Wednesday, 17 October 2018

012 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha biyu 012_

Gabatarwa; *UMMU SINAN*

*ABUBUWAN DA BASU HALATTA GA MAI AL'ADA;*

A wannan karon zamu lissafa abubuwan da basu halatta mace mai al'ada ta aikatasu ko a aikata mata, abubuwan sune kamar haka;

1⃣ *SALLAH;*
Baya halatta mai al'ada ta yi sallar
farilla ko nafila, idan kuma tayi, ta yi ba'a karba ba, sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta
kammala al'adar ba zata rama sallolin ba.

2⃣  *SAKI;*
Baya halatta matar da take al'ada a sake ta, wannan ya sabawa karantarwar
musulunci, saboda haka koda yana son ya sake ta to ya bari sai ta kammala al'ada kafin ya sadu da ita sai ya sake ta, amma idan ya sake ta tana jinin al'adar to sakin ya yi amma
za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai uku ba.

3⃣ *DAWAFI;*
Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin
Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsayuwar Arafah da
kwanan mina dana muzdalifa da jifa da
Labbaika, da daidai sauransu.

4⃣ *ZAMA A MASALLACI;*
  Mai al'adah ba zata zauna a cikin masallaci ba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu(SAI DA KWAKWARAN DALILI).

5⃣ *AZUMI;*
Baya halatta mai al'ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yi ba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta rama su.
  Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo,
amma dazaran ta zo to ba azumi.

6⃣ *TABA ALQUR'ANI;*
Mai al'ada bata taba ALQUR'ANI,
kasantuwar sa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.

7⃣ *KARATUN ALQUR'ANI;*
Mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duk da cewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karanta daga abunda ta haddace domin kada ta manta sabanin dauka.

8⃣ *SADUWA;*
Baya halatta saduwa da mace
a lokacin al'ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu
da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa Allah ba hasali ma ta yi biyayya ne ga reshi, baya halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai
al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al'adar ta dauke amma batayi wanka ba to bai halatta a sadu da ita ba. Ya
halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa a lokacin da take al'ada bayan ta yi
*kunzugu* in banda daga *cibiyarta* zuwa *gwiwarta*
wannan kam bai halatta ba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta
taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.

9⃣ *TABBATAR DA RASHIN TSARKI;*  Al'ada tana
tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.

🔟 *WAJABTA WANKA;*
  Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANI AKAN JININ BIKI(JININ HAIHUWA) INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

Monday, 15 October 2018

011 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha daya 011_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*


*ALAMOMIN DAUKEWAR JININ AL'ADA;*

Idan jinin al'ada ya dauke akwai wasu  alamomi da shari'ah ta sanya domin su zama manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, ga alamomin kamar haka:

1⃣ *BUSHEWAR GABA;*
Abunda ake nufi shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gaban ta, sannan ta fito dashi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata
al'adarta ta dauke.

2⃣ *FARAR KUMFA;* 

Wannan wani ruwa ne fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka karshen al'adar ta, ta sani ta kammala Al'adar ta.

Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba yin al'ada ba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki, ba sai ta jira farar kumfa ba, amma idan wacce ta saba gani ce sai ta ga bushewar gaba to malamai suka ce zata dan saurara kadan domin jiran farar kumfa, amma jinkirin ba zai kai
ga fitar zababbun lokutan sallah ba.

    A dunkule dai kowane daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu a lokaci
guda ba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai kiyi wankan tsarki domin ki cigaba da
ibada, domin idan ba kiyi wanka ba ko da jinin ya dauke mijin ki ba zai sadu da dake ba kuma baza kiyi  sallah ba, da dai sauransu.

Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga - diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jini ne, amma idan a karshen jini ne to wannan ba komai,
Ummu Adiyyah matar Manzon Allah  (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: *((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)).* [Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368 , Ibnu Majah Hadisi Na: 647,
Darimi Hadisi Na: 865].

Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar
asuba, amma ba'a ce ta tashi cikin dare ba domin ta duba.!!!

