Friday, 8 December 2017

HUDUBA MAI TAKEN TSORATARWA GAME DA RASHIN BADA ZAKKAH

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE



A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #TSORATARWA GA
MASU HANA # ZAKKAH
Bayan mukaddima.....
Yan uwa musulmi masu albarka, A wancan
makon daya gaba munyi bayani game da
#ZAKKAH da hukunce hukunce ta.
To a wannan makon da ikon Allah zamu yi
magana akan tsoratarwar ga halayyar ga masu
hana #ZAKKAH
Yan uwan musulmi muji tsoron Allah gaskiyar jin
tsoron sa musani yana kallo duk abubuwan da
muke aikata a kullum.
Muhimancin #ZAKKAH ba karami bane a
musulunce har Allah yahada ta tare da sallah
wurare 32 a cikin alqur'ani mai tsari,
Babban dalilin wajabta #ZAKKAH shine nuna
godiya ga Allah, Da kuma sadar da umarnin
Allah.
#ZAKKAH tana kankare talauci a tsakanin
mutane, Bada #ZAKKAH tsarkakewa ne wato
tsarkake dukiya da kuma rayuwa baki daya.
Saboda matsayin Allah ya umurci Manzon Allah
s.a.w akan ya karbo #ZAKKAH "KA ANSO
#ZAKKAH DAGA GARESU DAN ZAMA
TSARKAKEWA GARESU"
Yan uwa musulmi masu albarka, Hakika fidda
#ZAKKAH wajibi ne a musulunci kuma dole ne,
Rashin fidda #ZAKKAH yana kawo fitononi da
musibu a cikin al'ummah baki daya. Allah ya
umarce mu da fiddawa da yake cewa "KU FIDDA
DAGA ABUNDA MUKA AZURTA KU DASHI"
Rashin bada #ZAKKAH yana jawo masibu da
bala'oi kala kala!!
Nana Aisha r.a ta ruwaito daga Manzo s.a.w
cewa "Babu dukiyar da za'a tara ba'a fitar mata
da #ZAKKAH sai Allah tarwatsa ta"
Yan uwa musulmi masu albarka muna ganin
musibu da ake samu na gobara da masibu kala
kala, Hakika wannan duk daga hana #ZAKKAH
ne!
Rashin bada #ZAKKAH na kawo debe albarka ga
noma da kudi, Idan muka diba zamu ga yadda
anan garin aka noma shinkafa da farko tayi kyau
amma daga karshe wasu sun fadi warwas!
Duk fa wannan daga rashin bada #ZAKKAH da
muke yi, Manzo s.a.w na cewa "Mutane bazasu
hana #ZAKKAH ba face sai Allah ya debe
albarka ga abun su"
Hakika tsoratarwa mai karfi tazo akan masu qin
fidda #ZAKKAH har ma wani wuri a Qur'ani da
mushrikai.
Sau da yawa zakaga wami yasamu kudi da suka
kai nisabi, Ko kuma yayi noma yasamu albarka
amma sai ya rike #ZAKKAH ko kuma yabada ga
wanda yaga dama ko kuma badawa a lokachin da
yaso maimakon lokachin da yasamu.
Duk wanda yabada #ZAKKAH yadda yaga dama
malamai sunce kamar bai bada wato dashi da
wanda bai bada duk daya.
Rashin bada #ZAKKAH yana kawo musibu, Ita
kuma musiba munsan tana shafuwar har wanda
baiji ba bai gani ba, Wata qila ma tana iya wuce
wanda ya hana #ZAKKAHR Ta fada wani shi
kuma a kyale sa sai ranar kiyama!
Yan uwa musulmi masu albarka, Idan akwai
abokin ka ko dan uwanka ko wani makusancin ka
yake hana #ZAKKAH to kayi masa nasiha tare da
gargadi.
ALLAH Fa yayi mana babban gargadi (Serious
warning) game da hana #ZAKKAH
*BANI YA TABBATA MARAR BADA #ZAKKAH SU
(masu hana zakkah) MUSHRIKAI GA KIYAMA"
*MASU TARA DUKIYA #ZAKKAH DA SANMU
ZA'A JEFA SU A WUTAR JAHANNANAMA TANA
SUYA SU"
*"MASU TARA DUKIYA BASU BADA #ZAKKAH
KUMA BABU ABUNDA YASAMI DUKIYAR
WALLAHI YABAR MURNA DOMIN BALA'I CE
GARESA"
Manzo s.a.w ya fassara wannan ayar da cewa
"Allah zah maida dukiyar maciji mai baki biyu
yana saransa a wutar jahanama yana cewa 'Nine
dukiyar ka da ka hana #ZAKKAH' "
Yan uwa musulmi masu albarka Allah shirewa
duk dukiyar da aka hana #ZAKKAH albarka,
Idan muka diba matsalar tsaro da sauran
abubuwan da suka dame mu duk suna da alaqa
da kaucewa umarnin Allah.
Bayan wafatin Manzo s.a.w wasu sunce sunce
'Sun daina bada #ZAKKAH saboda Manzo s.a.w
ya rassu, Khalifan Manzo s.a.w ya yake su har
garuruwan su ya bisu ya karbo #ZAKKAH
Aliyu bn abi Thalib khalifan Manzo s.a.w ya hudu
yace 'ALLAH Baya dauke musiba sai an tuba!
Allah madaukakin sarki na cewa "DUK ABUNDA
YASAME KU TO DAGA ABUNDA KUKE
AIKATAWA NE"
Hakika ALLAH Yabamu labarin mutane da yawa
wadanda yayi wa ni'ima suka kafurce!
ALLAH Yana fada mana cikin suratul nahal cewa
"ALLAH YABUGA MISALI WATA ALKARYA DATA
KAFURCE"
Sai mu diba muga yanzu wace ni'imah ce Allah
baiyi mana ba??
Munsan labarin wani da ake kira Saba'a yadda
suka kafurce daga karshe ALLAH Kwace ni'imar
daga garesu.
Lallai ne kuma dole ne mu sadar da umarnin
ALLAH Dan samun falala da rahama wata bata
yankewa daga garesa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzo
s.a.w da iyalansa da sahabban sa dukkan
wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Ya Allah ka biya mana bukatun mu kayi rahama
garemu ka gafarta mana yaye mana damuwa, Ya
Allah kara albarka ga dukiyar da ake bada
#ZAKKAH ya Allah ka tarwatsa duk dukiyar da
ake hana #ZAKKAH


©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 28-Safar-1439
Friday 17-November-2017

No comments: