📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_Fitowa Na sha biyar 015_
Gabatarwa; *UMMU SINAN*
*FALALAR ALWALA;*
Kasantuwar cewa alwala wajiba ce wannan kadai ya isa ka gane falalar ta a
musulunci domin dukkan abunda akace farillah ne
to wannan matsayi ne mai zaman kanshi, bayan hadisi na 62 a cikin *Muwadda Malik* yana cewa; An karbo daga Abdullahi As-Sunaabihi, lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: *''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi kuskurar baki dukkanin laifukan dake bakin sun Wanke, idan kuma ya shaqa ruwa sai ya fyace, dukkan laifukan daya shaka sun fice, idan kuma ya wanke fuskarsa laifukan da ke fuskar ta sa sun wanke, har wadanda ke karkashin girar shi, idan ya wanke hannayensa laifukan dake hannayensa sun fice, har wadanda ke karkashin akaifarsa (farce), idan kuma ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun fice har wadanda ke kunnuwansa, idan kuma ya wanke kafafuwansa duk laifukan dake kafafuwansa sun fice, har wadanda ke karkashin farcen kafafun nashi."*
Sannan kuma
tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya zama wani
kari ne da yake da shi na lada''.
Lalle wannan bakamar falala bace da alwala take da shi, domin mai alwala zai kasance yana kammala alwala zunubanshi suna digewa a
kasa, amma wani hanzari ba gudu ba, wannan ladan zai tabbata ne ga wanda ya yi alwala a yadda shari'a ta tabbatar da ita ba wacce ya tsinta a
kan titi ba.
*SHARUDDAN ALWALA*
Sharuddan alwala sune abubuwan da ake so mai alwala ya cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:
1⃣ *Musulunci*
kenan idan wanda ba musulmi ba ya yi alwala bata yi ba.
2⃣ *Hankali*
Idan mahaukaci ya yi alwala itama bata yi ba.
3⃣ *Wayau*
Idan dan karamin yaro mara dabara
ya yi bata yi ba.
4⃣ *Ruwan ya zama mai tsarki*
Idan ya zama ruwa ne mara tsarki to alwalar bata yi ba, bayanai sun gabata akan hukunce hukuncen ruwa.
5⃣ *Ruwan ya zama na halas*
Idan ruwa ne da
mutum ya sata ko ya same shi bata shar'antacciyar hanya ba to alwalar bata yi ba.
6⃣ *Ya kasance mai tsarki*
Idan mai alwala ya
kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba.
7⃣ *Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga*
Kenan idan mutum ya kasance yana sanye da wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi, kamar zobe da sauransu.
ZAMU DAKATA A NAN INSHA ALLAHU SAI WANO LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *FARILLAN ALWALA*
DOMIN SHIGA GROUPS DIN;
*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911
*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613
No comments:
Post a Comment