Thursday, 15 November 2018

16 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha shida 016_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*FARILLAN ALWALA*

1⃣ *Niyyah:*
Domin a bambance wanda ya sa ruwa domin sanyaya jiki, ko domin gusar da
datti, duk wannan ba niyya ce ta alwala ba.

2⃣ *Wanke Fuska:*
  Ita kuma fuska ta bangaren tsawo tana farawa ne daga matsirar gashin kai zuwa karkashin haba(gemu), amma
ta fuskar fadi tana farawa ne daga kunnen dama zuwa kunnen hagu, wannan shine abinda yake amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar ko ina ya samu ruwa kamar kasan haba, gefen
ido da gefan kunne da matsa-matsin karan hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu
kamar alwalar yarace.

3⃣ *Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu;*
Mai alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke hannayensa tun daga saman yatsunsa (farce/kaifa) har zuwa gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga inda ya wanke, anan ma akwai manyan mutane masu alwalar yara.

4⃣ *Shafar Kai:*
Ka tabbata ka hada yatsunka sannan kuma ka fara shafar daga goshi (dai-dai
matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya.

5⃣ *Wanke Kafa:*
Haka nan mai alwala ya tabbata ya wanke kafarsa har zuwa idon sawu,
wato wadannan kasusuwan guda biyu dake
gefen kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.

6⃣ *Cudanyawa:*
  Mai alwala ya tabbata ya cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya
shiga ko ina.

7⃣ *Jerantawa:*
  Abinda ake nufi shine a lokacin da ka fara alwala to ka dakatar da komai sai ka kammala, amma kana alwala kana kuma wata sabga daban wannan ba dai dai bane.

Mai alwala ya tabbata ya gabatar da wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta yadda idan aka rasa daya daga cikin su to alwalarka ta shiga chakwakiya.


ZAMU DAKATA ANAN INSHA ALLAHU SAI WANI LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *SUNNONIN ALWALA*


DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

No comments: