Monday, 6 May 2019

01BARKA DA SHAN RUWA

🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉
*_BARKA DA SHAN RUWA_*
🍉🍉🥭🍑🍎🍊🍋🍌🍉🍉

_001_

1⃣ *MI KE TABBATAR DA SHIGAR WATAN RAMADAN???*

*_AMSA_*

Yana tabbatuwa da abubuwa guda biyu;

*_Na farko:_* cikar watan sha'aban kwana talatin

*_Na biyu:_* Ganin jinjirin watan Ramadan

2⃣ *MENENE HUKUNCIN WANDA YAGA JINJIRIN WATAN RAMADAN SHI KADAI 👌 AMMA BA'A KARBI SHAIDARSHI BA???*

*_AMSA_*

Ba zaiyi azumi ba sai tare da mutane, saboda hadisin da yazo a jaami'ut-thirmidhi da waninsa, Manzon Allah s.a.w yace: "azuminku ranar da kuke azumi(ranar da kowa ya fara)"

3⃣ *MUTUM NAWA NE ZA'A IYA KARBAR SHAIDARSU TA GANIN JINJIRIN WATAN RAMADAN???*

*_AMSA:_*

Za'a Karbi shaidar mutum daya zuwa sama, saboda hadisin da imamu Abu daud da waninsa suka ruwaito, Abdullahi Dan Umar (RA) yace; "Mutane sunga wata, sai naje na fadawa Manzon Allah s.a.w cewa ni naga wata, sai Annabi s.a.w yayi azumi, kuma ya umurci mutane da suyi azumi, imamut tirmidhi yace: ma'abota ilimi suna aiki da wannan karantarwa.

*FADAKARWA*

_Amma a wurin fitar watan Ramadan sai da shaidar mutane biyu ake ajiye azumi, kuma malamai basuyi sabani akan wannan ba._

#ABU_SINAN
+2348064734911

Friday, 15 February 2019

01 MATSALOLIN SHAYE SHAYE

💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
*MATSALOLIN SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA.*
🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬

Rubutawa: *SHEIKH NASIR BALA BUNGUDU*


*ABUBUWAN DAKE CIKI*

✅ GABATARWA

✅ MA’ANAR MAGANI

✅ MA’ANAR SHAYE-SHAYE

✅ DALILAN DA SUKE JAWO SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA

✅ WASU DAGA CIKIN MIYAGUN MAGUNGUNNA /DA KAYAN MAYE DA AKE TU’AMMALI DASU

✅ MATAKAN SOMA SHAYE-SHAYE

✅ ALAMOMIN DA AKE GANE MAI SHAYE-SHAYE DASU

✅ SLANGS DA AKE AMFANI DASU DOMIN BADDA SAWU

✅ ILLOLIN SHAYE-SHAYE

✅ MAFITA

     Shaye-shaye dadadden abu ne a cikin al’ummomi daban-daban
Shaye-shaye ya zama ruwan dare ba birni ba kauye ba rugga ba zango ba manya ba kanana ba maza ba mata. Kuma musulunci yabi matakai daban-daban don magance matsalar shaye-shaye da kawar dashi kasancewar larabawa suna cikin wadanda ke tu’ammali da shaye-shaye kamar yadda Hassanu bin Thabit yake cewa: )WA NASRABUHA FA TATRUKUNA MULUKAN WALA YANAHNIHUNA AL-LIQA’ U)

MA’ANAR MAGANI: Shi dai magani ko kwaya shine duk wani abu da in ya shiga jikin dan adam yake kawo wani canji ga kwakwalwa ko jikin sa, ta ko wane fanni misali, ko ta hanyar sha, ko shafawa, Ko shakawa ko yin allura, ko kurkura.

MA’ANAR SHAYE-SHAYE:

Sha ko amfani da maganin da doka ta hana amfani dashi
Sha ko amfani da magani barkatai ba tare da izinin likita ba. Sha ko amfani da abubuwan da addinin musulunci ya hana Wuce umurnin likita wajen shan magani

*DALILAN DA SUKE JAWO SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA*

Jahilci Matsalolin rayuwa kamar (rashin aikin yi, mutuwar aure, damuwa ko bacin rai) Miyagun abokai
Koyo daga masu yi,
Al’adu, gado Hada-hadar siyasa, Sakacin iyaye game da tarbiyya da rashin tsawatawa,
Yanayin wurin zama (Environment),Sakar ma yara dukiya,
'Bata garin masu sayar da magani,
Shan magani da nufin biya ma juna bukatar aure, Samun magungunnan cikin sauki,
Sakacin hukuma,
Bata garin jamián tsaro, Cin hanci da rashawa, Sha don samar da kuzari ko karfin jiki.

Wadannan kadan ne daga ciki.

Zamu cigaba insha Allahu

✍ *Hashim Siraj Uba atstsamawy ( _ABU-SINAN_ )*
+2348064734911

WAZAN ZABA? 2015/2019

🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶🔶
*وليتذكرأولولألباب !!!*
*Domin masu hankali suyi tunani!!!*
🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷🔷

_Rubutawa;_ *MURYAR SHABABU AHLIS-SUNNAH WALJAMA'AH TSAFE*

_Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu._

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda ya fifita Addinin Musulunci akan duk sauran addinai a bayan kasa, Ya kuma fifita Musulmai akan wanda ba Musulmi ba, ya kuma bayyana shine addinin da zai karba a ranar alkiyama.
Tsira da aminci Allah su tabbata ga shugaban mu da yafi duk wani shugaba a doron kasa, wanda yafi kowa cikin halittun Allah (S.W.T) baki daya; Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka taimaki addinin  Allah da dukiyarsu da kawunansu, da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

1⃣ *SHIN KO SIYASA ADDINI CE???*
          Siyasa na iya zama  addini ta lura da fadar Allah (S.W.T) *“Kace lallai sallah ta da yanka na da rayuwata da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin halittu, babu abokin tarayya a gareshi, Kuma da wannan ne aka umarce ni kuma nine farkon masu mika wuya”*
{Al-An’am; 162-163}.

Tunda an umarci Manzon Allah (S.A.W) da cewa dukkan rayuwarshi yayi ta ga Allah (S.W.T), haka ma kai/ke aka umurce ku da dukkan rayuwar ka/ki yita ga Allah (S.W.T). Duk wanda zai jagorance ku zai jibinci Al’amurranku ne da addinin ku, to wajibine ya zama musulmi na kwarai.
Hakanan malamai sunce za’a saka addini a cikin siyasa ta lura da wasu abubuwa masu zuwa, ga kadan daga cikinsu:

✅ *_Ya kasance ga musulmi ga kafiri:_*
wajibine a zabi Musulmi.

✅ *_Ya kasance ga musulmi na kwarai ga kuma na banza (Fasiki):_*
Wajibine a zabi Musulmi na kwarai.

✅ *_Ya kasance ga Musulmai duka na kwarai amma daya yafi daya Imani, tausayi, taimako da son addini:_*
wajibi ne a zabi mai imani da tausayi da taimakon al’umma da son addini.

Duk wannan wajibi ne a saka addini a cikin siyasa domin duba ga abunda zai kawo ci gaba ga addini da al’umma, sannan wace amsa za ka/ki ba ma Allah (S.W.T) a ranar alkiyama idan ya tambayeka/ki dalilinka/ki na zabar kafiri ko fasiki alhali ga Musulmi ko mumini.

2. *Shin ko ya halatta in zabi kafiri alhali ga Musulmi?*

A’a baya halasta a zabi kafiri alhali ga musulmi, dalili kuwa Allah (S.W.T) yana cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki kafirai a matsayin masoya koma bayan muminai shin kuna nufin sanya ma Allah dalili bayyananne ne a kanku”._*
{Al-Nisa’; 144}.

Allah ya kara cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki abokan sirri daga waninku (wadanda ba Musulmai ba), basu takaita maku barna kuma suna gurin abunda zai cutar da ku, hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu amma abunda zukatansu ke boyewa ne mafi girma, kuma lallai mun bayyana ayoyi ne a gareku domin ku hankalta. Ku dinnan kune kuke sonsu (alhali) su basu son ku…”_*
{Ali-Imran; 118-119}.

Allah ya kara cewa: *_“Ya ku wadanda sukayi imani kada ku riki makiyana da makiyanku (a matsayin) masoya kuna jefa soyayya zuwa garesu alhali kuwa sun kafirta da abunda yazo maku na gaskiya…”_*
{Al-mumtahina; 1}.

3. *Wa ya kamata in zaba a matsayin shugaba (wanda zai jibinci al-amurrana)?*

Zabar shugaba nuni ne ga so da kauna da kuma yarda da cewa wanda ka zaba ka yarda ya jibinci al-amurran rayuwar ka da addininka, to dole ne ka zabi wanda yasan kima da mutuncin rayuwar taka da addininka.
Allah (S.W.T) yana cewa *_“Abun sani majibincin al-amurranku (shine) Allah da ManzonSa da wadanda suke tsayar da sallah suke bada zakkah...._*

Duk wanda ya jibinci Allah da ManzonSa, kace rundunar Allah itace mai rinjaye” {Al-Ma’idah; 55-56}.

Muna rokon Allah yasa ayi wannan zabe lafiya, ya zaba muna shuwagabanni na kwarai masu kaunar addininmu na musulunci ba masu fada dashi ba.

*SANARWA!!!*

Mun rubuta wannan takarda ba don goyon bayan wata jam’iyya ko wani mutum ba, a’a munyi ta ne domin isar da sakon Allah (S.W.T) zuwa ga bayinsa da nufin kawo gyara ga al’ummarmu da rayuwarmu.

Wassalamu Alaikum.

*SHABABU AHLIS SUNNAH WAL JAMA’AH TSAFE ZAMFARA STATE*
08064607294, 08139348898

shababuahlissunnahwjtsf@gmail.com

02 MATSALOLIN SHAYE SHAYE

💊💊💊💊💊💊💊💊💊💊
*MATSALOLIN SHAYE-SHAYE A CIKIN AL'UMMA.*
🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬

_Fitowa Na biyu 002_

Rubutawa: *SHEIKH NASIR BALA BUNGUDU*


*WASU DAGA CIKIN MIYAGUN KWAYOYIN DA AKE TU’AMMALI DASU.*

Giya (burkutu), golder, power stout, googgoro, Star, lion dragen), Tabar wiwi, (indian Hemp) Cociene (Hodar ibilis), Heroine
D5, (Valium, Diazepam, Exol5),
Tramol(Tramadol),
Sholisho(sholi),
Snuff tobacco (Shisha), Maganin mura da ake sha ba bisa ka’ida ba kamar: (Emzolyn, tutolyn/codein, benalyn/codein)
Afarci kasa (pemolin tablet)
R C D, Kashin kadangare,Baabaa jijji, Buke, Zamalo,
Bula, Kwata, Tururin masai, Kan ashana,
Lohi, Alabukun, Shake,Kurkura.

*MATAKAN SOMA SHAYE-SHAYE*

✅ *GWAJI*: wannan shine mataki na farko wanda mutun zai soma ko fara kusantar mu’amala da shaye-shaye har fara tabawa kadan .

✅ *MASU SHAYE-SHAYEN GANIN DAMA:* Wannan matakin yana shane lokacin da yaga dama baya sa kudin sa sai ya samu na banza. Kamar irin wuraren taruwar jama’a wuraren biki,da ayukkan gayya da suran su.

✅ *MASU SHAYE-SHAYE AKAI AKAI:*
Wannan shine matakin fara shaye shaye gadan-gadan ko yana da kudi ko baya dasu sai ya sha.

✅ *WADANDA SUKA DOGARA AKAN SHAYE-SHAYE:*
  wadannan sune suka kai matakin ba zasu iya komi ba sai sun sha idan basu sha ba ba zasu zauna lafiya ba wanda yakai wannan matakinkullum zaka same shi cikin maye.