 

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ABUBUWAN DA BASU HALATTA GA MAI AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*

http://wa.me/+2349031666613

010 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na Goma 010_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*


*KARKASUWAR MATA GAME DA JININ AL'ADA:*
    Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; *WACCE TA FARA,* Kashi na biyu kuma; *WACCE TA SABA,* sannan sai kashi na uku; *MAI JUNA BIYU,*
mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka;
1⃣ *WACCE TA FARA;*
  Ita wacce ta fara al'ada ya zama shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwar ta, to abunda ke kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zai  dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha- biyar ba,(KAMAR YADDA BAYANI YA GABATA A RUBUTUKAN DA SUKA GABATA) idan ko ya wuce sha-biyar to abunda ya
doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'ada ba, kenan mafi yawan kwanakin da zata yi la'akari dasu sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama abunda ake kira
*(Isthala)* wato cuta sai a nemi magani, a karkashin wannan nake cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu mata su rika tuntubar su suna fahimtar da su
tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci yayi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka,ko makaman tan hakan Wanda wannan Na faruwa kwarai da gaske, wata babbar mace ce amma bata san menene jinin al'ada ba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganin shi,  kunga akwai hadari kwarai da gaske.

2⃣ *WACCE TA SABA:*
Abunda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku, a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai yayi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai a kira ta da sunan
wacce ta saba, domin ta saba akan kwanaki sanannu.
  Amma idan ta yi al'adar karo na farko
kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar
karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da
tsayayyun kwanaki.
  Ita wacce ta saba wato wacce take da
sanannun kwanakin al'ada to wadannan
kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada,
amma idan kwana kin suka cika al'adar kuma bata dauke ba sai ta kara kwanaki uku,haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki sha biyar su cika, misali idan al'adar ta kwanaki biyar ne sai kuma jinin bai dauke ba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan kwanaki takwas din sun zama sha-daya idan bai dauke ba sai ta kara uku sun zama sha-hudu idan bai dauke ba sai ta
kara kwana daya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai dauke ba domin kwanakin al'ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma
sun cika, abunda ya cigaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada ba,sunanshi jinincuta *(Istihala)*
  sai a nemi magani.  A dukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na
saurare sai ya dauke a kwana na daya cikin ukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

3⃣ *MAI JUNA BIYU(mai ciki);*  Galibin mata masu
juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga
al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita.
  Idan al'ada ta zowa mace mai juna-biyu, to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin
al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata
iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan
Kina da juna biyu kuma kika ga jini.

   *TANBIHI NA DAYA:*
   Idan mace jini yana mata wasa wato yazo yau ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abunda zata yi anan shine, ta tsaya ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki
domin da hakane zata cika kwanakin ta na al'ada, *MISALI,* kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki tara, wannan matar ita
ake kira *(Al-Mulaffiqa)* a larabcin mata masu
al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da
dawowarsa to na biyun zai zama sabon jini ne kenan, ba na da ne ya dawo ba.


ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ALAMOMIN  DAUKEWAR JININ AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

