Friday, 24 March 2017

YAR JAMI'AH

```YAR JAMI'AH!

MEYE ILLAR DAKE SANYA WASU MAZA (MUSAMMAN GAYU DA KANANAN USTAZAI) CEWA BASA IYA AUREN YAR JAMI'AH???

WACECE YAR JAMI'AH???

MEYE BAMBANCI DAKE TSAKANIN YAR JAMI'AH DA YAR SAKANDARE KO WACCE BA TAYI BOKO BA???

HMMMMM

Wannan sune tambayoyin da Wata baiwar Allah YAR JAMI'AH tayi man, kuma ta nemi na bata Amsa.

Sai dai na bata hakuri zuwa wani lokaci kadan,bayan mun kare exams zanyi nazari sossai sannan na bata amsoshin tambayar ta.

Need ur prayer exam mode actvt

ABBAN SINAN(Hashim Surajo Uba Tsamiya)```

Http://abusinan.mywapblog.com
http://hashimtsamiya.mywapblog.com

Monday, 13 March 2017

PRAYER

Assalamu alaikum warahmatullah.

Dear brother and sister's,
I need your prayer bcos our examination commence on Monday insha Allah. So dat your prayer is very considerable to me.

ABU~SINAN
Hashim Surajo Uba Tsamiya Tsafe

Thursday, 9 March 2017

SHI'ANCI

*وإذا ذكر الله وحده اشمأزت قلوب الذين لا يؤمنون بالأخرة، وإذا ذكر الذين من دونه إذا هم يستبشرون*

```Idan ka duba Tafsirin 'kummy, wani jibgegen malamin Addinin shi'anci ne, a karkashin wannan Ayar wai sai yace ta sauka ne akan wane da wane! A akidar shi'anci idan sukace wane da wane, toh suna nufin Abubakar da umar, ko kuma suce Na farko da na biyu shima duk ma'anar daya ce! Toh amma a wannan suna nufin Abubakar da umar!
Toh amma ga fassarar ayar kafin muyi nisa
"Idan aka ambaci sunan Allah shi kadai, sai zukatan wadanda basuyi imani da ranar lahira ba su firgita, amma idan aka ambaci sunan wanin Allah(gumakansu ko waliyyai ko Wani Abun bauta) sai surinka fara'a suna jin dadi saboda wannan Albishir Na fadin sunayen"

Idan mai karatu zai iya daure wa ya duba littafan tafsirai Na manyan malaman musulunci insha Allahu zai samu cikakken bayani, amma ga Wani bayani daga littafan tafsiri guda biyu! أيسر التفاسر تأليف أبي بكر جابر الجزائري،   صفوت التفاسير تأليف محمد علي الصا بوني 
Sukace wannan ayar tana magana akan halin mushirikai ne, idan aka fadi sunan Allah saboda duhun jahilci da bata dake tare dasu  sai su rinka bayyana fushi suna damuwa, amma idan aka ambaci sunan gumakansu ko waliyyai ko wani Wanda suke bauta mawa sai kagansu suna farin ciki da jin dadi.
Toh komin hassadarka sai ka yarda da cewa Abubakar ba mushiriki bane! Duk Wanda kuma yace Abubakar mushiriki ne, wallahi sunanshi kafiri, da Nassin kur'ani, domin Abubakar da Nasarar Allah yake tafiya a cikin Al'amurransa.

Allah ka kara mana son sahabban Annabi Muhammad s.a.w kamar yadda kace ka yadda dasu. Allah ka kaskantar da duk mai Akeedar zagin sahabban Annabinka.```

Copyright©
Hashim Surajo Uba Tsamiya
Http://hashim141473.mywapblog.com

ALHAMDULILLAH.

*ALHAMDULILLAH!*

*Allah ya saka ma _MALAM NURA ALIYU TSAMIYA_*  ```Malam ya kasance a duk lokacin da za'a fara wa'azi na kwamitin da'awah ya na wani jawabi inda yake cewa; "A duk lokacin da kaji za'a fara wa'azi kira'ar Qur'ani na tashi, toh Alama ce da ke nuna cewa za'ayi wa'azin musulunci!  Bude taro da kide kide ko wake-wake alama ce dake ta Addinin kirista! Mai kokwanto ya bari ranar lahadi yaje church yaji da me suke budewa!"
Toh wa'azin Malam ya fara tasiri ga daliban waliyyin baro na Tsafe! Duk da cewa farko kide kide a kasa, amma kafin OGA ya fara jawabi sai naji Ankira wani domin bude jawabin ko ba'a lura ba, da karatun Qur'ani.
Toh adai cigaba da wannan fadakarwar MALAM NURA, insha Allahu sai gaskiyar ta ida bayyana.```

*_Hashim Surajo Uba Tsamiya_*

IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA BIDI'AR MSULIDI BA, HASALI MA YAYI FADA DA ITA...

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*_IBN TAIMIYYA BAI YARDA DA BIDI'AR MAULIDI BA, HASALI MA YAYI FADA DA ITA..._*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
**
**
**
**
_002 fitowa ta biyu_

   _Rubutawa:_ *_Hashim Surajo Uba Tsamiya(ABU SINÃN)_*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

```Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga Wanda babu wani Annabi bayansa, tare da iyalan gidansa da sahabbansa da duk Wanda ya bi tafarkinsa da kyautatawa.

Bayan haka;

Kamar yadda shimfida ta gabata akan wannan posting, yanxu kai tsaye zanje ga maganar ibn Taimiyya wacce ya fada har yan bidi'ah ke ganin hujja ne garesu.
   Ibn Taimiyya a lokacin da yake ambaton nau'o'in da suka shafi lokaci ga abin da yake cewa;```
((وكذلك ما يحدثه بعض الناس إما مضاهات للنصارى في ميلاد عيسى عليه السلام وإما محبة للنبي صلى الله عليه وسلم وتعظيما له. والله قد يثيبهم على هذه المحبة والإجتهاد لا على البدع من اتخاذ مولد النبي صلى الله عليه وسلم عيدا، مع احتلاف الناس فى مولده-))

_Ma'ana;_ *_"Haka ma abin da wasu mutane suka 'kir'kira ko dai don koyi da nasara ga kirsimeti ko kuma don son Annabi da girmamawa gareshi, Allah zai iya basu lada akan wannan son da suke yiwa Annabi ba akan bidi'ar bukin maulidi ba, duk da malamai sunyi sabani akan ranar da aka haifeshi..."_*

```Ya kai Dan uwa mai karatu ko kasan ma'anar wannan magana ta ibn taimiyya?
  Hakika manyan Malamai sunyi maganganu akan wannan magana ta ibn taimiyya, daga ciki akwai wadanda sukayi Raddi ga ibn taimiyya, kamar sheikh Al-Tuwaijiri a cikin littafinsa(ARRADUL QAWIY) bayan ya kawo wannan magana ta sheikhul Islam sai yace; "Sai na CE: A nan akwai magana".
Haka sheikh Muhammad Ahmad ALFAQIHI-Allah yayi masa rahama- shima yayi irin wannan maganar.

     Amma sheikh ibn uthaimin ya ba wannan magana ma'ana mai kyau a cikin littafinsa(ALQAULUL MUFID ALA KITABUT TAUHID) inda yake cewa;```

*((ولو حسن قصد الفاعل: أي إن االبدعة شر ولو حسن قصد فاعلها، ويأثم إن كان عالما أنها بدعة ولو حسن قصده، لأنه أقدم على المعصية كمن يجيز الكذب والغش ويدعي أنه مصلحه، أما لو كان جاهلا فإنه لايأثك، لأن جميع المعاصي لايأثم بها إلا مع العلم، وقد يثاب على حسن قصده، وقد نبه على ذلك شيخ الإسلام ابن تيمية في كتابه[اقتضاء الصراط المستقيم] فيثاب على نيته دون عمله، فعمله هذا غير صالح ولامقبول عند الله ولامرضى، لكن لحسن نيته مع الجهل يكون له أجر، ولهذا قال صلى الله عليه وسلم للرجل الذي صلى وأعاد الوضوء بعد ما وجد الماء وصلى ثانية:"لك الأجر مرتين" لحسن قصده، ولأن عمله عمل صالح في الأصل، لكن لو أراد أحد أن يعمل العمل مرتين مع عمله أنه غير مشروع، لم يكن له أجر لأن عمله غير مشروع لكونه خلاف السنة، فقد قال النبي صلى الله عليه وسلم للذي لم يعد: "وأصبت السنة" [صحيح أخرجه أبو داود ٣٣٨]          فإن قال: إني بهذه البدعة أحيي الهمم والتنشيط وما أشبه ذلك.                        أجيب: بأن هذا الإرادة طعن في الر سالة الرسول الله صلى الله عليه وسلم لأنه اتهام له بالتقصير أو القصور، أي مقصر في الإخبار عن ذلك أو قاصر في العلم، وهذا أمر عظيم وخطر جسيم ولأن هذا لم يكن عليه الرسول صلى الله عليه وسلم ولا خلفاؤه الراشدون.                 أما إذا كان حسن القصد ولم يعلم أن هذا بدعة، فإنه يثاب على نيته ولايثاب على عمله، لأن عمله شر حابط كما قال النبي صلى الله عليه وسلم: "من عمل عملا ليس عليه أمرنا، فهو رد"  [صحيح أخرجه مسلم ١٣٤٤].                                وأما العامة الذين لايعلمون، وقد لبس عليهم هذه البدعة، وغيرها، نقول: ما دامو قاصدين للحق ولا علموا به! فإثمهم على من أفتاهم ومن أضلهم...))).                            {القول المفيد على كتاب التوحيد ٣٨٧-٣٨٥}*

_Ma'ana;_ *_"Bidi'ah sharri ce koda mai aikatata ya kyautata niyya kuma zai samu zunubi idan yasan bidi'ah ce yake aikatawa ko da ya kyautata niyya, kamar Wanda zai halattar da karya da Algusshu da sunan maslaha, amma da bai San cewa wannan aiki bidi'ah bane, to bashi da laifi, domin babu laifi akan aikin da aka aikata akan rashin sani, kuma ana iya ba mutum lada akan kyakykyawar niyyarsa kamar yanda sheikhul Islam ya fadakar a cikin littafinsa(IQTIDHA'UL SIRA'DUL MUSTAQEEM) sai aba mutum lada akan niyyarsa ba akan aikinsa ba domin aikinsa ba na kwarai bane, kuma ba karbabbe bane a wurin Allah, sai dai saboda kyawon niyyarsa tare da jahiltar hukuncin sai ya zama ya samu lada, don haka ne ma Annabi Muhammad s.a.w yace ga mutumin da yayi sallah da taimama bayan ya samu ruwa sai yayi alwala ya sake sallah:'kana da lada biyu' saboda kyawon niyyarsa, kuma asalin aikinsa aiki ne mai kyau, sai dai yanxu da mutum zai aikata wani aiki sau biyu kuma ya San cewa shari'ah bata bada damar aikata haka ba, to bashi da lada saboda ya sabawa sunnah, hakika Annabi Muhammad s.a.w yace ga dayan da bai sake sallah ba; 'ka dace da sunnah' [Abu daud 338].                            Da wani zai ce; 'Na aikata wannan bidi'ah ne  domin Karin himma da nishadi da abin da yayi kama da haka.              Za'a bashi amsa da cewa; irin wannan nufi naka suka ne ga manzancin Manzon Allah s.a.w domin tuhumarsa ne da kasawa ko rashin isar da sako ga wannan aiki, kuma wannan al'amari ne babba kuma mai hadari.                       Amma idan ya kyautata niyya kuma bai San wannan aiki bidi'ah ne ba, to za'a bashi lada akan niyyarsa amma ba akan aikinsa ba, domin aikinsa sharri ne kuma lalatacce ne kamar yadda Manzon Allah s.a.w yace: 'duk Wanda ya aikata wani aiki Wanda ba umurninmu a ciki an mayar masa [Muslim 1344]   amma gama garin mutane da basu da ilimi kuma aka samu wasu suka rudesu akan wannan bidi'ah da waninta da sunan son Annabi ko da sunan abu ne mai kyau to su matukar suna yine tsakaninsu da Allah kuma basu da ilimi to laifinsu yana akan Wanda ya batar dasu..."_*
[ALQAULUL MUFID ALA KITABUT TAUHID, 1/385-387]
  
     ```Wannan ya nuna cewa matukar kasan Abu baida kyau, amma kace kai sai ka aikata toh tabbas kana da zunubin aikatawar, ko kuma maluman Sunnah sunyi maka Wa'azi sun fadakar amma ka kiyin amfani da nasihohinsu saboda son zuciya to tabbas karshen Alewa kasa a cigaba da tafiya sai kowa ya fahimci wake kan gaskiya da kuma Wanda yake akan bata.

Allah ka tabbatar damu akan bin sunnar Annabi Muhammad s.a.w da aiki da ita.

   SAI MUN HADU A FITOWA NA GABA INSHA ALLAHU...```



Copyright©
*_Hashim Surajo Uba Tsamiya (ABU SINÃN)_*
📞08064734911📞
Https://mobile.facebook.com/hashimusurajo.tsamiya

atstsamawy@gmail.com

Http://hashimtsamiya.blogspot.com

TUNATARWA

*ياأمة محمد صلى الله عليه وسلم!!!*

*اعلموا الانجاة لنا إلا بعد رجعوعنا إلى ماكان عليه سلفنا الصالح من العلم والإخلاص. وإخراج هذا العلم من حيز القراءة إلى حيز التطبيق.*
(قاله الشيخ أحمد آدم الغركوى حفظه الله)

         *MADUBI*

*_Ba abinda zai tseratar damu, face mu koma ga abinda magabatan mu suka bi na karatu da ikhlasi tare da dauko karatun daga duniyar karatun zuwa duniyar aiki dashi._*
*(zancen sheikh Adam Al-garkawy)*

```Hashim Surajo Uba Tsamiya```

Dr jalo

Ibrahim Jalo Jalingo
BA MAZHABA BA CE LAIFI MAZHABANCI SHI NE LAIFI:
Ba mazhaba ba ce laifi a'a mazhabanci shi ne laifi, ma'anar mazhabanci shi ne: nassin Annabi mai
tsira da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan kai ka ki yin aiki da
shi wannan nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa abin da ke rubuce cikin mazhabarka.
Ba kungiya ba ce laifi a'a kungiyanci shi ne laifi, ma'anar kungiyanci shi ne: nassin Annabi mai tsira
da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan kai ka ki yin aiki da
wannan nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa wata ka'ida da kungiyarka ta shata wa kanta.
Allah muke roko da Ya tausaya mana Ya cusa son Annabi mai tsira da amincin Allah, da son fifita
maganarsa a kan maganar kowa cikin zukatanmu. Ameen.