Monday, 18 December 2017

TARIHIN RASUWAR MANYAN MUTANE, MASU DARAJA A CIKIN MUSULUNCI, WADANDA AKE YAWAN TAMBAYA A KANSU.

🗓 *TARIHIN RASUWAR MANYAN MUTANE, MASU DARAJA A CIKIN MUSULUNCI, WADANDA AKE YAWAN TAMBAYA A KANSU*




📒 ```Annabi Muhammad (salallahu alaihi wasallam) ya rasu a shekara ta 11AH

📕 Abubakar sideeq R.A shekara ta 13AH


📔 Umar bin khaddab R.A shekara ta 23AH

📙 Usman bin Affan R.A shekara ta 23AH

📘 Aliyu bn Abi dalib R.A shekara ta 40AH

📗 Aisha bintu Abubakar R.Anha  shekara ta 57AH


📕 Abdullahi bn Abbas R.A shekara ta 68AH

📔 Abdullahi bn umar R.A shekara ta  73AH

📘 Sa'eed Ibnul musayyib R.H shekara ta 94AH

📙 Umar ibn Abdulaziz R.H shekara ta 101AH

📗 Hasanul busri R.H shekara ta 110AH

📕 Abu Hanifa R.H shekara ta 150AH

📗 Malik ibn Anas R.H shekara ta 79AH

📘 Shafi'i R.H shekara ta 204AH

📕 Ibn Rahawiya R.H shekara ta 238AH

📙 Ahmad ibn Hambal R.H shekara ta 241AH

📗 Ahmad Ibn sa'eed AD-DARUMY R.H shekara ta 253AH

📘 Abdullahi Ibn Abdulrahman AD-DARUMY R.H shekara ta 255AH


📔 imamul Bukhary R.H shekara ta 256AH



📕 Imam Muslim R.H shekara ta 261AH


📗 Ibn majah R.H shekara ta 273AH



📘 Abu daud R.H shekara ta 275AH



📙 Tirmidhi R.H shekara ta 279AH

📗 Usman bin sa'eed AD-DARUMY R.H shekara ta 280AH



📗 imamun nasa'i R.H shekara ta 303AH



📔 Ibn jareer AD-DABARY R.H shekara ta 310AH

📘 Ibn khuzaimah R.H shekara ta 311AH


📕 Ibn Hibban R.H shekara ta 354AH


📙 Imamu DARAQUDUNY R.H shekara ta 385AH


📔 imam Hakim R.H shekara ta 405AH


📗 Ibn hazam R.H shekara ta 456AH


📘 BaihaQy R.H shekara ta 458AH


📕 Ibn Abdulbarr R.H shekara ta 463AH


📔 khadeebul baghadady R.H shekara ta 463AH


📗 Ibnul Araby R.H shekara ta 543AH


📘 Ibn rushid R.H shekara ta 595AH

📙 Ibnul jauzy R.H shekara ta 597AH

📔 Alkurduby(mai littafin الجامع لأحكام القرآن) R.H shekara ta 671AH


📕 Imamun-Nawawy R.H shekara ta 676AH

📗 Ibn Taimiyya R.H shekara ta 728AH

📔 Imamuz-Zahaby R.H shekara ta 748AH

📘 Ibnul kayyim R.H shekara ta 751AH


📙 Ibn Katheer R.H shekara ta 774AH


📗 Ibn Rajab R.H shekara ta 795AH


📔 Ibn Hajar AL-ASQALANY R.H shekara ta 852AH


📗 Imamus - suyudy R.H shekara ta 911AH


📘 Ameerus - san'any R.H shekara ta 1182AH



📕 Muhammad Ibn Abdulwahab R.H shekara ta 1206AH



📗 Imamush -shaukany R.H shekara ta 1250AH


📔 AL-ALUSY R.H shekara ta 1342AH


📙 Ibn Sa'ady R.H shekara ta 1376AH


📕 SHANQIDY R.H shekara ta 1393AH


📘 Ibn baz R.H shekara ta 1419AH


📗 Albany R.H shekara ta 1420AH


📔 Ibn uthaimin R.H shekara ta 1421AH

📕 Abdullahi bn Abdulrahman bn jibreen R.H shekara ta 1430AH


⭕ Ku tura ta zuwa ga daliban ilimi

⭕ Ku tura ta zuwa ga wadanda Luke kusa dasu domin mu hadu wurin amfanuwa.