009 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na Tara 009_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*TABBATUWAR JININ AL'ADA;*
     Shifa abinda ya
shafi jinin al'ada al'amari ne da Allah madaukain sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa:

```''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada,
Kace: Shidinnan cutane, ku nisanci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke), idan suka tsarkaka
(suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba
kuma yana son masu tsarkaka''.```
*[Bakara, ayata:222.]*

Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; ```(Wannan)
Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan
Adam''.```
> Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci
a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane
ya rike masa makoshi(makogaro) sai ya amayar da ganyen shi yasa maza basa yi.
   Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar.

Shifa jinin al'ada kada amanta jini ne da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu,
Allah madaukakin Sarki ya halicceshi domin ya zama abinci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da
mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sai Allah ya sanya shi ya zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga
mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada.

Idan kuma ta haihu sai Allah ya mayar dashi nono jaririn yana sha amatsayin abinci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata
da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya
kasance ba inda zaije(jinin al'adar) to shine sai ya taru a
mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko
bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan (kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah).

ZAMU TUQE A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANI AKAN KARKASUWAR MATA AKAN JININ AL'ADA INSHA ALLAHU

ALLAH YAYI MANA JAGORA

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE;

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

008 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na takwas 008_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*MINENE MAFI QARANCIN JININ AL'ADA?*
   Malamai sun karawa juna sani
kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.

*MINENE MAFI YAWAN JININ AL'ADA?*
  Mafi yawan kwanakin jinin al'ada shine kwanaki goma sha-biyar, kenan idan ya
wuce haka to bai zama jinin al'ada ba muddin ba ciki take da shiba.

*MATA DANGANE DA JININ AL'ADA:*

  Anan ya kamata mu san cewa mata
suna da halaye biyar musamman idan muka yi
la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya
zo na al'ada ne ko bana al'ada bane, halayyar itace kamar haka:

1. *KASA DA SHEKARA TARA;*    Idan jini ya zowa
yarinyar da take kasa da shekara tara, to malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada bane, jinin ciwone sai a nemi magani.

2. *SHEKARA TARA ZUWA SAMA;*    Idan ya  zamana jinin ya zo ne
ga wacce ta cika she kara tara zuwa zamanta budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi
kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin na al'adane ko na ciwo.
Kada mu sha'afa
yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da
hutu da wahala suna tasiri a irin wannan wuri.
3. *BUDURCI ZUWA SHEKARA HAMSIN;* 
  Idan jini yazo
daga lokacin da ta zama budurwa zuwa shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun
tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.

4. *DAGA SHEKARA HAMSIN ZUWA SITTIN DA TARA(50-69);*
  Idan jini ya zowa mace a tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara
hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai sukace za'a tambayi kwararrun mata da likitoci domin sanin wannan jinin na ciwone ko na
al'ada.

5. *DAGA SHEKARA SABA'IN ZUWA SAMA;*
  Idan jini ya zo bayan mace ta cika
shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai sukace wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane.
Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce-hukunce akansu, kuma ana gini ne akan tsarin
kalandar musulunci, wadannan bayanai na karkasuwar mata har zuwa gida biyar kamar yadda ya gabata haka *MALAM ADAWY*
  ya kawo a cikin littafinsa *'Hashiyatul Adawi'*, Allah ya ji kansa da gafara.

  Ina Kara jaddada cewa yanayin abin ci da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri
matuka, dukkan abinda ba'a mahimta ba
dangane da yana yin zuwan jini ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi
tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi
bayani da cewa yanada alaka da hukunce
hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da
aka *SAKI* zata iya kammala idda a kasa da watanni uku.
Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shine zuwansa na farko sannan ya tabbata
cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga,
dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau
kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta mata lada idan kuma ta bari samari suna
jagwalgwalarta ita za'a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara yi mata rubutu, kenan har azumi idan ta sha sai ta ranka.


ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN TABBATUWAR JININ AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE;
✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

007 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na bakwai 007_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*



*HUKUNCIN JININ AL'ADA ( JININ HAILA)*

Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad s.a.w, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya.
   Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jerin hukunce-hukuncen jinin al'ada wanda ake kira jinin haila,
da izinin Allah bayanshi za mu
kawo hukunce-hukuncen jinin biki (wato jinin
haihuwa).

*Muhimmanci:*   yana da matukar muhimmanci sanin hukunce hukunce jinin al'ada, muhimancin
bawai ya tsaya ga mata bane kadai, a'a har da maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada, misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko
dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta
bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a
sakinta ba kuma a saduwa da ita, sannan ga yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta
yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku
(al'ada uku) kafin ace ta kammala idda, sannan sai ai maganar sabon aure, to idan tana
al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan
sai bayan shekara daya da rabi za'a fara maganar aure, shi yasa muka ce sanin hukunce-hukuncen wannan jini ba wai ya rataya ga mata bane kadai har da maza.

*MINENE JININ AL'ADA:???*

    Jinin al'ada jinine da yake fita da karan kansa ta gaban macen da a
al'adance zata iya daukar ciki, ba tare da ya wuce
kwanaki goma sha-biyar ba.

Wannan shi ake nufi da jinin al'ada, da akace *'jinine da yake fita da kansa'* kenan idan ya
zamana ba da kansa ya fita ba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jini
ya balle mata to wannan bai zama jinin al'adaba.
   Da akace *Ta gaba*' kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al'adaba.
  Da akace *'Wacce a al'adance zata iya daukar ciki'* kenan idan ya fita daga wacce a al'adance ba zata iya daukar ciki ba sabo da
yarinta ko girma to wannan shima bai zama jinin al'adaba.

Amma da aka ce *'Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba'* kenan idan ya wuce kwanaki
sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba.

Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin
al'adaba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau kansu ba, za su yi sallah domin jinin ciwone sai a
nemi magani, Allah ya sawwaka.

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA, INDA ZAMUYI BAYANIN MAFI QARANCIN JININ AL'ADA.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE; *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

006 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na shida 006_

Gabatarwa: *UMMU SUNAN*

🔸 *DAGA CIKIN ABUBUWAN DAKE WAJABTA WANKA.*

1⃣  ```FITAR DA MINIYYI TA HANYAR SHA'AWA, A CIKIN BARCI KO A FARKE.```

2⃣ ```SADUWA DA IYALI(JIMA'I)```

3⃣ ```FITAR JININ HAILA(Al'ada) KO NA BIQI(Na haihuwa)```

4⃣ ```MUTUWA```

✍ *AL-ALLAMA SHEIKH MUHAMMAD BIN SALIH AL-UTHAIMIN*
(RAHIMAHULLAH) YAKE CEWA;

1⃣ *FITAR DA MANIYYI TA HANYAR SHA'AWA, A CIKIN BARCI KO A FARKE;* Duk Wanda ya fitar da maniyyi a cikin barci, wanka ya wajaba a gareshi, saboda Wanda yake barci yana mafarki, idan mafarkin yasa ya fitar da maniyyi, yana wajaba yayi wanka a kowane hali.

2⃣ *SADUWA(JIMA'I);*
    Idan miji ya sadu da matarshi, yana wajaba wanka a garesu, saboda boyuwar hashafa a cikin al'aurar matarshi, saboda fadar manzon Allah s.a.w cewa;

➡ << Ruwa daga ruwa suke>> Ma'ana: wanka yana wajaba a lokacin da namiji ko mace suka fitar da maniyyi.

➡<< Idan miji ya zauna tsakanin gabobinta guda hudu(matarsa) kuma yaji dadi da ita, wanka ya wajaba a garesu, koda basu fitar da komai ba, wannan matsalar(SADUWA BA TARE DA FITAR DA MANIYYI BA) da yawa daga cikin mutane suna jahiltar wannan hukuncin, ta inda wasu mazan suke amfani da yatsunsu a wajen saduwa da iyalansu ba tare da fitar da maniyyi ba sai suki yin wanka saboda jahilcin dake addabarsu, Malam yace wannan al'amari akwai hadari a cikinsa kwarai da gaske, abunda yake wajibi shine mutum yasan cewa idan ya sadu da iyalansa koda bai fitar da komai ba, wanka ya wajaba a garesu(mijin da matar).

3⃣ *FITAR JININ AL'ADA KO NA HAIHUWA;*
   Ita mace idan HAILA tazo mata sai ta dauke, yana wajaba tayi wanka, saboda fadar Allah S.W.T;
  "KU NISANCI MATA A LOKACIN DA SUKE HAILA, KADA KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI, IDAN SUNYI TSARKI TOH SAI KUZO MASU TA INDA ALLAH YA UMURCEKU, LALLAI ALLAH YANASON MASU TUBA, KUMA YANASON MASU TSARKAKEWA".
  Da fadar Manzon Allah s.a.w cewa; " MAI HAILA IDAN TA KARE KWANAKIN HAILARTA, DA MATA WADANDA SUKA HAIHU IDAN JINI YA DAUKE MUSU, NA GARESU SUYI WANKA."

  Siffar yadda ake wankan haila da na haihuwa kamar siffar yadda ake na janaba yake, sai dai wasu malaman sun so a wankan haila ko haihuwa ayi da ganyen magarya, saboda shi yafi a wurin tsafta da tsarki.

4⃣ *MUTUWA;* Dalili akan wankan gawa shine fadar Manzon Allah s.a.w cewa; "KU WANKE TA SAU UKU, KO SAU BIYAR KO SAU BAKWAI KO FIYE DA HAKA IDAN KUNGA YIYUWAR HAKAN.....HADITH

Da fadar Manzon Allah s.a.w cewa; " KU WANKE SHI DA RUWA, DA GANYEN MAGARYA, KU RUFESHI DA TUFAFINSA"...(mutumin da ya mutu a arfa a lokacin Manzon Allah s.a.w)

Sai Malamai sukace; Su wadanda suka mutu, wanka Na wajaba garesu, sai sai dai wajabcin yana hawa akan yan uwansu rayayyu, saboda shi Wanda ya mutu komi nashi ya yanke, bazai iya aikata komai ba, saboda haka yan uwansu dake raye su zasu yi musu wanka, kamar yadda Manzon Allah s.a.w ya umurta da yin haka.

▪_________________
◼ *Majmu'u fatawa warrasa'il Na Sheikh Muhammad bin Salih Al-uthaimin, Mujalladi Na sha daya, babin wanka.*

SAI WANI LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE; *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613