Thursday, 15 November 2018

01DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...

🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘

*وليتذكر أولو الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*
🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶

_Fitowa Na Farko 001_

Gabatarwa: *MUKYAUTATA NIYYA GROUPS*

*ASALIN MAULIDI A MUSULUNCI DA WA’DANDA SUKA K’IRK’IRE SHI!!*

MAGABATAN WANNAR AL’UMMA BA SU YI MAULIDI BA KAMAR YADDA KOWA YA SANI, K’ARNUKAN DA MANZON ALLAH (SAW) YA YABESU WATO K’ARNI NA FARKO DA NA BIYU DA NA UKU DUKA SUN GABATA AMMA LITATTAFAN TARIHI BA SU KIYAYE MANA CEWA AN SAMU WANI DAGA CIKIN SAHABBAI KO TABI’AI KO MABIYA TABI’AI, DA MA WA’DANDA SUKA ZO A BAYANSU DA YA YI MAULIDIN ANNABI (SAW) BA, DUK DA TSANANIN SOYAYYARSU GA MANZON ALLAH S.A.W, KUMA DUK DA CEWA SUN FI KOWA ILIMIN SANIN ADDININ MUSULUNCI, KUMA DUK DA CEWA SUN FI KOWA KWA’DAYIN BIN SHARI’AR ANNABI (SAW).

FARKON WA’DANDA SUKA FARA MAULIDIN ANNABI S.A.W  SUNE :
*BANU UBAID AL-K’ADDAH*, WA’DANDA SUKE KIRAN KANSU DA *FA’DIMIYYUNA*
MA’ANA JIKOKIN FATIMA (R A). SABODA SUNA DANGANTA KANSU ZUWA GA ZURIYYAR ALIYU (R A),
ALHALI A HAK’IK’ANIN GASKIYA WA’DANNAN MUTANE SU NE SUKA ASSASA *DA’AWAR BA’DINIYYA,* WATO ‘YAN BA’DINIYYA MASU CEWA ADDINI YANA DA ZAHIRI YANA DA BA’DINI, KUMA WAI SUNE SUKA SAN BA’DININ.

*ASALIN KAKANSU*
SHI NE *IBNU DISAN,* WANDA AKA FI SANI DA *AL- K’ADDAH,* YA KASANCE MAULA NE NA *JA’AFARUS SADIK’* WATO ‘YANTACCEN BAWANSA, KUMA ‘DAN ASALIN GARIN *AHWAZ* NE, ‘DAYA DAGA CIKIN WA’DANDA SUKA ASSASA MAZHABAR *BA’DINIYYA* A IRAK’I, SANNAN SAI  YA BAR GARIN ZUWA MAGRIB, TO A WANCAN YANKIN NE YA DANGANTA KANSA ZUWA GA *AK’ILU ‘DAN ABI ‘DALIB,* YA RIYA CEWA SHI DAGA TSATSONSA YAKE,  TO A LOKACIN DA *RAFIDA* MASU GULUWI SUKA AMSA DA’AWARSA, SAI YAYI DA’AWAR CEWA WAI SHI ZURIYYAN *MUHAMMAD BIN ISMA’IL BIN JA’AFAR AL- SADIK’* NE, KAWAI SAI SUKA YARDA DA HAKAN DUK DA CEWA SHI *MUHAMMAD BIN ISMA’IL*  YA MUTU BAI BAR *‘DA* BA,
DAGA CIKIN WA’DANDA SUKA BI SHI AKWAI *HAMDAN K’URMU’D*, WANDA *K’ARAMI’DA* SUKE DANGATUWA GARE SHI. DA ZAMANI YA YI NISA SAI *SA’ID BIN HUSAINI BIN AHMAD BIN ABDULLAH BIN MAIMUN BIN DISAN* YA BAYYANA, SAI YA CANZA SUNANSA DA NASABARSA, SAI YACE WA MABIYANSA SHINE *UBAIDULLAHI BIN HASAN BIN MUHAMMAD BIN ISMA’IL BIN JA’AFAR AL- SADIK’*, A HAKA SAI FITINARSA TA BAYYANA A MAGRIB.

DON K’ARIN BAYANI AKAN WANNAN BAYANI, DUBA *WAFIYYATUL A’AYAN*( 3/ 118), *ALBIDAYA WAN NIHAYA* (11/ 202), *FABHA’IHUL BA’DINIYYA* SHAFI NA (11), *ALFARK’U BAINAL FIRAK’ NA BAGDADIY* SHAFI NA (266 – 267).

KHALIFOFIN DAULAR RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA/FA’DIMIYYA DAKE *MISRA* SUNE SUKA FARA DUKKANNIN MAULIDI!

DON HAKA FARKON WA’DANDA SUKA FARA MAULIDI SU NE RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA WA’DANDA SUKA YI NUFIN CANZA WA MUSULMAI ADDININSU, TA HANYAR SHIGAR DA ABIN DA BA YA CIKINSA.
UBAIDIYYUNA SUN SHIGA MISRA NE A *SHEKARA TA 362 BAYAN HIJIRA*, A RANAR *5 GA RAMADAN*, WANNAN NE FARKON LOKACIN DA SUKA FARA MULKINSU A MISRA, WASU SUN CE: RANAR *7 NE GA RAMADAN,* TO DUKKANNIN MAULIDI NA ANNABI (SAW) DA NA WANINSA WA’DANNAN MUTANE UBAIDIYYUNA SUNE SUKA FARASHI,
BABU WANDA YA TA’BA YIN MAULIDI KAFINSU.
*AL- MIK’RIZIY* YACE; KWANAKIN DA KHALIFOFIN FA’DIMIYYA SUKA RIK’A A MATSAYIN RANAKUN IDI, DA RANAKUN TARO WA’DANDA AKE YALWATAWA TALAKAWA DA YAWAITA MUSU NI’IMOMI YA KASANCE KHALIFOFIN FA’DIMIYYA SUNA DA RANAKUN IDI DA NA TARO A TSAWON SHEKARA, GA SU KAMAR HAKA:
*BIKIN DAREN FARKON SHEKARA,* DA, *BIKIN RANAR FARKON SHEKARA,* *RANAR ASHURA,* *RANAR HAIHUWAR ANNABI (SAW),* *RANAR HAIHUWAR ALIYU (RA),* *DA RANAR HAHUWAR HASAN (RA),* *DA RANAR HAHUWAR HUSAINI (RA),* DA RANAR HAIHUWAR *FATIMA AL- ZAHARA’U (RA),* DA RANAR HAIHUWAR *KHALIFA MAI CI A LOKACIN,* DA IDIN DAREN *RAJAB,* DA DAREN TSAKIYAR *RAJAB,* DA DAREN FARKON *SHA’ABAN,* DA TSAKIYAR *SHA’ABAN,* DA TARON IDIN *SALLAR AZUMI,* DA NA IDIN *LAYYAH,* DA IDIN *GADEER,* da sauransu...

SA’ANNAN SAI *AL- MAK’RIZIY* YA ‘DAUKESU ‘DAYA BAYAN ‘DAYA YANA BAYANIN YADDA SUKE YINSU. DUBA *AL- KHI’DA’DUL MIK’RIZIYYA* (1/ 490).

*YANAYIN MULKIN KHALIFOFIN RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA TA DAULAR FA’DIMIYYA, WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI:*

SARAKUNAN DAULAR FA’DIMIYYA TA RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA SUN FUSKANTAR DA SIYASARSU NE ZUWA GA MANUFA GUDA ‘DAYA, ITA CE: YIN DUKKAN IYA K’OK’ARINSU NA TILASTAWA MUTANE AKAN SU BI ADDININSU NA RAFIDANCIN BA’DINIYYA, DA SANYA SHI YA ZAMA SHI NE AWWALU MAA YAJIBU A DUKKAN GARURUWAN MISRA, DA MA SAURAN GARURUWAN DA SUKE MULKI, DA MAK’OBTANSU.
SARAKUNAN WANNAR DAULA SUN YI MATUK’AR MU’AMALA DA YAHUDAWA DA NASARA, TA YADDA SUN NUNA MUSU SOYAYYA SOSAI, SUN BASU MUK’AMAI MASU GIRMA A CIKIN WANNAR DAULA.
DUBA *ALBIDAYA WAN NIHAYA* (11/ 358), *AL- MUNTAZIM* (7/ 190), *ITTI’AZUL HUNAFA* (1/ 297), *AL- DAULAR FA’DIMIYYA* SHAFI NA (202).

HAK’IK’A AL- UBAIDIYYUNA/RAFIDA/‘YAN BA’DINIYYA DA SARAKUNAN DAULAR FA’DIMIYYA, SUN KAI MATUK’A WAJEN YA’DA TSINUWA GA KHALIFOFIN ANNABI (SAW) GUDA 3; *ABUBAKAR* (RA), DA *UMAR* (RA), DA *USMAN* (RA) DA SAURAN SAHABBAI.
SABODA SUNA K’IRGASU A CIKIN MAK’IYA ALIYU (RA). TARE DA WATSA FALALAR ALIYU (RA) DA ‘YA’YANSA TA HANYAR ZANAWA A JIKIN MANYAN K’ARFUNA DA RUBUTAWA A JIKIN KATANGUN MASALLATAI,
KUMA MASU HU’DUBA SUN KASANCE SUNA TSINE MA SAHABBAI AKAN DUKKANNIN MINBARORIN K’ASAR MISRA GABA ‘DAYA.


KADA RUBUTUN YAYI TSAYI, ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU.

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*


*ABU-SINAN*

ISTIKHARA

*SALLAR ISTIKHARA(NEMAN ZABIN ALLAH) A MUSULUNCI*
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

Wallafar Dalibinku;
✍ *ABBAN SINAN*

http://darulfikr.com/ebook/41913

KU SAUKE KU KARANTA ZAKU KARU MATUKA

http://wa.me+2348064734911

BINCIKE...

*ANALYSIS*

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Yan uwa na masu albarka dake group din *MUKYAUTATA NIYYA* both, na *Mata* dana *Maza* ina bukatar taimakonku a wannan shekarar domin Isar da sakon Allah.
Wane irin taimako ne???
Nayi shiri na musamman domin fadakar da yan uwa musulmi cewa *Maulidi* bashi da Asali a cikin addinin Islama, a tare da haka sai nayi wani bincike, *Misali:* Ni ina da Abokai masu WhatsApp mutum 500+, ina da groups 100+, a Facebook ina da abokai 5000, da masu bibiya 1000+ a Facebook ina da groups, Wanda idan aka Tara mutanenshi sun kai 100,000+ bari na tsaya a haka, idan nayi posting duka wadannan zasu gani, abokanansu ma zasu gani, toh abunda Nike bukata a yanzu shine, kaima/kema kuna da WhatsApp friends da groups, me kake/kike tsammani idan kikayi copy na post din ka/kika watsa shi ga abokanka/ki???
Muyi tarayya a wurin yada alkhairi shi yafi domin mu rabauta a wurin Allah, kamar yadda sanarwa ta gabata cewa, salon da'awar a wannan karon zai chanja, taken rubututtukan shine;
ﻭَﻟِﻴَﺘَﺬَﻛَّﺮَ ﺃُﻭﻟُﻮ ﺍﻟْﺄَﻟْﺒَﺎﺏِ...
those of understanding would be reminded...
Domin masu hankali suyi tunani...
Suratu sad aya ta 29

Miye shawararku, ko goyon bayanku akan hakan???

Ina saurare domin karba, ina saran fara rubutu a 29 safar 1440AH insha Allahu

#ABBAN_SINAN
#MAULIDI
#SHAWARA
#MUKYAUTATA NIYYA

http://wa.me+2348064734911

17 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha bakwai 017_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*SUNNONIN ALWALA:*
1⃣ Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A Ruwa, ta yadda mai alwala zai karkato butar alwala domin ya wanke hannayen sa zuwa  wuyan hannu.

2⃣ *Kuskurar Baki:*    
  Mai alwala ya tabbata ya sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya kuskure bakinsa da
ruwan.

3⃣ *Sha'ka Ruwa:*
  Shine mai alwala ya shaki ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai, sai dai kawai idan yana azumi ne sai yayi kadan. Amma yadda mutane suke shafar hancinsu wai da sunan shaka ruwa wannan bai dace ba, ya kamata mu gyara.

4⃣ *Facewa:*
  Mai alwala zai shaki ruwa ne da
hannun dama sai ya sa hannun hagu akan karan hancin sa, sannan sai ya fyato ruwan da
ya shaka.

5⃣ *Shafar Kunne;*
  Mai alwala ya tabbata ya shafi cikin kunnensa da wajen kunnen, zaka/ki sanya yatsanka manuniya(☝) a cikin kunnen sannan kasa babban yatsa(👍) a wajen kunnen sannan sai ka shafa.

6⃣ *Sake Taba Ruwa:*
A lokacin da zaka shafi kunne shin zaka shafi kunnen ne da ragowar
danshin hannuka da ka yi shafar kai da shi? Ko ko zaka sake taba ruwa na musamman domin
shafar kunne, malamai sun karawa juna sani, ko
wanne ka yi ya yi daidai.

7⃣ *Dawo Da Shafar Kai:*
Ka tsaya ka fahimta, shi shafar kai farilla ne, amma dawo da shafar
kai sunnah ce daga cikin sonnonin alwala.

8⃣ *Jeranto Farillai:*
Ta yadda zaka kawosu daya-bayan-daya kamar yadda aka lissafosu, kada ka dauki na uku ya zama shine na farko
sannan ka biyo shi dana biyar, misali…'.

Wadannan sunnonin matsayinsu bai kai matsayin farillai ba,
amma suna cikin manyan abubuwan da suke cika alwala.


ZAMU DAKATA ANAN SAI LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANIN *MUSTAHABBAN ALWALA* INSHA ALLAHU



WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE;
✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_)*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

16 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha shida 016_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*FARILLAN ALWALA*

1⃣ *Niyyah:*
Domin a bambance wanda ya sa ruwa domin sanyaya jiki, ko domin gusar da
datti, duk wannan ba niyya ce ta alwala ba.

2⃣ *Wanke Fuska:*
  Ita kuma fuska ta bangaren tsawo tana farawa ne daga matsirar gashin kai zuwa karkashin haba(gemu), amma
ta fuskar fadi tana farawa ne daga kunnen dama zuwa kunnen hagu, wannan shine abinda yake amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar ko ina ya samu ruwa kamar kasan haba, gefen
ido da gefan kunne da matsa-matsin karan hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu
kamar alwalar yarace.

3⃣ *Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu;*
Mai alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke hannayensa tun daga saman yatsunsa (farce/kaifa) har zuwa gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga inda ya wanke, anan ma akwai manyan mutane masu alwalar yara.

4⃣ *Shafar Kai:*
Ka tabbata ka hada yatsunka sannan kuma ka fara shafar daga goshi (dai-dai
matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya.

5⃣ *Wanke Kafa:*
Haka nan mai alwala ya tabbata ya wanke kafarsa har zuwa idon sawu,
wato wadannan kasusuwan guda biyu dake
gefen kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.

6⃣ *Cudanyawa:*
  Mai alwala ya tabbata ya cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya
shiga ko ina.

7⃣ *Jerantawa:*
  Abinda ake nufi shine a lokacin da ka fara alwala to ka dakatar da komai sai ka kammala, amma kana alwala kana kuma wata sabga daban wannan ba dai dai bane.

Mai alwala ya tabbata ya gabatar da wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta yadda idan aka rasa daya daga cikin su to alwalarka ta shiga chakwakiya.


ZAMU DAKATA ANAN INSHA ALLAHU SAI WANI LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *SUNNONIN ALWALA*


DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

15 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha biyar 015_

Gabatarwa; *UMMU SINAN*

*FALALAR ALWALA;*
Kasantuwar cewa alwala wajiba ce wannan kadai ya isa ka gane falalar ta a
musulunci domin dukkan abunda akace farillah ne
to wannan matsayi ne mai zaman kanshi, bayan hadisi na 62 a cikin *Muwadda Malik* yana cewa; An karbo daga Abdullahi As-Sunaabihi, lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:  *''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi kuskurar baki dukkanin laifukan dake bakin sun Wanke, idan kuma ya shaqa ruwa sai ya fyace, dukkan laifukan daya shaka sun fice, idan kuma ya wanke fuskarsa laifukan da ke fuskar ta sa sun wanke, har wadanda ke karkashin girar shi, idan ya wanke hannayensa laifukan dake hannayensa sun fice, har wadanda ke karkashin akaifarsa (farce), idan kuma ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun fice har wadanda ke kunnuwansa, idan kuma ya wanke kafafuwansa duk laifukan dake kafafuwansa sun fice, har wadanda ke karkashin farcen kafafun nashi."*
Sannan kuma
tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya zama wani
kari ne da yake da shi na lada''.
Lalle wannan bakamar falala bace da alwala take da shi, domin mai alwala zai kasance yana kammala alwala zunubanshi suna digewa a
kasa, amma wani hanzari ba gudu ba, wannan ladan zai tabbata ne ga wanda ya yi alwala a yadda shari'a ta tabbatar da ita ba wacce ya tsinta a
kan titi ba.

*SHARUDDAN ALWALA*

  Sharuddan alwala sune abubuwan da ake so mai alwala ya cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:

1⃣ *Musulunci*
  kenan idan wanda ba musulmi ba ya yi alwala bata yi ba.

2⃣ *Hankali*
Idan mahaukaci ya yi alwala itama bata yi ba.

3⃣ *Wayau*
Idan dan karamin yaro mara dabara
ya yi bata yi ba.

4⃣ *Ruwan ya zama mai tsarki*
Idan ya zama ruwa ne mara tsarki to alwalar bata yi ba, bayanai sun gabata akan hukunce hukuncen ruwa.
5⃣ *Ruwan ya zama na halas*
Idan ruwa ne da
mutum ya sata ko ya same shi bata shar'antacciyar hanya ba to alwalar bata yi ba.

6⃣ *Ya kasance mai tsarki*
  Idan mai alwala ya
kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba.

7⃣ *Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga*
Kenan idan mutum ya kasance yana sanye da wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi, kamar zobe da sauransu.


ZAMU DAKATA A NAN INSHA ALLAHU SAI WANO LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *FARILLAN ALWALA*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

14 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha hudu 014_

Gabatarwa; *UMMU SINAN*

   Alwala ibadace mai zaman kanta
wacce Allah madaukakin sarki ya shar'anta ta
kafin gabatar da wadansu ibadu musamman ma
sallah, mutum yana samun cikakken ladan alwala idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin
sarki ya saukar da hukunce-hukuncen alwala a cikin littafinsa mai girma alkur'ani:

*''Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan kuka ta shi za ku yi sallah to ku wanke fuskokin ku da hannayanku zuwa gwiwar hannu ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa idon sawu (idon kafa)…''* [Suratu Ma'ida, aya ta: 6].

Tabbas wannan aya ta yi bayanin wajibcin alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi a wanke ko kuma a shafa, sannan kuma ayar ta iya kance
ko wanne mahalli.
       Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana siffar yadda alwalar take da maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake
gamsasshen bayani.

Ka sani lalle ita wannan alwala tana da falala da kuma sharudda da kuma farillai sannan tana da sunnoni da kuma mustahabbai, sharuddan nan
da farillai tabbas a tabbata mun sansu alokacin gabatar da alwala iya gwargwado domin da sune alwala zata zama karbabbiya, amma su sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne ta inda matsayinsu bai kai matsayin farillai ba.

ZAMU DAKATA A NAN INSHA ALLAHU SAI WANI LOKACI NA GABA ZAMUYI BAYANI AKAN *FALALAR ALWALA*

DOMIN SHIGA GROUP DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613