Tuesday, 30 March 2021

03 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA UKU (003)

📒ABU NA UKU: BA'A IYAKANCE TA'AZIYYA DA KWANA UKU BA KAMAR YADDA WASU SUKE RIYAWA 📒

Ita Ta'aziyya ba'a iyakance lokacin yin ta da kwana uku ba, a'a, ana yin ta duk lokacin da aka ga fa'idar yin ta ko kuma lokacin da aka samu haduwa da wanda aka yiwa rassuwa, saboda Hadithin Abdullahi bin ja'afar da ya gabata a darasi na biyu kamar yadda yake cewa: bayan shi ja'afar yayi shahada sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WASALLAM yayi jinkiri na kwana uku bai je gidan Ja'afar ba, sannan yazo yace: "KADA KU SAKE KUKA GA DAN UWANA DAGA YAU".
Abdullahi yace: sai Annabi yasa aka zo damu, sai muka zama kamar 'ya'yan tsuntsaye (saboda maraici) kuma yasa aka aske muna kawunan mu sannan ya mike hannu na a sama yace: YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA, KA SANYA ALBARKA GA ABDULLAHI (dansa) KUMA KA SANYA ALBARKA GA KASUWANCIN SA". ya fadi haka har dau uku. Daga nan dai mahaifiyar mu ta zo tana ambata masa maraicin mu kuma tana cike da damuwa, sai Annabi ya ce mata: "KINA JI MASU TSORON TALAUCI NE? ALHALI NINE MAJIBINCIN SU DUNIYA DA LAHIRA?".

Wallahu a'alamu bissawab.

Mu hadu a darasi na hudu(004) insha'allah.

✍️ Nasiru Bala Bungudu
(Chief Imam Salih bin Abdil Aziz juma'at Mosque, Bungudu)

Thursday, 25 March 2021

02 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

DARASI NA BIYU (002)

📒ABU NA BIYU: YIWA IYALAN MAMACI TA'AZIYYA DA KUMA LAFUZZAN DA AKE AMFANI DASU📒

Ana yiwa iyalan mamaci ta'aziyya da duk wadansu kalamai da ake sa ran zasu lallashe su, su rage masu radadi da damuwar wannan rashi tare da sanya su yarda da hukuncin Allah da kuma hakuri, musamman ma lafuzzan da Annabi Muhammad SALAL LAHU ALAIHI WA SALLAM yayi amfani da su, idan mutum ya san su, idan kuwa mutum bai san su ba, to, sai yayi amfani da kyakkyawar kalma domin cimma wannan manufa, kuma kada su sabawa Shari'ah. Dangane da wannan akwai hadithai kamar haka:

📌1. Hadithin Usama bin Zayd (R.A) yace:..... Wata diyar Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ta aika masa cewa danta na dab da mutuwa sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare sa ya aika mata cewa: Yana yi mata sallama kuma yace: "DUK ABINDA ALLAH YA KARBA NASA NE KUMA ABINDA YA BAYAR NASA NE, KO WANE ABU A WURIN SA YANA DA IYAKANTACCEN LOKACI, TAYI HAKURI TA NEMI LADA (a wurin Allah)."  [Bukhariy da Muslim suka ruwaito sa] .

📌2. Hadithin Buraidah bin Husaib (R.A) inda ya nuna cewa:....... Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ya je yiwa wata mata daga cikin matan Madina ta'aziyya sai ya ce mata:" BABU WANI MUTUM KO MACE MUSULMA DAKE DA 'YA' YA UKU (da suka rassu) FACE ALLAH YA SHIGAR DA SU ALJANNA SANADIYAR 'YA' YAN" Sayyidina Umar (R.A) yana gafen dama da Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAM, sai yace koda 'ya' ya biyu?, sai Annabi yace: "KODA BIYU" [Bazzar da Hakim suka ruwaito sa, kuma Hadithi ne ingantcce] 

📌3. Ta'aziyyar da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare sa ya yiwa Ummu Salamah a lokacin da mijin ta abu-Salamah ya rassu, sai Annabi SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAM ya ce: "YA ALLAH KA GAFARTAWA ABU SALAMAH KA DAUKAKA DARAJAR SA A CIKIN SHIRYAYYU, KA MAYE BAYAN SA, KA GAFARTA MUNA TARE DA SHI, YA UBANGIJIN HALITTU, KA YILWATA MASA KABARIN SA KA HASKAKA MASA". [Muslim ne ya ruwaito sa] 

📌4. Ta'aziyyar da Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM yayiwa Abdullahi bin Ja'afar sai Manzon Allah ya ce:.... "YA ALLAH KA MAYEWA JA'AFAR A CIKIN IYALAN SA, KA SANYA ALBARKA GA DANSA ABDULLAHI (dansa) KUMA KA (Sanya Albarka ga) KASUWANCI" ya fadi haka sau uku. [Ahmad ya ruwaito sa, kuma hadithi ne ingantcce] 

💡Wasu kenan daga cikin lafuzzan da Annabi Muhammad SALAL LAHU ALAIHI WA SALLAM yayi amfani dasu wurin yiwa Sahabban sa ta'aziyya. 

Wallahu a'alamu bissawab. 

Mu hadu a darasi na uku (003)

✍️Nasiru Bala Bungudu. 
(Chief Imam Salih bin Abdul Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

001 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI

HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI.

DARASI NA FARKO (001)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah. 

Bisa ga la'akari da muhimmancin ta'aziyya da kuma bukatuwar musulmi ga sanin yadda take a Sunnar Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM, domin kaucewa bidi'o'i naga ya dace in tunatar da kaina game da takaitaccen bayani akan ta'aziyya wanda ya kunshi abubuwa guda shidda (6) kamar haka:
👉1. Shar'antuwar Ta'aziyya a Musulunci
👉2. Yiwa iyalan mamaci ta'aziyya da kuma lafuzzan da ake amfani dasu.
👉3. Ba'a iyakance ta'aziyya da kwana uku ba kamar yadda wasu suke riyawa.
👉4. Abubuwa biyu (2) da ya kamata a nisanta a lokacin mutuwa.
👉5. Sunnah ne dangin mamaci da makwabtan sa suyi abincin da zai kosar da iyalan mamacin su aika masu.
👉6. Mustahabbancin shafa kan maraya da tausaya masa.

📒NA FARKO: SHAR'ANTUWAR TA'AZIYYA A MUSULUNCI:📒

An Shar'anta yin ta'aziyya ga iyalai da dangin mamaci, saboda hadithai da suka yi bayanin haka:

📌 1. Hadithin Qurra Al-Muzanniy (R.A), cewa: a lokacin da Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM ya samu labarin rassuwar dandan wani daga cikin Sahabban sa, ya je yayi masa ta'aziyya har ma yace masa "MINENE YAFI SOYUWA A GAREKA? SHIN KAJI DADIN RAYUWAR KA TARE DA WANNAN YARO? KO (kafi son) KA ISKO SHI BAKIN KOFAR ALJANNA YANA JIRAN KA, YA BUDE MAKA (don ka shiga)?" sai yace: ya Annabin Allah!, nafi son ya riga ni ya bude mani. Wannan Hadithi [[Nasa'iy ya ruwaito shi da wannan siyaqi, haka kuma ibn Hibban da Hakim da Ahmad duka sun ruwaito sa. Kuma hadithin Sahihi ne.]]

📌 2. Hadithin Anas dan Malik (R.A), yace: Manzon Allah SALLAL ALAIHI WA SALLAM yace: "DUK WANDA YAYIWA DAN UWAN SA MUMINI TA'AZIYYA AKAN WATA MUSIBA, (da ta same sa) ALLAH ZAI TUFATAR DA SHI CIKAKKUN TUFAFI A RANAR ALKIYAMA WADANDA MUTANE ZASU YI FATAR SAMUN IRINSU" [Khadeeb Al-Baghdadiy ya fitar da shi da bin Asakir da kuma bin Adiy. Hadithi ne ingantcce] 

Wallahu a'alamu bissawab. 

Mu hadu a darasi na biyu (002) insha'allah. 

✍️ Nasiru Bala Bungudu. 
(Chief Imam Salih bin Abdul Aziz Juma'at Mosque Bungudu)

Wednesday, 13 January 2021

MUSAN MALAMANMU NA SUNNAH - ALOSAIMI

MUSAN MALAMANMU NA SUNNAH...


Waye Sheikh Salih  Al-Osaimi?

Shine Sheikh Dr. Swalih Bn Abdullahi bn Hamad Al-Osaimi, Al-Otaibi

An haifeshi ne a Birnin Riyadh dake Saudiyya, a watan Safar shekara ta 1391AH kuma yana zaune a garin Riyadh har yanzu.
Malam ya himmatu da neman karatu tun yana ɗan ƙarami, yayi tafiye tafiye zuwa ƙasashe masu yawa domin neman ilimi.
Malam ma'aboci sunnah ne
Yayi karatu a wurin malamai masu tarin yawa daga cikin malaman dake Saudiyya, yana da alaƙar ilimi mai ƙarfi da Sheikh Bukar Abu Zaid (R)
Malaman da yayi karatu a wurin su suna da yawa, daga ci akwai:
1. Sheikh Abdulaziz bn Baaz
2. Sheikh Muhammad bn Salihul Usaimin
3. Sheikh Abdullahi bn Aƙeel
4. Sheikh Abdullahi bn Abdulrahman jibrin
5. Sheikh Bukar Abu Zaid
6. Sheikh Salih bn Fauzan Al-fauzan
7. Sheikh Abdulmuhsin Al'abbad

@ Dr. Osaimi yayi karatu a jami'atu Ummul Ƙura, sannan yayi karatun shi tun daga matakin digiri na farko har digirin digir gir a fannin Ulumul Hadith.

@ Dr. Osaimi Mai Fatawa ne kuma limami ne mai hudubar juma'ah a Masallacin Abubakar Assiddiq dake birnin Riyadh

@ An zaɓi Dr. Osaimi a a matsayin member a majalisar manya manyan malamai dake Saudiyya a ranar 3, Rabi'ul Awwal, 1438H

@ Sheikh Swalihul Osaimi yana da halƙoƙi da yake karantawa a wurare kamar haka:
1. Yana karantarwa a Masallacin Manzon Allah S.A.W, darasin da ake kira:
برنامج مهمات العلم

2. Yana karantawa a birnin Riyadh, yana karantar da:
برنامج أصول العلم
3. Yana karantar da mahajjata kafin fara aikin hajji a Masallacin Harami, darasin da ake kira:
برنامج تعليم الحجاج 
4. Yana karantarwa a lokacin azumi a Masallacin Manzon Allah S.A.W, tun daga 1 har zuwa 20 ga Ramadan, sunan darasin
برنامج السرد المجود

Wannan kaɗan kenan daga cikin wurare da kuma Karatuttukan da yake gabatarwa, wanda adadin su zai kusan kai 18-20

Rubuce rubucen da yayi

@ Dr. Osaimi yayi wallafe-wallafe masu yawan gaske, tsakanin waɗanda ya rubuta da kanshi, da kuma waɗanda yayi ma sharhi da Takhriji suna da yawa, amma ga wasu daga cikin su:

١. ﺗﻌﻈﻴﻢ ﺍﻟﻌﻠﻢ
٢. ﺍﻟﺒﻴِّﻨﺔ ﻓﻲ ﺍﻗﺘﺒﺎﺱ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﺍﻟﺤﺬﻕ ﻓﻴﻪ
٣. ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ ﺍﻷﺭﺑﻌﻴﻦَ ﻋﻦِ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﺍﻷﺭﺑﻌﺔ ﺍﻟﻤُﺘَّﺒﻌﻴﻦ
٤. ﺍﻟﻤُﻌﺠَﻢ ﺍﻟﻤُﺨﺘﺎﺭ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻨَّﺒﻮﻳَّﺔ ﺍﻟﻘِﺼﺎﺭ
٥. ﺍﻟﻘَﺮﻳﺾ ﺍﻟﻤُﺒﺪَﻉ ﻧﻈﻢ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻷﺭﺑﻊ
٦. ﻣﻌﺎﻧﻲ ﺍﻟﻔﺎﺗﺤﺔ ﻭﻗِﺼَﺎﺭ ﺍﻟﻤﻔﺼَّﻞ
٧. ﺍﻟﻄُّﺮْﻓﺔ ﺍﻟﺴَّﻨﻴَّﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴَّﺔ
٨. ﺧﻼﺻﺔ ﻣﻘﺪِّﻣﺔ ﺃُﺻﻮﻝ ﺍﻟﺘَّﻔﺴﻴﺮ
٩. ﺇﻣﺘﺎﻉ ﺍﻟﻤﺸﻴﺨﺔ ﺍﻷﺣﻤﺪﻳﺔ ﺑﻄﺮﻕ ﺣﺪﻳﺚ ﻓﻀﻞ ﺍﻟﻤﺮﻭﻳﺎﺕ ﺍﻻﺭﺑﻴﻌﻴﺔ - ﻃﺒﻌﺔ ﺩﺍﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ 1413 ﻫـ
١٠. ﺭﻓﻊ ﺍﻟﻤﻨﺎﺭ ﻟﻄﺮﻕ ﺣﺪﻳﺚ ﻣﻦ ﺳﺌﻞ ﻋﻦ ﻋﻠﻢ ﻓﻜﺘﻤﻪ ﺍﻟﺠﻢ ﺑﻠﺠﺎﻡ ﻣﻦ ﻧﺎﺭ - ﻃﺒﻌﺔ ﺩﺍﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ 1413 ﻫـ
١١. ﺍﻟﻔﺼﻞ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺘﻨﺎﺯﻋﻴﻦ ﻓﻲ ﺣﺪﻳﺚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺑﺤﻖ ﺍﻟﺴﺎﺋﻠﻴﻦ - ﻃﺒﻌﺔ ﺩﺍﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ 1413 ﻫـ
١٢. ﺍﻟﺪﺭﺀ ﻟﺘﺼﺤﻴﺢ ﺣﺪﻳﺚ ﻣﻦ ﺣﺴﻦ ﺇﺳﻼﻡ ﺍﻟﻤﺮﺀ - ﻃﺒﻌﺔ ﺩﺍﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ 1413 ﻫـ
١٣. ﻓﻘﻪ ﺍﻟﻮﺍﻗﻊ ﻋﻨﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ .
١٤. ﺍﻟﺪﺭﺀ ﺍﻟﻨﻀﻴﺪ ﻓﻲ ﺗﺨﺮﻳﺞ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ .
١٥. ﻭﺍﻗﻌﻨﺎ ﺍﻟﻤﻌﺎﺻﺮ ﻋﻠﻰ ﺿﻮﺀ ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ .
١٦. ﻫﺬﻱ ﻫﻲ ﺍﻟﺴﻠﻔﻴﺔ : ﻣﻨﻬﺞ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ .
١٧. ﺍﻟﻮﻓﺎﺀ ﺑﺼﺤﻴﺢ ﺍﺫﻛﺎﺭ ﺍﻟﺼﺒﺎﺡ ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺀ .
١٩. ﺍﻟﺸﻜﺎﻳﺔ ﻭﺍﻟﻨﻜﺎﻳﺔ : ﺑﺮﻗﻴﺎﺕ ﻣﻮﺟﻬﺔ ﺇﻟﻰ ﻃﻠﺒﺔ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺓ .
ﺍﻻﻧﺒﺎﻩ ﺇﻟﻰ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﺃﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ .
٢٠. ﺁﺩﺍﺏ ﺍﻟﺼﺤﺒﺔ ﻭﺣﻘﻮﻕ ﺍﻟﻌﺸﺮﺓ ﺑﻴﻦ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ .
٢١. ﺗﺬﻛﺮﺓ ﺍﻟﺤﺪﻳﺜﻲ ﻭﺍﻟﻤﺘﻔﻘﻪ .
ﺍﻻﻧﺘﻤﺎﺀ ﺍﻟﺤﻖ .
٢٢. ﻛﺸﻒ ﺍﻟﻨﻘﺎﺏ ﻋﻦ ﺿﻌﻒ ﺣﺪﻳﺚ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺠﺎﺏ .
٢٣. ﺭﺳﺎﺋﻞ ﺇﻟﻰ ﺷﺒﻞ ﺍﻹﺳﻼﻡ
٢٤. ﺍﻟﻤﻔﺘﺎﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﻘﻪ
٢٥. ﺍﻟﻤﻘﺪﻣﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ﺍﻟﺼﻐﺮﻯ
٢٦. ﺍﻟﻤﻘﺪﻣﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ
٢٧. ﺍﻟﻌﺮﻭﺓ ﺍﻟﻮﺛﻘﻰ
٢٨. ﺍﻟﻐﺎﻳﺔ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﻉ ﻭﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺔ
٢٩. ﻧﻌﺖ ﺍﻟﺪﺭﺟﺎﺕ ﻟﺘﻠﻘﻲ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻭﺍﻟﻘﺮﺍﺀﺍﺕ
٣٠. ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻔﺎﺗﺤﺔ ﻭﻗﺼﺎﺭ ﺍﻟﻤﻔﺼﻞ
٣١. ﻧﺠﻢ ﺍﻟﻤﻨﺒﻬﺎﺕ ﻓﻲ ﻧﺼﺢ ﻃﻼﺏ ﺍﻟﻤﻬﻤﺎﺕ
٣٢. ﺍﻟﺤﻠﺔ ﺍﻟﺴﻴﺮﺍﺀ
٣٣. ﺭﺳﺎﻟﺔ ﺍﻟﻤﺎﺟﺴﺘﻴﺮ : ﺍﻟﻤﺘﺎﺑﻌﺎﺕ ﻭﺍﻟﺸﻮﺍﻫﺪ ﺩﺭﺍﺳﺔ ﻧﻈﺮﻳﺔ ﺗﻄﺒﻴﻘﻴﺔ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﺇﺷﺮﺍﻑ ﺃ . ﺩ . ﻣﻮﻓﻖ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻘﺎﺩﺭ

@ Dr. Osaimi yana da usulubi mai kyau na karantarwa, yana yawan maimaita duk wata jumla mai fa'ida domin ɗalibbai su fahimci inda karatun ya nufa, kamar dai yadda Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (H) yake da irin wannan usulubi mai kyau a nan gida Nigeria

@Na bibiyi wasu daga cikin Karatuttukan da malam ya gabatar kuma ina fa'idantuwa kwarai da gaske, daga Karatuttukan da na bibiya akwai:
١. تفسير سورة الفاتحة وقصار المفصل
٢. الباقيات الصالحات من الأذكار بعد الصلوات لصالح بن عبد الله العصيمي
٣. شرح آداب العشرة
٤. شرح خلاصة الحسناء
٥. شرح خلاصة مقدمة أصول التفسير
٦. شرح الأرجوزة الميئية في ذكر حال أشرف البرية
Waɗannan duk na saurare su daga farko har ƙarshe kuma na fa'idantu sosai.
Haka nan na bibiyi wasu Muhadarori da malam ya gabatar kamar haka:
١. واجب طلاب العلم في النوازل والحوادث المدلهمة

٢. واجب المرأة عند الفتن

٣. الأمر باتباع السنة والتحذير من ردها
Wannan na ƙarshen na saurari muhadarar kuma na sauke littafin saboda muhimmancisa, musamman a wannan lokaci da matsiyata masu ƙaryata hadisan Annabi da sukar maruwaita.

Malam yana nan a raye har yanzu a birnin Riyadh


Allah ya ƙara mashi lafiya da tabbatuwa akan sunnar Annabi Muhammad S.A.W


✍️ Hashim Siraj Uba Ats~tsamawy
29/05/1442AH
13/01/2021AC

Monday, 20 July 2020

WASU DAGA CIKIN AYYUKAN DA AKE SON MUSULMI YA AIKATA A GOMAN FARKO NA ZUL-HIJJAH

*WASU DAGA CIKIN AYYUKAN DA AKE SO MUTUM YA AIKATA A GOMAN FARKO NA WATAN ZUL-HIJJAH*


1. *AIKIN HAJJI:* yazo a cikin bukhari da Muslim, Annabi Muhammad S.A.W yana cewa: (Aikin hajji karbabbe ba yada sakamako sai aljannah).
Abun nufi shine: idan bawa yayi aikin hajji wacce Allah S.W.T ya karba mashi, hajjin da mutum ya tattara ayukan alkhairi, lallai irin wannan baida sakamako, da falala daga wurin Allah sai shigar shi aljannah.

2. *AZUMIN RANAR ARFA:*
 Manzon Allah S.A.W yace: (Azumin ranar arfa yana kankare zunubin shekarar da ta gabata, da wacce zata zo bayanshi.

3. *YANKA ABUN LAYYA DOMIN NEMAN KUSANCI ZUWA GA ALLAH:* Abun nufi a cikin yin layya ba wai kawai cin nama da sadaka da kyauta ne ba kawai, abun nufi shine zubar da jinin dabbar domin neman kusanci ga Allah S.W.T

A karkashin wannan akwai wasu abubuwa kamar haka:
*NA FARKO:*
 Kayi kokarin ganin ka yanka abun layyarka da kanka

*NA BIYU:* idan baka yanka da kanka ba, ka tabbata kana wurin da za'a yanka, a yanka ta a gaban ka.

*NA UKU:* idan baka samu damar yankawa da kanka ba, baka samu damar da zaka tsaya a yanka a gaban ka ba, toh sai kayi umurni, ya zamana cewa an yanka da umurninka cewa a yanka maka

4. *KABBARA, DA GIRMAMA ALLAH S.W.T:*
Ya tabbata daga sahabban Annabi Muhammad S.A.W, Abi hurairah, da Abdullahi dan umar(Allah ya yarda dasu) sun kasance suna kabbarori a kwanaki goma na zul hijja.

5. *AZUMTAR KWANAKI TARA NA FARKON ZUL-HIJJAH:*
Ana son musulmi ya azumci wadannan kwanaki masu daraja, yin ayyukan alkhairi a cikin wadannan kwanaki Yana da falala da lada sosai.


Allah ya datar damu da aikata aiki na kwarai a wadannan kwanaki masu albarka.


https://t.me/muryarsunnah1



✍️ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABU SINAN_ )*
atstsamawy@gmail.com

Tuesday, 14 July 2020

MAKABARTA GIDAN KOWA DA KOWA

*MAKABARTA GIDAN KOWA DA KOWA*

*LADUBBAN ZIYARAR MAKABARTA*


Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai Wanda ya halitta rayuwa kamar yanda yaso Kuma yake karbarta a lokacin da yaso, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W Wanda aka baiwa zabin zaman duniya ko Kuma komawa zuwa ga Allah, ya zabi ya koma zuwa ga mahaliccinsa.

Bayan haka:

Dalilin wannan rubutun shine, kasantuwar Koda yaushe Allah yana karbar rayukan mutane, wadanda ke raye kuma suna ziyarar makabartu domin binne wadanda Allah ya karbi rayukansu, toh amma Sai naga yanzu al'ummar da muke rayuwa a cikinta mun gafala daga kabari da Kuma Azabar dake tattare dashi, wannan ne yasa naga dacewar in tunatar da yan uwana musulmi akan kabari da Kuma ziyarar shi.

*HAKURI IDAN ANYI MAKA MUTUWA*

Manzon Allah S.A.W ya wuce wasu kaburbura a wata Rana, Sai ya ga wata mata tana kuka😢 a kusa da Wani kabari, Sai Annabi S.A.W yace mata: kiji tsoron Allah, kiyi hakuri, ita wannan matar Bata San cewa Annabi S.A.W bane yake mata magana, Sai tace mashi: tafi ka kyale ni, saboda Kai musibar da ta sameni bata same ka bane don haka.
Sai Manzon Allah S.A.W ya wuce ya kyaleta, Sai ake fada mata cewa: Shifa Wanda yake maki magana Annabi ne! Sai ta tafi da sauri ta sameshi, tace: Ni bansan kai Annabi bane. Sai Annabi S.A.W yace mata:
Hakuri a lokacin mutuwa shi yafi.[Bukhari da Muslim]
Ita musiba tana bukatar hakuri, dole ne musulmi yayi hakuri idan Wani Abu na damuwa ya sameshi, Manzon Allah S.A.W ya ziyarci kabarin mahaifiyarshi, Sai yace: na nemi izinin ubangiji akan a bani dama in nema mata gafara, Amma ba'a bani izini ba, Sai na nemi izini akan ziyartar kabarinta, Sai akayi mani izini. Sai Annabi S.A.W yace: ku ziyarci kaburbura, domin suna tuna mutuwa.
 [مسلم وأبو داود]
Daya daga cikin magabata yake cewa: Idan al'amurra suka tsananta gareka, toh ka ziyarci kaburbura, domin ziyarar kabari tana tausasa zukata, tana tuna maka da lahira.
Uthman bn Affan(R.A) ya kasance idan aka ambaci Aljanna da Wuta a gabanshi baya kuka, Amma da zarar an ambaci kabari Sai ya fashe da kuka. Sai aka tambayeshi akan hakan, Sai yace: Naji Manzon Allah S.A.W yaana cewa:
Kabari shine farkon masaukin lahira, idan ka tsira daga gareshi, abunda zai biyo bayanshi yafi sauki, idan baka tsira daga gareshi ba, abunda zai biyo bayanshi yafi tsanani
  [أحمد]

Ziyarar kaburbura Yana da wasu ladubba da ya kamata musulmi ya ladabtu dasu, daga cikinsu akwai:

1. HALARTO DA NIYYA: Dole ne musulmi ya kudurce zai ziyarci makabarta ne don Allah, sannan Kuma domin ya gyara bannar da zuciyar shi ke aikatawa.

2. YIMA MAMATA ADDU'AH: Ana bukatar Mai ziyarar makabarta yayima mamatan dake kwance a cikin kaburbura addu'ah, kamar yadda Annabi Muhammad S.A.W ya koyar da sahabbanshi, addu'ar itace kamar haka:
السلام عليكم أهل الديار من المؤمنين والمسلمين، ويرحم الله المستقدمين منا والمستأخرين، وإنا إن شاء الله بكم لاحقون.
 [مسلم].

Fassarar addu'ar itace kamar haka: 
Amincin Allah ya tabbata ga ma'abota wadannan gidaje, muminai da musulmai, Allah yayi rahama ga wadannan suka Dade da mutuwa daga cikinmu da Kuma yan baya, Kuma in Allah ya yarda mu ma zamuyi tarayya daku a wannan gida

3. BA'A ZAUNAWA, KO TAFIYA AKAN KABURBURA:
Dole ne musulmi yayi kokarin ganin daina zama ko kishingid'a, ko zirga zirga a saman kaburbura, saboda fadar Annabi Muhammad S.A.W cewa: Mutum ya zauna akan garwashin Wuta, ya Kona tufafinsa, ya taba fatar jikinsa, shi yafi alkhairi gareshi akan ya zauna/ya du'ka akan/a gaban kabari
 [مسلم]

4. KARANTA ALQUR'ANI DA KUMA TAWASSALI AKAN ALLAH YA KAI LADAR GA MAMATA:
Babu laifi mutum ya karanta Wani Abu daga cikin abunda ya sawwaka gareshi na Qur'ani Mai girma, sannan ya roki Allah ya karba mashi abunda ya karanta, sannan ladar Allah ya Kai ga mamacin.

5. BAYA HALASTA TABARRUKI DA KABURBURA:
Baya halasta a nemi tabarruki da kaburbura, kamar yadda baya halasta a sumbaci kabari kamar yadda jahilai daga cikin gama-garin mutane suke aikatawa, dogaro da Hadisin da Annabi Muhammad S.A.W yake cewa: Idan zakayi roko ka roki Allah, idan zaka nemi tsari, ka nemi tsarin Allah
[الترمذي].

6. BA'A DARIYA KO WASA A MAKABARTA:
Dariya da wasa a cikin makabarta dalilai ne na kekashewar zuciya, makabarta wuri ne dake sa musulmi ya nisanci wasan tsalle tsalle da guje guje a cikinta, saboda kaburbura suna tunatar da Mai dauke duk Wani jin dadi(MUTUWA), a cikinta akwai tunani Amma ga Masu hankali daga cikin mutane.

7. YABO GA WADANDA SUKA MUTU, DA AMBATON KYAWAWAN AYYUKANSU:
Baya halasta zagin mamata, ko ambaton kurakuran su, matukar sun mutu akan musulunci,
Annabi Muhammad S.A.W Yana cewa: kada ku zagi mamata, domin su sun Rika sun riski abunda suka gabatar
 [البخاري]

A Wani Hadisin Manzon Allah S.A.W Yana cewa: kada ku ambaci matattunku Sai da alkhairi
 [النسائي]

8. BA'A SALLAH A MAKABARTA:
Annabin Rahama S.A.W yayi hani akan yin sallah a a makabarta, ko fuskantar makabarta a lokacin da mutum yake sallah, an riwaito daga Abdullahi Dan Umar (R.A) yace: Manzon Allah S.A.W yayi hani akan yin sallah a wurare guda bakwai, 1. A cikin bola(juji), 2. Kwata(Mayanka), 3. Makabarta, 4. Magamar hanya, 5. Makewayi(Toilet), 6. Wurin da ake daure rakuma, 7. Da kuma saman dakin ka'aba
[ابن ماجه]

Musulmi Yana da kyau ya Rika ziyarar makabarta, zuciyarshi zata cika da tausayi da imani, Sai kaga kana aikata ayyukan kwarai, Sai kaga Allah ya datar dakai kana yi mashi biyayya, kana lizimtar abubuwan da Allah yace ayi, kana nisantar abubuwan da Allah ya hana. Haka nan Kuma ziyarar musulmi zuwa makabarta tana sanya musulmi ya Rika tsoron wannan rayuwar ta duniya, musamman idan ya tsaya a gaban kabari tsayuwa ta dubo da tunani, kana tunanin halin da wadanda ke cikin kaburburan suke a lokacin da suna duniya, suna Kai da kawo, suna ayyuka mabanbanta, Amma fa yanzu gashi basu iya aikata komai daga cikin abubuwan da suke aikatawa a duniya, abunda zai tseratar dasu kadai ayyukansu na Alkhairi da suka aikata a duniya, sannan Sai Kai kayi tunani a karan kanka, kaima Wani lokaci zaka kasance a cikin irin wannan halin. Wannan Sai ya taimakeka wurin yin aiki na kwarai a nan duniya, domin tseratar da kanka daga azaba a ranar hisabi.


Allah muke roko daya gafartawa mamatanmu, mu Kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani🤲🤲🤲



Dan uwanku a musulunci
✍ *ABU SINAN*
+2349030201868
atstsamawy@gmail.com

Thursday, 20 February 2020

006 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*

_006_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

✅ *ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA*

   Akwai abubuwa da yawa da suke taimakawa mutum wajan sadar da zumunta.
Ga kadan daga cikinsu kamar haka:

1. Yin tunanin manya-manyan darajoji da suka tabbata ga mai sadar da zumunta: Lallai sanin kyakykyawan sakamakon aiki da kuma hango kyakykyawan karshe dake samun mai sadar da zumunta yana taimaka maka wajen sadar da zumunta.

2. Nazari akan mummunan karshe ga mai yanke zumunta:
kula da abin da yanke zumunci yake janyowa na bakin ciki da damuwa da hasara, da nadama da sauransu, yana taimakawa mutun ya nisanci yanke zumunta ya kuma sadar da ita.

3. Neman taimakon Allah:
Wannan yana tabbata ne ta hanyar rokon Allah ya datar da kai ya kuma taimake ka bisa sadar da zumunta ga yan uwanka.

4. Maida mummuna da kyakykyawa:
  Yana daga cikin abin da yake wanzar da soyayya da kuma kiyaye zumuncin dake tsakin yan'uwa shine musanya mummuna da kyakykyawa. Karbar uzurinsu idan sun yi kuskure da kuma basu uzuri. Yana daga mafi kyawon abin da zan fada acikin wannan shine abin da ya gudana tsakanin Annabi Yusuf da yan'uwan sa, hakika sun aikata abin da suka aikata amma yayin da suka bada uzuri ya karbi uzurinsu ya musu rangwame mai kyau, bama wannan kadai ba, har addu’a yayi musu kuma ya roki Allah ya gafarta musu.

5. Yi musu rangwame da kauda kai daga aibobansu koda basu baka uzuri ba:
Wannan yana daga cikin abin da yake nuna karamcin mutum da kuma girman himmarsa, mai hankali tatacce yana yin rangwame da kau da kai daga ambaton aiboban yan'uwansa, baya ambaton laifukan su ko da kuwa basu bada uziri ba.

6. Kan-kan dakai da saukin ma’amala:
  Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suke sanya soyayyar yan uwa ga dan uwansu kuma su kusance shi.

7. Nisantar husuma da yawan jayayya da jidali ko fada da yan uwa.

8. Barin yi masu gori da neman sai sun ran kamaka:
ya zama dole mutun ya bar yima yan'uwansa gori idan ya basu wani abu ko ya ziyarcesu, ko ya basu wata kyauta da dai sauransu.

10. Juriya da daukar duk wani aibantawa daga yan'uwa:
Lallai wannan yana daga cikin abubuwa mafi kyau, shine mutun ya kauda kai yayi hakuri da duk wata suka ko tsegumi da yan’uwansa suke mashi, saboda shedan na shige da fice don ganin ya haifar da matsala a tsakanin yan'wa.

11. Gaugawar aikawa da kyauta idan aka samu sabani a tsakanin yan’uwa:
Kyauta tana janyo Soyayya da kaunar juna, sannan kuma tana hana mummunan zato. Saboda Annabi (SAW) yace; ''KUYI KYAUTA KU SO JUNA''

12. Kwadayin kawo gyara da sulhu a tsakanin yan'uwa idan an samu sabani:
  Yana daga cikin abin da ya kamata ga duk masu hankali da natsuwa shine su yi sauri su kawo gyara da sulhu idan wata matsala ta taso a tsakanin yan'uwa, domin idan ba’ayi haka ba sharrin yana iya game kowa.

13. Gaggauta rabon gado:
Ya kamata idan aka samu rasa rai a gida na uba ko na uwa a gaggauta raba gado domin kowa ya amshi rabonshi, wannan yana kawar da rigima da yawan neman sai anraba kuma wannan yana kara dankon zumunci a tsakain yan’uwa.

14. Shirya taro na wata-wata ko shekara-shekara:
Lallai ire-iren wadannan tarukka suna dauke da alherai masu yawa domin a nan ne za’a san juna a sadar da zumunta ga juna, a yima juna wassiya da dai sauransu.

15. Kaddamar da gidauniya ko kafa asusu:
  Yana daga cikin abin da ke karfafa zumunta, shine samar da gidauniya ko wani asusu da za'a rika tara kudi duk wata ko shekara domin tallafawa yan'uwa. Da wannan gudunmawa da aka bada za'a iya tallafawa yan'uwa idan wasu matsaloli sun tunkaresu.

16. Kwamitin masu bada shawara:
  Yana da kyau a samar da kwamito ta wadanda zasu rika bada shawara a karkashin kwamitin zumunta, kamar kwamitin ilimi, Kwamitin sulhu, da sauransu. Ta haka ne kowa zai san hakkinsa da kuma hakkin yan'uwansa a kansa.
17. Kula da halayensu da ba kowa matsayinsa:
  Akwai daga cikin yan'uwa wanda yake yarda da kadan daga sadarwar da akayi masa, koda a shekara za’a ziyarceshi sau daya, koda ta wayar salula ne, wani ma ko da sakin fuskane da kuma Magana. Akwai wanda bai yarda da komai sai ziyara ako da yaushe. Duka wadannan a kula dasu saboda zumunta ta tabbata.

18. Sadar da zumunta don Allah:
  Zumunta Ibada ce mai girma don haka ana sadar da ita ne don Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kamar yadda Allah (SWT) yake fada: ''KUJI TSORON ALLAH DA KUKE ROQON JUNA DASHI, KUMA KU KIYAYE ZUMUNTA. [Nisa'i aya ta 1]
Hakikanin mai sadar da zumunta don Allah shine mai sadar da zumuntar sa ga yan uwanshi ko sun sadar mashi ko basu sadar mashi ba, kamar yadda Bukhari ya ruwaito cikin sahihin littafinsa, manzon Allah (SAW) yana cewa: ''BAI ZAMA MAI SADAR DA ZUMUNTA BA, WANDA SAI AN SADAR MASHI SANNAN YA SADAR, HAKIKANIN MAI SADAR DA ZUMUNTA SHINE WANDA IDAN AN YANKE MASHI SAI YAYI KOKARIN SADARWA''.  [Bukhari 5991]

A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU

DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*

#ABBAN_SINAN

https://fb.me/abbansinan