📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
_Fitowa Na sha hudu 014_
Gabatarwa; *UMMU SINAN*
Alwala ibadace mai zaman kanta
wacce Allah madaukakin sarki ya shar'anta ta
kafin gabatar da wadansu ibadu musamman ma
sallah, mutum yana samun cikakken ladan alwala idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin
sarki ya saukar da hukunce-hukuncen alwala a cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
*''Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan kuka ta shi za ku yi sallah to ku wanke fuskokin ku da hannayanku zuwa gwiwar hannu ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa idon sawu (idon kafa)…''* [Suratu Ma'ida, aya ta: 6].
Tabbas wannan aya ta yi bayanin wajibcin alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi a wanke ko kuma a shafa, sannan kuma ayar ta iya kance
ko wanne mahalli.
Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana siffar yadda alwalar take da maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake
gamsasshen bayani.
Ka sani lalle ita wannan alwala tana da falala da kuma sharudda da kuma farillai sannan tana da sunnoni da kuma mustahabbai, sharuddan nan
da farillai tabbas a tabbata mun sansu alokacin gabatar da alwala iya gwargwado domin da sune alwala zata zama karbabbiya, amma su sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne ta inda matsayinsu bai kai matsayin farillai ba.
ZAMU DAKATA A NAN INSHA ALLAHU SAI WANI LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *FALALAR ALWALA*
DOMIN SHIGA GROUP DIN;
*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911
*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613
No comments:
Post a Comment