🔘 *HUKUNCIN BIKIN MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W*
✍🏻 *_SHEIKH AL-ALLAMA SALIH BN FAUZAN AL-FAUZANY R.H YAKE CEWA:_*
```Lallai bikin maulidin Annabi Muhammad s.a.w bai da kyau kuma haramun ne, saboda wadannan dalilai:
🍏 Na farko: Zamanshi bidi'ah a cikin addini, وكل بدعة ضلالة ba zaka samu ba daga wadanda ke gabatar dashi wani dalili tsayayye Na shari'ah dake nuna ingancin yinsa.(sai dai kame kame
🍐 Na biyu: Zamansh kamanceceniya da kiristoci a wajen bikin kirsimeti Na haihuwar Annabi Isah A.S, bayan kuwa an hanemu da kamanceceniya dasu.
🍊 Na uku: Saboda wasu Abubuwa masu yawa da ake aikatawa wadanda basu da kyau da wadanda aka haramta, mafi girmansu shine hada Allah da wani(Shirkah) ta Hanyar hada Allah da Manzo s.a.w a matsayi daya, da karanta wasu kasidu Na shirka a wajen yabon manzon Allah s.a.w, kamar kasidar Alburda da makamantansu.
🍋 Na Hudu: kasancewarshi babu wata idi a musulunci sai guda biyu: idin babbar sallah(idin layya) da idin karamar sallah(idi bayan kammala azumi) duk Wanda ya kirkiro wata idi ta uku; hakika ya kirkiro abunda babu shi a musulunci.```
MADOGARA:
http://www.alfawzan.af.org.sa/node/13811
ALLAH YA SHIRYAR DA YAN UWANMU MASU WANNAN AIKI, SU GANE CEWA KAUNA CE TA SA MUKE FADAKAR DASU.
DAN UWANKU A MUSULUNCI, MAI NEMAN GAFARAR UBANGIJINSA:
*ABU~SINAN*
_HASHIM SIRAJO UBA TSAMIYA_
+2348064734911
atstsamawy@gmail.com
hashimtsamoya.blogspot.com