Sunday, 3 February 2019

SUNNONIN SALLAH

SUNNONIN SALLAH
Shinfida: Su sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah, saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba.
Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya. Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyaran sallah ta hanyar yin kabaliyyah ko ba’adiyyah, amma ita farilla ba’a yi mata hakan.
Sunnonin Sallah: su sunnonin sallah suna da yawa, sun fi farillan sallah yawa, ga kadan daga cikin su:
1.Tada Ikamar Sallah: Ita ikamar sallah ta shafi mai sallah shi kadai ko wadanda za su yi ta cikin jam’i, kuma bayananta sun gabata a Babi Na shabakwai (017).
2. Karatun Sura Bayan Fatiha: Kasancewar shi karatun Fatiha yana cikin farillan sallah to yanzu shi karatun sura bayan fatiha yana cikin sunnonin sallah ne, kuma wadannan bayanai sun shafi maza da matane baki daya, domin duk abinda aka umarci maza da shi an umarci mata das hi saidai abinda shar’a ta ware tace banda mata. Kuma mutum ya tashi ya koyi karatun sallah daga bakin malamai. Sannan mu sani shi karatun sura bayan fatiha ana yin shi ne a raka’o’i biyun farko, kenan banda na karshe, kamar haka: Asuba ana yi a duka raka’o’in, Azahar ana yi ne a raka’o’I biyun farko banda biyun karshe, la’asar ma haka, haka namma magariba banda dayar karshe, sannan ita ma isha banda biyun karshe.
3. Tsayuwa Domin Karatun Sura: Kenan kamar yadda karatun surar yake sunnane to hakama yin karatun a tsaye, kenan ba’a karatun sura a zaune sai dai idan akwai larura da shari’a ta yadda da ita.
4. Sirrantawa A Inda Ake Sirrantawar : Abinda ake nufi da sirrantawa shine ka motsa harshe domin yana furta karatun Alkur’ani, wato bakinka na motsi kenan, amma idan mutum ya yi shiru yai dunkum ba’a kiran wannan asurtawa. Inda ake surrantawa kuma sune: Azahar da la’asar bakidaya raka’oinsu, sai kuma raka’ar karshe ta magariba da kuma raka’oi biyun karshen Lisha. Haka kuma nafilfilin rana suma ana asurta su ne.
5. Bayyanawa A Inda Ake Bayyanawa: Idan kuma akace bayyanawa ana nufin ka jiyar da kanka da kuma wanda yake kusa da kai, wannan idan kai kadai kake sallah kennan, amma idan kai limanne to zaka daga murya yadda kowa zai ji, ai domin karatun limanne aka hana mamu su yi na su karatun.
Kuskuren da ake samu anan shine, idan mutum ya shigo masallaci zai yi sallah ko kuma ya mike yana ramo raka’o’in da suka wuce shi sai ya bude baki yana karatun sallah da karfi, wanda wannan yana shiga cikin karatun wani, yana kuma hargitsawa wani nashi karatun, inda kowa zaibi yadda bayan suke to da an yi komai cikin jin dadi da walwala, zuwa inda ake karatu shi zai magance wadannan matsalolin.
Wuraran da ake bayyana karatun sallah kuma sune kamar haka; Karatun sallar asuba baki-dayanta, raka’ar karshe ta sallar magariba, da kuma raka’o’in karshe na sallar lisha.
6. Kabarbari: Dukkanin kabarbarin sallah sunnane in banda kabbarar farko wacce take ita farillace wato kabbarar harama. Saidai malamai sun karawa juna sani akan cewa; shin dukkanin kabarbarin a dunkule suke sunnan guda koko kowacce kabbara sunnace mai zaman kanta?.
7. Tahiyyah: Itama tana cikin abinda ya kamata mutum ya koya daga bakin malami kai tsaye, yana karantawa kana karantawa, domin ana samun kura kurai masu tarin yawa a lokacin mutane suke karantata.
8. Zama Domin Tahiyyah: Ashe itama ba’a yinta a tsaye, kuma inda mutum zai zauna amma bai karantata ba to yabar sunnah guda daya, idan kuma ya manta bai yi zaman farkoba misali to yabar sunnoni biyu kenan, karatun tahiyyar da kuma zama domin karatunta.
9. Gabatar Da Fatiha Kafin Surah: Inda mutum zai zai fara karanta surah sannan ya zo ya karanta fatiha to da ya bata tsarin sallah, domin yadda ake so shine ka fara gabatar da fatiha sannan ka sai ka karanta surah.
10. Bayyanar Da Sallama: Kenan ita sallama ba’a asurce ake yenta ba, ana bayyana tane, anan mu ban-bance shi yin sallamar wajibine, amma yenta kuma a bayyane sunnane daga cikin sunnonin sallah.
11. Salati Ga Ma’aikin Allah : Yin salati ga manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana daga cikin sunnonin sallah. Kuma shi salati ga ma’aikin Allah yana da muhimmanci da lada da kuma falala mai zaman kanta, malamai sun kawo sigogi na salati ga ma’aikin Allah a kicin littafansu kamar mai littafin Ashmawi ya kawo haka nan ma mai littafin Iziyyah da kuma mai Risalah, mafi kyawun littafi da aka rubuta domin bayanin salati ga ma’aikin Allah shi kadai, shine littafin ‘Jila’ul Afham’ , zaka same a shagunan da ake sayar da littafan musulunci.
12. Suturah: Duk wanda yake sallah shi kadai ko shine liman to anan ana bukatar ya sanya suturah a gabanshi, domin baiwa mai wucewa damar wucewa ta bayan suturar, amma shi mamu baya sanya sutura domin suturar liman ta wadatar masa, saboda haka idan kuna sallah da liman sai wani ya wuce ta gabanku babu komai inda ba ya wuce ta tsakanin liman da suturarshi bane.

Sunday, 20 January 2019

001 GIDAN NI'IMA

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
*GIDAN NI'IMA*
🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠

Gabatarwa; *BABAN-SINAN*

_Fitowa Na Farko 001_

🔴 *ZABEN ABOKI/ABOKIYAR ZAMA NA KWARAI*

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda yake cewa;
*وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ بُيُوتِكُمْ سَكَنًا...(النحل ٨٠)*

Tsira da aminci su kara tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w, da iyalan gidansa da sahabbansa da duk wanda yabi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar addini.

_Bayan haka:_

Allah madaukakin sarki a cikin Qur'ani yana cewa;

*وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ*

Ma'ana;

*_Ku Aurar da ayama(namiji ko mace wadanda basu da aure) daga cikin Ku, da mutanen kwarai daga cikin bayinku maza da bayi mata, idan kuna tsoron talauci Allah zai wadata Ku daga cikin falalarsa, Allah  mai yalwataccen falala ne kuma masani._*

Babu makawa ga namiji ko mace akan wajibi ne su zabi abokin zama na kwarai, saboda hadisin Annabin rahama s.a.w da yake cewa;

*_Ana auren mace don Abu hudu; Saboda dukiyarta, ko don dagantakarta, ko don kyau, ko don addini, sai Annabi yace na horeka da ma'abociyar addini._* (bukhari da Muslim)

Haka a wani hadisin da Muslim ya ruwaito manzon Allah s.a.w cewa yayi;

*_Duniya wani jin dadi ne, mafi alkhairin jin dadin duniya shine ka samu mace ta gari._*

A wani wurin kuma sai Manzon Allah s.a.w yake ba samari shawara akan cewa;

*_Ku auri yan mata kuma masu haihuwa, saboda inyi alfahari daku a ranar kiyama._*

Kenan a wannan hadisi na karashe manzon Allah s.a.w baya goyon family planning, Allah ya kiyaye.

Daga karshe zan rufe da zancen Magabata cewa:

*الرجل الصالح مع المرأة الصالحة يبنيان بيتا صالحا لأن البلد الطيب يخرج نباته بإذن ربه، والذي خبث لايخرج إلا نكدا.*

*_Mutumin kwarai idan ya hadu da mata ta kwarai suna Gina gida na kwarai, saboda gari tsaftatacce yana fitar da tsirrai da izinin ubangiji, Wanda ya lalace babu abunda zai fitar sai lalatattun tsirrai._*

ZAMU DAKATA A NAN SAI WANI LOKACI IDAN ALLAH YA KAIMU

_SUBHANAKAL-LAHUMMA WABI HAMDIKHA, ASH-HADU AN LAA'ILAHA ILLA ANTA, ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIHI_

✍🏻 Hashim Siraj Uba Tsamiya ( ABU-SINAN )
+2349030201868

https://hashimtsamiya.blogspot.com

atstsamawy@yahoo.com

Wednesday, 26 December 2018

HUKUNCIN HADE SALLOLI A LOKACIN TAFIYA

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HUKUNCIN HADE SALLOLIN AZUHR DA LA'ASAR KO MAGRIB DA ISHAA A LOKACIN TAFIYA*
🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah s.w.t, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w da iyalan gidansa da sahabbansa da duk Wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

_Bayan haka:_

Maganganu sun yawaita akan wannan matsalar ta inda zaka samu daliban ilimi kullum cikin rigima muke da junanmu akan wannan matsalar, wannan yace GA abunda malaminshi yace shima dayan sai ya kawo maganar shugaban islamiyyarsu, wannan duka yana faruwa ne imma a haduwar mota ce ko a campuses na manyan makarantu, wannan shine dalilin da yasa nabi malamai domin nayi rubutu akan wannan matsalar, nima kuma zan kawo maganganun mai gidana *Manzon Allah s.a.w,* sai dai tunda ance matsala ce da ta shafi daliban ilimi inaga ba dole sai an bude komai ba, za'a Dan haska fitila ne kadan sai mutum yayi dogon hange kafin hasken ya dauke.

Allah yayi mana jagora.

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah s.a.w, hadisin da Abdullahi Dan Abbas R.A ya ruwaito cewa:
كَان
َ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَجْمَعُ بَيْنَ صَلاةِ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ , إذَا كَانَ عَلَى ظَهْرِ سَيْرٍ , وَيَجْمَعُ بَيْنَ الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ .
Wannan hadisi ne sahihi da karara yake nuna mana cewa Manzon Allah s.a.w yana hade salloli.

Idan baka fahimci wannan hadisin ba, toh ga wani Wanda Anas Dan maliku R.A ya ruwaito yace:

كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا ارتحل قبل أن تَزيغ الشمس أخّر الظهر إلى وقت العصر ثم نزل فجمع بينهما ، وإذا زاغت قبل أن يَرْتَحِل صَلَّى الظهر ثم ركب . رواه البخاري ومسلم .
Tirkashi kaji hadisi daga littafan da malamai kecewa sune mafi girman littafai bayan Qur'ani wato(SAHIHUL bukhari da Muslim), kunji fa Manzon Allah s.a.w idan ya daura aniyar tafiya kafin rana ta kawo(wato kafin lokacin sallar azuhr) yana jinkirta azuhr zuwa lokacin sallar La'asar, sannan sai ya sauka ya hade sallolin, idan kuma lokacin sallar azuhr yayi kafin ya fara tafiya yana yin azuhr kawai sai ya fara tafiya.

Ga hadisin mu'az bin jabal R.A a gazwati tabuka yake cewa:

أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ فِي غَزْوَةِ تَبُوكَ إِذَا زَاغَتْ الشَّمْسُ قَبْلَ أَنْ يَرْتَحِلَ جَمَعَ بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ ، وَإِنْ يَرْتَحِلْ قَبْلَ أَنْ تَزِيغَ الشَّمْسُ أَخَّرَ الظُّهْرَ حَتَّى يَنْزِلَ لِلْعَصْرِ ، وَفِي الْمَغْرِبِ مِثْلُ ذَلِكَ ؛ إِنْ غَابَتْ الشَّمْسُ قَبْلَ أَنْ يَرْتَحِلَ جَمَعَ بَيْنَ الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ ، وَإِنْ يَرْتَحِلْ قَبْلَ أَنْ تَغِيبَ الشَّمْسُ أَخَّرَ الْمَغْرِبَ حَتَّى يَنْزِلَ لِلْعِشَاءِ ثُمَّ جَمَعَ بَيْنَهُمَا . رواه الإمام أحمد وأبو داود والترمذي .

Kunga shima wannan hadisin yana tabbatar muna da halascin hade salloli biyu a lokacin tafiya.

A wannan hadisin sai imamut tirmidhi yake cewa;

وبهذا الحديث يقول الشافعي ، وأحمد وإسحاق يقولان : لا بأس أن يَجمع بين الصلاتين في السفر في وقت إحداهما .
Kundai ji, a wurin su imamush shafi'i da imamu Ahmad da ISHAQ bin rahwiyya dukkansu sunce babu laifi a hade salloli biyu a lokacin daya, idan ana cikin tafiya.

Wancan hadisin da ya gabata na tabuka, imamu Muslim ya ruwaitoshi da wani lafazi kamar haka;

خَرَجْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَامَ غَزْوَةِ تَبُوكَ ، فَكَانَ يَجْمَعُ الصَّلاةَ ، فَصَلَّى الظُّهْرَ وَالْعَصْرَ جَمِيعًا ، وَالْمَغْرِبَ وَالْعِشَاءَ جَمِيعًا .
A riwayar Muslim hade sallolin sai ya bayyanar mana da riwayar Imamu Ahmad da tirmidhi da Abi daud da ta gabata.

Abu na gaba shine addinin Allah sauki gareshi, tunda Allah yayiwa matafiyi rangwame akan ya ajiye *azumi* saboda kada ya wahala, ai banga abun rikici ba akan hade salloli, ana zaune gida ma akwai wasu dalilai da suna iya sa a hade salloli.
Hade salloli ga matafiyi ya kasu gida biyu;
1. تقديم
2. أو تأخير

Wato yin sallar azuhr da la'asar a lokacin azuhr ko yin sallar azuhr da la'asar a lokacin la'asar, sai dai dole idan zakayi taqdeem ko ta'akheer sai kayi niyya, ma'ana idan zakayi ta'akheer, dole sai kayi niyya kafin fitar lokacin sallar farko(azuhr)

Abu na gaba shine;

*DAGA KILOMETERS NAWA NE KASARU KE KAMAWA???*

TIRQASHI!!!

Wannan itace matsalar da nafi cin karo da ita a tsakaninmu dalibai yan islamiyya, Wanda kowa na ganin shi malamin kanshi ne, tare da ta'assubanci ga wani malami ko mazhaba, a karkashin wannan zan kawo wata gamsassar magana da Sheikhul Islam ibn Taimiyya ya kawo akan wannan matsalar Wanda ina kyautata zaton zata gamsar da duk wani mai Neman gaskiya akan wannan matsalar, Sheikhul Islam ibn taimiyya yake cewa;
فالفرق بين السفر الطويل والقصير لا أصل له في كتاب الله ولا في سنة رسوله بل الأحكام التي علقها الله بالسفر علقها به مطلقا .

Allahu Akbar, wannan magana ta ibn Taimiyya ta wadatar akan muce sai munyi dogon bayani, abune Wanda yake bude Allah bai kayyade ba kai waye da zaka kayyade?

Toh, rubutun idan akace za'ayi tayi baya karewa, don akwai hujjoji barkatai dake nuna halascin hade salloli a lokacin tafiya, a hakika yanzu nayi rauni a wurin rubutu, amma mu dauka cewa wannan kamar mukaddima ce, idan bukatuwar hakan ta kama zamu kara cewa wani Abu insha Allahu.

ALLAH YA KARA MANA IKHLASI DA KARFIN GWUIWA A WURIN AIKI DA DAI DAI DA FADAR GASKIYA.


✍ *Hashim Siraj Uba Tsamiya ( _ABU~SINAN_ )*

+2348064734911
+2349030201868

atstsamawy@gmail.com

atstsamawy@yahoo.com

Sunday, 25 November 2018

(B) DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI

⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪
*وليتذكر ألوا الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Gabatarwa: *MUKYAUTATA NIYYA*

_PART_ *B*


*KASHI/BAYAN GIDA YAFI MAULIDI A SALI A CIKIN ADDINI...!!!*

*LADUBBAN SHIGA BAYAN GIDA(BIYAN BUKATA)*

Abubuwan da aka so ayi wajen shiga bayan gida don biyan bukata.

*Gasu kamar haka:-*

1. A lokacin shiga, zaka fadi ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ ﻭﺍﻟﺨﺒﺎﺋﺚ . ```ALLAHUMMA INNI A'UZU BIKA MINAL KHUBSI WAL KHABA ISI```
watau [ALLAH INA NEMAN TSARI DAGA GAREKA, KA KARENI DAGA SHARRIN ALJANNU (SHAIDANU MAZA DA MATA)

2. Shiga bayan gida da kafar hagu.

3.sanya gajeren wando lokacin wanka, domin ka kare tsiraicinka idan a fili ne a wajen wankan

4. Fara yin bisimillah

5. Sanya ruwan wanka a gefen hannun dama

6. Amfani da takaitaccen lokaci a bayan gida(kashi)

7. Fitowa da kafar dama

8. Kebewa daga idanun mutane

9. Tsugunnawa lokacin da ake bayan gida

10. Mayar da nauyin jiki zuwa bangaren hagu

Bai kamata ba a shiga bayan gida da abin da ya ke dauke da sunan Allah s.w.t a jikinsa(sai dai domin gudun kada a sace shi), bayan an gama ana son a wanke hannaye da ruwa, ko da sabulu ko kuma tur6aya ko yashi.

Musulmai ya kamata lokacin da za suyi bayan gida ko wanka, su kebe kansu daga inda mutane zasu iya ganinsu.

An kar6o daga jabir yace; "idan muna tafiya tare da manzon Allah s.a.w, ya kanyi bayan gida idan ya kebe daga mutane (wato ya kan sakaya kansa inda ba mai ganinsa.

*ABUBUWAN DA BA'A SON A AIWATAR DANGANE DA BAYAN GIDA...!!*

1. Fuskantar/juya wa Alkibla baya idan a fili ne.

2. Magana ko kuma wa'ka yayin da ake bayan gida

3. Yin wanka a gaban jama'a

4. Karanta ayoyin alkur'ani a ban daki

5. Yin amfani da ruwa mai yawa.

6. Yin wanka, fitsari, ko bayan gida a wajen da ake ibada, misali;
*MASALLACI, COCI,* ko wani majalisi na al'umma.

7. Wanke can cikin dubura

8. Barin wasu mutane su ga tsiraicin dan uwansu.

9. Yin fitsari a cikin rami.

10. Ta6a azzakari ko dubura da hannun dama.

Yan uwa munji kadan daga cikin ladubban bayan gida(KASHI)
Domin karin bayani, ka duba ﺑﻠﻮﻍ ﺍﻟﻤﺮﺍﻡ -ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻄﻬﺎﺭﺓ - ﺑﺎﺏ ﺁﺩﺍﺏ ﻗﻀﺎﺀ ﺍﻟﺤﺎﺟﺔ

*YAN TA MAULIDE MUNA JIRAN NAKU LADUBBAN NA CASHEWA, DAGA HADISSAI INGANTATTU, DA INDA AKA CIROSU.*

*HAATU BURHAANAKUM INKUNTUM SADIQEEN*

HUJJA MUKE BUKATA BA ZAGI BA


✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABBAN-SINAN_ )*
+2348064734911

018 MUKOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUPS DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha takwas 018_


Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*MUSTAHABBAN ALWALA:*
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni, kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su, domin kowannen mu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalla, to kuwa tunda hakane bai kamata kace ai wannan mustahabbi ne ka daukeshi kamar wani karamin abu. Su mustahabban alwala suna da yawa, amma yanzu ga kadan daga cikinsu:

1⃣ Ambaton Allah kace *Bismillah* a daidai lokacin da zaka fara alwala, amma idan mutum
ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna
ba komai sai kayi a lokacin.

2⃣ Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma kamar haka:

*ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍَﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍَﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻳﻦَ.*

_Ma'ana:_ ```Ina shaidawa da babu abun bauta da
cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma manzonsa ne,
Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman
tsarkaka.```

3⃣ 'Karanta Ruwa;
   Bawai ana nufin mai alwala ya shashshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar yayi amfani da ruwa amma kada ya malalar dasu, domin yana daga cikin tsarin musulunci
tattali da tsimi da tanadi.

4⃣ Gabatar Da Asuwaki:
Bayani kuma dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da
busasshe, idan bai samu ba sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma
daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin sallah yayi amma yana da alwala to abinda ake so shine ya yi asuwaki.

5⃣ Wuri Mai Tsarki:
  An so inda zaka yi alwala ya zama wurine mai tsarki.

6⃣ Dama Kafin Hagu:
  Abun nufi shine ka fara wanke hannun dama kafin hannun hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta
dama.

7⃣ Jerantawa:
  Wato jeranta kowacce sunnah
tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da kuskurar baki kafin shaka ruwa.

8⃣ Wankewa Sau Uku:
  Ma'ana wanke wuraren da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau uku zai zama mustahabbine idan wankewar farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata
game ba to ta biyu tananan amatsayin wajibi, haka idan ta biyun bata game ba
to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai
ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare da barna ba.
Amma shi kai sau daya ake shafarsa, ba'a shafar kai sau biyu ko uku. Sannan kuma mutum ya tabbata a wadannan wankewa da akace yayi sau uku bai kara akan hakan ba, yayi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.

Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai
sun shafi mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai
mata su sani gashin kansu al'aurane, saboda haka bai
halatta su bayyanar dasu ga maza ba, kenan idan zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kebance
kanki.

Wadannan bayanai da suka gabata zasu haskaka mana yadda alwala take, amma hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an
tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka kawo mishi butar alawala yayi musu ita a aikace, yace kuma irinta manzon Allah s.a.w yayi.

A nan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a dana sauran masallatai da kuma malamai a
jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a sakandare da firamare da malaman islamiyyu da malamai masu karantarwa a masallatai da
masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa kamar kungiyoyin addini
dasu karantar da mutane alwala a
aikace, yadda kowa zai gani ya kuma yi tambaya, kada kaga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada
hakan a *Federal university birnin kebbi,* ita ibada sai an koyawa mutum ba wai daka akeyi ba, kai da ganin
alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah ya karba mana ibadummu.

A NAN MUKA KAWO KARSHE DANGANE DA BAYANI AKAN ABUNDA YA SHAFI ALWALA, A GABA ZAMU BAYANIN ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN;
✍ *Hashim Siraj Uba atstsamawy ( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

(A) DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI

*وليتذكر ألوا الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*

_Gabatarwa:_ *MUKYAUTATA NIYYA GROUPS*

PART *A*

📌 *WANNAN ITACE HUJJAR MU AKAN CEWA MAULIDI BIDI'AH NE...!!!*

*==============*

▫ Abubakar siddiq(RA) yayi khalifanci tsawon shekara biyu amma baiyi maulidi ba, tare da cewa shi mai gaskiyar wannan al'ummar ne, kuma abokin manzon Allah s.a.w a cikin kogo lokacin hijira..!!
*▪▪▪▪▪▪▪*

🔸 Umar bn khaddab(RA) yayi khalifanci shekaru goma(10), amma ba'a ruwaito cewa yayi maulidi ba, tare da cewa shine FARUQ na wannan al'umma..!

*▪▪▪▪▪▪▪*

🔹Usman bn affan(RA) yayi khalifanci shekaru 13, amma baiyi maulidi ba, kuma baice ayi ba, tare da cewa ya auri yayan annabi guda biyu, kuma yayi hijira guda biyu, Wanda yafi kowa kunya a cikin wannan al'umma..!
*▪▪▪▪▪▪▪*

🔸 Aliyu bn Abi dalib(RA) yayi khalifanci shekaru 4 amma bai aikata maulidi ba, baiyi umurni da ayi ba, kuma shi Dan baffan manzon Allah s.a.w ne, kuma shine ya auri shugabar matan yan aljanna...!
▪▪▪▪▪▪▪

▫Hassan bn Aliyu bn Abi dalib yayi khalifanci wata shida(6) amma baiyi maulidi ba, gashi jikan Manzon Allah s.a.w, kuma shine shugaban samarin aljanna...!
▪▪▪▪▪▪▪

◼ Mu'awiya bn Abu sufyan yayi mulki na adalci a cikin kabilun larabawa, amma baiyi maulidi ba, bai kuma ce ayi ba
▪▪▪▪▪▪▪
◻Daular umawiyya tazo, a cikinta akwai irinsu Umar bn Abdulaziz, daular Abbasiyya tazo, a cikinta akwai misalin Harun Ar-rasheed, amma dukansu basuyi maulidi ba, basu kuma yi umurni da ayi ba..!
▪▪▪▪▪▪▪

🔹 Yanzu ma malaman gaskiya, masoya manzon Allah s.a.w gaskiyar so, basuyi maulidi ba tun daga karnukan nan guda uku, tare da tsananin sanin su akan abunda Allah ya saukar, da kuma girman fahimtarsu ga Qur'ani, ya akayi basuyi ba? Tare da cewa sune suka iso da Qur'ani da hadissai zuwa garemu..?

▪▪▪▪▪▪▪
  Mu dai yanzu zamu ce;  Da maulidi alkhairi ne da sun rigamu aikatashi..!
▪▪▪▪▪▪▪
Zamu fadi Abunda Imamu Malik(RH) ya Fada; ```Duk abunda bai zama addini a lokacin manzon Allah s.a.w da sahabbai ba, ba zai taba zama addini ba har tashin Al-kiyama..!```
▪▪▪▪▪▪▪
➡ Abu sananne kawai shine; Manzon Allah s.a.w bai bar duniya ba sai da ya kammala Isar da sakon da Allah ya aikoshi dashi..!
▪▪▪▪▪▪▪
   ▪ ya tsoratar da sahabbanshi akan kirkirar wani abu a cikin addini, da aikata abunda bai aikata ba..!
▪▪▪▪▪▪▪

▫ Ya kamata kusan cewa; wadancan karnukan masu girma basu San wani biki mai suna Maulidi ba! Shifa Maulidi wata bidi'ah ce da yan shi'ah *(FADIMIYYUNA)* suka kirkira, a karkashin wani shugabansu da suke kira Mai daukaka addinin Allah, sai dai karya suke, shi mai cutar da addini ne..!
▪▪▪▪▪▪▪
🔸 yayi mulki a bisa kafirci, da fasikanci, ta inda ya halasta shangiya, ya halasta kowane  farji na mace, ya tsinewa sahabbai kuma yayi umurni da hakan a saman mimbarorin juma'ah, wannan Dan ta'addan shine ya kirkiri maulidi fa! Ya kasa maulidin gida shida, Na farko; Maulidin Manzon Allah s.a.w, sai na Fadima, Aliyu, Hassan, Hussaini(ALLAH YA YARDA DASU) sai Maulidin kanshi..!
▪▪▪▪▪▪▪

Daga nan sai yan fadimiyyuna suka jahiltar da musulmai akan wannan bidi'ar, ya kamata kusan cewa babu wani dalili a wurin yan tamaulide akan halascin maulidi, kawai hujjarsu wasu nassosi ne suke yim a gurguwar fahimta, ko kuma hadissai na karya koda sun inganta sai ka samu basu nuni akan maulidi amma sai su juyar da ma'anarsu.
▪▪▪▪▪▪▪

◼ *YANZU GA WASU YAN TAMBAYOYI GUDA UKU DA MUKESON MU JEFAWA YAN TAMAULIDE, MUNA NEMAN AMSARSU:*
▪▪▪▪▪▪▪

1⃣ Shin bikin maulidi biyayya ne ga Allah da Manzon Allah s.a.w ko sabon Allah ne??

Idan sunce biyayya ne! Ko kuma sunce Sabo ne, duka akwai tuhuma garesu..!

2⃣ Yawwa, idan sukace biyayya ne ga Allah kuma zasu samu lada akai!
Sai muce Ko Manzon Allah s.a.w yasan da wannan biyayyar?
Ko bai sani ba?

➡ Da zasu ce bai sani ba, da sai muce kaiconku! Yanzu kuna tuhumar Babban malami(Manzon Allah s.a.w) da jahilci, wannan kafurci ne, kuma zindikanci ne..!
▪▪▪▪▪▪▪

🔸 Da zasu ce ya sani, toh sai muje a tambaya ta uku.

3⃣ Kunce biyayya ne, kuma Manzon Allah s. a.w ya sani, shin ya bayyanar dashi ga mutane ko kuwa ya boye???

Idan sunce bai Isar ba, wannan tozarci ne ga Manzon Allah s.a.w, da kuma tuhumar Manzon Allah s.a.w da boye wani Abu na manzanci, bayan a Qur'ani Allah s.w.t ya Fada cewa; ```Yaa kai Manzon Allah ka Isar da abunda ya sauka gareka daga ubangijinka, idan bakayi haka ba, baka Isar da Manzancin ba.```

Idan kuma sunce ya Isar, sai muce; Toh kuzo mana da dalili, ina aikin magabata akai?
Yanzu muna bukatar amsoshi daga gareku.

ALLAH YA NUNA MANA GASKIYA YA BAMU IKON BINTA, YA NUNA MANA BIDI'AH YA BAMU IKON KAUCE MATA

KU WATSA WANNAN A TSAKANIN MUTANE DOMIN AL'UMMA SU GANE GASKIYAR BIDI'AR MAULIDI...

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN;
✍ *Hashim Siraj Uba Tsamiya ( _ABBAN-SINAN_ )*
+2348064734911

Thursday, 15 November 2018

002 DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI

🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘🔘
*وليتذكر ألوا الألباب...*

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*
🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶

_Fitowa Na biyu 002_

Gabatarwa: *MUKYAUTATA NIYYA GROUPS*

*ASALIN MAULIDI A MUSULUNCI DA WADANDA SUKA KIRKIRESHI!! KASHI NA BIYU(002)*

HAK’IK’A RAFIDA UBAIDIYYUNA, SUN TILASTA WA DUKKAN MA’AIKATANSU ‘YAN MISRA, DA SU RUNGUMI ADDININSU NA RAFIDANCIN BA’DINIYYA, KAMAR YADDA SUKA WAJABTA WA ALK’ALAI SU ZARTAR DA HUKUNCE – HUKUNCE A BISA DOKOKIN WANNAN ADDINI NASU. KAI, HAR YA KAI GA CEWA; SHARA’DI NE NA SAMUN MATSAYI A DAULAR, SAI MUTUM YA JUYA YA KOMA ADDININ RAFIDANCIN BA’DINIYYA. WANDA HAKAN YA SA DA YAWA DAGA CIKIN KAFIRAN AMANA SUN NUNA SHIGA MUSLUNCI TARE DA RUNGUMAR RAFIDANCI.

*DUBA AL- DAULAR FA’DIMIYYA SHAFI NA 218*.

WA’DANNAN MUTANE ‘YAN SHI’A BA’DINIYYA, WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI, YANA DAGA CIKIN GABARSU DA SUNNAR ANNABI (SAW), DA AHLINTA; AZEEZ SARKIN LOKACIN YA YI UMURNI DA A DENA SALLAR TARAWIHI A DUKKAN K’ASAR MASAR. WATO A SHEKARA TA *372.* SA’ANNAN A SHEKARA *393* AN KAMA WASU MUTANE *13,* AKA YI MUSU DUKA, SA’ANNAN AKA YI YAWO DA SU AKAN RAK’UMA A CIKIN GARI, AKA TSARESU TSAWON KWANA *3,* DUK WANNAN SABODA KAWAI SUN YI SALLAR *WALAHA.* A SHEKARA *381,* AN BUGI WANI MUTUM AKA ZAGAYA A CIKIN GARI DA SHI SABODA KAWAI AN SAMU LITTAFIN *”MUWA’D’DA’A”* TA IMAMU MALIK (R) A WAJENSA.

*TSANANIN GABAR UBAIDIYYUNA (RAFIDA BA’DINIYYA) WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI GA SAHABBAI DA AHLUS SUNNA:*

A SHEKARA TA *395H* A CIKIN WATAN *SAFAR,* AN RUBUTA ZAGIN MAGABATA (SAHABBAI) DA TSINE MUSU A BABBAN MASALLACIN *MISRA ”JAMI’UL ATIK”’* DA MA SAURAN MASALLATAN, TA CIKI DA WAJENSU, DA TA DUKKAN GEFE – DA – GEFENSU, DA K’OFOFIN SHAGUNA DA MAK’ABARTU. AKA ZANA SHI DA ZINARI. HAKA AKA YI A K’OFOFIN GIDAJE DA NA MANYAN ‘DAKUNAN TARO. KUMA AKA TILASTA MUTANE AKAN YIN HAKAN, TSINE MA AHLUS SUNNA ABU NE DA YA WATSU A BAKUNAN MUTANE, AKAN MINBARORI A DUKKAN FA’DIN MASAR TSAWON MULKIN UBAIDIYYUNA. HAR TA KAI GA SHI *ABHID* – SARKINSU NA K’ARSHE- SABODA TSANANIN SHI’ANCINSA, DA GULUWWINSA WAJEN ZAGIN SAHABBAI (RA) – IDAN YA GA MUTUM AHLUS SUNNA SAI YA HALATTA JININSA.

*DUBA AL- KHI’DA’DA NA MAK’RIZIY,* (2/ 341). DA *TARIKHUD DAULATIL FA’DIMIYYA* SHAFI NA (620). DA *WAFIYYATUL A’AYAN* (3/ 110).

*KAFIRCIN UBAIDIYYUNA (RAFIDA BA’DINIYYA) WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI:*

WANI ABU DA YA FI DUKKAN ABIN DA MUKA AMBATA A BAYA SHI NE; *AL- HAKIM* SARKIN DAULAR FA’DIMIYYA, YA YI DA’AWAR CEWA; SHI ALLAH NE. *(SUBHANALLAH)!!*  SAI YA UMURCI MUTANE DA SU TASHI SU TSAYA DA K’AFAFUNSU A CIKIN SAHUN SALLAH A LOKACIN DA MAI HU’DUBA YAKE HU’DUBA IDAN YA KIRA SUNANSA, DON GIRMAMA AMBATONSA DA SUNAN NASA. KUMA HAKA YA SA AYI A DUKKAN MASARAUTAR TASA. HAR A HARAMAINI (MAKKA DA MADINA). AMMA YA WARE MUTANEN MISRA YA UMURCE SU DA SUNA FA’DUWA K’ASA SU YI SUJADA, IDAN AN KIRA SUNAN NASA. HAR YA ZAMA MUTANEN DA SUKE KASUWA MA WA’DANDA BA SA ZUWA JUMA’A SUKAN FA’DIN SU YI SUJADA IN NA CIKIN MASALLACIN SUN FA’DI, IN MAI HU’DUBAN YA AMBACI SUNAN NASA, A RANAR JUMA’A. HAR AN SAMU WASU JAHILAN IDAN SUN GAN SHI SAI SU CE: YA *WAHIDANA,* YA *AHADANA,* YA *MUHYI,* YA *MUMITU.* SA’ANNAN YA UMURCI BAK’AK’E DA SU K’ONA MASAR, SU WAWASHE DUKIYOYINTA, DA KAYAYYAKI, DA MATA. KUMA SUKA BI UMURNIN NASA, SUKA KAMA MATA SUKA YI TA ALFASHA DA MUNANAN AIYUKA DA SU. SUKA K’ONA ‘DAYA BISA 3 NA MISRA SUKA WAWUSHE RABINTA.

DUBA *AL- BIDAYA WAN NIHAYA* (12/ 10 – 11), DA *AL- MUNTAZIM* (7/ 298).

*WANNAN SHINE TARIHIN MAULIDI DA WADANDA SUKA KIRKIRESHI A TAKAICE.*

Note: AKWAI BUKATUWAR DUK WANDA YA KARANTA NA FARKO YAYI KOKARI YA NEMI NA BIYU, IDAN KA KARANTA NA BIYU KADA KAYI HUKUNCI SAI KA NEMI NA DAYA.

*DOMIN MASU HANKALI SUYI TUNANI...*




✍ *ABBAN_SINAN*