FASSARAWA:
_HASHIM IBN SURAJ IBN UBA (ABU~SINAN)_```
+2348064734911

http://hashimtsamiya.blogspot.com/

atstsamawy@gmail.com

MUHADARAMUHADARA

📀📀📀📀📀📀📀📀📀
*MUSLIM UMMAH WELFARE AND DA'AWAH ASSOCIATION TSAFE*
💿💿💿💿💿💿💿💿💿


*WA'AZIN DA AKA  GUDANAR A RANAR  ASABAR  27/RABIU AUWAL/1439)*

*DAGA BAKIN SHUGABAN KWAMITIN: (MALAM IBRAHIM MUHAMMAD FILO) TSAFE*

*MAUDU'IN KARATUN SHINE:--- WAJABCIN NEMAN ILMI DA AIKI DA SHI*

Shiga Link dake kasa domin saukewa

💽💽💽💽💽💽💽💽💽💽
http://darulfikr.com/s/37564

*AYI SAURARO LAFIYA CIKIN SAUTI MAI KYAU*

Kasance da darulfikr.com a koda yaushe, domin samun KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH.

#ABBAN_SINAN
+2348064734911

Friday, 15 December 2017

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN; MUHIMMANCIN NAFILA

FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH   DAGA MASJID ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon  limam Sani Abi hurairah Tsafe ya gabatar da khudbar ne akan #MUHIMMANCIN_NAFILAH

Bayan mukaddimah......

Yan uwa musulmi masu albarka hakika gaskiyar zance shine Alqur'ani Mai tsarki, Mafi kyawun shiriya itace shiriya ta Annabi Muhammadu sallal lahu alaihi wassalam, Mafi sharrin ayyuka shine kirkirar abu ga addini.

Yan uwa musulmi masu albarka ina maku Nasiha tare da ni kaina da muji tsoron ALLAH domin jin tsoron ALLAH shine jagora ga rayuwar mu, ALLAH yana fada cikin suratul kasas cewa "WANNAN GIDAN NA LAHIRA MU SANYA SHINE GA MASU TSORON ALLAH HAKIKA AQIBA MAI KYAU ITA KUWA AQIBA MAI KYAU TANA GA MASU TSORON ALLAH"

Saboda kaunar da ALLAH keyi mana ya sanya mana abubuwa da Zamu amfana dasu, kamar nafilfili da sauransu,  Nafila ta sallah tana Matukar muhimmancin ga ibada,

Yan uwa musulmi masu albarka sallah itace abunda za'a fara bincike a gobe Kiyama, Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa "Farkon abunda za'a yiwa dan Adam hisabi akanshi shine sallah idan tayi kyau to dan Adam ya dace idan kuma an samu matsala sai ALLAH ya umarci mala'iku su binciki shin akwai nafila?
Idan akwai to sai ayi amfani da ita wajen cike sallar farilla"

Haka ma a azumi da zakkah sai a diba idan akwai wakafi da sauran ibadu!!

Kenan koda a wannan hadisin muka tsaya lallai zamu fahimci cewa nafila nada matukar muhimmanci.

A wajen yin ibadar sallah ana bukatar natsuwa sosai Ibn Abbas ya ruwaito yace" Sai kana da natsuwa sannan sallahr ka zata karbu "

Yan uwa musulmi masu albarka yawan yin nafila yana sa mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah

Akwai wani sahabin Manzo sallal Sallal lahu alaihi wassalam idan Annabi zai yi alwala sai sahabin ya dauki talkaman Annabi ya rike a hannunsa hakama idan Manzo sallal lahu alaihi wassalam zai yi sallah yakan tsaya har sai Annabi ya fito, Wata rana sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya tambaye shi mi kake bukata inyi maka??

Sai yace ina so in zama abokin ka a gidan aljannah.....

Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka taimake ni da yin nafila a koda yaushe. "

Yan uwa musulmi masu albarka yawaita nafila na kara kusan tar da dan Adam ga ubangiji, ALLAH madaukakin sarki na cewa" BAWA BAZAI GUSHE YANA SUJJADAH HAR SAI NA SOSHI "

Yan uwa musulmi masu albarka yawaita yin nafila kara maka kusanci da ubangiji ALLAH

Abdullahi bn Umar ya ruwaito cewa" Kafin sallar azahar kayi raka'a 2 bayan sallar kuma kayi 2 la'asar kayi 2 bayan ta kayi 2 hakama a magrib da isha'i hakama a sallar asuba kafin ta wato sallar fajir "

Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace" Duk wanda yake yawaita yin nafila raka'a 12 a rana ALLAH zai gina mashi gida a aljannah "

Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana cewa" Kuyi raka'a 2 kafin magrib ya fadi haka har sau uku amma ga wanda yake sa hali "

Haka ma Aisha radiyyallahu anha ta ruwaito cewa" Manzo sallal lahu alaihi wassalam bai taba barin nafila ba a lokachin sallar asuba ba "

Yan uwa musulmi masu albarka hadisin dake magana game da ba'a sallah bayan la'asar na nufin idan an dade da gama sallar ne.

