Friday, 8 December 2017

HUDUBAH MAI TAKEN BIDI'AH

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #BIDI 'AH DA
HUKUNCIN TA A MUSLUNCHI
Bayan mukaddimah...
Yan uwa musulmi a yau Khudbar tamu zata yi
magana ne game da #BIDI'AH da kuma hukuncin
ta a musulunce!!
Yan uwa musulmi muji tsoron ALLAH Gaskiyar jin
tsoron sa, Mu sani cewa da tsoron ALLAH
Rayuwa ke gudana .
Babbar ni'imah garemu ita ce musulunci domin
musulunci shine hanya daya rak dake sada dan
Adam da ubangiji ALLAH , ALLAH Yabamu
rayuwa (Musulunci) kamar yadda ya labarta
mana cewa "YANZU WANDA YA KASANCE
MATACCE (JAHILI) ZAI YI DAI DAI DA MAI RAI
(MAI ILMI)"
Hakika akwai abubuwa wadanda ke ruguza addini
da dama,Babba Daga ciki shine bidi'ah!
Ita bakwai ne kawo ita bidi'ar,
1-Son rai, Shi son rai shine babban jagora ga
qago bidi'ah a cikin addini, ALLAH Madaukakin
sarki kuma ya gargadi masu son da yake cewa
"BABU WANDA YAFI KOWA ZAMA BATACCE SAI
WANDA KE BIN SON RAI".
2-JAHILCI, Tabbas jahilci ya taka gagarumar
rawa a wajen qago bidi'ah a cikin musulunci,
ALLAH Madaukakin sarki na cewa "MAFI YAWAN
MUTANEN DUNIYA JAHILAI NE"
3-Kau da kai daga karbar gaskiya, Tabbas kauda
kai daga karbar gaskiya yana matukar kai dan
Adam ga kirkiro bidi'ah, Ita kau gaskiya duk
wanda ya karbe ta baya tabewa kamar yadda
madaukakin sarki ke cewa "DUK WANDA
SHARI'A TA BAYA TABEWA DUK WANDA YABI
SON RANSA ZA'A TABAR DASHI KUMA ZA'A
TADA SHI MAKAHO"
4-Nisantar masu ilmi, Tabbas nisantar masu ilmi
na fadin gaskiya da kuma takama da jahilci na
kawo kago bidi'ah a addini, Duk abunda mutun
bai sani yakamata yayi ya tambaya amma sai ya
kiya, ALLAH Kuma na cewa "KU TAMBAYI
MA'ABOTA ILMI IDAN BAKU SANI BA"
5- Jiji da kah da son ra'ayi, Hakika ji da kai yana
kawo mutun ya fadawa bidi'a ko kuma ya kirkiro
ta,
6-Son duniya, Tabbas masu mugun son duniya
suna kirkirar bidi'ah su kawo ta a musulunci,
ALLAH Kuma na cewa "SUN ZABI DUNIYA A
BISA LAHIRA " Wani wuri kuma yana cewa "SUN
ZABI RAYUWAR DUNIYA BISA GA TA LAHIRA"
Abubuwa biyu ne bidi'ah take...
1-Bidi'ah ta magana wadanda suke magana ta
izgili da sunan addini kamar mu'utazilawa da yan
Shi'ah.
2-Bidi'ah ta aiki, Kamar bautawa ALLAH Da
shari'ar da bai umarta ba, Ko kuma kari a cikin
ibadah, Misali wani yace maka 'Assalamu
Alaikum' to sai kaji wurin ansawa ance 'Ameen
'Wa alaikum salam anan cewa Ameen bidi'ah duk
da kalmar amin kalma ce mai kyau amma dai
sunnah bata karantar da haka ba, Akwai kara
wani abu wajen yin sallah da sauran su.
Manzo s.a.w ya koyar damu yadda ake yin Zikirai
kowane iri ya koyar damu na safe na rana na
yammah na dare dana komai,
Sannan akwai bidi'ar kebance wani lokachi
wanda shari'ah bata kebe ba dan yin ibadah,
Wannan baya cikin tsarin musulunci.
Hukuncin #BIDI'AH shine tana rushe aiki baki
daya.
Manzo s.a.w na cewa "Mafi sharrin ayyuka shine
kirkiro wani abu cikin addini"
Wata rana Umar bn Abdul'aziz r.a ya fito sai yaga
wani tsoho mai gudun duniya mai tsoron ALLAH
Ya yawaita ibadah amma kirista ne!!
Dan haka sai ya koma gida yayi ta kuka da aka
tambaye shi miye dalilin kukansa sai yace ganin
wannan ya tuna mashi da ayar nan dake cewa
"RANAR DA ZA'A
KIFE FUSKAM SU A CIKIN WUTA"
Ita #BIDI'AH tana kawo kasala ga aikata Sunnah!
Imam hasanul busary na cewa 'ALLAH Baya
karbar ibadun mai bidi'ah sai almajiransa suka ce
saboda mi? sai yace yana da hujja daga hadisin
dake cewa "ALLAH Ya tsinewa mai yin bidi'ah"
Muna rokon ALLAH Ya gafarta mana yayi mana
rahama, Ya karemu daga aikata bidi'ah yayi
rahama garemuda iyayen mu, Ya biya bukatun
mu.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 12-Rabi'ul auwal-1439
Friday 01-December-2017

No comments: