Sunday, 1 January 2017

NAJASA DA HUKUNCE HUKUNCETA A MUSULUNCI

NAJASA DA HUKUNCE-
HUKUNCENTA

Bayanda a darasin da ya gabata aka kawo
bayanai da suka shafi ruwa, a yanzu za'a kawo
abubuwan da ake yi da ruwan, akan haka za'a
fara da najasa da yadda ake gusar da ita da
ruwa da sauran hukunce hukuncen ita najasar,
Allah Ya yi mana jagora amin.
Abubuwan Da Suke Najasa:
Na farko: Fitsari. (Na mutum) Na babba ko na
karami na mace ko na namiji, ya fara cin abinci
ko bai faraba. Na biyu: Bayangida (Kashi na
mutum). Na uku: Mushe, shine abinda ya mutu
da karan kansa, ko aka yankashi ta hanyar da
bata musulunci ba. Na hudu: Nonon dabbar da
ta yi mushe. Na biyar: Nonon dabbar da aka
haramta cin ta, kamar nonon karya, ko alade ko
jaka...' Na shida: Fitsarin dabbar da aka
haramta cin ta, kamar fitsarin jaki, ko kare…' Na
bakwai: Kashin dukkanin dabbar da aka
harantata, kamar kashin alade (alhanzir), kashin
jaka/jaki..' Na takwas: Kashi da fitsari na
dukkanin dabbar da take cin najasa. Na tara:
Giya. Na goma: Jini, saboda haka bai halatta a
tari jinin da aka yanka dabba ba wai ace za'a
gasa shi ko a soya ko ayiwa dabbobi abinci da
shi ba domin najasa ne (in banda jinin da ake
samu a cikin dabba bayan anyankata wanda bai
fitaba, ai dakyar a rasa jini a cikin dabba). Na
sha-daya: Ruwan ciwo. Na sha-biyu: Maziyyi,
shi kuma ruwane da yake fari yana da laushi
yana fitane lokacin motsawar sha'awa ta mace
ko namiji ta hanyar wasa ko kallo ko nitsewa
cikin tunani, amma idan sha'awa ta kara
karkafafa to maniyyine ke fita, shi kuma
maniyyi ana jin fitarshi sabanin maziyyi, sannan
shi kuma maniyyi yana da kauri sabanin maziyyi
shi yana da laushine, bayanai za su zo akan shi
nan gaba kada idan Allah Ya yarda. Na sha-uku:
Wadiyyi, shi kuma ruwane fari yana kauri sau da
yawa yana fine akarshen fitsari, ta sanadiyyar
daukar kaya mai nauyi, ko matsanancin sanyi,
ko kullewar ciki. Na sha-hudu: Ragowar ruwa ko
aminci na dabbar da ba'a ci, kamar rowan da
jaki ya sha ya raje, in banda mage. Na goma
sha-biyar: Yawun kare da na alade, ko na
dukkan babbar da ta samu ta hanyar su. Na
goma sha-shida: Amai, alokacin da canza daga
yanayin abinci, kenan idan aka ci abin ci yanzu
sai kuma aka harar da shi wannan harawwar ba
najasa bace. Wadannan sune abubuwan da suke
najasa, amma akwai wadansu da malamai suka
karawa juna sani akansu kan najasa ne ko ba
najasa ne ba, kamar ragowar ruwa na wanda ba
musulmi bane ya sha, hakanan akan maniyyi.
Shidai Maniyyi na namiji: Ruwa ne da yake
fari maikauri yana tunkudar junansa alokacin da
zai fita, idan ka shinshina shi ya yi kama da
hudar dabino, kuma ya yi kusa da kanshin kulli,
amma idan ya bushe yana kasancewa kamar
karnin fasasshan kwai. Wannan shine galibin
yadda maniyyin namiji yake kasancewa, wani
lokacin ya kanzo sabanin wadannan bayanai da
suka gabata. Yana fitane lokacin matsananciyar
sha'awa ta sanadiyyar kallo ko wasa ko
matsanancin tunani ko lokacin saduwa. Shi
kuma Maniyyin mace, shi ma: Ruwane fatsi-fatsi
yana da laushi. Wannan ya tabbatar da cewa
mace ma tana da maniyyi kuma da shi ne da na
namiji Allah Yake halitta da su.
Wasu malamai sunce maniyyi najasa ne
domin yana fitane ta mafitar fitsari wanda yake
shi kuma fitsari najasane, wasu malaman kuma
sukace ba najasa bane domin da shi ne Allah
Ya halicci dan'adam kuma a cikinsu akwai
Annabawa da Manzanni, kenan ya za'a mutum
da Allah ya karramashi da yaukaka shi har ya
fitar da Annabawa da Manzanni ace kuma da
najasa aka yi shi??. Wadannan sune abubuwan
da suke najasa da kuma wadanda malamai suka
yi wa juna Karin fahimta.
Hukuncin Najasa:
Wajibine gusar da najasa daga jiki da tufafi da
wurin da za'a yi sallah, idan mutum yana da
ikon gusar da ita kuma yana sane bai gusar da
ita dinba ya yi sallah da ita to ba shi da sallah.
Addinin musulunci addinin tsaftane abinda
musulunci yake so shine akoda yaushe ka
sance cikin tsarki, mafificin tsarki kuma shi ne
tsarkin zuciya a kakkabeta daga barin shirka da
zalinci da hassada da munafunci da dukkan
wata mummunar dabi'a, idan aka samu tsarkin
zuciya kuma ga tsarkin tufafi da ganganjiki da
kuma mahalli to lalle wannan shi ke nuna
kammaluwar mutum.
Yadda Ake Gusar Da Najasa:
Idan ka ga inda najasar take a jikinka ko a
tufafinka to iya inda yake iya nan zaka kama ka
wanke, sabanin yadda wasu matan suke yi wai
dukkanin tufafin da tasa alokaci da take al'ada
to sai ta wanke su, kama daga dankwali da zani
da riga…' wannan musulunci bai zo da shi ba,
inda kwai kika ga jini iya nan kawai za ki
wanke. Idan kuma najasar ta rikice maka baka
ganta ba, amma ka tabbata akwaita ajikin
tufafin na ka shikenan sai ka wanke tufafin
gabadaya. Amma idan najasa ta fantsamo sai
kake kokwanton ta tabaka ko bata taba ka ba,
kuma kai baka ganta ba kuma ka duba mai
Ahlari yace sai ka yayyafa ruwa a wurin.
Amma kuma idan wani abu ya fallatso maka
sai kake kokwanto wannan abun najasane ko ba
najasa ba ne, to awannan lokaci ba wani
hukunci akanka, ba yayyafa ruwa ballantana
wankewa, domin mafiyawan abubuwa masu
tsarki ne, najasa kadanne shi yasa ake iya
lissafe su.
Idan inda najasar take kuma filine ko bango
ko wani dutse sai aka yi ruwan sama ko kuma
aka kwarara ruwa mai tsarki akai shikenen an
gusar da wannan najasar. Amma idan ta kasace
yawun karene wato karene ya baki a kwano ko
a kwarya to za'a zubar da abinda yake ciki
sannan a wanke sau bakwai sannan asa kasa a
daya daga cikin bakwai din. Amma najasar da
ba wannan ba sai a wanke ya wanku sabanin
yadda ake yi, da yaro ya yi fitsari sai ace wai
za'a yayyafa ruwa alhali wankewa akace a yi,
wani ruwamma da aka yayyafa kamar karawa
fitsarin yawa aka yi, Allah ya sawwake. Ya
zama wajibi a tshi tsaye a gusar da najasa a
tsaftace muhalli, musulmi ya kasance
tsaftattace tsafta cikon addini ai ta fi ace ita
ciko ce, ita sharadice sai mutum ya tsarkaka
daga wadannan najasar ibadar shi zata karbu.
Abubuwan Da Najasa Take Hanawa:
Anan za'a anbaci wadansu abubuwa ne da basu
halatta ga dukkan mara tsarki ya aikata su
saboda darajarsu da matsayinsu, kuma hadasin
babbane ko karami, wadannan abubuwa sune:
(1) Taba Alkur'ani: Bai halatta ga mara tsarki
ya taba Alkur'ani, har sai ya yi tsarki inda so
samune ma ya yi alwala musamman idan ya
kasance ba mai yawan daukan Alkur'ani bane.
(2) Sllah: Hakanan bai halatta ga mara tsaki ya
yi sallah ba farillace ko nafila, har sai ya
tsarkaka ya kuma yi alwala, kamar yadda
Ma'aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi- yace: '' Allah ba zai karbi sallar wanda
ya yi hadasiba har sai ya yi alwala'' Bukhari:135,
Muslim:225. Hakanan kuma ko da mutum yana
da tsarki amma tufafinsa ko wurin sallar baida
tsarki to delene ya tsarkake su kafin fara sallar,
saidai idan bai saniba ko ya manta cewa a
tufafinsa ko wurin da ya yi sallah akwai najasa
sai kuma da lokacin sallar ya fita sannan ya
gani ko ya tuna to anan ba komai sallar shi ta
yi.
(3) Tawafi: Kuma dukkan mutumin da bashi da
tsarki to bai halatta ya yi Tawafin Ka'aba ba,
daman kuma ananne kadai ake dawafi a sararin
duniyar nan.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka
gabata munsan abubuwan da suke najasa ta
yadda ko yanzu akace ka kawo biyar zaka iya
cikin gaggawa, da kuma hanyoyin da akebi
wurin gusar da wannan najasa, wanda yake
gusar da ita din wajibine domin munji abubuwan
da bai halatta mara tsarki ya yi ba, akaro na
gaba zamu kawo bayanai akan wadansu
abubuwa da ake ganinsu kamar najasane alhali
kuma ba najasa bane.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.

No comments: