📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_Fitowa Na Goma 010_
Gabatarwa: *UMMU SINAN*
*KARKASUWAR MATA GAME DA JININ AL'ADA:*
Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; *WACCE TA FARA,* Kashi na biyu kuma; *WACCE TA SABA,* sannan sai kashi na uku; *MAI JUNA BIYU,*
mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka;
1⃣ *WACCE TA FARA;*
Ita wacce ta fara al'ada ya zama shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwar ta, to abunda ke kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zai dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha- biyar ba,(KAMAR YADDA BAYANI YA GABATA A RUBUTUKAN DA SUKA GABATA) idan ko ya wuce sha-biyar to abunda ya
doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'ada ba, kenan mafi yawan kwanakin da zata yi la'akari dasu sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama abunda ake kira
*(Isthala)* wato cuta sai a nemi magani, a karkashin wannan nake cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu mata su rika tuntubar su suna fahimtar da su
tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci yayi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka,ko makaman tan hakan Wanda wannan Na faruwa kwarai da gaske, wata babbar mace ce amma bata san menene jinin al'ada ba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganin shi, kunga akwai hadari kwarai da gaske.
2⃣ *WACCE TA SABA:*
Abunda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku, a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai yayi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai a kira ta da sunan
wacce ta saba, domin ta saba akan kwanaki sanannu.
Amma idan ta yi al'adar karo na farko
kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar
karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da
tsayayyun kwanaki.
Ita wacce ta saba wato wacce take da
sanannun kwanakin al'ada to wadannan
kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada,
amma idan kwana kin suka cika al'adar kuma bata dauke ba sai ta kara kwanaki uku,haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki sha biyar su cika, misali idan al'adar ta kwanaki biyar ne sai kuma jinin bai dauke ba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan kwanaki takwas din sun zama sha-daya idan bai dauke ba sai ta kara uku sun zama sha-hudu idan bai dauke ba sai ta
kara kwana daya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai dauke ba domin kwanakin al'ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma
sun cika, abunda ya cigaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada ba,sunanshi jinincuta *(Istihala)*
sai a nemi magani. A dukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na
saurare sai ya dauke a kwana na daya cikin ukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.
3⃣ *MAI JUNA BIYU(mai ciki);* Galibin mata masu
juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga
al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita.
Idan al'ada ta zowa mace mai juna-biyu, to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin
al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata
iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan
Kina da juna biyu kuma kika ga jini.
*TANBIHI NA DAYA:*
Idan mace jini yana mata wasa wato yazo yau ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abunda zata yi anan shine, ta tsaya ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki
domin da hakane zata cika kwanakin ta na al'ada, *MISALI,* kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki tara, wannan matar ita
ake kira *(Al-Mulaffiqa)* a larabcin mata masu
al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da
dawowarsa to na biyun zai zama sabon jini ne kenan, ba na da ne ya dawo ba.
ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ALAMOMIN DAUKEWAR JININ AL'ADA INSHA ALLAHU.
ALLAH YAYI MANA JAGORA.
WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:
✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*
DOMIN SHIGA GROUPS DIN;
*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911
*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613
No comments:
Post a Comment