Daga cikin nafilolin da ake bukatar yawaita aikatawa akwai sallar duha wato ita anayi ta ne da safe, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Dan Adam yana da gabobi guda 360 ana bukatar a kullum kabada Sadaka kwatan kwacin haka sai sahabbai suka ce to idan baka da kudin bada Sadakar??  Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka tsaftace massallaci (kamar shara ko kuma dauke wani tsinke) koda ma ace ka gaza haka to kayi sallar duha "

Yan uwa musulmi masu albarka hakika addinin musulunci yana da Matukar dadi da kuma garabasa ga wani hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa

" Duk wanda ya fito daga gida yayi aikatawa zaije massallaci to ana rubuta mashi ladar aikin hajji da umrah "

Hakika yan uwa musulmi idan muka yawaita yin nafila za'a rubuta sunayen mu cikin illiyun

Yan uwa musulmi bayan sallar asuba yana da kyau mu rika zaunawa koda awa guda ko biyu ne Muna yin tasbih domin falalar dake ciki, Hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa "Bayan kammala sallar asuba ka zauna har rana ta fito kana da ladar aikin hajji cikakke cikakke cikakke!!

Yan uwa musulmi dole ne mu rage yawan zama ana hira ana surutu fiye da awa guda alhali zaman baida wani amfani garemu,

Imam Muslim ya ruwaito daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa "Dayanku bazai yi alwala yana jiran sallah ba face wuta ta haramta gareshi!!"

Yan uwa musulmi kunji falala mai kyau kenan masu zuwa massallaci da Wuri suna jiran limam sun samu shiga a wannan.

Sannan kuma yan uwa musulmi yana da kyau mu yawaita yin nafila a gidajen mu domin Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Kada mu maida gidajen mu kamar makabartu (Domin ba'a sallah a makabarta)

Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace" Mafificin nafila itace nafillar da akayi a gida "

Yan uwa musulmi kada mu rangwantar da kawunan mu mu kashe jikin mu da hira da surutai marar sa amfani domin wallahi akwai ranar da Zamu nemi ina ma ace Zamu yi aiki koda na kwayar zarra ne!!

Akwai falala mai yawa a cikin sallar nafila, Manzo sallal lahu alaihi wassalam "SALLAR fajir (Kafin asuba) tafi duniya da abunda ke cikin ta"


To yan uwa musulmi kunji fa......

Tabi'ai da sahabbai sun kasance idan wani yayi laifi yana zuwa yayi nafila ya roki Allah ya gafarta masa.

*Sallar nafila tana daga Darajar dan Adam a wurin ALLAH

Hakika sahabbai da Tabi'ai suna yawaita yin nafila domin tsannanin koyi da Annabi, Saboda Annabi ya karantar dasu kuma yayi a gaban su har ma ya kwadaitar da wannan ibadar.

Yawaita nafila yana kawo abubuwa kamar haka :

*Gidan mutun yana albarka

*Darajar dan Adam tana karuwa

*Yana sanya mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah.

*Nafila na zama abokiyar hira ga dan Adam a cikin kabari.

*Zai kara maka son ALLAH

*Tana maida dan Adam yazama mutanen kirki.

*Samun ladar aikin hajji da umrah

*Kankarewar Zunubai.!!

Yan uwa musulmi masu albarka a yadda duniya ta chanza a yanzu dole ne mu rungumi koyar wa Manzo sallal lahu alaihi wassalam da duk abubuwan da ya karantar damu.

ALLAH ka gafarta mana kayi mana rahama kabamu lafiya da zaman lafiya, Ya ubangiji ALLAH kayi rahama garemu ka biya mana bukatun mu ka haskaka rayuwar mu, Ameen

©®Ibrahim Rabilu Tsafe  Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 20-Rabi'ul auwal-1439
Friday 15-December-2017 AB

Friday, 8 December 2017

HUDUBAH MAI TAKEN LOKACIN SANYI

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon limamin  Massallacin Jumu'a na Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na Liman'

Yayi Hudubar Sane Akan #LOKACHIN_HUNTURU

Bayan mukkaddimah........

Yan uwa musulmi masu albarka a yau Khudbar mu zatayi magana ne game da halin da muke ciki, Watau yanayi na hunturu da sanyi da kadawar iska.

Idan muka diba lokachin da muka fito na baya zamu ga cewa lallai yanayi yayi matukar chanzawa, Hakika yan uwa musulmi chanzawar lokachi wani sababi ne ga mai imani da zai kara masa imani, Da kara maida kai ga ALLAH Da jajircewa ga biyar sa!

ALLAH Madaukakin sarki cikin hikimar sa da yarda sa yana shata mana zuwan wannan lokachin duk shekara.

Ibn kaiyumul jauzi yana cewa 'Idan aka lura da yadda ALLAH juya lokutta zamu fahimci cewa akwai wata maslaha dake cikin yin hakan'

Idan da yaso sai ya barmu da lokachi daya ko zafi kawai ko sanyi kawai ko kuma ruwan sama kawai!

Yan uwa musulmi masu albarka ina maku wasiya dani da ku da muji tsoron ALLAH, Hakika da tsoron ALLAH Ne zukata ke kamuwa da natsuwa kuma ake fahimta ayoyi da manufofin ubangiji.

ALLAH Madaukakin sarki na cewa "SUNE (Masu imani) MASU DIBA YADDA MUKE JUYA AKAN LAMURA HAKIKA SUN SAMU IMANI KUMA SUNE MASU AMBATON ALLAH BA DARE BA RANA "

Hakama ALLAH S.W.T Na cewa "LALLAH JUYAWAR DARE DA YINI AYAH CE GA MASU IMANI"

Shi wannan lokachin na sanyi ALLAH Madaukakin sarki ne ya kaddaro shi da haka, Domin wuta ce keyin lumfashi!!

Ga hadisi daga Manzo s.a.w "Wata rana wuta takai kara ga ALLAH S.W.T Cewa wani sashen ta yana cin sashen ta sai ALLAH Yabata dama cewa ta rika numfashi wato taja iska (shine muke samun lokachin sanyi) sannan ta saki numfashi (shine lokachin zahi)"

Iman hasanul busariy na cewa 'ALLAH Ya tanadar da wannan lokutta ne dan tunatar damu game da kiyama, Domin idan nukaji sanyi yayi yawa sai mu tuna cewa sanyin azaba da kiyama yafi na duniya, Hakama zafi na duniya bai kai zahin kiyama ba"

Abdullahi dan Mas'ud r.a ya kasance idan sanyi yazo yana cewa 'Maraba da zuwan sanyi maraba da zuwan sanyi idan aka tambaye shi miye dalilin shi na fadar haka sai yace 'Lokachin sanyi lokachi ne da dare keda tsawo (Ana samun damar yin ibadah da kusantar ALLAH) Rana kuma batada tsawo ana yawaita azumi'

Yan uwa musulmi masu albarka lokachin hunturu yana da HUKUNCE HUKUNCEN sa..

*Yin alwala da kyau-Yazama wajibi mu kiyaye yadda muke alwala a lokachin sanyi, Domin muna sanya manya kaya kuma wajen alwala zakaga wasu saboda kaya masu nauyi basu yin alwala da kyau.

Manzo s.a.w "Yaga wasu na alwala amma basu shafawa yadda yakama sai Manzo s.a.w yace 'Boni ya tabbata ga masu alwala basu cikawa ' "

Babu laifi saboda sanyi ayi alwala da ruwan zafi wajen yin alwala.

*Ana son tuna saukin da shari'ah ta kawo mana, Ya halatta shafa sama safa ko takalma ko huffi, Idan har anyi alwala kafin a sanya safar ko takalman.

Mugira ya ruwaito hadisi kuma an ruwaito shi a sunnanin dauda cewa "Manzo s.a.w yana shafa saman khuffi amma idan yayi alwala,

Hakama wata rana Manzo s.a.w zai yi alwala sai Mugira yazo zai cire masa takalma sai Manzo s.a.w yace kabarshi domin nayi alwala kafin insa!

Larabawa na cewa lokachin sanyi namiji zahi kuma macce, Saboda yanayin karfin su ba daya ba.

A zamanin khalifan Manzo s.a.w na biyu wato Umar bn Khattab r.a yana kewa yawa cikin gari yana cewa 'Sanyi yazo sanyi makiyin mu ne dan haka mu tanadi kayan kariya kamar manya barguna da sauran kayan kariya daga sanyi'

Yaku yan uwa musulmi masu albarka, Hakika Umar r.a ya kasance yana taimakon marar sa galihu da kayan rufe jiki dan kariya daga sanyi.

Anan muna kira ga yan uwa musulmi da mu taimaki yan uwa marayu da makwabta da sauran mara sa galihu, Da kuma kula da iyali da kananan yara a tanadar masu kayan sanya kada mu barsu kamar  dabbobi domin zai iya yin illah garesu.

*Yawaita bautar ALLAH, Hunturu lokachi da dan Adam ke samun lafiya da walwala da kebantuwa daga mutane, Domin ko doguwar hirar da ake yi ragewa ake yi, Zaka fito karfe goma ka tarar babu kowa,

Dan haka sai muyi amfani da wanoan lokachin wajen bautar ALLAH ba yawan bacci ba.

*Mu rika cika alwala, Manzo s.a.w na cewa "Cika alwala ne mafi so a yanzu (Lokachin hunturu).

*Dumama jiki dan samun sauki, Sai dai yana da kyau musulmi ayi hattara sosai, Domin kada mu ajiye wuta ta rika kwana a dakunan mu.

Abul musa al'ashry ya ruwaito cewa "Wata rana ayi gobara a Madinah sai aka fadawa Manzo s.a.w sai yace 'Wannan wutar makiyar muce mu daina aje ta a dakunan mu'!!

Dan haka da zarar zamu kwanta sai mu kashe wuta a fito da ita waje,

Yan uwa musulmi mu taimaki yan uwa marar sa galihu, Mu taimaki marar kayan sanyawa.

Lallai ALLAH Na taimakon bawa, Matukar yana taimakon yan uwansa.

ALLAH Ka taimakemu da taimaka, Ka karemu da kariyar ka.

Ya ALLAH Ka biya mana bukatun mu na alkahri ka kiyaye mu kuma ka tsare mu.

Ya ubangiji kayi rahama garemu da iyayen mu.

Ya ubangiji ka zaunar damu lafiya, Ka albarka ci garin mu.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe  Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 19-Rabi'ul auwal-1439
Friday 18-December-2017 AB

HUDUBA MAI TAKEN TSORATARWA GAME DA RASHIN BADA ZAKKAH

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE



A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #TSORATARWA GA
MASU HANA # ZAKKAH
Bayan mukaddima.....
Yan uwa musulmi masu albarka, A wancan
makon daya gaba munyi bayani game da
#ZAKKAH da hukunce hukunce ta.
To a wannan makon da ikon Allah zamu yi
magana akan tsoratarwar ga halayyar ga masu
hana #ZAKKAH
Yan uwan musulmi muji tsoron Allah gaskiyar jin
tsoron sa musani yana kallo duk abubuwan da
muke aikata a kullum.
Muhimancin #ZAKKAH ba karami bane a
musulunce har Allah yahada ta tare da sallah
wurare 32 a cikin alqur'ani mai tsari,
Babban dalilin wajabta #ZAKKAH shine nuna
godiya ga Allah, Da kuma sadar da umarnin
Allah.
#ZAKKAH tana kankare talauci a tsakanin
mutane, Bada #ZAKKAH tsarkakewa ne wato
tsarkake dukiya da kuma rayuwa baki daya.
Saboda matsayin Allah ya umurci Manzon Allah
s.a.w akan ya karbo #ZAKKAH "KA ANSO
#ZAKKAH DAGA GARESU DAN ZAMA
TSARKAKEWA GARESU"
Yan uwa musulmi masu albarka, Hakika fidda
#ZAKKAH wajibi ne a musulunci kuma dole ne,
Rashin fidda #ZAKKAH yana kawo fitononi da
musibu a cikin al'ummah baki daya. Allah ya
umarce mu da fiddawa da yake cewa "KU FIDDA
DAGA ABUNDA MUKA AZURTA KU DASHI"
Rashin bada #ZAKKAH yana jawo masibu da
bala'oi kala kala!!
Nana Aisha r.a ta ruwaito daga Manzo s.a.w
cewa "Babu dukiyar da za'a tara ba'a fitar mata
da #ZAKKAH sai Allah tarwatsa ta"
Yan uwa musulmi masu albarka muna ganin
musibu da ake samu na gobara da masibu kala
kala, Hakika wannan duk daga hana #ZAKKAH
ne!
Rashin bada #ZAKKAH na kawo debe albarka ga
noma da kudi, Idan muka diba zamu ga yadda
anan garin aka noma shinkafa da farko tayi kyau
amma daga karshe wasu sun fadi warwas!
Duk fa wannan daga rashin bada #ZAKKAH da
muke yi, Manzo s.a.w na cewa "Mutane bazasu
hana #ZAKKAH ba face sai Allah ya debe
albarka ga abun su"
Hakika tsoratarwa mai karfi tazo akan masu qin
fidda #ZAKKAH har ma wani wuri a Qur'ani da
mushrikai.
Sau da yawa zakaga wami yasamu kudi da suka
kai nisabi, Ko kuma yayi noma yasamu albarka
amma sai ya rike #ZAKKAH ko kuma yabada ga
wanda yaga dama ko kuma badawa a lokachin da
yaso maimakon lokachin da yasamu.
Duk wanda yabada #ZAKKAH yadda yaga dama
malamai sunce kamar bai bada wato dashi da
wanda bai bada duk daya.
Rashin bada #ZAKKAH yana kawo musibu, Ita
kuma musiba munsan tana shafuwar har wanda
baiji ba bai gani ba, Wata qila ma tana iya wuce
wanda ya hana #ZAKKAHR Ta fada wani shi
kuma a kyale sa sai ranar kiyama!
Yan uwa musulmi masu albarka, Idan akwai
abokin ka ko dan uwanka ko wani makusancin ka
yake hana #ZAKKAH to kayi masa nasiha tare da
gargadi.
ALLAH Fa yayi mana babban gargadi (Serious
warning) game da hana #ZAKKAH
*BANI YA TABBATA MARAR BADA #ZAKKAH SU
(masu hana zakkah) MUSHRIKAI GA KIYAMA"
*MASU TARA DUKIYA #ZAKKAH DA SANMU
ZA'A JEFA SU A WUTAR JAHANNANAMA TANA
SUYA SU"
*"MASU TARA DUKIYA BASU BADA #ZAKKAH
KUMA BABU ABUNDA YASAMI DUKIYAR
WALLAHI YABAR MURNA DOMIN BALA'I CE
GARESA"
Manzo s.a.w ya fassara wannan ayar da cewa
"Allah zah maida dukiyar maciji mai baki biyu
yana saransa a wutar jahanama yana cewa 'Nine
dukiyar ka da ka hana #ZAKKAH' "
Yan uwa musulmi masu albarka Allah shirewa
duk dukiyar da aka hana #ZAKKAH albarka,
Idan muka diba matsalar tsaro da sauran
abubuwan da suka dame mu duk suna da alaqa
da kaucewa umarnin Allah.
Bayan wafatin Manzo s.a.w wasu sunce sunce
'Sun daina bada #ZAKKAH saboda Manzo s.a.w
ya rassu, Khalifan Manzo s.a.w ya yake su har
garuruwan su ya bisu ya karbo #ZAKKAH
Aliyu bn abi Thalib khalifan Manzo s.a.w ya hudu
yace 'ALLAH Baya dauke musiba sai an tuba!
Allah madaukakin sarki na cewa "DUK ABUNDA
YASAME KU TO DAGA ABUNDA KUKE
AIKATAWA NE"
Hakika ALLAH Yabamu labarin mutane da yawa
wadanda yayi wa ni'ima suka kafurce!
ALLAH Yana fada mana cikin suratul nahal cewa
"ALLAH YABUGA MISALI WATA ALKARYA DATA
KAFURCE"
Sai mu diba muga yanzu wace ni'imah ce Allah
baiyi mana ba??
Munsan labarin wani da ake kira Saba'a yadda
suka kafurce daga karshe ALLAH Kwace ni'imar
daga garesu.
Lallai ne kuma dole ne mu sadar da umarnin
ALLAH Dan samun falala da rahama wata bata
yankewa daga garesa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzo
s.a.w da iyalansa da sahabban sa dukkan
wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Ya Allah ka biya mana bukatun mu kayi rahama
garemu ka gafarta mana yaye mana damuwa, Ya
Allah kara albarka ga dukiyar da ake bada
#ZAKKAH ya Allah ka tarwatsa duk dukiyar da
ake hana #ZAKKAH


©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 28-Safar-1439
Friday 17-November-2017

HUDUBAH MAI TAKEN BIDI'AH

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #BIDI 'AH DA
HUKUNCIN TA A MUSLUNCHI
Bayan mukaddimah...
Yan uwa musulmi a yau Khudbar tamu zata yi
magana ne game da #BIDI'AH da kuma hukuncin
ta a musulunce!!
Yan uwa musulmi muji tsoron ALLAH Gaskiyar jin
tsoron sa, Mu sani cewa da tsoron ALLAH
Rayuwa ke gudana .
Babbar ni'imah garemu ita ce musulunci domin
musulunci shine hanya daya rak dake sada dan
Adam da ubangiji ALLAH , ALLAH Yabamu
rayuwa (Musulunci) kamar yadda ya labarta
mana cewa "YANZU WANDA YA KASANCE
MATACCE (JAHILI) ZAI YI DAI DAI DA MAI RAI
(MAI ILMI)"
Hakika akwai abubuwa wadanda ke ruguza addini
da dama,Babba Daga ciki shine bidi'ah!
Ita bakwai ne kawo ita bidi'ar,
1-Son rai, Shi son rai shine babban jagora ga
qago bidi'ah a cikin addini, ALLAH Madaukakin
sarki kuma ya gargadi masu son da yake cewa
"BABU WANDA YAFI KOWA ZAMA BATACCE SAI
WANDA KE BIN SON RAI".
2-JAHILCI, Tabbas jahilci ya taka gagarumar
rawa a wajen qago bidi'ah a cikin musulunci,
ALLAH Madaukakin sarki na cewa "MAFI YAWAN
MUTANEN DUNIYA JAHILAI NE"
3-Kau da kai daga karbar gaskiya, Tabbas kauda
kai daga karbar gaskiya yana matukar kai dan
Adam ga kirkiro bidi'ah, Ita kau gaskiya duk
wanda ya karbe ta baya tabewa kamar yadda
madaukakin sarki ke cewa "DUK WANDA
SHARI'A TA BAYA TABEWA DUK WANDA YABI
SON RANSA ZA'A TABAR DASHI KUMA ZA'A
TADA SHI MAKAHO"
4-Nisantar masu ilmi, Tabbas nisantar masu ilmi
na fadin gaskiya da kuma takama da jahilci na
kawo kago bidi'ah a addini, Duk abunda mutun
bai sani yakamata yayi ya tambaya amma sai ya
kiya, ALLAH Kuma na cewa "KU TAMBAYI
MA'ABOTA ILMI IDAN BAKU SANI BA"
5- Jiji da kah da son ra'ayi, Hakika ji da kai yana
kawo mutun ya fadawa bidi'a ko kuma ya kirkiro
ta,
6-Son duniya, Tabbas masu mugun son duniya
suna kirkirar bidi'ah su kawo ta a musulunci,
ALLAH Kuma na cewa "SUN ZABI DUNIYA A
BISA LAHIRA " Wani wuri kuma yana cewa "SUN
ZABI RAYUWAR DUNIYA BISA GA TA LAHIRA"
Abubuwa biyu ne bidi'ah take...
1-Bidi'ah ta magana wadanda suke magana ta
izgili da sunan addini kamar mu'utazilawa da yan
Shi'ah.
2-Bidi'ah ta aiki, Kamar bautawa ALLAH Da
shari'ar da bai umarta ba, Ko kuma kari a cikin
ibadah, Misali wani yace maka 'Assalamu
Alaikum' to sai kaji wurin ansawa ance 'Ameen
'Wa alaikum salam anan cewa Ameen bidi'ah duk
da kalmar amin kalma ce mai kyau amma dai
sunnah bata karantar da haka ba, Akwai kara
wani abu wajen yin sallah da sauran su.
Manzo s.a.w ya koyar damu yadda ake yin Zikirai
kowane iri ya koyar damu na safe na rana na
yammah na dare dana komai,
Sannan akwai bidi'ar kebance wani lokachi
wanda shari'ah bata kebe ba dan yin ibadah,
Wannan baya cikin tsarin musulunci.
Hukuncin #BIDI'AH shine tana rushe aiki baki
daya.
Manzo s.a.w na cewa "Mafi sharrin ayyuka shine
kirkiro wani abu cikin addini"
Wata rana Umar bn Abdul'aziz r.a ya fito sai yaga
wani tsoho mai gudun duniya mai tsoron ALLAH
Ya yawaita ibadah amma kirista ne!!
Dan haka sai ya koma gida yayi ta kuka da aka
tambaye shi miye dalilin kukansa sai yace ganin
wannan ya tuna mashi da ayar nan dake cewa
"RANAR DA ZA'A
KIFE FUSKAM SU A CIKIN WUTA"
Ita #BIDI'AH tana kawo kasala ga aikata Sunnah!
Imam hasanul busary na cewa 'ALLAH Baya
karbar ibadun mai bidi'ah sai almajiransa suka ce
saboda mi? sai yace yana da hujja daga hadisin
dake cewa "ALLAH Ya tsinewa mai yin bidi'ah"
Muna rokon ALLAH Ya gafarta mana yayi mana
rahama, Ya karemu daga aikata bidi'ah yayi
rahama garemuda iyayen mu, Ya biya bukatun
mu.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 12-Rabi'ul auwal-1439
Friday 01-December-2017

HUDUBA MAI TAKEN HARAMCIN SATA A MUSULUNCI

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #SATA
Godiya ta tabbata ga ALLAH S.W.T Wanda yayi
halitta ya kuma dai dai ta halittar kamar yadda
yake bukata!
Na shaida Annabi Muhammad s.a.w manzo
ALLAH, ALLAH Kayi salati da taslimi ka kara
aminci garesa, da iyalansa da sahabai da dukkan
wadanda suka biyo bayan shi da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Yan uwa musulmi masu albarka yau Khudbar
tamu zatayi magana ne kan wata dabi'a wadda
zamu iya cewa ta zama ruwan dare a rayuwar
mu, Wannan dabi'ar ita ce #SATA
Yan uwa musulmi ina maku wasiya na ni kaina da
muji tsoron ALLAH, Kamar yadda ALLAH Da
kansa ya umarce mu cewa "KUJI TSORON WANI
YINI DA ZA'A MAIDA KU GA ALLAH SANNAN
ZA'A SAKAWA KOWACE RAI DA ABUNDA TA
AIKATA KUMA BAZA'A ZALUNCE TA BA"
Su kudi ALLAH Madaukakin sarki ne ya saukar da
su daga sama dan amfanin mu, Dan mu gudanar
da rayuwar mu ta yau da kullum da kuma
gudanar da addini... ALLAH S.W.T Ya gargade
mu game da cin dukiya wadda ba tamu ba da
yake cewa "KADA KUCI KUDI KAN BARNA SAI
DA YARJEJENIYA (Cinikayya a tsakani)"
ALLAH S.W.T Cikin ikon sa ya hukunta cire
hannu ga duk wanda aka kama da laifin satar
dukiya, Kamar yadda yake cewa "BARAWO
NAMIJI DA BARAUNIYA KU YANKE HANNUWAN
SU"
Hatta wadanda ba musulmi basu aminta da
#SATA ba!!
Ko kudi ko wani abun amfani haramun ne satar
sa...
A farkon musulunci idan anzo yin mubayi'a ga
Manzo s.a.w daga cikin sharuddan yin mubayi'a
har da sai an barranta daga sata! kamar yadda
ALLAH Madaukakin sarki ke shaidawa cewa
"IDAN MUMINAI MATA SUKAZO WURINKA SUNA
SHAIDA MAKA CEWA SUNYI IMANI TO SAI SUN
BAR SHIRKA SUNBAR ZINA KUMA SUN BAR
KASHE YAYAN SU KUMA KADA SU SABA MAKA
GAME DA UMARNIN DAKA BASU"
Tun farko musulunci kenan, Ashe yana gwadama
mana illar #SATA kenan!!
A yanzu #SATA ta zama ba maza ba mata, Ba
yara ba tsoffin da matasa, An maida sata kamar
ibadah!!
A yanzu yan kasuwa na sata!
Ma'aikata na sata!
Kai lamarin ya kai har makabarta ma ba'a kyale
ba ana sata!
Ba makabarta ba kadai, Har massallaci sata, Inda
ake koyon imani, Kamar yadda aka sace mana
batir a nan massallacin!!
Har a asibiti ma ba'a tsira ba.
Ana sata ta hanyar bashi, Wato ka ranci kudin
mutun kuma kaki biya, A lokachi Manzo s.a.w ya
taba yanke hannun wata babbar mata saboda
idan taci bashi sai tace bata ci ba..
Idan muka diba hadisin Manzo s.a.w da yake
cewa "Karshen zamani mutun zai tara dukiya bai
damu da abunda ya tara ba na halal ko na
haram"
ABUBUWAN Dake kawo #SATA nada ta yawa
daga cikin akwai-
*Son dukiya da yawa yana kawo sata!
A yanzu #SATA har a sallar farilla ana sata,
Wata rana Manzo s.a.w ya fadawa sahabbai
cewa 'Barawon da yafi kowane barawo shine
barawo a sallah, Sai suka ce kamar yaya? Sai
Manzo s.a.w yace mai yin qotan kurciya'
*Ma'aikata suna sata, Idan ka saci kudin
Zamfara kamar ka saci kudin duk wani
bazamfare ne.
*Yan kasuwa suna sata, Masu tauye ma'auni
suna sata ne.
*Ma'aikatan lafiya, Gwamnati na biyam su amma
sai suna yan kauye suna karbar kudaden su.
*Wadanda ake ba bashi basu biya.
*Marar cika sallah, kamar yadda bayi ya gabata.
*Matar aure mai satar kudin mijinta ko bincikar
aljihu.
*Na tare da barayi, Wanda ake cewa kunci.
*Mai cin iyaka, Ta gona ko ta gida.
*Satar wutar lantarki.
*Direbobi masu cin amana.
*Satar ansar jarabawa.
Da sauran su...
Wallahi duk kudin da aka sata ALLAH Ya debe
masu albarka, Koda kuwa anyi aikin alkhairi da
kudin.
"SHI ALLAH MAI TSARKI NE BAYA KARBAR AIKI
SAI MAI TSARKI"
"ALLAH BAYA KARBAR SADAKA DA AKAYI DA
HARAM"
ALLAH SWT Ya haramta sata ne dan samar da
zama lafiya al'ummah,
Malamai sunce idan mutun ya saye kayam sata
kuma yasani to shima barawo ne!!
Yana da kyau iyaye su rika kwabawa yayan su
domin lura da tarbiyar su.
Saboda fargabar #SATA a yanzu ko massallaci
kazo kana shakka kada ayi maka sata, Duk da
nan ne fa wajen tsoron ALLAH.
KADAN Daga cikin illolin sata akwai-
>#SATA tana korar imani.
>#SATA tana sanya macewar zuciya.
#SATA aibi ce ga duniya da lahira, Domin tana
tasiri har ga yaya da jikoki.
>#SATA tana sa ALLAH Yabar karbar addu'a.
Yan uwa musulmi masu albarka mu tashi tsaye
mu tuba daga aikata #SATA
Duk abunda ka dauka ka maida shi zuwa ga
maishi, Idan bayanan ka kaiwa magadan sa, Idan
kuma babu su to ka sadakar da niyar ALLAH Ya
kai ladar garesa, Kuma ka yawaita istigfari!!
Yan uwa musulmi masu albarka mu yawaita yin
nafila domin ita nafila tana cika mana ayyuka
marar kyau da muke aikatawa.
Mu tuba tun kafin lokachin mu yakare, Domin
baya mantuwa kuma mai adalci ne ga bayi baki
daya.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 21-Safar-1439
Friday 10-November-2017