✅ *ALAMOMIN DA AKE GANE MAI SHAYE-SHAYE DASU:*
Rashin natsuwa
Halin lalaci Yawan abokai barkatai
Yawan fushi da rashin hakuri
Rashin ladabi da rashin kunya Amfani da bakin gilashi (Ba bisa kai’ida ba) Tinted Glass Yawan arangama da jami’an tsaro
Samun mutum da miyagun kwayoyi
Yawan yawo da ruwa ko lemon kwalba Rashin biyayya ga maganar magabata da rena su.
Yawan bacci
Ladabin kura
Jan lebo ko bakin baki
Dafewar tafukkan hannu da kafa
Amfani da kayan kamshi don kawar da wari eg comfo,tiger etc

*SLANGS DA AKE AMFANI DASU DOMIN BADDA SAWU:*

Masu tu’ammali da kayan maye suna amfani da wasu yarurrukka ko sunaye domin badda sawu ga sauran jama’a, ga misalign wasu daga ciki:
COCAINE: Blow,bump,c,candy,coke,crack,flake,rock,snow,snuff,sneeze.da dai sauransu.

DAGA: Blunt,green,dope,ganja,grass,smoke,chacks,herb,marry jane, pot,reefer, tree. Hashish,ganye, weed,cannabis, Magani, kaya.

✅ *ILLOLIN SHAYE-SHAYE A ADDINANCE:*
raunin Imani, hana ibada, gusar da kunya, bude kofofin alfasha da kaba’irori, zubar da mutunci, gusar da ni’ima, aikin shedan ne.

✅ *ZAMANTAKEWA:* lalata zumunci da wargaza dangantaka, kora daga wurin aiki ko makaranta

✅ *TATTALIN ARZIKI:*
yawan kashin kudade don ceto masu shaye-shaye ko biyan barnar da suka yi, sace-sace da barnata dukiyoyi, talauci.

✅ *KIWON LAFIYA:*
yawan kawo hatsari yayin tuki, ciwon huhu, ciwon hauka, yawan tunani mai tsanani mai muni, daukar mummunan mataki, kasha mazakuta, yawan lalaci, cancer ko wace iri ta mahaifa,na nono da sauran su.

✅ *TSARO:*
yawan tashe-tashen hankulla da zaman dar-dar da rashin tabbas, yawan kashe-kashe, zubar jinin wanda baiji bai gani ba bugling.

✅ *MAFITA*
Ya zama wajibi iyeye da tarbiyar da Allah ya wajabata masu ta yayan su musamman matasa da budurwai masu shekaru 15-20 (Teenagers) golden age of a teenagers galibi suke shiga wasu dabi’u na banza. Don haka dole ne a dinga kula da harkokin su na yau da kullum da kuma abokan da yaran su ke hulda dasu.
Dole ne magidanta su kula da irin mutanen dake shige da fice a gidajen su kuma su kula da irin mutanen da matan su da yayan su suke mua’amala dasu (maza da mata) kasancewar yanzu matan aure sun shiga cikin shaye-shaye dumu-dumu.
Wajibi ne sarakuna da malaman addini su tashi tsaye haikan wajen tsawatarwa da fadakarwa akan illolin shaye-shaye a mahangar addini da rayuwa.
Wajibi ne al’umma su bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga jami’an tsaro da jami’an hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a lokacin da suke gudanar da ayukkan su.
Wajibi ne ga makarantu kungiyoyin addini,da kungiyoyin sa kai da ban a gwamnati ba wurin taimakawa kokarin gwamnati wurin wayar da kai game da illolin shaye-shaye tare da fallasawa gami da bankado masu ruwa da tsaki wurin wannan mummunar dabi’a.
Daga karshe wajibi ne ga dai-daikun al’umma da su tashi tsaye wajen bada gudummuwa ga yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi domin kaucewa fadawar al’umma cikin halaka.
Yazama wajibi ga gwamnati da masu rike da mukaman siyasa da kungiyoyi kai harma da dai-daiku masu hannu da shuni su samar da cibiyoyin koyar da sana’ o’in hannu (skills acquisition centres) domin horar da dimbin matasa da basu da aikin yi.
A karshe muna yabawa gwamnatin tarayya wato Federal Government akan haramta shigowa tare da sarrafa sinadarin codein, kuma muna kira ga sauran matakan gwamnati da su marawa wannan mataki na gwamnati wajen samar da dokoki da daukar matakai da zasu rage ko kawar da shaye-shaye daga cikin al’ umma.

✍ *Nasiru Bala Bungudu (Abu-Khadijah)*
08067234355

6- Ramadan 1439 AH / 22- May 2018

Sunday, 3 February 2019

SUNNONIN SALLAH

SUNNONIN SALLAH
Shinfida: Su sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah, saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba.
Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya. Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyaran sallah ta hanyar yin kabaliyyah ko ba’adiyyah, amma ita farilla ba’a yi mata hakan.
Sunnonin Sallah: su sunnonin sallah suna da yawa, sun fi farillan sallah yawa, ga kadan daga cikin su:
1.Tada Ikamar Sallah: Ita ikamar sallah ta shafi mai sallah shi kadai ko wadanda za su yi ta cikin jam’i, kuma bayananta sun gabata a Babi Na shabakwai (017).
2. Karatun Sura Bayan Fatiha: Kasancewar shi karatun Fatiha yana cikin farillan sallah to yanzu shi karatun sura bayan fatiha yana cikin sunnonin sallah ne, kuma wadannan bayanai sun shafi maza da matane baki daya, domin duk abinda aka umarci maza da shi an umarci mata das hi saidai abinda shar’a ta ware tace banda mata. Kuma mutum ya tashi ya koyi karatun sallah daga bakin malamai. Sannan mu sani shi karatun sura bayan fatiha ana yin shi ne a raka’o’i biyun farko, kenan banda na karshe, kamar haka: Asuba ana yi a duka raka’o’in, Azahar ana yi ne a raka’o’I biyun farko banda biyun karshe, la’asar ma haka, haka namma magariba banda dayar karshe, sannan ita ma isha banda biyun karshe.
3. Tsayuwa Domin Karatun Sura: Kenan kamar yadda karatun surar yake sunnane to hakama yin karatun a tsaye, kenan ba’a karatun sura a zaune sai dai idan akwai larura da shari’a ta yadda da ita.
4. Sirrantawa A Inda Ake Sirrantawar : Abinda ake nufi da sirrantawa shine ka motsa harshe domin yana furta karatun Alkur’ani, wato bakinka na motsi kenan, amma idan mutum ya yi shiru yai dunkum ba’a kiran wannan asurtawa. Inda ake surrantawa kuma sune: Azahar da la’asar bakidaya raka’oinsu, sai kuma raka’ar karshe ta magariba da kuma raka’oi biyun karshen Lisha. Haka kuma nafilfilin rana suma ana asurta su ne.
5. Bayyanawa A Inda Ake Bayyanawa: Idan kuma akace bayyanawa ana nufin ka jiyar da kanka da kuma wanda yake kusa da kai, wannan idan kai kadai kake sallah kennan, amma idan kai limanne to zaka daga murya yadda kowa zai ji, ai domin karatun limanne aka hana mamu su yi na su karatun.
Kuskuren da ake samu anan shine, idan mutum ya shigo masallaci zai yi sallah ko kuma ya mike yana ramo raka’o’in da suka wuce shi sai ya bude baki yana karatun sallah da karfi, wanda wannan yana shiga cikin karatun wani, yana kuma hargitsawa wani nashi karatun, inda kowa zaibi yadda bayan suke to da an yi komai cikin jin dadi da walwala, zuwa inda ake karatu shi zai magance wadannan matsalolin.
Wuraran da ake bayyana karatun sallah kuma sune kamar haka; Karatun sallar asuba baki-dayanta, raka’ar karshe ta sallar magariba, da kuma raka’o’in karshe na sallar lisha.
6. Kabarbari: Dukkanin kabarbarin sallah sunnane in banda kabbarar farko wacce take ita farillace wato kabbarar harama. Saidai malamai sun karawa juna sani akan cewa; shin dukkanin kabarbarin a dunkule suke sunnan guda koko kowacce kabbara sunnace mai zaman kanta?.
7. Tahiyyah: Itama tana cikin abinda ya kamata mutum ya koya daga bakin malami kai tsaye, yana karantawa kana karantawa, domin ana samun kura kurai masu tarin yawa a lokacin mutane suke karantata.
8. Zama Domin Tahiyyah: Ashe itama ba’a yinta a tsaye, kuma inda mutum zai zauna amma bai karantata ba to yabar sunnah guda daya, idan kuma ya manta bai yi zaman farkoba misali to yabar sunnoni biyu kenan, karatun tahiyyar da kuma zama domin karatunta.
9. Gabatar Da Fatiha Kafin Surah: Inda mutum zai zai fara karanta surah sannan ya zo ya karanta fatiha to da ya bata tsarin sallah, domin yadda ake so shine ka fara gabatar da fatiha sannan ka sai ka karanta surah.
10. Bayyanar Da Sallama: Kenan ita sallama ba’a asurce ake yenta ba, ana bayyana tane, anan mu ban-bance shi yin sallamar wajibine, amma yenta kuma a bayyane sunnane daga cikin sunnonin sallah.
11. Salati Ga Ma’aikin Allah : Yin salati ga manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana daga cikin sunnonin sallah. Kuma shi salati ga ma’aikin Allah yana da muhimmanci da lada da kuma falala mai zaman kanta, malamai sun kawo sigogi na salati ga ma’aikin Allah a kicin littafansu kamar mai littafin Ashmawi ya kawo haka nan ma mai littafin Iziyyah da kuma mai Risalah, mafi kyawun littafi da aka rubuta domin bayanin salati ga ma’aikin Allah shi kadai, shine littafin ‘Jila’ul Afham’ , zaka same a shagunan da ake sayar da littafan musulunci.
12. Suturah: Duk wanda yake sallah shi kadai ko shine liman to anan ana bukatar ya sanya suturah a gabanshi, domin baiwa mai wucewa damar wucewa ta bayan suturar, amma shi mamu baya sanya sutura domin suturar liman ta wadatar masa, saboda haka idan kuna sallah da liman sai wani ya wuce ta gabanku babu komai inda ba ya wuce ta tsakanin liman da suturarshi bane.

Sunday, 20 January 2019

001 GIDAN NI'IMA

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
*GIDAN NI'IMA*
🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠🏠

Gabatarwa; *BABAN-SINAN*

_Fitowa Na Farko 001_

🔴 *ZABEN ABOKI/ABOKIYAR ZAMA NA KWARAI*

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda yake cewa;
*وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ بُيُوتِكُمْ سَكَنًا...(النحل ٨٠)*

Tsira da aminci su kara tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w, da iyalan gidansa da sahabbansa da duk wanda yabi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar addini.

_Bayan haka:_

Allah madaukakin sarki a cikin Qur'ani yana cewa;

*وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ*

Ma'ana;

*_Ku Aurar da ayama(namiji ko mace wadanda basu da aure) daga cikin Ku, da mutanen kwarai daga cikin bayinku maza da bayi mata, idan kuna tsoron talauci Allah zai wadata Ku daga cikin falalarsa, Allah  mai yalwataccen falala ne kuma masani._*

Babu makawa ga namiji ko mace akan wajibi ne su zabi abokin zama na kwarai, saboda hadisin Annabin rahama s.a.w da yake cewa;

*_Ana auren mace don Abu hudu; Saboda dukiyarta, ko don dagantakarta, ko don kyau, ko don addini, sai Annabi yace na horeka da ma'abociyar addini._* (bukhari da Muslim)

Haka a wani hadisin da Muslim ya ruwaito manzon Allah s.a.w cewa yayi;

*_Duniya wani jin dadi ne, mafi alkhairin jin dadin duniya shine ka samu mace ta gari._*

A wani wurin kuma sai Manzon Allah s.a.w yake ba samari shawara akan cewa;

*_Ku auri yan mata kuma masu haihuwa, saboda inyi alfahari daku a ranar kiyama._*

Kenan a wannan hadisi na karashe manzon Allah s.a.w baya goyon family planning, Allah ya kiyaye.

Daga karshe zan rufe da zancen Magabata cewa:

*الرجل الصالح مع المرأة الصالحة يبنيان بيتا صالحا لأن البلد الطيب يخرج نباته بإذن ربه، والذي خبث لايخرج إلا نكدا.*

*_Mutumin kwarai idan ya hadu da mata ta kwarai suna Gina gida na kwarai, saboda gari tsaftatacce yana fitar da tsirrai da izinin ubangiji, Wanda ya lalace babu abunda zai fitar sai lalatattun tsirrai._*

ZAMU DAKATA A NAN SAI WANI LOKACI IDAN ALLAH YA KAIMU

_SUBHANAKAL-LAHUMMA WABI HAMDIKHA, ASH-HADU AN LAA'ILAHA ILLA ANTA, ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIHI_

✍🏻 Hashim Siraj Uba Tsamiya ( ABU-SINAN )
+2349030201868

https://hashimtsamiya.blogspot.com

atstsamawy@yahoo.com

Wednesday, 26 December 2018

HUKUNCIN HADE SALLOLI A LOKACIN TAFIYA

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HUKUNCIN HADE SALLOLIN AZUHR DA LA'ASAR KO MAGRIB DA ISHAA A LOKACIN TAFIYA*
🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah s.w.t, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga farin jekada Annabi Muhammad s.a.w da iyalan gidansa da sahabbansa da duk Wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

_Bayan haka:_

Maganganu sun yawaita akan wannan matsalar ta inda zaka samu daliban ilimi kullum cikin rigima muke da junanmu akan wannan matsalar, wannan yace GA abunda malaminshi yace shima dayan sai ya kawo maganar shugaban islamiyyarsu, wannan duka yana faruwa ne imma a haduwar mota ce ko a campuses na manyan makarantu, wannan shine dalilin da yasa nabi malamai domin nayi rubutu akan wannan matsalar, nima kuma zan kawo maganganun mai gidana *Manzon Allah s.a.w,* sai dai tunda ance matsala ce da ta shafi daliban ilimi inaga ba dole sai an bude komai ba, za'a Dan haska fitila ne kadan sai mutum yayi dogon hange kafin hasken ya dauke.

Allah yayi mana jagora.

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah s.a.w, hadisin da Abdullahi Dan Abbas R.A ya ruwaito cewa:
كَان
َ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَجْمَعُ بَيْنَ صَلاةِ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ , إذَا كَانَ عَلَى ظَهْرِ سَيْرٍ , وَيَجْمَعُ بَيْنَ الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ .
Wannan hadisi ne sahihi da karara yake nuna mana cewa Manzon Allah s.a.w yana hade salloli.

Idan baka fahimci wannan hadisin ba, toh ga wani Wanda Anas Dan maliku R.A ya ruwaito yace:

كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا ارتحل قبل أن تَزيغ الشمس أخّر الظهر إلى وقت العصر ثم نزل فجمع بينهما ، وإذا زاغت قبل أن يَرْتَحِل صَلَّى الظهر ثم ركب . رواه البخاري ومسلم .
Tirkashi kaji hadisi daga littafan da malamai kecewa sune mafi girman littafai bayan Qur'ani wato(SAHIHUL bukhari da Muslim), kunji fa Manzon Allah s.a.w idan ya daura aniyar tafiya kafin rana ta kawo(wato kafin lokacin sallar azuhr) yana jinkirta azuhr zuwa lokacin sallar La'asar, sannan sai ya sauka ya hade sallolin, idan kuma lokacin sallar azuhr yayi kafin ya fara tafiya yana yin azuhr kawai sai ya fara tafiya.

Ga hadisin mu'az bin jabal R.A a gazwati tabuka yake cewa:

أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ فِي غَزْوَةِ تَبُوكَ إِذَا زَاغَتْ الشَّمْسُ قَبْلَ أَنْ يَرْتَحِلَ جَمَعَ بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ ، وَإِنْ يَرْتَحِلْ قَبْلَ أَنْ تَزِيغَ الشَّمْسُ أَخَّرَ الظُّهْرَ حَتَّى يَنْزِلَ لِلْعَصْرِ ، وَفِي الْمَغْرِبِ مِثْلُ ذَلِكَ ؛ إِنْ غَابَتْ الشَّمْسُ قَبْلَ أَنْ يَرْتَحِلَ جَمَعَ بَيْنَ الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ ، وَإِنْ يَرْتَحِلْ قَبْلَ أَنْ تَغِيبَ الشَّمْسُ أَخَّرَ الْمَغْرِبَ حَتَّى يَنْزِلَ لِلْعِشَاءِ ثُمَّ جَمَعَ بَيْنَهُمَا . رواه الإمام أحمد وأبو داود والترمذي .

Kunga shima wannan hadisin yana tabbatar muna da halascin hade salloli biyu a lokacin tafiya.

A wannan hadisin sai imamut tirmidhi yake cewa;

وبهذا الحديث يقول الشافعي ، وأحمد وإسحاق يقولان : لا بأس أن يَجمع بين الصلاتين في السفر في وقت إحداهما .
Kundai ji, a wurin su imamush shafi'i da imamu Ahmad da ISHAQ bin rahwiyya dukkansu sunce babu laifi a hade salloli biyu a lokacin daya, idan ana cikin tafiya.

Wancan hadisin da ya gabata na tabuka, imamu Muslim ya ruwaitoshi da wani lafazi kamar haka;

خَرَجْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَامَ غَزْوَةِ تَبُوكَ ، فَكَانَ يَجْمَعُ الصَّلاةَ ، فَصَلَّى الظُّهْرَ وَالْعَصْرَ جَمِيعًا ، وَالْمَغْرِبَ وَالْعِشَاءَ جَمِيعًا .
A riwayar Muslim hade sallolin sai ya bayyanar mana da riwayar Imamu Ahmad da tirmidhi da Abi daud da ta gabata.

Abu na gaba shine addinin Allah sauki gareshi, tunda Allah yayiwa matafiyi rangwame akan ya ajiye *azumi* saboda kada ya wahala, ai banga abun rikici ba akan hade salloli, ana zaune gida ma akwai wasu dalilai da suna iya sa a hade salloli.
Hade salloli ga matafiyi ya kasu gida biyu;
1. تقديم
2. أو تأخير

Wato yin sallar azuhr da la'asar a lokacin azuhr ko yin sallar azuhr da la'asar a lokacin la'asar, sai dai dole idan zakayi taqdeem ko ta'akheer sai kayi niyya, ma'ana idan zakayi ta'akheer, dole sai kayi niyya kafin fitar lokacin sallar farko(azuhr)

Abu na gaba shine;

*DAGA KILOMETERS NAWA NE KASARU KE KAMAWA???*

TIRQASHI!!!

Wannan itace matsalar da nafi cin karo da ita a tsakaninmu dalibai yan islamiyya, Wanda kowa na ganin shi malamin kanshi ne, tare da ta'assubanci ga wani malami ko mazhaba, a karkashin wannan zan kawo wata gamsassar magana da Sheikhul Islam ibn Taimiyya ya kawo akan wannan matsalar Wanda ina kyautata zaton zata gamsar da duk wani mai Neman gaskiya akan wannan matsalar, Sheikhul Islam ibn taimiyya yake cewa;
فالفرق بين السفر الطويل والقصير لا أصل له في كتاب الله ولا في سنة رسوله بل الأحكام التي علقها الله بالسفر علقها به مطلقا .

Allahu Akbar, wannan magana ta ibn Taimiyya ta wadatar akan muce sai munyi dogon bayani, abune Wanda yake bude Allah bai kayyade ba kai waye da zaka kayyade?

Toh, rubutun idan akace za'ayi tayi baya karewa, don akwai hujjoji barkatai dake nuna halascin hade salloli a lokacin tafiya, a hakika yanzu nayi rauni a wurin rubutu, amma mu dauka cewa wannan kamar mukaddima ce, idan bukatuwar hakan ta kama zamu kara cewa wani Abu insha Allahu.

ALLAH YA KARA MANA IKHLASI DA KARFIN GWUIWA A WURIN AIKI DA DAI DAI DA FADAR GASKIYA.


✍ *Hashim Siraj Uba Tsamiya ( _ABU~SINAN_ )*

+2348064734911
+2349030201868

atstsamawy@gmail.com

atstsamawy@yahoo.com