Saturday, 2 December 2017

HUKUNCIN BAYYANA ALAQAR AURE TSAKANIN MIJI DA MATA

🔴 *HUKUNCIN BAYYANA ALAQAR AURE TSAKANIN MIJI DA MATA*

🌱 *SHEIKH AL-ALLAMA SALIH BN FAUZAN AL-FAUZAN (RAHIMAHULLAH)*

▪ *TAMBAYA:*

```Menene hukuncin bayyanar da alaqar aure tsakanin ma'aurata, da bada labarin abunda ya Faru tsakaninsu a wurin abokanansu, saboda da yawa suna fadin/bada labarin da mutane suna jin kunyar fadarsa???

▫ *AMSA:*

❌Haramun ne!

▪ Manzon Allah s.a.w yayi hani akan hakan, sirrin dake tsakanin ma'aurata baya halasta bayyanar dashi.

👉 Harumun ne akan macce yin hakan.

👉 Haka haramun ne akan miji aikata hakan

⛔ Wajibi ne a boye shi.```

📚MADOGARA:
http://www.alfawzan.af.org.sa/node/16049

*DAN UWANKU A MUSULUNCI, MAI NEMAN AFUWAR MAHALICCINSA.

*ABU~SINAN*
_Hashim Sirajo Uba Tsamiya_
+2348064734911

atstsamawy@gmail.com

http://hashimtsamiya.blogspot.com

HUKUNCIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W

🔘 *HUKUNCIN BIKIN  MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

✍🏻 *_SHEIKH AL-ALLAMA SALIH BN FAUZAN AL-FAUZANY R.H YAKE CEWA:_*

```Lallai bikin maulidin Annabi Muhammad s.a.w bai da kyau kuma haramun ne, saboda wadannan dalilai:

🍏 Na farko: Zamanshi bidi'ah a cikin addini, وكل بدعة ضلالة ba zaka samu ba daga wadanda ke gabatar dashi wani dalili tsayayye Na shari'ah dake nuna ingancin yinsa.(sai dai kame kame

🍐 Na biyu: Zamansh kamanceceniya da kiristoci a wajen bikin kirsimeti Na haihuwar Annabi Isah A.S, bayan kuwa an hanemu da kamanceceniya dasu.

🍊 Na uku: Saboda wasu Abubuwa masu yawa da ake aikatawa wadanda basu da kyau da wadanda aka haramta, mafi girmansu shine hada Allah da wani(Shirkah) ta Hanyar hada Allah da Manzo s.a.w a matsayi daya, da karanta wasu kasidu Na shirka a wajen yabon manzon Allah s.a.w, kamar kasidar Alburda da makamantansu.

🍋 Na Hudu: kasancewarshi babu wata idi a musulunci sai guda biyu: idin babbar sallah(idin layya) da idin karamar sallah(idi bayan kammala azumi) duk Wanda ya kirkiro wata idi ta uku; hakika ya kirkiro abunda babu shi a musulunci.```

MADOGARA:
http://www.alfawzan.af.org.sa/node/13811

ALLAH YA SHIRYAR DA YAN UWANMU MASU WANNAN AIKI, SU GANE CEWA KAUNA CE TA SA MUKE FADAKAR DASU.

DAN UWANKU A MUSULUNCI, MAI NEMAN GAFARAR UBANGIJINSA:

*ABU~SINAN*
_HASHIM SIRAJO UBA TSAMIYA_
+2348064734911

atstsamawy@gmail.com

hashimtsamoya.blogspot.com

HUKUNCIN TAHIYYATUL MASJID

⛔ *HUKUNCIN TAHIYYATUL MASJID* ⛔

💬TAMBAYA🔻

➖ Raka'o'i guda biyu da akeyi lokacin shiga masallaci wajibi ne akan duk Wanda ya shiga masallaci???

➖ Menene akan Wanda ya shigo sai ya tarar za'a tada ikama, zaiyi nafilolin biyu ko kuwa zaiyi sallar farillar bayan an kare sai ya ranka???

🌷 *_FADHILATUSH SHEIKH AL-ALLAMA SALIH AL-FAUZANY HAFIZAHULLAH_*

✍🏻 *AMSA*

🔻 ```Manzon Allah s.a.w yace;

🗯(idan dayanku ya shiga masallaci, yayi raka'a biyu kafin ya zauna)

[Imamul-bukhari ya ruwaito shi a cikin sahihinsa 1/114. Daga hadisin Abi Qatadha Assulamy R.A].

✋ Wanda ya shiga masallaci kuma yayi nufin zama a ciki, toh yayi nafila raka'a biyu kafin ya zauna, amma Wanda ya shiga ba tare da yayi nufin zama ba(wato ya shiga ya tarar da za'a tada sallah ko ya shiga ne kawai ya karbi wani Abu ya fita).

🔻 Wannan babu Tahiyyatul-masjid a gareshi

🔻 Hakanan kuma idan ka shiga da niyyar yin sallar farilla, kuma ka iske an tayar da sallar wacce take farilla, toh zakayi sallar farilla a cikin jama'a.

sallar farillar ta wadatar maka akan Tahiyyatul-masjid.

ALLAH YAYI MANA JAGORA

📚Madogara:
المنتقى من فتاوى الشيخ الفوزان
س/54باب الصلاة

DAN UWANKU A MUSULUNCI:```

*ABU-SINAN*
_HASHIM SIRAJ UBA TSAMIYA_
+2348064734911

atstsamawy@gmail.com

hashimtsamiya.blogspot.com

HUKUNCIN FADAR INA KWANA KO INA WUNI KO BARKA DA DARE KO BARKA DA WARHAKA

*HUKUNCI FADAR INA KWANA KO INA WUNI KO BARKA DA DARE KO BARKA DA WARHAKA*

*_FADHILATUSH-SHEIKH ABDULAZIZ BN ABDULLAHI BN BAZ HAFIZAHULLAH_*

*TAMBAYA:* wasu daga cikin  Mutane suna wadatuwa da fadar INA KWANA KO INA WUNI da sauransu, suka watsar da ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARATUHU, sallamar musulunci, ko akwai wani bayani game da hakan???

*AMSA:*

```Eh baya halasta gabatar da wannan, abunda ke wajibi shine farawa da sallama ASSALAMU ALAIKUM, kafin fadar INA KWANA KO INA WUNI, idan kuma ka kara WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, ka kammala kuma hakan yafi falala, sannan bayan sallama sai INA KWANA KO INA WUNI YAYA KUKE, YA YAYANKU, YA IYALANKU, da sauransu gaishe gaishe masu kyau, sai dai a fara da ASSALAMU ALAIKUM wannan shine karanci, idan kuma ka kara da WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, ka hada duka kenan,  Annabi Muhammad s.a.w ya kasance yana tare da sahabbansa, sai ga wani ya shigo yace: ASSALAMU ALAIKUM, sai Manzon Allah s.a.w yace(goma) ma'ana yana da lada goma, sai ga wani ya shigo yace; ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, sai manzon Allah s.a.w yace;(Ashirin) ma'ana: Lada ashirin, sai ga wani mutum ya kara shigowa yace: ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU, sai Annabi Muhammad s.a.w yace;(Talatin) ma'ana; lada talatin.

Wannan shine falalar hadewa duka.

Allah yayi mana jagora.```

Copyright©
*_ABU-SINAN_*
*Hashim Sirajo Uba Tsamiya*

atstsamawy@gmail.com

hashimtsamiya.blogspot.com

http://www.binbaz.org.sa/mat/17636

MAGANAR IMAM AHMAD BN HAMBAL AKAN DAIDAITUWAR ALLAH A SAMA

MALAM MUSA SALIH LAWAL TSAFE(ABU SALIH): http://youtu.be/jm9aqvijKl0

Monday, 27 November 2017

HALASCIN SALLAH DA TAKALMI A MUSULUNCI

```HALASCIN SALLAH DA TAKALMI

Hadisi ya tabbata cewa An tamabayi Anas bn
Malik "shin ko Manzon Allah s.a.w ya kasance
yana SALLAH da Takalminshi???" Sai ya amsa
musu da cewa Ehhh.
Sahihul bukhari [1/494]
A wani Hadisin Annabi Muhammad s.a.w cewa
yayi" Ku saba ma yahudawa, domin su basu
SALLAH da Takalminsu ko huffinsu.
[Abu daud da ibn hibban suka fitar, imamush-
shaukany yace; babu wani abu na suka a cikin
wannan hadisin, domin sabawa yahudawa abune
Wanda shari'ah tayi umurni da hakan a wurare da
dama.]
Amma fa ba wai munce wajibi bane!!!, A'a
Sunnah ce ta Annabi Muhammad s.a.w kuma
Malamai sunce mustahabbi ne yin SALLAH da
takalmi.
Kada wani yace ABU SINAAN yace wajibi ne!!!
Amma ya kamata ka Dan raya wannan sunnar
koda sau daya ne, amma fa kada kaje masallacin
anguwarku Wanda basu san da wannan sunnar
ba kace zakayi musu SALLAH da takalmi!!! Idan
sukayo waje da kai toh laifinka ne kuma kai ka
janyo!!!

Allah ya tabbatar damu akan Sunnah.

ABU SINAN
Hashim Siraj Uba Tsamiya```

KISHIN MATA

.
*MACE BA'A TABA YI MATA KISHIYA*
*TA KIRKI*

1● In ka auro *USTAZIYA,* tace:
Munafukan gari, Allah a baki,
sharri a zuci, in ko ka auro 'yar
gayu tace ta fitsare kafa, ba tada
kamun kai.

2● In ka auro *MAI KYAU* tace
kyalkyal banza, ka auro mara
kyau tace an cuce ka.

3● In ka auro *FARA* tace Sadaka
Yalla ko Hasken Ambi, in baka ce
tace Bayan Tukunya.

4● Ka auro daga *DANGINTA* tace
kana son bata zumunta, in kaje
wani gun tace Tsintattar Mage.

5● Ka auro *yar makota,* tace
wadda ta gama sanin sirrimmu?,
in kaje nesa tace baa san asalinta
ba.

6● In ka auro *Babba,* tace an
kwaso kwashi kwaraf, in ko
karama tace girma ya fadi.

7● In ka auro *KAWARTA* tace duk
matan duniya?, don cin fuska da
cin amana?, in ko ka auri 'yar
aikin gidan, tace Tir !, wai iyakar
wulakanci ke nan, kuma baka da
taste.

8● Ka auro *YAR MANYA* tace: Kuda
wajen kwadayi akan mutu, in
'yar talakawa ka auro tace: Allazi
Wahidin, Allah baku mu samu.

9● In ka auri  *YAR AMININ KA* tace:
Tsohon Banza, yau Baba ya koma
Bobo, in ko abokiyar aikinka a
ofis ka auro, sai tace: Abin boye
ya fito fili.

10● In ka auro mai *ABIN HANNUNTA*, ( wato Business woman)  tace: Kano Jiddah
ko 'yar Dubai, in ko ba mai sana'a
bace, tace an kwaso cima zaune.

11●  In ka auro *YAR MALAMAI* tace
asirce ka aka yi ba yinka bane, in
ko 'yar bata da karatu, sai tace
gidansu ko sallah baa iya ba.

12● In ka auro daga *DANGINKA*
tace ana son a hade kai a ware
ta, in kuwa bazawara ka auro, sai
tace: In kaga godiya da sirdi, to
wani ta kayar kuma wani mai
gigi zata sake kayarwa..........
_
Yaushe kenan zaa auro kishiya ta
kirki?
_
WAI ME YA SA mata basa SON
KISHIYA NE?