Friday, 8 December 2017

HUDUBA MAI TAKEN HARAMCIN SATA A MUSULUNCI

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #SATA
Godiya ta tabbata ga ALLAH S.W.T Wanda yayi
halitta ya kuma dai dai ta halittar kamar yadda
yake bukata!
Na shaida Annabi Muhammad s.a.w manzo
ALLAH, ALLAH Kayi salati da taslimi ka kara
aminci garesa, da iyalansa da sahabai da dukkan
wadanda suka biyo bayan shi da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Yan uwa musulmi masu albarka yau Khudbar
tamu zatayi magana ne kan wata dabi'a wadda
zamu iya cewa ta zama ruwan dare a rayuwar
mu, Wannan dabi'ar ita ce #SATA
Yan uwa musulmi ina maku wasiya na ni kaina da
muji tsoron ALLAH, Kamar yadda ALLAH Da
kansa ya umarce mu cewa "KUJI TSORON WANI
YINI DA ZA'A MAIDA KU GA ALLAH SANNAN
ZA'A SAKAWA KOWACE RAI DA ABUNDA TA
AIKATA KUMA BAZA'A ZALUNCE TA BA"
Su kudi ALLAH Madaukakin sarki ne ya saukar da
su daga sama dan amfanin mu, Dan mu gudanar
da rayuwar mu ta yau da kullum da kuma
gudanar da addini... ALLAH S.W.T Ya gargade
mu game da cin dukiya wadda ba tamu ba da
yake cewa "KADA KUCI KUDI KAN BARNA SAI
DA YARJEJENIYA (Cinikayya a tsakani)"
ALLAH S.W.T Cikin ikon sa ya hukunta cire
hannu ga duk wanda aka kama da laifin satar
dukiya, Kamar yadda yake cewa "BARAWO
NAMIJI DA BARAUNIYA KU YANKE HANNUWAN
SU"
Hatta wadanda ba musulmi basu aminta da
#SATA ba!!
Ko kudi ko wani abun amfani haramun ne satar
sa...
A farkon musulunci idan anzo yin mubayi'a ga
Manzo s.a.w daga cikin sharuddan yin mubayi'a
har da sai an barranta daga sata! kamar yadda
ALLAH Madaukakin sarki ke shaidawa cewa
"IDAN MUMINAI MATA SUKAZO WURINKA SUNA
SHAIDA MAKA CEWA SUNYI IMANI TO SAI SUN
BAR SHIRKA SUNBAR ZINA KUMA SUN BAR
KASHE YAYAN SU KUMA KADA SU SABA MAKA
GAME DA UMARNIN DAKA BASU"
Tun farko musulunci kenan, Ashe yana gwadama
mana illar #SATA kenan!!
A yanzu #SATA ta zama ba maza ba mata, Ba
yara ba tsoffin da matasa, An maida sata kamar
ibadah!!
A yanzu yan kasuwa na sata!
Ma'aikata na sata!
Kai lamarin ya kai har makabarta ma ba'a kyale
ba ana sata!
Ba makabarta ba kadai, Har massallaci sata, Inda
ake koyon imani, Kamar yadda aka sace mana
batir a nan massallacin!!
Har a asibiti ma ba'a tsira ba.
Ana sata ta hanyar bashi, Wato ka ranci kudin
mutun kuma kaki biya, A lokachi Manzo s.a.w ya
taba yanke hannun wata babbar mata saboda
idan taci bashi sai tace bata ci ba..
Idan muka diba hadisin Manzo s.a.w da yake
cewa "Karshen zamani mutun zai tara dukiya bai
damu da abunda ya tara ba na halal ko na
haram"
ABUBUWAN Dake kawo #SATA nada ta yawa
daga cikin akwai-
*Son dukiya da yawa yana kawo sata!
A yanzu #SATA har a sallar farilla ana sata,
Wata rana Manzo s.a.w ya fadawa sahabbai
cewa 'Barawon da yafi kowane barawo shine
barawo a sallah, Sai suka ce kamar yaya? Sai
Manzo s.a.w yace mai yin qotan kurciya'
*Ma'aikata suna sata, Idan ka saci kudin
Zamfara kamar ka saci kudin duk wani
bazamfare ne.
*Yan kasuwa suna sata, Masu tauye ma'auni
suna sata ne.
*Ma'aikatan lafiya, Gwamnati na biyam su amma
sai suna yan kauye suna karbar kudaden su.
*Wadanda ake ba bashi basu biya.
*Marar cika sallah, kamar yadda bayi ya gabata.
*Matar aure mai satar kudin mijinta ko bincikar
aljihu.
*Na tare da barayi, Wanda ake cewa kunci.
*Mai cin iyaka, Ta gona ko ta gida.
*Satar wutar lantarki.
*Direbobi masu cin amana.
*Satar ansar jarabawa.
Da sauran su...
Wallahi duk kudin da aka sata ALLAH Ya debe
masu albarka, Koda kuwa anyi aikin alkhairi da
kudin.
"SHI ALLAH MAI TSARKI NE BAYA KARBAR AIKI
SAI MAI TSARKI"
"ALLAH BAYA KARBAR SADAKA DA AKAYI DA
HARAM"
ALLAH SWT Ya haramta sata ne dan samar da
zama lafiya al'ummah,
Malamai sunce idan mutun ya saye kayam sata
kuma yasani to shima barawo ne!!
Yana da kyau iyaye su rika kwabawa yayan su
domin lura da tarbiyar su.
Saboda fargabar #SATA a yanzu ko massallaci
kazo kana shakka kada ayi maka sata, Duk da
nan ne fa wajen tsoron ALLAH.
KADAN Daga cikin illolin sata akwai-
>#SATA tana korar imani.
>#SATA tana sanya macewar zuciya.
#SATA aibi ce ga duniya da lahira, Domin tana
tasiri har ga yaya da jikoki.
>#SATA tana sa ALLAH Yabar karbar addu'a.
Yan uwa musulmi masu albarka mu tashi tsaye
mu tuba daga aikata #SATA
Duk abunda ka dauka ka maida shi zuwa ga
maishi, Idan bayanan ka kaiwa magadan sa, Idan
kuma babu su to ka sadakar da niyar ALLAH Ya
kai ladar garesa, Kuma ka yawaita istigfari!!
Yan uwa musulmi masu albarka mu yawaita yin
nafila domin ita nafila tana cika mana ayyuka
marar kyau da muke aikatawa.
Mu tuba tun kafin lokachin mu yakare, Domin
baya mantuwa kuma mai adalci ne ga bayi baki
daya.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 21-Safar-1439
Friday 10-November-2017

No comments: