FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #LOKACHIN_HUNTURU
Bayan mukkaddimah........
Yan uwa musulmi masu albarka a yau Khudbar mu zatayi magana ne game da halin da muke ciki, Watau yanayi na hunturu da sanyi da kadawar iska.
Idan muka diba lokachin da muka fito na baya zamu ga cewa lallai yanayi yayi matukar chanzawa, Hakika yan uwa musulmi chanzawar lokachi wani sababi ne ga mai imani da zai kara masa imani, Da kara maida kai ga ALLAH Da jajircewa ga biyar sa!
ALLAH Madaukakin sarki cikin hikimar sa da yarda sa yana shata mana zuwan wannan lokachin duk shekara.
Ibn kaiyumul jauzi yana cewa 'Idan aka lura da yadda ALLAH juya lokutta zamu fahimci cewa akwai wata maslaha dake cikin yin hakan'
Idan da yaso sai ya barmu da lokachi daya ko zafi kawai ko sanyi kawai ko kuma ruwan sama kawai!
Yan uwa musulmi masu albarka ina maku wasiya dani da ku da muji tsoron ALLAH, Hakika da tsoron ALLAH Ne zukata ke kamuwa da natsuwa kuma ake fahimta ayoyi da manufofin ubangiji.
ALLAH Madaukakin sarki na cewa "SUNE (Masu imani) MASU DIBA YADDA MUKE JUYA AKAN LAMURA HAKIKA SUN SAMU IMANI KUMA SUNE MASU AMBATON ALLAH BA DARE BA RANA "
Hakama ALLAH S.W.T Na cewa "LALLAH JUYAWAR DARE DA YINI AYAH CE GA MASU IMANI"
Shi wannan lokachin na sanyi ALLAH Madaukakin sarki ne ya kaddaro shi da haka, Domin wuta ce keyin lumfashi!!
Ga hadisi daga Manzo s.a.w "Wata rana wuta takai kara ga ALLAH S.W.T Cewa wani sashen ta yana cin sashen ta sai ALLAH Yabata dama cewa ta rika numfashi wato taja iska (shine muke samun lokachin sanyi) sannan ta saki numfashi (shine lokachin zahi)"
Iman hasanul busariy na cewa 'ALLAH Ya tanadar da wannan lokutta ne dan tunatar damu game da kiyama, Domin idan nukaji sanyi yayi yawa sai mu tuna cewa sanyin azaba da kiyama yafi na duniya, Hakama zafi na duniya bai kai zahin kiyama ba"
Abdullahi dan Mas'ud r.a ya kasance idan sanyi yazo yana cewa 'Maraba da zuwan sanyi maraba da zuwan sanyi idan aka tambaye shi miye dalilin shi na fadar haka sai yace 'Lokachin sanyi lokachi ne da dare keda tsawo (Ana samun damar yin ibadah da kusantar ALLAH) Rana kuma batada tsawo ana yawaita azumi'
Yan uwa musulmi masu albarka lokachin hunturu yana da HUKUNCE HUKUNCEN sa..
*Yin alwala da kyau-Yazama wajibi mu kiyaye yadda muke alwala a lokachin sanyi, Domin muna sanya manya kaya kuma wajen alwala zakaga wasu saboda kaya masu nauyi basu yin alwala da kyau.
Manzo s.a.w "Yaga wasu na alwala amma basu shafawa yadda yakama sai Manzo s.a.w yace 'Boni ya tabbata ga masu alwala basu cikawa ' "
Babu laifi saboda sanyi ayi alwala da ruwan zafi wajen yin alwala.
*Ana son tuna saukin da shari'ah ta kawo mana, Ya halatta shafa sama safa ko takalma ko huffi, Idan har anyi alwala kafin a sanya safar ko takalman.
Mugira ya ruwaito hadisi kuma an ruwaito shi a sunnanin dauda cewa "Manzo s.a.w yana shafa saman khuffi amma idan yayi alwala,
Hakama wata rana Manzo s.a.w zai yi alwala sai Mugira yazo zai cire masa takalma sai Manzo s.a.w yace kabarshi domin nayi alwala kafin insa!
Larabawa na cewa lokachin sanyi namiji zahi kuma macce, Saboda yanayin karfin su ba daya ba.
A zamanin khalifan Manzo s.a.w na biyu wato Umar bn Khattab r.a yana kewa yawa cikin gari yana cewa 'Sanyi yazo sanyi makiyin mu ne dan haka mu tanadi kayan kariya kamar manya barguna da sauran kayan kariya daga sanyi'
Yaku yan uwa musulmi masu albarka, Hakika Umar r.a ya kasance yana taimakon marar sa galihu da kayan rufe jiki dan kariya daga sanyi.
Anan muna kira ga yan uwa musulmi da mu taimaki yan uwa marayu da makwabta da sauran mara sa galihu, Da kuma kula da iyali da kananan yara a tanadar masu kayan sanya kada mu barsu kamar dabbobi domin zai iya yin illah garesu.
*Yawaita bautar ALLAH, Hunturu lokachi da dan Adam ke samun lafiya da walwala da kebantuwa daga mutane, Domin ko doguwar hirar da ake yi ragewa ake yi, Zaka fito karfe goma ka tarar babu kowa,
Dan haka sai muyi amfani da wanoan lokachin wajen bautar ALLAH ba yawan bacci ba.
*Mu rika cika alwala, Manzo s.a.w na cewa "Cika alwala ne mafi so a yanzu (Lokachin hunturu).
*Dumama jiki dan samun sauki, Sai dai yana da kyau musulmi ayi hattara sosai, Domin kada mu ajiye wuta ta rika kwana a dakunan mu.
Abul musa al'ashry ya ruwaito cewa "Wata rana ayi gobara a Madinah sai aka fadawa Manzo s.a.w sai yace 'Wannan wutar makiyar muce mu daina aje ta a dakunan mu'!!
Dan haka da zarar zamu kwanta sai mu kashe wuta a fito da ita waje,
Yan uwa musulmi mu taimaki yan uwa marar sa galihu, Mu taimaki marar kayan sanyawa.
Lallai ALLAH Na taimakon bawa, Matukar yana taimakon yan uwansa.
ALLAH Ka taimakemu da taimaka, Ka karemu da kariyar ka.
Ya ALLAH Ka biya mana bukatun mu na alkahri ka kiyaye mu kuma ka tsare mu.
Ya ubangiji kayi rahama garemu da iyayen mu.
Ya ubangiji ka zaunar damu lafiya, Ka albarka ci garin mu.
©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 19-Rabi'ul auwal-1439
Friday 18-December-2017 AB
No comments:
Post a Comment