ABUBUWAN DAKE KARYA
ALWALA
Shinfida: Lalle wannan babi yana da matukar
muhimmanci, domin bayan da kasan alwala to
ya kamata kasan abin da ke warwareta, akan
haka ya ka yiwa kanka hukunci idan zaka yi
sallah ko abinda dole sai da alwala ake yinsa,
saboda haka yana da matukar kyau mu kula da
wadannan hukunce-hukunce. Allah ya yi mana
jagora.
Abubuwan da suke bata alwala sunkasu kashi
biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi anan
shine, akwai abinda shi karankan sa yake bata
alwala to wannan shi ake kira Hadasi
(Al'ahdaas) . Akwai kuma wanda shi karankan
sa bai warware alwala amma zai kai ka ga
abinda yake warware alwalar to wannan shi ake
kira, Sabuban Hadasi (Asbabul Ahdas).
To shi hadasin wato abinda yake karya alwala
da karankansa, abubuwane guda shidane, hudu
daga cikinsu suna fitane ta gaba, sune kuma;
Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi da kuma Maniyyi.
Wadannan idan suka faru ko dayansu ya faru to
tsarki kawai za'a yi a sake alwala in banda
maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya bata
alwala sai kuma anyi wanka. Sai kuma guda
biyu daga da suke fita daga dubura, sune kuma;
Bayangida da kuma tusa. Amma shi bayan-gida
tsarki za'a yi sai a sake alwala, sabanin tusa
wacce take ita ba'a yi mata tsarki alwala kawai
za'a sake.
Sai kuma abubuwan da suke sabubbane na
hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai,
amma su wadancan da zarar ya diga komai
kankantarsa to ya karya alwala inbanda mai
fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa
sune;
(1) Bacci: Shi bacci a nan ya kasu kashi hudu;
(a) Dogon bacci mai nauyi, kai tsaye wannan ya
karya alwala.
(b) Takaitaccan bacci mai nauyi, shi ma ya
karya alwala.
(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai
karya alwala ba.
(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala
amma an so a sake ta.
Ma'aunin da ake auna bacci da shi domin a
gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shine;
Idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to
baccinka bai yi nauyi ba, amma idan baka san
wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to baccin
ya yi nauyi. Kenan idan kuna fira sai amma
kana gyangyadi sai da ka farka sai kace; ina
wane? Ko; wane yaushe ka zo? To kasan
baccinka ya yi nauyi, Allah ya sa mu dace.
(2) Gushewar Hankali: Idan hankalin mutun ya
gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma ko
maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan idan
mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko kuma
suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a asbiti
ko kuma ya sha ta yi Marisa-ta sha kafso to
alwalar ko wannensu ta karye.
(3) Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi
al'aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba
al'aurarsa bawai ta samani riga ko wandoba ko
kuma wani kyalleba to malamai sun karawa
juna sani kan makomar al'walarsa, wadansu
suke ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma
suka ce idan ya tabane domin ya ji dadi to ta
karye amma idan ba wai ya yi hakanne domin
ya ji dadi ba alwalarsa nanan, wannan maganar
kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai
sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al'aurarsa
ba kai tsayeba ko dai ta saman wando ko
saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa
nanan daram.
(4) Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi
mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji
ba alwalarsa ta karye, haka kuma al'amari yake
idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta
ji dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye,
malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu;
(a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji
dadin to alwalar ta karye.
(b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma
ya ji dadin to ta karye.
( c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji da
din ba to alwalar ta karye.
(d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma
bai ji dadinba to alwalarshi tanan daram.
Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya
kawosu. Mu sani wadannan bayanai sun shafi
macema idan ita ta yi.
Akwai wadansu da malamai suka karawa juna
sani akan suna karya alwala ko basa karyawa?,
wadannan kuma sune:
(5) Shakka Akan Hadasi: Idan mutum ya
tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokwanto
ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan bashi da
tabbas? Wasu malamai sukace; Ai da ya yi
kokwanto alwalarsa ta karye domin ba'a sallah
da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma
suke: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai
daga bayane yake shakka to ai shakka bata ture
abinda yake dahir, saboda haka sukace alwalar
nanan, Allah shine masani.
(6) Ridda: Shine mutum musulmi ya kafirta
(Allah Ya tsaremu). Wadansu malamai sukace
da zarar ya bar musulunci to da zarar alwalar ta
karye, wasu malaman kuma sukace; A'a, ai
ayyukansa da ya yi ba za su baciba sai in ya
mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na
cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga
wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi
yafi.
Alwala bata baci idan mutum ya yanke farce
(Kunba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko
anyi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko
kuma tuntube har jini ya fita duk alwala bat
abaci saboda wadannan, ko mace ta shafi
gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu
sunce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin
fitsari ko tusa ko bayan gida abinda musulunci
ya karantar shine mutum ya je ya biya wannan
bukatar ta shi tukunna, maimakon ya matse.
Kammalawa: Alwala tana da muhimmanci
matuka saboda haka a kiyayeta a san kuma
abinda yake warwareta, kuma wannan yake
nuna mana cewa tunda har alwala za'a ce
akwai abubuwan da suke warwareta dudda ga
laima a jikin mutum amma ace alwalarsa ta
warware to lalle yana da kyau musan kuma
abubuwan da suke warware musulunci domin
kullun mutum ya dinga ba addininsa kariya ta
yadda kada ya warware, Allah yak are mana
addinimmu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.