zunubanshi suna digewa a
kasa, amma gudu ba hanzariba wannan ladan
zai tabbata ne ga wanda ya yi alwala da
shara'a ta tabbatar da ita ba wacce ya tsinta a
kan titi ba.
Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala sune
abubuwan da ake so mai alwala ya cika su
kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:
(1) Musulunci , kenan idan wanda ba musulmiba
ya yi alwala bata yi ba.
(2) Hankali , idan mahaukaci ya yi alwala itama
bata yi ba.
(3) Wayau , idan dan karamin yaro mara dabara
ya yi bata yi ba.
(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya zama
ruwane mara tsarki to alwalar bata yi, bayanai
sun gabata akan hukunce-hukuncen ruwa.
(5) Ruwan ya zama na halas, idan ruwane da
mutum ya sata ko ya same shi bata shar'an
tacciyar hanyaba to alwalar bata yi ba.
(6) Ya kasance mai tsarki , idan mai alwala ya
kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato
ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi
alwalar bata yi ba.
(7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga,
kenan idan mutum ya kasance yaba sanye da
wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki
to dolene ya cire shi, kamar tabo (laka)…'.
Farillan Alwala :
(1) Niyyah: Domin a banbance wanda ya sa
ruwa donin sanyaya jiki, ko domin gusar da
datti, duk wannan ba niyyace ta alwalaba.
(2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta bangaren
tsawo tana farawane daga matsirar gashin kai
(banda sanko) zuwa karshen mukamiki, amma
ta fuskar fadi tana farawane daga kunnan dama
zuwa kunnan hagu, wannan shine abinda yake
amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar
ko ina ya sami ruwa kamar kasan haba, gefan
ido da gefan kunne da matsa-matsin karan
hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu
kamar alwalar yarace.
(3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu. Mai
alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke
hannayansa tun daga saman yatsunsa (farce-
akaifa) harzuwa gwiwar hannu ya tabbata
gwiwar ta shiga inda ya wanke, anamma akwai
manya masu alwalar yara.
(4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada yatsunka
sannan kuma ka fara shafar daga goshi (daidai
matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya.
(5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya
tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon sawu,
wato wadannan kasusuwan guba biyu dake
gefan kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.
(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya
cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya
shiga ko ina.
(7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine
alokacin da ka fara alwala to ka dakatar da
komai sai ka kammala, amma kana alwala kana
kuma wata sabga daban wannan bai yi ba.
Mai alwala ya tabbata ya gabatar da
wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta
yadda idan aka rasa daya daga cikin su to
alwalarsa ta shiga hadari.
Sinnonin Alwala:
(1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A Ruwa.
Ta yadda mai alwala zai karkato butar alwala
domin ya wanke hannayansa zuwa Ku'u wato
wuyan hannu.
(2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata ya
sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya kada
ruwan a baki, wannan shi ake kira da kuskurar
baki.
(3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya shaki
ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai, sai dai
kawai idan yana azumine sai yayi kadan. Amma
yadda mutane suke shafar hancinsu wai da
sunan shaka ruwa wannan baiba.
(4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne da
hannun dama sai ya sa hannun haku akan
karan hancinsa, sannan sai ya fyato ruwan da
ya shaka.
(5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata ya
shafi cikin kunnensa da wajan kunnan, zaka/ki
sanya yatsanka 'yar-manuniya a cikin kunnan
sannan ka babban yatsa a wajan kunnan
sannan sai ka shafa, Dirkashi!.
(6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka shafi
kunne shin zaka shafi kunnanne da ragowar
danshin hannuka da ka yi shafar kai da shi? Ko
ko zaka sake taba ruwa na musamman domin
shafar kunne, malamai sun karawa juna san, ko
wanne ka yi ya yi daidai.
(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka fahimta,
ita shafar kai farillace, amma dawo da shafar
kai sunnace daga cikin sonnonin alwala.
(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka kawosu
daya-bayan-daka kamar yadda aka lissafosu,
kada ka dauki na uku ya zama shine na farko
sannan ka biyo shi dana biyar, misali…'.
Wadannan matsayisu bai kai matsayin farillaiba,
amma suna cikin manyan abubuwan da suke
cika alwala.
Mustahabban Alwala:
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni,
kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na
gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su,
domin kowannanmu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalliya, to ko tunda hakane bai
kamata yace ai wannan mustahabbine ya
daukeshi kamar wani kankanin abu.
Su mustahabban alwala suna da yawa, amma
yanzu ga kadan daga cikinsu:
(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'' , adaidai
loakcin da zaka fara alwala, amma idan mutum
ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna
bakomai sai ya yi a lokacin.
(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma
kamar haka:
ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍَﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ،
ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍَﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ
ﻣِﻦَ ﺍَﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻳﻦَ .
Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu abinbauta da
cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma manzansa ne,
Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan
tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman
tsarkaka.''
(3) Karanta Ruwa : Bawai ana nufin mai alwala
ya shasshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar
ya yi anfani da ruwa amma kada ya malalar da
shi, domin yana daga cikin tsarin musulunci
tattali da tsimi da tanadi.
(4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma dama ya
gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da
busasshe, idan bai samuba sai ayi da yatsa,
amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma
daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin
sallah ya yi kuma amma yana da alwala to
abinda ake so shine ya yi asuwaki.
(5) Wuri Mai Tsarki : An so inda zaka yi alwala
ya zama wurine mai tsarki.
(6) Dama Kafin Hagu : abin nufi shine ka fara
wanke hannun dama kafin hannun hagu,
hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta
dama.
( 7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce sunnah
tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da
kuskurar baki kafin shaka ruwa.
(8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke wuraran
da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau
uku zai zama mustahabbine idain wankewar
farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata
gamaba to ta biyu tananan amatsayin wajibi,
haka namma idan ta biyun idan bat agama ba
to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama
wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai
ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare
da barnaba. Amma shi kais au daya ake
shafarsa, ba'a shafar kai sau uku. Sannan kuma
mutum ya tabbata a wadannan wankewa da
akace ya yi sau uku bai kara akan hakan ba, ya
yi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.
Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai
sun mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai
mata su sani gashin kansu da sangalin
hannuwansu duka al'aurane, saboda haka bai
halatta su bayyanar da su ga maza, ken an idan
zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kawwame
kanki.
Wadannan bayanai da suka gabata zasu
haskaka mana yadda alwala take, amma hanya
mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani
domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an
tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala
sai yasa aka kawo mishi butar alawala ya yi
musu ita a aikace, yace kuma irinta ma'aikin
Allah ce.
Anan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a
dana sauran masallatai da kuma malamai a
jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a
sakandare da firamare da malaman islamiyyu da
malamai masu karantarwa a masallatai da
masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa
da su karantar da mutane ita wannan alwalar a
aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya, kada
ka ga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a
aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada
hakan, ita ibada sai an koyawa mutum ba wai
daka kawai shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi
iyaye da kakanni duk musulmai ne sabo da haka
ba sai ya koyaba, duk wannan maganace ta
wanda yake nesa da makaranta, kai da ganin
alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah
ya karba mana ibadummu.
Kammalawa: Lalle wadannan bayanai sun
kara tabbatar mana ashe alwa abace da sai an
tashi tuku domin a koyeta tana da falala da
kuma sharudda sannan ga farillai da sunnoni da
kuma mustahabbai, lalle ka nana bukatar
malamai daga kowanne bangare su tashi tsaye
su karantar da al'umma wannan ibada a aikace,
domin a gudu tare a tsira tare.

No comments: