📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_Fitowa Na sha daya 011_
Gabatarwa: *UMMU SINAN*
*ALAMOMIN DAUKEWAR JININ AL'ADA;*
Idan jinin al'ada ya dauke akwai wasu alamomi da shari'ah ta sanya domin su zama manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, ga alamomin kamar haka:
1⃣ *BUSHEWAR GABA;*
Abunda ake nufi shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gaban ta, sannan ta fito dashi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata
al'adarta ta dauke.
2⃣ *FARAR KUMFA;*
Wannan wani ruwa ne fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka karshen al'adar ta, ta sani ta kammala Al'adar ta.
Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba yin al'ada ba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki, ba sai ta jira farar kumfa ba, amma idan wacce ta saba gani ce sai ta ga bushewar gaba to malamai suka ce zata dan saurara kadan domin jiran farar kumfa, amma jinkirin ba zai kai
ga fitar zababbun lokutan sallah ba.
A dunkule dai kowane daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu a lokaci
guda ba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai kiyi wankan tsarki domin ki cigaba da
ibada, domin idan ba kiyi wanka ba ko da jinin ya dauke mijin ki ba zai sadu da dake ba kuma baza kiyi sallah ba, da dai sauransu.
Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga - diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jini ne, amma idan a karshen jini ne to wannan ba komai,
Ummu Adiyyah matar Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: *((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)).* [Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368 , Ibnu Majah Hadisi Na: 647,
Darimi Hadisi Na: 865].
Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar
asuba, amma ba'a ce ta tashi cikin dare ba domin ta duba.!!!
ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ABUBUWAN DA BASU HALATTA GA MAI AL'ADA INSHA ALLAHU.
ALLAH YAYI MANA JAGORA.
WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:
✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*
DOMIN SHIGA GROUPS DIN;
*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911
*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613
No comments:
Post a Comment