WANKAN TSARKI
(JANABA)...
Shinfida: Bayan da bayanai suka gabata akan
abinda ya shafi karamin hadasi wanda yake ya
takaitune ga tsarki da kuma alwala, sannan
bayanai suka zo akan abinda ya shafi kadan
daga cikin hukunce-hukuncen alwala, to a
yanzu za'a yi bayani ne akan abinda ya shafi
babban hadasi wanda yake bai tsaya ga tsarki
ko alwalaba a'a, shi tsarkinsa shine ayi wanka
shine an tsarkaka, wadannan abubuwa da suke
wajabta wanka suna da yawa za mu yi iya
kokari damin mu kawo su daki-daki, da fatan
Allah ya yi mana jagora, amin.
(1) Janaba: Janaba dayace daga cikin
abubuwan da suke wajanta wanka, wanda yake
hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar
haka:
(a) Fitar Mani: Idan maniyyi ya fita daga mace
ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin
wankan ya wajaba sai ya zama maniyyin ya
fitane ta hanyar jin dadi, kamar kallo ko wasa
ko tabe-tabe ko jingina…' amma idan ya fita ba
ta hanyar jin dadiba ya fitane ta hanyar wahala,
kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma
watar lantarki ta ja shi…' to wannan wanka bai
wajaba a kanshiba saida kawai ya yi alwala. Shi
wannan fitar maniyyi da ake Magana akan shi
ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana bacci,
idan ya fita ana farke shine ake maganar an ji
dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana
baccine to ba wata maganar jin dadi wanka ya
wajaba.
(b) Shigar Azzakari Cikin Farji: Idan kan kaciyar
namiji ya bace cikin gaban mace to wanka ya
wajaba. Anan ba'a maganar an fitar da mani ko
ba'a fitarba, da zarar hakan ya faru ko macen
ce ta fitar amma namijin bai fitarba ko kuma
namijin ne ya fitar amma macen bada fitar ba
ko ma dukansu basu fitarba wankadai ya
kamasu su duka, da wanda ya fitar da wanda
bai fitarba, tunda ba maganar fitarwa ake yi ba
maganar saduwace, amma inda wasa aka yi ba
saduwa ba to wanda ya fitar shi wanka ya
wajaba a kanshi.
Idan aka yi saduwa sannan aka kara yi to
idan an tashi wanka wanka guda kawai za'a yi,
koda an yi saduwar sau gomane sannan ake so
ayi wanka to wanka guda za'a yi ba wanka
goma ba.
Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so
ya jinkirta wankan janaba zuwa an jima to
abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala,
domin alwalar tana rage kaifin janaba, sannan
kuma tana kara kuzari lokacin da ake so akara
saduwar.
Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da
maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi kamar
yadda bayini ya gabata, to bayan ya yi wankan
sai kuma ya ga maniyyi ya zubo, to anan idan
wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan
maniyyin wani wankan ya kama shi, amma idan
janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo
yanzu to alwala kawai zai yi.
Abayan da suka gabata mun yi bayani na
babbancin maniyyi da kuma maziyyi, sannan
kuma da banbance-banbancen maniyyin mace
da na namiji. Sannan mu sani wadannan
bayanai sun shafi maza da mata, sannan kuma
ka'ida ta musulunci itace bayanin abubuwa a
yadda suke, domin kada a ga maganganun sun
yi tsauri, mahalline na bayanin hukunce-
hukunce.
Fitar maniyyi a farke ko ta hanyar nafarki,
kamar mutum ya yi mafarkin yana saduwa da
mace, ko mace ta yi mafarkin namiji yana
saduwa da ita to wannan al'amari yana tabbatar
da abubuwa kamar haka; abu na farko wannan
wanda ya fitar da maniyyin janaba ta hau
kanshi, abu na biyu; idan wannan shine fitar
maniyyinsa na farko to ya sani daga wannan
lokacin ya balaga, saboda haka hukunce-
hukuncen musulunci sun hau kanshi ko kanta.
Idan mutum ya yi mafarkin yana saduwa da
mace, ko mace ta yi mafarkin ana saduwa da
ita, sannan kuma ya farka bai ga maniyyi ba to
ba wata janaba akanshi, saboda haka ba zai
wanka ba kuma zai yi tsarkiba saboda hakan.
Wadannan kadan kenan daga cikin bayanan
da suka shafi janaba, kuma dole a tashi tsaye
domin a karantar da mutane, wani da ake
Magana da shi cewa yake yi shi bai san idan
mutum ya sadu da matarsa wai sai ya yi
wankaba, wai abinda ya dauka shine wanda ya
yi zina shine wanda zai yi wanka. Wannan
jahilci har ina!.
Abubuwan Da Janaba Ke Hanawa: Bai halatta
ga wanda yake da janaba ba ya shiga
masallaciba, ko kuma ya karanta Alkur'ani ba,
sai aya daya ko biyu domin neman tsari.
Mutumin da yasan ba zai iya taba rowan
sanyi ba to malamai sunce kada ya kusanci
iyalinsa sai ya tanadi abinda zai dumama rowan
dashi, kamar hita, risho ko itace…'.
(2) Daukewar Jinin Al'ada: Abu na biyu cikin
abubuwan da suke wajabta wanka shine
daukewar jinin al'ada, kenan idan jinin al'adar
mace ya dauke to abu na farko dake gabanta
shine wanka. Bayanai akan abinda ya shafi jinin
al'ada da hukunce-hukuncensa da alamar
daukewarshi da izinin Allah za su zo nan gaba,
mudai sani idan jinin al'ada ya dauke to dole
mace ta yi wanka, kuma zuwan jinin al'ada
lamace dake nuna wannan mai jinin ta balaga
musamman ace shine zuwansa na farko a
wurinta, bayanai dai za su zo da izinin Allah.
(3) Daukewar Jinin Biji: Wannan shine abu na
uku daga cikin abubuwan da suke wajabta
wanka, watau daukewar jinni haihuwa, da zarar
mace ta ga jinin haihuwa ya dauke mata ko da
ranar data haihune to wanka ya wajaba akanta
domin ta fara sallah, ba wanda yace sai mai
jego ta yi kwanaki arba'in kafin ta kama sallah,
shima bayai akan jinin biji zai zo da izimin mai
duka shine Allah, kawai mu sani anan daukewar
jinin haihuwa yana wajabta wanka.
(4) Mutuwa: Mutuwa tana wajabta a yiwa
wanda ya mutu wanka, shi kuma bayanai kan
abinda ya shafi wankan da yadda ake yinsa zai
zo ne alokacin da za'a kawo bayanai kan
jana'iza da izinin Allah, kuma Allah ya kaimu
lokacin, abinda ake so a fahimta anan shine
idan mutum ya mutu to dole ayi mishi wanka
sai dai idan shahidine da ya rasu a fagen fama.
(5) Musulunta: Wannan yana cikin abinda
malamai suka karawa juna sani, shin idan
wanda ba musulmiba ya musulunta wajibine sai
ya yi wanka? Wasu sukace wajibine domin
Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi- ya umarci wasu da suka
musulunta da su yi wanka, su kuma wadanda
sukace ba wajibi bane wankan sunce ba'a
ruwaito cewa Ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- ya umarci dukkan
wadanda suka musulunta da cewa kowa sai ya
yi wanka ba.
Kammalawa: A yanzudai munsan abubuwan
da idan yada daga cikinsu ya faru to wanka ya
wajaba, kuma mun sami takaitaccan bayani
akan abinda ya shafi janaba, kama daga
hanyoyin da ake samunta, bayanan da zasu zo
nan gaba za su kun yadda wankan tsarki yake,
wato wankan janaba da kuma na daukewar jinin
al'ada (haila) da bambance-bancen dake cikin
su, Allah ya kai mu lokacin da sauran kwana da
kuma imani.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.
No comments:
Post a Comment