Thursday, 15 November 2018

13 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha biyu 013_

Gabatarwa; *UMMU SINAN*


*MENENE JININ BIKI???*
  Jini ne da yake fitowa daga mahaifa ta sanadiyyar haihuwa.
Kenan shi jinin
biki jini ne da yake da alaka da haihuwa, idan mace taga jini kwana daya ko biyu kafin
haihuwa to shima malamai suna lissafashi cikin
jinin haihuwa.

*MAFI YAWAN KWANAKINSA;*

    Mafi yawan kwanakin da macen da ta haihu zata ga jinin haihuwa malamai sun karawa juna sani, wadansu sukace
kwanaki ar'bain ne (40), wadansu kuma sukace kwanaki sittin ne(60) kamar yadda mai Akhdari
ya bayyana.
Sabanin na al'ada shi kwanaki goma sha-biyar ne.

  Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to zata jira kwanaki arba'in, ko sittin, idan ya dauke a kwanakin shikenan sai ta yi wankan tsarki na daukewar jinin haihuwa ta ci gaba da sallah da kuma sauran ayyuka na ibada, idan kuma bai dauke ba to sai a nemi magani ya
zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da ibada, idan kuma jinin ya dauke kafin kwanakin kamar ya dauke ranar da aka yi haihuwar to a nan ma zata yi wanka ne ta cigaba da sallah, laifi ne mai girman gaske mace
jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin sallah wai sai ta yi arba'in wannan ba tsari bane na addinin musulunci.

Imam Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi ijima'i tun daga Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan cewa lalle mace mai haihuwa zata bar salla tsawon kwanaki arba'in sai dai idan ta ga tsarki kafin hakan (kafin kwanaki arba'in din) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah.
Idan mace ta yi bari sai ya zama na halittar mutum ta bayyana a barin, kamar ace ga tsarin
halittar ba wai gudan jini bane ya zama na kuma akwai jini daya zuba to anan tana da hukuncin jinin biki(jinin haihuwa), gwargwadon kwanakin da sune  halittar take bayyana a ciki sune
watanni uku galibi amma dai mafi karanci sune kwanaki tamanin (80).
Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta yadda halittar mutum bata bayyana ba to ba'a
la'akari da wannan jinin da ya zubo, saboda
haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar
azumi ba saboda jinin domin bata da hukuncin
jinin biki.

Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan
kwanakin da aka yi bayaninsu to zata yi
wankane ta kuma yi sallah ko da jinin ya
dauke ne a ranar da aka yi haihuwar.


ZAMU DAKATA A NAN SAI WANI LOKACI NA GABA IDAN ALLAH YA KAIMU INSHA ALLAHU.

DOMIN SHIGA GROUP DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

No comments: