Saturday, 14 January 2017

WANDON MUMINI RABIN KWABRI NE.

🎤🎤🎤🎤🎤🎤🎤
*NASIHARMU TA YAU DAGA GROUP DIN MUKYAUTATA NIYYA!!!*
🎙🎙🎙🎙🎙🎙🎙

*WANDON MUMINI RABIN KWABRI NE!!!*

```Hadissai masu tarin yawa sun tabbata daga Manzon Allah s.a.w dangane da dangale tufafi ga maza. Zamu kawo kadan daga cikinsu domin fadakar da Al'umma.```
*عن ابن عمر رضى الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: "من جر ثوبه خيلاء لم ينظر الله يوم القيامة(متفق عليه)*

*_Daga ibn umar (Allah ya yadda dasu) manzon Allah s.a.w yace; duk Wanda ya saki tufafinsa yana jansu a kasa saboda German kai! Allah bazai kalleshi ba a ranar gobe kiyama._*

*وعن أبي هريرة رضى الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ما أسفل من الكعبين من الإزار ففي النار. (رواه البخاري)*

```Daga Abi hurairah(R.A) daga Annabi Muhammad s.a.w yace sashen tufafin da aka saki ya wuce idon sawu to zai shiga wuta. Har ila yau akwai wani hadisin Na Abi hurairah(R.A) yace: manzon Allah (s.a.w) yace;...Allah (s.w.t) ba ya amsar sallar mutumin da ya saki tufafinsa kasa.```

*Saboda haka duk Wanda ya karyata wadannan hadissan ko kuma yayi izgili ga masu dage tufafinsu, Dan fodio yace kafiri ne! Kuma wallahi yana da hujja. Shi kuwa imam Ahmad bin hambal(imamu Ahlus Sunnah waljama'ah) cewa yayi;*
*من رد حديث رسول الله صلى الله عليه وسلم فهو شفا هلكة*
*wato duk Wanda kaga yana Raddi ga hadissan Manzon Allah s.a.w! Toh yana gefen halaka.*

```Saboda haka yan uwa yan dariku kuyi hattara da izgilanci ga hadissan Manzon Allah s. a.w.

Manzon Allah s.a.w yayi bayani yadda ya kamata musulmi ya sanya tufafinsa inda yace; Tufafin musulmi wando ko Riga ya tsaya tsakanin kwabrinsa na kafa ko kuma tsakanin idon sawu da gwiwar kabrinsa na kafa. Ko kuma yace "can kasan idon sawu an kaddara mashi shiga wuta. Wani wurin yace; Allah bazai kalli mutumin da ya saki tufafinsa ba don German kai.

Wadannan hadissai na sama sunyi nuni a fili cewa irin dinkin da samari keyi a wannan zamani Wanda rigarsu ko wandonsu ya wuce idon sawu, musulunci ya haramta irin wannan dinkin.! Har ma idan Anyi sallah da irinshi sallar mutum Rana da rauni, saboda haka yana da matukar muhimmanci muyi kokarin gyarawa don mu samu Rahamar ubangiji.```

*_Abdullahi bn umar(R.A) yace; wata rana na wuce gaban  Manzon Allah s.a.w Alhali tufafi na suna reto(Jan kasa) sai Manzon Allah s.a.w yace" Abdullahi ka ja tufafinka sama! Sai na ja tufar sama kadan. Sai Manzon Allah s.a.w yace; ka kara jawo tufar ka sama kadan! Sai na kara Jan tufar sama kadan. Abdullahi bn umar yace tun daga Ranar na rinka sanya tufafi sama. Wani daga cikin kabilarsa(Abdullahi) ya tambayeshi sama kamar ya? Sai nace tsakanin idon sawu da gwiwar kafa. Saboda haka duk Wanda keson muwafaka da sunnah shine wando ko Rigarsa kada su wuce idon sawu._*

*Allah muke roko ya tabbatar damu akan sunnar Annabi Muhammad s.a.w*

Ga masu bukatar shiga group din *MUKYAUTATA NIYYA*  kai tsaye zasu iya danna wannan link dake kasa domin shiga, sai dai duk Wanda ya karya dokar group, Admins zasuyi waje dashi.
https://chat.whatsapp.com/2dm86OqUUNB69euFNsdOjM

Allah ya bada ikon kiyayewa.


Copyright©
```Hashim Surajo Uba Tsamiya
08064734911```

Monday, 2 January 2017

YADDA AKE WANKAN TSARKI

YADDA AKE WANKAN
TSARKI

Matashiya: Bayanda bayanai suka gabata akan
abubuwan da suke wajabta wanka, ayanzu za
mu kawo bayani akan yadda ake gabatar da
waken da izinin Allah.
Da farko dai mu sani shi wannan wanka
amanace daga cikin tarin amanar dake tsakanin
bawa da mahaliccinsa, saboda haka ya zama
wajibi ka kiyaye wannan amanar, kuma ka
himmatu da sanin hukunce hukuncen wannan
wanka, domin ka gabatar da shi a yadda
musulunci ya tsara, abinda ya rikice maka sai
ka yi tambaya, kada kace wai kunya zata
hanaka, jin kunya a irin wadannan al'amurra
abune da musulunci bai yarda da shiba, kuma
wani nau'ne na tsoro da shaidan yake tsoratar
da mutane da shi, kuma ya sanyawa mutum
kasalar da ba zai iya gudanar da cikakken
addiniba. Al'amarin hukunce-hukuncen tsarki
al'amarine mai girman gaske, sakaci a cikin
wannan lamari yana da matukar hadari, domin
kada ka manta hukunce-hukunce sallah ya
ratayune fa da tsarki wacce kuma sallar nan
itace ginshikin addini.
Farillan Wanka: Ka/Ki sani shi wankan tsarki
yana da farillai da kuma sunnoni dama
mustahabbai, amfanin saninsu shine domin duk
abinda yake farillane sai baka yi shi to wankan
bai yiba, amma idan sunnah ka bari wankan ya
yi saidai ka rage lada. Su farillan guda biyarne;
(1) Niyya: Abinda ake nufi shine ka kudurce a
zuciyarka/ki yanzu hakannan wankan janaba
zaka yi ko zaki yi, ko kuma na daukewar al'ada
ko biki…', wannan itace niyya, ba wadansu
abubuwa ake karantawaba, niyya kuma tana da
matukar muhimmanci, ai kaga shi yasa ta zo a
farko.
(2) Game Jiki Da Ruwa: Ana so ka tabbatar ko
ina a jikinka ya sami ruwa, kada ka manta da
dukkan mahadar gaba.
(3) Cuccudawa: Ka tabbata ka cuccuda ka
gurza ko ina da gwargwadon hali, kada ka
manta da kasan hammata da dukkan matse-
matsi…'.
(4) Tsefe Gashi: Ka tabbata ruwa ya shiga ko
ina a cikin gashin kanka ko kanki, Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
yana cewa: ''Karkashi ko wanne gashi akwai
janaba, ku wanke gashi, ku kuma tsaftace jiki'' .
Abudaud, 248, Tirmizi: 106, Ibnu Maja: 597.
(5) Yi Lokaci Guda: Wannan shi ake nufi
'Muwalat' ma'ana idan ka fara to kada wani abu
ya katseka sai ka kammala.
Wadannan sune farillai ka tabbata sun cika a
duk lokacin da kake wanka, kada ka manta shi
wankan tsarki anayin shine da ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa ken an banda mai sabulu. Ka
samu idan kana da janaba kuma kanason ka yi
wankan tsarki da kuma wankan zuwa wurin aiki
ko kasuwa da sauransu, sai ka fara gabatar da
wankan tsarki tukunna, idan ka gama sai ka sa
sabulu ka ci gaba da wankanka.
Siiffar Wankan Janaba: Da farko za ka yi niyya
a zuciyarka (kamar yadda bayani ya gabata).
Sannan ka ce: Bismillah , sai ka wanke
hannayanka biyu sau uku, sai kuma ka wanke
gabanta (al'aura), hannun dama na zuba ruwa
na hagu yana wankewa, sannan sai ka goge
hannun naka a bango, sai ka gabatar da
cikakkiyar alwala, sannan sai ka kamfaci ruwa
ka zuba a kanka domin ka kosar da gashin
kanka zaka yi hakanne sau uku. Sannan sai ka
dibi ruwa ka kwarara a jikinka kana cuccudawa
domin rowan ya kai ko ina, Shikenan ka gama.
Kana da dama ka wuce zuwa sallah kai tsaye
batare da ka yi alwalaba, sai dai idan wani abu
cikin abubuwan da suke karya alwala ya faru.
Kada ka manta koda kana cikin wanka
alwalarka ta karye wankanka nanan ba abinda
ya sameshi, sai idan kana so ka yi sallah to sai
ka yi alwala.
Banbanci Janaba Da Al'ada: Anan ana so ki
gane wankan janaba da wankan daukewar jinin
al'ada ko biki duk iri dayane, inda suka
banbanta kadanne. Wuri na farko: Niyya, domin
da ita ake banbace ibada da ibada kamar
wannan da muke Magana kai. A wankan janaba
mace ba sai ta kwance kitson ta ba domin
hakan zai zama akwai wahalarwa sai ya wajaba
ta tabbata ruwa ya shiga asalin tushan gashin
kai, amma a wankan daukewar al'ada ko na biki
ya halatta ta kwance kitson dake kanata, amma
ba wajibi bane, a dai tabbata ruwa ya shiga ko
ina wannan kuma ya shafi maza kamar yadda
ya shafi mata, akwai maza masu yawan gemu
da suma to dolene a tabbata ruwa ya kai ga
asalin tushan gashi, a cuccuda ko ina da ina,
idan mutum yana sanye da zobe ya tabbata
ruwa ya shiga karkashin zoben, akyautata
wanka a kuma karanta ruwa. Allah ya sa mu
dace.
Idan mace al'adarta ta dauke kuma ga
wankan janaba akanta, to wanka guda za ta yi
sai ta gwama niyyar kamar yadda wadansu
malamai suka fada, domin wankan janaba dana
al'ada duka wajibine kuma komai nasu
dayane…'.
Idan mutum yana da janaba kuma ga wankan
juma'a, to anan ya samu ya shgar da wankan
juma'a cikin na janaba, ba wai ya shigar da na
janaba cikin na juma'aba, domin na janaba
wajine, amma na juma'a ba wajibibane a mafi
yawan maganganun malamai.
Idan ka yi wankan janaba sai kuma ka manta
baka yi alwalaba wankanka ya yi, kuma ka
samu ka yi sallah ko da baka yi alwalaba
muddin ba wani abun da ke karya alwala da ya
faru, domin alwalar ta shiga wanka duk inda
zaka wanke a alwala ka wanke shi a wanka,
kuma kamar yadda alwala take wajibi kafin
sallah haka wanka yake wajibi ga mai janaba.
Amma idan mutum ya yi wankan juma'a to
sai ya yi alwala kafin sallah.
Ya hallata miji da mata su yi wankan janaba
tare, kamar yadda aka ruwaito daga daya daga
matan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi- yana yi.
Ka samu ka jinkirta wanka amma sai ka yi
alwala domin alwalar na rage kaifin janaba,
kuma tana kara kuzari idan za'a sake saduwa.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka
gabata ya bayyana a fili yadda addinin
musulunci ya kula da tsarkaka da kuma lafiya,
domin janaba bakaramin al'amari bace, saboda
haka aka shar'anta wanka, kuma aka kawo
siffar wankan daki-daki domin ka fahimci a
musulunci ba'a yin abu da ka, fatammu shine
Allah ya karba mana kurakurai kuma ya gafarta
mana, amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.

TAIMAMA DA HUKUNCE- HUKUNCENTA

TAIMAMA DA HUKUNCE-
HUKUNCENTA

Matashiya: Hakika Allah mai girma da daukaka
ya shar'anta tsarkaka daga hadasin da yake
karami ko babba kafin gabatar da sallah,
wannan tsarkaka kuma bata yiwa sai da ruwa
mai tsarki mai tsarkakewa, gabatar da wannan
tsarki da kuma rowan da aka ambata shine
abinda yake wajibi muddin akwai dama, sai dai
akan sami wasu lokuta da ake rasa rowan
kwatakwata ko kuma ga ruwan amma idan aka
yi alwala da shi ko wanka za'a rasa wanda za'a
sha, koma yin anfani da rowan zai haifar da
wasu cututtuka da dai sauran wasu dalilai
shar'antattu da zasu hana amfani da ruwan to
akan haka aka shar'anta Taimama domin
sawwakewa al'umma, da kuma dauke dukkan
wata damuwa akan hakan.
Mecece Taimama?: Taimama itace; Shafar
fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi
kebantacce.
Kenan ba kowacce shafar fuska da hannu ne
yake zama taimama ba, sannan kuma ba a
kowanne wuri ake yi ba, sannan ba yadda aka
ga dama ake yi ba.
Tabbatuwar Taimama: Taimama ta tabbata
daga haske na Alkur'ani da kuma Hadisan
ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allan su
tabbata a gareshi- kana da ijima'in malamai.
Tabbatuwarta A Kur'ani : Allah ya yi bayanini
shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai
girma a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma
Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu
kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato
aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki yana
cewa:
''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani! Idan
kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku
da kuma hannayanku zuwa gwiwar hannu, ku
kuma shafi kawunanku kuma ku (wanke)
kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance
masu janaba to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan
kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan
tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan
gida, ko kuma kun taba mata (janaba) baku sami
ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki
sai ku sahfi fuskokinku da kuma hannayanku
daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun
kunci ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku
kuma domin ya cika ni'imarsa a gareku domin ku
gode masa. (Ma'idah, aya ta:6).
Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi
hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake
karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan
tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi
taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da
manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar,
Allah muna gode maka, akan wannan ni'ima.
Tabbatuwar Taimama A Hadisi : Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare
shi- yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba
wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana
sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira
tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta
zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani
mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to
ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda
yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''.
Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521.
Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin
ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan
al'ummar gatan da bai yiwa wata al'ummaba, a
ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta
zama wurin sallah, al'ummomi da suka gabata
basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu,
amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka
kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an
sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi
tsarki da ita kamar yadda bayanai suka gabata
a baya akan istijmari, sannan kuma zaka yi
taimama da ita kamar yadda ake kawo bayani a
yanzu haka.
Taimama matsayine na musamman da wannan
al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya
taimama ga wata al'ummaba kafin wannan
al'ummar domin yalwatawa ga wannan
al'ummar.
I jima'i: Malamai duk sun yi ijima'i akan
tabbatuwar taimama.
Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a
shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan
abinda kasan ba'a yi said a ruwa to ana yi da
taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani
da dai sauransu.
Taimama Tana Tsayawa Matsayin A Lokuta
Kamar: Kenan anan za'a lissafo abubuwan da
suke sawa a yi taimama, domin kada kabar
sallah ta wuce maka kace ai baka sami ruwa
bane wannan ba zai sa ka sami sassauci ba
domin sabo da hakan aka shar'anta taimama,
wadannan wurare sune kamar haka:
1. Rashin Ruwa: Kasan cewa suna cikin tafiya
ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun
nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba,
to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su
bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai
su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a
cikin su akwai masu janaba, ko matan da
al'adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar
da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko
da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi
addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane
shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da
sauki a gareka.
2. Ruwan Ba Zai Isaba: Idan kuma a tare da ku
akwai ruwan amma kuna da matukar mukata
domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi
za ku ba dabbobi ko shi kuke sawa a injin mota
ta yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe
ku wadancan bukatuba, asalima za'a iya
tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa
to amma miyagun namun dajine a wurin ko
kuma matattarar barayine wurin to anan fa
hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa,
saboda haka wadanda suke dashi kadan domin
bukatunsu sai su sha su yi taimama.
3. Cuta: Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta
a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin
warkewa, sai ka yi taimama.
4. Rashin Motsi: Idan ya zamana yana fama da
rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai
iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar
kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko
babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya
yi taimama.
5. Sanyi : Idan yana matukar jin tsoron sanyi
idan ya yi anfani da ruwa, kuma ga shi yana son
yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami
abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya
yi taimama.
Wadannan bayanan suna nuna mana cewa
rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba
zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin
warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da
aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici
shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya
to abu na farko da zai ajiye shine sallah, inda
zaka je gai dashi kace ya yi sallah kuwa sai ka
ga ana kallonka ana nuna maka halin da yake
ciki kamar kai baka da tausayi, inda kuma zaka
dan shafa masa dari ko dari biyu sai ya miko
hannu, Allah Ya sawwake.
Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai
bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a
barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba.
Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa
kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa
akan bandejin ko karan dorin to sai ya yi
alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba
sai ya wankeba.
Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya
zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan
kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi
bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi
sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo
matsanancin rashin lafiya day a shafi gabban
alwala ko taimama darasine mai zaman kansa,
a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-
daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin
cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya
kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan
taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa
da alkhairi.
Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake
doron kasa kamar inda yake; rairayi ko
jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko
ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.
Siffar Taimama: Yadda ake gabatar da taimama
shine; zaka wara yatsun hannayanka biyu ne sai
ka buga a kasa, sannan sai ya shafi fuskassa
da cikin tafikan hannunsa, sai kuma ya shafi
hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), zai yi ko
kari ya tabbata ya game ko'ina na fuskarsa a
lokacin da yake shafar kar ya manta da
karkashin gemu da kuma hannayansa, idan yana
da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko
ina, idan lokacin da ya shafo kasar kwai yayi ko
kura sai ya karkade, ba'ace dole sai mutum ya
sa kasa a fuskarsa ba.
Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau
biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun
kuma ya shafi hannuwa zuwa gwiwar hannu.
Za'a ko yi yadda ake taimamane da sauran
ibadu a gaban malamai, karantawa anan kadai
ba zata wadatarba, su kuma malamai su ji
tsoron Allah su koyawa al'umma wadannan
ayyuka a'aikace, sawa'un makarantun
islamiyyune ko malaman da suke koyar da
darussan addinin musulunci a cikin jami'o'i ko a
kwalejojin ilimi, ko kuma malamai da suke
karantarwa a cikin masallatai, kada ka taba jin
dan ka karantar da baki kowa ya gane, a'a sai
ka yi a aikace, kada ka manta sai da ma'aikin
Allah ya koyawa sahabbansa wadannan ayyuka
a aikace, ka ko san idan saurin ganewane sun
fika sun fi daliban da kake koyarwa.
Abundake Bata Taimama; Taimama tana baci
da duk abinda yake bata alwala babbane ko
karami, kamar tusa fitsari…. Fitar maniyyi, jinin
al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi
taimama ya gushe to taimama ta gushe.
Wanda ya rasa ruwa kuma ya rasa kasar da
zai yi taimama akanta, ko kuma ya kai wani
halin dab a zai iya taba ruwaba ko kasa to shi
wannan zai yi sallar ne a yadda ya sami kansa,
ba tare da alwala ko taimama ba, domin Allah
bai dorawa rai sai abinda zata iya.
Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar
farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan
taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi
sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi
kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama
to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar,
domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa
idan bai samu ba to sai ya yi taimama.
Idan mutum ana binshi wadansu salloli da ya
manta da su to ya samu ya sallacesu da
taimama guda.
Kammalawa: wannan kadan kenan daga cikin
abubuwan da suka shafi taimama da fatan sun
wadatar, kuma za'a koma ga malamai.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.

HUKUNCIN JININ AL'ADA(JININ HAILA)

HUKUNCIN JININ AL'ADA
( JININ HAILA)

Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su
tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban
shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jerin hukunce
hukuncen jinin al'ada wanda ake kira jinin haila
wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu
kawo hukunce hukuncen jinin biki (wato jinin
haihuwa.
Muhimmanci: yana da matukar muhimmanci
sanin hukunce hukunce jinin al'ada, muhimancin
bawai ya tsaya ga mata bane kadai a'a harda
maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na
zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada,
misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko
dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta
bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a
sakinta ba kuma a saduwa da ita, sannan ga
yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta
yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku
(al'ada uku) kafin akace ta kammala idda
sannan ai maganar sabon aure, to idan tana
al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan
sai bayan shekara daya da rabi za'a fara
maganar aure, shi yasa muka ce sanin hukunce
hukuncen wannan jinni ba wai ya rataya ga
mata bane kadai har da maza.
Menene Jinin Al'ada: Jinin al'ada jinine da yake
fita da karan kansa daka gaban macan da a
al'dance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce
kwanaki goma sha-biyarba.
Wannan shi ake nufii da jinin al'ada, da akace
'jinine da yake fita da kansa' kenan idan ya
zamana ba da kansa ya fitaba kamar ace
cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinni
ya balle mata to wannan bai zama jinin
al'adaba.
   Da akace 'Ta gaba' kenan idan ya fita ta
dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin
al'adaba. Da akace 'Wacce a al'adance zata iya
daukar ciki' kenan idan ya fita daga wacce a
al'adance ba zata iya daukar cikiba sabo da
yarinta ko girma to wannan shima bai zama
jinin al'adaba.
Amma da aka ce 'Ba tare da ya wuce kwanaki
goma sha-biyarba' kenan idan ya wuce kwanaki
sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba.
Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin
al'adaba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau
kansuba za su yi sallah domin jinin ciwone sai a
nemi magani, Allah ya sawwake.
Mafi Karancinsa: Malamai sun karawa juna sani
kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa
shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan
ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.
Mafi Yawansa: Mafi yawan kwanakin jinin al'ada
shine kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya
wuce haka to bai zama jinin al'adaba muddin ba
ciki take da shiba.
Mata Dangane Da Al'ada: anan mu sani mata
suna da halaye biyar musamman idan muka yi
la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya
zo na al'adane ko bana al'ada bane, kamar
haka:
1. Kasa da shekara tara: Idan jinni ya zowa
yarinyar da take kasa da shekara tara to
malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada
bane, jinin ciwone sai a nemi magani.
2. Tara Zuwa Sama: Idan zamana jinin ya zo ne
ga wacce ta cika she kara tara zuwa zamanta
budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi
kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin
na al'adane ko na ciwo. Kada mu sha'afa
yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da
hutu da wahala suna tasiri.
3. Budurci Zuwa Sheka 50: Idan jinni ya zo
daga lokacin da ta zama mudurwa zuwa
shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun
tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.
4. Daga 50 - 69: Idan jini ya zowa mace a
tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara
hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai
sukace za'a tambayi kwararrun mata da likitoci
domin sanin wannan jinin na ciwone ko na
al'ada.
5. Daga 70: Idan jini ya zo bayan mace ta cika
shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai
sukace wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane.
Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin
abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce
hukunce akansu, kuma ana ginine akan tsarin
kalandar musulunci, wadannan bayanai na
karkasuwar mata har zuwa gida buyar kamar
yadda ya gabata haka malam Adawi ya kawo a
cikin littafinsa 'Hashiyatul Adawi' , Allah ya ji
kansa da gafara.
Ina dada jadda cewa yanayin abin ci da da
abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri
matuka, dukkan abinda ba'a mahimtaba
dangane da yana yin zuwan jinni ko daukewarsa
yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi
tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi
bayan da cewa yanada alaka da hukunce
hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce
miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da
aka saka zata iya kammala idda akasa da
watanni uku.
Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama
shine zuwansa na farko sannan ya tabbata
cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga,
dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau
kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta bata
lada idan kuma ta bari samari suna
jagwalgwalata ita za'a rubutawa zunubi, ba
wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara
yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka
wanda ta sha.
Tabbatuwar Jinin Al'ada: Shifa abinda ya
shafi jinin al'ada al'amari da Allah madaukain
sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai
girma, Allah yana cewa:
''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada,
Kace: Shidinnan cutane, ku ninci (saduwa da)
mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai
sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka
(suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya
umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba
kuma yana son masu tsarkaka'' . Bakara, ayata:
222.
Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan)
Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan
Adam'' . Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane
ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine
wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci
a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane
ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya
amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan
labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin
Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci
itaciyar.
Shifa jinin al'ada kada amanta jinine da yake
fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu,
Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya
zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin
mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da
mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da
karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya
zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga
mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada.
Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi
nono jaririn yana sha amatsayin abin ci, shi
yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa
kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata
da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya
kasance ba inda zaii je to shine sai ya taru a
mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake
fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko
bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan –
kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah-
gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.
Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari
ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin
al'ada, kashi na farko; itace wacce ta fara,
kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai
kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga
bayanansu kamar haka;
1. Wacce Ta Fara: Ita wacce ta fara al'ada ya
zama yinta na yanzu shi ne ganin al'adarta na
farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata
zuba idone ta ga kwanaki nawa zauka kafin ya
yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-
biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya
doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'adaba,
kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara
sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa
kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama
(Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake
cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu
mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su
tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi
yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko
makamantan haka, wata babbar macece amma
bata san menene jinin al'adaba ita dai kawai
tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu
kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.
2. Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta
saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku
a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi
al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai
ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima
kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta
wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki
sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farko
kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar
karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira
wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da
tsayayyun kwanaki.
Ita wacce ta saba wato wacce take da
sanannun kwanakin al'ada to wadannan
kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan
kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai
ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada,
amma idan kwanakin suka cika al'adar kuma
bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka
zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki
shabiyar su cika, misali idan al'adarta kwanaki
biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki
biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron
daukewar sun zama takwas kenan, idan ya
dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke
ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin
sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara
uku sun zama sha-hudu idan bai daukeba sai ta
kara kwana daaya, ya zama goma sha-biyar
kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya
dauke ko bai daukeba domin kwanakin al'ada
makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma
sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan
shi jinin al'ada sunanshi jinin cuta (Istihala) sai
a nemi magani.
Adukkan wadancan kare-karen kwanaki da
aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na
saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin
hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi
jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga
wacce ta fara da wacce ta saba.
3. Mai Juna-biyu (Mai ciki): Galibin mata masu
juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar
mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga
al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita .
Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu to ida
cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin
al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan
kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata
iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da
biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan
ana da juna biyu kuma aka ga jini.
Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata
wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke
bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda
zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta
natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo
sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware
kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki
domin da hakane zata cika kwanakinta na
al'ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta
farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta
hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a
ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da
ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana
biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita
ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu
al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki
takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da
dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine
kenan, ba na dane ya dawaoba.
Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jinin
al'ada ya dauke akwai alama da shara'a ta
sanya domin ya zama shine manuniya akan
cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun
kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin
kantane, sune kamar haka:
1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine
mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin
gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a
tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata
al'adarta ta dauke.
2. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai
laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace
ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta
kammala.
Wadannan alamomi su suke nuna daukewar
al'adar mace, idan mace bata taba ganin
al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin
bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba
sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta
saba ganice sai ta ga bushewar gaba to
malamai sukace zata zata dan saurara kadan
domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai
ga fitar zababban lokacin sallah ba.
A dunkuledai kowanne daya daga cikin
wadannan abubuwa guda biyu yana nuna
samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci
gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata
sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da
ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin
ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma
zata yi sallaba, da dai sauransu.
Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-
diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta
damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama
matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma
idan a karshen jinine to wannan ba komai,
Ummu Atiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: ((Mun
kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da
diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani
abune)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i,
Hadisi Na: 368 , Ibnu Majah Hadisi Na: 647,
Darimi Hadisi Na: 865.
Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin
da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar
asuba, amma ba'ace tat shi cikin dareba domin
ta duba.
Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta
ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da
la'asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga
tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi
sallar magariba da lisha.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai-al'adaba:
Anan za'a lissafa abubuwan da basu halatta
mai al'ada ta yi su ba ko ayi mata ba,
wadannan abubuwane guda goma:
1. Sallah: Bai halatta mai al'ada ta yi sallaba
farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yi ba'akarba
ba sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta
kammala al'adar ba zata rama sallolinba.
2. Saki: Baya halatta matar da take al'ada a
saketa, wannan ya sabawa karantarwar
musulunci, saboda haka koda yana son ya
saketa to ya bari sai ta kammala al'ada kafin
ya sadu da ita sai ya saketa, amma idan ya
saketa tana jinin al'adar to sakin ya yi amma
za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai
kai ukuba.
3. Dawafi: Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin
Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda
maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da
kwanan mina dana muzdalifa da jifa da
Labbaika, da daidai sauransu.
4. Zama A Masallaci: mai al'adah ba zata
zauna a cikin masallaciba, domin sauraron
karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.
5. Azumi: Bai halatta mai al'ada ta yi azumi na
farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba,
saboda haka zata lissafa azumin da ta sha
bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba'a ajiye
azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo,
amma dazaran ta zo to dazaran ba azumi,
dazaran bata zoba to dazaran akwai azumi, ko
da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to
biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.
6. Taba Alkur'ani: mai al'ada bata taba
kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita
bata da tsarki, amma wannan bay a hana idan
ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa
wuri.
7. Karatun Alkur'ani: mai al'ada bata karanta
Alkur'ani, duddacewa wadansu malamai suna
ganin ya halatta ta karantashi da ka domin kada
ta manta sabanin dauka.
8. Saduwa: Bai halattaba saduwa da mace
tana al'ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu
da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa
Allahba asalima ta yi biyayyane ga reshi, bai
halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai
al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki,
kenan koda al'adar ta dauke amma batayi
wankaba to bai halatta a sadu da itaba. Ya
halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin
matarsa alokacin da take al'ada bayan ta yi
kunzugu inbanda daga cikbiyarta zugwiwarta
wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke
kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta
taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.
9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al'ada tana
tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.
10. Wajabta Wanka: Al'ada tana wajabta wanka,
wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar
ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.
Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan
tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah ya yi mana
jagora ya karba mana ayyukammu.
Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka
gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al'ada
bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba,
kuma lalle idan aka kallaci yadda ake sakaci
tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi
wannan al'amari to lalle abin yanada ban tsoro.
Anan gaba abinda zai biyo baya shine hukuncin
jinin biki wato jinin haihuwa.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja, Nijeriya.

Sunday, 1 January 2017

HUKUNCIN JININ HAIHUWA(JININ BIKI)

HUKUNCIN JININ
HAIHUWA ( JININ BIKI)

Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su
tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban
shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jerin hukunce
hukuncen jinin biki wanda ake kira jinin haihua
wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu
kawo a wannan karon bayan da abayanan da
suka gabata muka kawo bayanai akan jinin
al'ada.
Menene Jinni Biki: Jinine da yake fitowa daga
mahaiffa ta sanadiyyar haihuwa. Kenan shi jinin
biki jinine da yake da alaka da haihuwa, idan
mace taga jini kwana daya ko biyu kafin
haihuwa to shima malamai suna lissafashi cikin
jinin haihuwa.
Mafiyawan Kwanakinsa: Mafi yawan kwanakin
da macan data haihu zata ga jinin haihuwa
malamai sun karawa juna sani, wadansu sukace
kwanaki ar'bainne (40), wadansu kuma sukace
kwanaki sittinne (60) kamar yadda mai Akhdari
ya bayyana. Sabanin na al'ada shi kwanaki
goma sha-biyarne.
Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to
zata jira kwanaki arba'in, ko sittin, idan ya
dauke a kwanakin shikenan sai ta yi wankan
tsarki na daukewar jinin haihuwa ta ci gaba da
sallah da kuma sauran ayyuka na ibada, idan
kuma bai daukeba to sai a nemi magani ya
zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta ci
gaba da ibada, idan kuma jinin ya dauke kafin
kwanakin kamar ya dauke ranar da aka yi
haihuwar to annan ma zata yi wankana ta ci
gaba da sallah, laifine maigirman gaske mace
jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin sallah
wai sai ta yi arba'in wannan ba tsari bane na
addinin musulunci, domin tsarin musulunci
dazarar jinin yananan kafin kwanaki arba'in to
dazarar ba za'a yi sallah ba, amma dazarar jini
ya dauke ko kafin sunane to dazarar za'a ci
gaba da sallah, sai a kiyaye.
Imam Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi
ijima'i tun daga Sahabbai da Tabi'ai da wadanda
suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan cewa lalle
mace mai haihuwa zata bar salla tsawon
kwanaki arba'in sai dai idan ta ga tsarki kafin
hakan (kafin kwanaki arba'in din) sai ta yi
wanka ta kuma yi sallah.
Idan mace ta yi bari sai ya zamana halittar
mutum ta bayyana a barin kamar ace ga tsarin
halittar ba wai gudan jini bane ya zamana kuma
akwai jini day a zuba to anan tana da hukuncin
jinin biki jinin haihuwa, gwar gwadon kwanakin
da asune ahalittar take bayyana a ciki sune
watanni ukune galibi ammadai mafi karanci
sune kwanaki tamanin (80).
Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta
yadda halittar mutum bata bayyanaba to ba'a
la'akari da wannan jinin da ya zubo, saboda
haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar
azumiba saboda jinin domin bata da hukuncin
jinin biki.
Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan
kwanakin da aka yi bayaninsu to zata yi
wankane ta kuma yi sallah ko da jinin ya
daukene a ranar da aka yi haihuwar, to idan
jinin ya dauke kafin wadancan kwanakin sai
kuma ya dawo to sai mu tsaya mu gani idan
tsakani daukewar da dawowar ya kai kwanaki
goma sha-biyar zuwa abinda ya yi sama to
wanda ya dawodin jinin al'adane bana biki bane,
amma idan tazarar batakai kwanaki goma
shabiyarba to jinin da ya dawo cikon jinin
haihuwane.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai Jinin
Bikiba: Mu sani dukkan abuwan da jinin al'ada
yake hanawa ayiwa mai al'ada to jinin
haihuwama yana hanawa a yi wa mai biki, haka
namma abinda jinin al'ada yake hanawa mai
al'adar ta yi to jinin haihuwama yana hanawa ta
yi, kamar: Saki, saduwa, taba Alkur'ani, zama a
masallaci dadai sauransu kamar yadda bayani
ya gabata a jinin al'ada.
Haka namma kamar yadda ya halatta mai
al'ada ta yi kunzugu megidanta ya shasshafata
ya taba ko ina a jikinta in banda daga cikibiya
zuwa gwiwa to haka namma ya halatta ga mai
jinin haihuwa.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun
bayanai da suka gabata ya bayyana a fili cewa
al'amarin jinin haihuwa ba abune da za'a yi
wasa akansaba, watakila hankali ya tafi kan
bukukuwa suna maijego kuma bata sallah kuma
ga shi jinni ya dauke, kuma mun fahimci munin
tsohuwar al'adar nan na cewa maijego sai ta yi
arba'in kafin ta fara sallah ashe al'amari da
bashi da alaka da addinin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja, Nijeriya.

HUKUNCIN JININ ISTIHALA(JININ CIWO)

HUKUNCIN JININ
ISTIHALA ( JININ CIWO)


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su
tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban
shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jinin istihala wato
jinin ciwo, saboda baya amsa jinin al'ada wato
jinin haila haka kuma ba amsa sunan jinin biki
wato jinin haihuwa kenan, wato kenen shi
wannan jinin ba jinin al'ada bane ba kuma jinin
haihuwa bane saboda haka baya dauke da
hukunce-hukuncensu, baya hana sallah da
azumi da saduwa kamar yadda wadancan suke
hanawa.
Matashiya: Domin yin kandagarki yana da
matukar kyau da tsari mace ta lura da abubuwa
kamar haka:
(1) Launin Jininta: Ta yi kokari ta gane launin
jininta na al'ada wanne kala yake zuwa mata
'Baki ne ko Ja'.
(2) Lokacin Zuwa: Shin al'adarta tana zuwa
mata ne a farkon wata ko tsakiyarsa ko karshe.
(3) Kwanakinsa: Kuma ta kiyaye kwanaki nawa
yake zuwa mata a duk lokacin da take al'ada.
(4) Shinshina: Wato yanayinsa yana da karnine
ko wari.
Dukkanin wadannan abubuwa ana bukatar ta
gane su kuma ta fahimcesu tun lokaci da take
lafiya, -Allah ya sawwake – domin idan jini ya ci
gaba da zuwa saboda ciwo da wadannancan
bayanai za'a yi aiki domin a gano mata
kwanakin jininta na al'ada da kuma kwanakin da
suke na rashin lafiya.
Jinin Istihala : Shine ballewar jini ba'a
lokacinsaba, ta wata jijiya da ake kira 'Azil' .
Al'amari mai jinin Istihala al'amarine mai
rikitarwa domin yadda jinin al'ada yake kama da
jinin istihala, to idan jinin ya kasance yana zuba
a koda yaushe ko mafi yawancin lokaci to a irin
wannan lokaci me zata yi la'akari da shi a
matsayin al'ada me kuma zata yi la'akari da shi
a matsayin jinin istihala ta yadda ba zatabar
azumi da sallah ba saboda shi? Domin mai jinin
istihala ana mata hukunci mata masu tsarkine,
kada a manta ya kandauki mace tsawan
shekaru ko watanni ba al'amarine da za'a yi
wasa da shi ba. La'akari da wannan bayani lalle
mace mai jinin istihala tanada yanayi guda uku:
Yanayi Na Farko: Ya kasance dama tanada
lissafin tsarin al'adarta kafin wannan ciwo na
zubar jini ya sameta, kamar ace dama ta
kasance kafin jinin istihala tana al'adane tsawan
kwanaki biyar ko takwas missali a farkon wata
ko a tsakiya kuma ta san adadin lokacin, to
wannan zata zauna ne a matsayin mai al'ada
gwargwadon yadda ta saba, sai ta bar sallah da
azumi domin a wannan lokacin ana mata
hukuncin mace mai jinin al'ada, idan al'adar ta
dauke (Kwanakin da ta kaddarasu cewa sune na
al'adar) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah, sai
ya zama jinin da ya ci gaba da zuwa jinin
istihalane ba jinin al'adaba, kamar yadda
Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi) yace ma Ummu Habiba '' Ki
zauna gwargwadon da al'adarki take zuwa,
sannan sai ki yi wanka ki kuma yi sallah'' , Muslim
334, hakanan kuma Ma'aikin Allah (Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi) ya fadawa
Fatima diyar Abu Hubaish cewa : ''Ai wannan
wata jijiyace, ba al'ada bace idan lokacin al'adarki
ya iso sai ki bar sallah'' Bukhari 228 , Muslim
333 .
Yanayi Na Biyu: Idan ya zama bata da wani
yanayi sananne saidai jinin nata ana
banbanceshi yana dauke da siffar jinin al'ada,
kamar ya kasance baki ko mai kauri ko ya
kasance yana da wata shinshina amma sauran
baya kama da siffar jinin al'ada, kamar ya
kasance jaa amma bashi da shisshina kuma
bashi da kauri, to a irin wannan yanayi za ta yi
la'akari da jinin da yake dauke da siffar jinin
al'ada a matsayin jinin al'ada sai ta bar sallah
da azumi…' sai kuma ta yi la'akari da wanda ba
shiba jinin ciwone bana al'adaba, sannan sai ta
yi wanka idan wannan jinin da yake dauke da
siffar jinin al'adar ya dauke, daga nan kuma sai
ayi mata hukuncin mace mai tsarki, kenan sai
ta ci gaba da sallah da azumi…' ko dako jinni na
zuba, kamar yadda Ma'aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya fadawa
Fatima diyar Abi Hubaish:
'' Idan ya kasance jinin al'ada, shifa jinine baki
akasanshi, to sai ki dakatar da sallah, idan kuma
dayanne sai ki yi alwala ki yi sallah'' . Abu Daud
286, Nasa'I,220, Ibnu Hibban 1348.
Yanayi Na Uku: Idan ya kasance bata da wani
abu da take gane jinin al'ada da shi, kuma babu
wata siffa da take banbance jinin al'ada da
wanda ba na al'adaba, to anan zata yi la'akarine
da mafi yawan kwanakin al'ada a kowanne wata
wato kwanaki shida ko bakwai, domin wadannan
kwanakin sune mafi yawan kwanakin da mata
suke al'ada, wannan ko saboda hadisin
Hamnatu diyar Jahash Ma'aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi:
'' Abin sani kawai wannan (Jinin ciwon)
wani zungurine daga shaidan, saboda haka sai ki
yi al'adarki kwana shida ko kwanaki bakwai,
sannan sai ki yi wanka, idan kika tsarkaka sai ki
yi sallah kwanaki ashirin da hudu ko ashirin da
uku, kuma ki yi azumi ki yi sallah, yin haka ya
isarmiki, haka za ki dinga yi kamar yadda mata
suke al'ada'' . Tirmizi: 128, Abu Daud: 287, Ibnu
Majah: 627.
Atakaice: Idan aka yi la'akari da bayan da
suka gabata za mu fahimci cewa; mai yanayi
tabbatacce zata yi anfani da wannan yanayin
ne, wacce take abinda take banbance al'ada da
jinin da ba na al'adaba za ta yi anfanine da
wannan, amma wacce bata da wata alama to
za ta yi al'ada kwanaki shida ko bakwai.
Abinda kan mai jinin istihala (jiwo): Dudda
cewa a hukumce mace mai jinin istihala wato
jinin ciwo macece mai tsarki dudda cewa jinni
na tare da ita alokaci, saboda haka za ta yi lura
da abubuwa kamar haka:
1. Ya zama wajibi ta yi wankan daukewar jinin
al'ada bayan wucewar kwanakin da aka yi
la'akari da su a matsayin jinin al'ada.
2. Za ta wanke gabanta domin gusar da abinda
ya fita alokacin kowacce sallah.
3. Za ta sanya auduga ko makamancinta a
gabanta domin hana shi diga kasa, wato zata yi
kunzugu kenan.
4. Za ta dinga yin al'awala a kowacce sallah,
kenan ba zata yi salloli biyu da al'awala dayaba,
saidai idan ramuwace, Allah kadai shine masani.
Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka
gabata ya bayyana a fili yadda musulunci ya
kula sosai kan abinda ya shafi hukunce-hukunce
jinin dake samun mata, kama daga jinin al'ada
jinin biki har zuwa wannan jinni na istihala wato
jinin ciwo, kuma wannan yana nuna
muhimmancin al'ummar muslmi su tashi tsaye
domin sanin wannan al'amari musammanma
mata, kuma daga nana za mu dasa aya akan
abinda ya shafi tsarki za kuma mu shiga abinda
ya sahafi Sallah da izinin Allah.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja, Nijeriya.

HUKUNCE HUKUNCEN ALWALA

HUKUNCE-HUKUNCEN
ALWALA

Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman kanta
wacce Allah madaukakin sarki ya sahar'antata
kafin gabatar da wadansu ibadu musammamma
sallah, mutum yana samun cikakken ladan
alwala idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin
sarki ya saukar da hukunce-hukuncen alwala a
cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan
kuka ta shi za ku yi sallah to ku wanke
fuskokinku da hannayanku zuwa gwiwar hannu
ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa
idan sawu (idan kafa)…'' Suratu Ma'ida, aya ta: 6.
Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin
alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi anwanke ko
kuma anshafa, sannan kuma ayar ta iya kance
ko wanne mahalli, sannan kuma Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
ya bayyana siffar yadda alwalar take da
maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake
gamsasshan bayani.
Ka sani lalle ita wannan alwala tanada falala da
kuma sharudda da kuma farillai sannan tana da
sunnoni da kuma mustahabbai, sharuddannan
da farillai tabbas a tabbata ansame alokacin
gabatar da alwala iya gwargwado domin da
sune alwala zata zama karbabbiya, amma su
sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne ta
inda matsayinsu bai kai matsayin sharuddai da
farillaiba.
Falalar Alwala: Dudda cewa alwala wajibice
wannan kadai ya isheta samun matsayi a
musulunci domin dukkan abinda akace farillane
to wannan matsayi ne me zaman kansa, bayan
hadisi na 62 a cikin Muwadda'u Malik yana
cewa: '' An karbo daga Abdullahi As-Sunaabihi,
lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi yace:
''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi
kuskurar baki dukkanin laifukan dake bakin sun
fice, idan kuma ya face laifukan (Day a shaka)
sun fice, to idan kuma ya wanke fuskarsa
laifukan da ke fuskar ta sa sun fice, har wadanda
ke karkashi girar shi, idan ya wanke hannayansa
laifukan dake hannayansa sun fice, har wadanda
ke karkashi faratansa (jam'in farce), to idan
kuma ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun
fice har wadandake kunnuwansa, to idan kuma
ya wanke kafafuwansa duk laifukan dake
kafafuwan nasa sun fice, har wadanda ke
karkashi farcen kafafun nashi. Sannan kuma
tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya zama wani
karine da yake da shi''.
Lalle wannan bakamar falala bace da alwala
take da shi, domin mai alwala zai kasance yana
kammala alwala zunubanshi suna digewa a
kasa, amma gudu ba hanzariba wannan ladan
zai tabbata ne ga wanda ya yi alwala da
shara'a ta tabbatar da ita ba wacce ya tsinta a
kan titi ba.
Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala sune
abubuwan da ake so mai alwala ya cika su
kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:
(1) Musulunci , kenan idan wanda ba musulmiba
ya yi alwala bata yi ba.
(2) Hankali , idan mahaukaci ya yi alwala itama
bata yi ba.
(3) Wayau , idan dan karamin yaro mara dabara
ya yi bata yi ba.
(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya zama
ruwane mara tsarki to alwalar bata yi, bayanai
sun gabata akan hukunce-hukuncen ruwa.
(5) Ruwan ya zama na halas, idan ruwane da
mutum ya sata ko ya same shi bata shar'an
tacciyar hanyaba to alwalar bata yi ba.
(6) Ya kasance mai tsarki , idan mai alwala ya
kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato
ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi
alwalar bata yi ba.
(7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga,
kenan idan mutum ya kasance yaba sanye da
wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki
to dolene ya cire shi, kamar tabo (laka)…'.
Farillan Alwala :
(1) Niyyah: Domin a banbance wanda ya sa
ruwa donin sanyaya jiki, ko domin gusar da
datti, duk wannan ba niyyace ta alwalaba.
(2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta bangaren
tsawo tana farawane daga matsirar gashin kai
(banda sanko) zuwa karshen mukamiki, amma
ta fuskar fadi tana farawane daga kunnan dama
zuwa kunnan hagu, wannan shine abinda yake
amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar
ko ina ya sami ruwa kamar kasan haba, gefan
ido da gefan kunne da matsa-matsin karan
hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu
kamar alwalar yarace.
(3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu. Mai
alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke
hannayansa tun daga saman yatsunsa (farce-
akaifa) harzuwa gwiwar hannu ya tabbata
gwiwar ta shiga inda ya wanke, anamma akwai
manya masu alwalar yara.
(4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada yatsunka
sannan kuma ka fara shafar daga goshi (daidai
matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya.
(5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya
tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon sawu,
wato wadannan kasusuwan guba biyu dake
gefan kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.
(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya
cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya
shiga ko ina.
(7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine
alokacin da ka fara alwala to ka dakatar da
komai sai ka kammala, amma kana alwala kana
kuma wata sabga daban wannan bai yi ba.
Mai alwala ya tabbata ya gabatar da
wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta
yadda idan aka rasa daya daga cikin su to
alwalarsa ta shiga hadari.
Sinnonin Alwala:
(1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A Ruwa.
Ta yadda mai alwala zai karkato butar alwala
domin ya wanke hannayansa zuwa Ku'u wato
wuyan hannu.
(2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata ya
sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya kada
ruwan a baki, wannan shi ake kira da kuskurar
baki.
(3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya shaki
ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai, sai dai
kawai idan yana azumine sai yayi kadan. Amma
yadda mutane suke shafar hancinsu wai da
sunan shaka ruwa wannan baiba.
(4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne da
hannun dama sai ya sa hannun haku akan
karan hancinsa, sannan sai ya fyato ruwan da
ya shaka.
(5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata ya
shafi cikin kunnensa da wajan kunnan, zaka/ki
sanya yatsanka 'yar-manuniya a cikin kunnan
sannan ka babban yatsa a wajan kunnan
sannan sai ka shafa, Dirkashi!.
(6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka shafi
kunne shin zaka shafi kunnanne da ragowar
danshin hannuka da ka yi shafar kai da shi? Ko
ko zaka sake taba ruwa na musamman domin
shafar kunne, malamai sun karawa juna san, ko
wanne ka yi ya yi daidai.
(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka fahimta,
ita shafar kai farillace, amma dawo da shafar
kai sunnace daga cikin sonnonin alwala.
(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka kawosu
daya-bayan-daka kamar yadda aka lissafosu,
kada ka dauki na uku ya zama shine na farko
sannan ka biyo shi dana biyar, misali…'.
Wadannan matsayisu bai kai matsayin farillaiba,
amma suna cikin manyan abubuwan da suke
cika alwala.
Mustahabban Alwala:
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni,
kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na
gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su,
domin kowannanmu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalliya, to ko tunda hakane bai
kamata yace ai wannan mustahabbine ya
daukeshi kamar wani kankanin abu.
Su mustahabban alwala suna da yawa, amma
yanzu ga kadan daga cikinsu:
(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'' , adaidai
loakcin da zaka fara alwala, amma idan mutum
ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna
bakomai sai ya yi a lokacin.
(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma
kamar haka:
ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍَﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ،
ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍَﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ
ﻣِﻦَ ﺍَﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻠْﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻳﻦَ .
Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu abinbauta da
cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma manzansa ne,
Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan
tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman
tsarkaka.''
(3) Karanta Ruwa : Bawai ana nufin mai alwala
ya shasshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar
ya yi anfani da ruwa amma kada ya malalar da
shi, domin yana daga cikin tsarin musulunci
tattali da tsimi da tanadi.
(4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma dama ya
gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da
busasshe, idan bai samuba sai ayi da yatsa,
amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma
daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin
sallah ya yi kuma amma yana da alwala to
abinda ake so shine ya yi asuwaki.
(5) Wuri Mai Tsarki : An so inda zaka yi alwala
ya zama wurine mai tsarki.
(6) Dama Kafin Hagu : abin nufi shine ka fara
wanke hannun dama kafin hannun hagu,
hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta
dama.
( 7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce sunnah
tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da
kuskurar baki kafin shaka ruwa.
(8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke wuraran
da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau
uku zai zama mustahabbine idain wankewar
farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata
gamaba to ta biyu tananan amatsayin wajibi,
haka namma idan ta biyun idan bat agama ba
to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama
wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai
ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare
da barnaba. Amma shi kais au daya ake
shafarsa, ba'a shafar kai sau uku. Sannan kuma
mutum ya tabbata a wadannan wankewa da
akace ya yi sau uku bai kara akan hakan ba, ya
yi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.
Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai
sun mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai
mata su sani gashin kansu da sangalin
hannuwansu duka al'aurane, saboda haka bai
halatta su bayyanar da su ga maza, ken an idan
zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kawwame
kanki.
Wadannan bayanai da suka gabata zasu
haskaka mana yadda alwala take, amma hanya
mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani
domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an
tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala
sai yasa aka kawo mishi butar alawala ya yi
musu ita a aikace, yace kuma irinta ma'aikin
Allah ce.
Anan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a
dana sauran masallatai da kuma malamai a
jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a
sakandare da firamare da malaman islamiyyu da
malamai masu karantarwa a masallatai da
masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa
da su karantar da mutane ita wannan alwalar a
aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya, kada
ka ga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a
aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada
hakan, ita ibada sai an koyawa mutum ba wai
daka kawai shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi
iyaye da kakanni duk musulmai ne sabo da haka
ba sai ya koyaba, duk wannan maganace ta
wanda yake nesa da makaranta, kai da ganin
alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah
ya karba mana ibadummu.
Kammalawa: Lalle wadannan bayanai sun
kara tabbatar mana ashe alwa abace da sai an
tashi tuku domin a koyeta tana da falala da
kuma sharudda sannan ga farillai da sunnoni da
kuma mustahabbai, lalle ka nana bukatar
malamai daga kowanne bangare su tashi tsaye
su karantar da al'umma wannan ibada a aikace,
domin a gudu tare a tsira tare.

TSARKI DA YADDA AKE YINSA

TSARKI DA YADDA AKE
YINSA

Shinfida: Mu sani ya 'yan-uwa masu albarka,
wannan addini na musulunci addinine da yake
cikakken addini ta kowanne bangare, bai takaitu
ga alwala da sallaba kadai, ya shafi kowanne
bangare na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya
zamantakewa, kasuwanci taimakon juna, tsare-
tsaren gudanarwa dadai sauransu.
A yanzu zamu kawo bayanaine da suka shafi
tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin
tsarkin yake jawowa? Ya ladubban yin tsarkin
suke? Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran
wadansu batutuwa da suke da alaka da wannan
maudu'i, da fatan Allah ya yi mana jagora ya
kuma fahimtar da mu.
Abubuwan Da Akewa Tsarki: ana yin tsarki ne
daga dukkan abinda ya fito ta daya daga
mafitar guda biyu ko ma ta duka inbanda hutu
(tusa). Kenan ana yiwa fitsari, bayangida
maniyyi maziyyi jinin al'ada….tsarki, kawai dai
idan mutum yana da alwala sai ya yi tusa to
alwalar kawai zai sake ba sai ya dauki butu ya
yi tsarki ba.
Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka
dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da
makamantansu suka same shi to dole ya
tabbata ya gabatar da ya yi tsarki.
Abinda Ake Tsarki Da Shi : Abinda ake tsarki da
ashar'ance shine ruwa mai tsarki mai
tsarkakewa, wannan shi ake kira Istinja'u .
Saidai idan mutum bai sami ruwanba sai ya yi
da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na
ukun ya fito a bushe ba wata laima shikenen,
idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai
biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan kuma
ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan
ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan
hukunci shi ake kira Istijmari , ka samu ka hada
duka a lokaci guda, misali idan ka yi bayan gida
sai kasa tsinke ko takarda mara rubutu sai ka
share sannan sai ka biyo shi da ruwa. Kenan
ba'a tsarki da yawu (miyau).
Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da abinda
ya fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a
raba tsarki zuwa gida biyu:
(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin abinda ya fita
daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari,
maziyyi…'.
(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake abinda ya
taba jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko
wannensu baya yiwuwa said a ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa.
Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin
girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:
(1) Babba wanda ake kira Hadasul Akbar:
Ankira shi babbane domin ba'a tsarkaka daga
gareshi sai an yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko
saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki.
(2) Karami wanda ake kira Hadasul Asghar:
wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar
fitsari ko maziyyi.
Yadda ake yi: Da farko mutum ya wanke
hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai
wanke, domin hannun sa ya koshi da ruwa,
sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan
kuma sai ya fara wanke wurin bayan gida
musamman idan ya kaatse, ana bukatar mutum
ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman
idan maziyyi ne ya fita.
Ladubban Zagawa (Fitsari Ko Bayangida):
Akwai tsari na ladubba da musulunci yake da su
a lokacin da mutum ya ke niyyar kewayawa,
wannan zai nuna maka cewa musulunci ya
karade komai:
(1) Anbaton Allah : Ana bukatar kafin ka shiga
ka ambaci Allah domin ba'a anbaton Allah a
makewayi, kuma ka nemi Allah ya tsareka da
sharrin aljanu, domin irin wadannan wurare
matattarace ta su, yace:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ
ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ
Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina
neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza da
kuma aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ
ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ
Ma'ana: (Ina neman) gafarar Ka , Dukkan godiya
ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.
Ka sani ba'a shiga bayi da dukkan wani da
yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko
carbi…'. Hakanan kuma ba'a katse bayangida da
dukkan wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga,
kafar dama kuma lokacin fita.
(3) Ayi A Tsugunne: kada mutum ya yi fitsari
ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin
kangone ko yana tsoron fitarin ya fallatso masa,
sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a
tsaye.
(4) Tabbatuwa A Cikin Sutura: ana bukatar
kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye,
sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga
suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar
wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko
unkula da wasu suke nunawa na bayyanar da
al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan
baidaceba, sai ka ji wana yace 'Ai duka
mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan
ba koyarwar musulunci bace, haka namma
mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube
suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda,
haka namma mata, wai sun dauka abinda yake
haram shine namiji ya ga al'aurar mace ko
mace ta ga al'aurar namiji, kai wani lokaci kana
tafiya a cikin mota sai kai arba da wani
gabjejen kato yana wanka a rafi, wani kuma a
gefan titi ya kafe mashin ko ya je kayan
tallansa, duk wadannan bakewawan halaye
bane, mutum musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu: Kenan
abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da
karfinsa a kan kafarsa ta hagu.
(6) Ya Bude Tsakanin Cinyoyinsa: kenan kada
ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai
fita, sannan idan ya mayar cikin wando sauran
ya gangaro, Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake: musulunci bai
yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda
ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai
haifar da cututtuka.
(8) Ya Rufe Kansa: Ana son wanda yake
bayangida ya rufe kansa a daidai lokacin da
yake yi, domin koda wani ya yi kuskuren
ganinsa to shi bai ganshiba, abin zai zo da
sauki, amma ba zaka ji dadiba kana bayan gida
ka hada ido da wani, wanda zai iya zama
dalibinka ne ko suruki ko da..,'.
(8) Kada Ayi Magana: anhana mutum yana
bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai
dalili mai kwari, kamar ka ga makaho ya nufi
rijiya ko karamin yaro…'.
(9) Kada A Tari Iska: an hana idan mutum zai
yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari iska,
domin zai bsowa jama'a warin bayan gidansa,
kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska
take kadawa.
(10) Kaucewa Rami: Ba'a yarda idan za ka yi
fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan
kai ka haka, domin bakasan mekecikin ramin ba,
takan yiwu akwai mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraran Tsinuwa: Wadannan
wurare sune wuraran da mutane suke yawan
tsinema dukkan wanda ya yi musu bayangida a
wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke zama su huta, jikin
bangone ko karkashin bishi komadai inane.
(b) Kan hanya: Akwai rashin mutunci mutum ya
zo kan hanya ya gicciya bayangida, wannan
dabi'a musulunci bai yarda da ita ba.
( c ) Mashayarruwa: Hakanan baya cikin
karantarwar musulunci mutum ya zo inda
al'umma suke diban ruwa rafine ko wani gulbi
ko gindin fanfo komadai inane ya aikata wannan
ta'asa. Wadannan wurare uku musulunci ya
hana a aikata wannan danyan aiki a wurin,
domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah
ya tsaremu.
(12) Nesa Da Jama'a : ana bukatar dukkan
wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta
yadda ba za su ganshiba kuma ba za su ji
nishin shiba, ba zai yi kyauba ace kana bayan
gida mutane suna ganinka ko suna jin nshinka,
ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka
boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a
mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a
barshiba.
(13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: wato inda
mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya
juya mata baya, wannan idan a dajine, amma
idan a gidane to da sauki.
Abubuwan Da Rashin Tsarki Yake Hanawa:
kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki
wajibine, to mu sani idan mutum bashi da tsarki
bai halatta a gareshi wadannan abubuwanba:
(1) Sallah: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki
ba ya yi sallah nafila ko farillah.
(2) Dawafi: Kewayan Ka'aba kenan a birnin
makkah, saboda haka idan mutum yana dawafi
sai ya yi tusa to dawafisa ya warware sai ya
sake alwala domin ita tusa ba'a yi mata tsarki.
(3) Sujjadar Tilawa: Wato sujjadar da mutum
zai yi ida yana karatun Alkur'ani mai girma sai
ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki,
dudda malamai sun kawa juna sani akai.
(4) Kabli Ko Ba'adi : Bai halatta ga wanda bashi
da tsarki ba ya yi kabli ko ba'adiba har sai ya yi
tsarki, idan akce kabli ana nufin sujjadar da
mutum zai yi kafin ya yi sallama, amma idan
ake ba'adi to wacce zai yi bayan sallama. Idan
jiya ba'adi ta kamaka sai kuma ka manta baka
yi to ya halatta ka yi ta a yanzu idan kana da
tsarki.
(5) Daukar Alkur'ani Mai Tsarki: idan mutum
bashi da tsarki to sai yi tsarki kafin ya taba
wannan littafi mai tsarki.
Kammalawa: ina fatan wadannan takaitattun
bayanai sun warkar da abinda ake bukata, kuma
sun nuna lallai addinin musulunci gamamman
addinine da ya shafi komai ya kuma yi bayani
akan komai, domin idan yakai bayan gida sai an
nunawa mutum yadda ya kamata ya yi to ashe
wannan ba karamin gata musulunci ya yi mana,
muna godiya ga Allah.

ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA

ABUBUWAN DAKE KARYA
ALWALA

Shinfida: Lalle wannan babi yana da matukar
muhimmanci, domin bayan da kasan alwala to
ya kamata kasan abin da ke warwareta, akan
haka ya ka yiwa kanka hukunci idan zaka yi
sallah ko abinda dole sai da alwala ake yinsa,
saboda haka yana da matukar kyau mu kula da
wadannan hukunce-hukunce. Allah ya yi mana
jagora.
Abubuwan da suke bata alwala sunkasu kashi
biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi anan
shine, akwai abinda shi karankan sa yake bata
alwala to wannan shi ake kira Hadasi
(Al'ahdaas) . Akwai kuma wanda shi karankan
sa bai warware alwala amma zai kai ka ga
abinda yake warware alwalar to wannan shi ake
kira, Sabuban Hadasi (Asbabul Ahdas).
To shi hadasin wato abinda yake karya alwala
da karankansa, abubuwane guda shidane, hudu
daga cikinsu suna fitane ta gaba, sune kuma;
Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi da kuma Maniyyi.
Wadannan idan suka faru ko dayansu ya faru to
tsarki kawai za'a yi a sake alwala in banda
maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya bata
alwala sai kuma anyi wanka. Sai kuma guda
biyu daga da suke fita daga dubura, sune kuma;
Bayangida da kuma tusa. Amma shi bayan-gida
tsarki za'a yi sai a sake alwala, sabanin tusa
wacce take ita ba'a yi mata tsarki alwala kawai
za'a sake.
Sai kuma abubuwan da suke sabubbane na
hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai,
amma su wadancan da zarar ya diga komai
kankantarsa to ya karya alwala inbanda mai
fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa
sune;
(1) Bacci: Shi bacci a nan ya kasu kashi hudu;
(a) Dogon bacci mai nauyi, kai tsaye wannan ya
karya alwala.
(b) Takaitaccan bacci mai nauyi, shi ma ya
karya alwala.
(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai
karya alwala ba.
(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala
amma an so a sake ta.
Ma'aunin da ake auna bacci da shi domin a
gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shine;
Idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to
baccinka bai yi nauyi ba, amma idan baka san
wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to baccin
ya yi nauyi. Kenan idan kuna fira sai amma
kana gyangyadi sai da ka farka sai kace; ina
wane? Ko; wane yaushe ka zo? To kasan
baccinka ya yi nauyi, Allah ya sa mu dace.
(2) Gushewar Hankali: Idan hankalin mutun ya
gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma ko
maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan idan
mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko kuma
suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a asbiti
ko kuma ya sha ta yi Marisa-ta sha kafso to
alwalar ko wannensu ta karye.
(3) Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi
al'aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba
al'aurarsa bawai ta samani riga ko wandoba ko
kuma wani kyalleba to malamai sun karawa
juna sani kan makomar al'walarsa, wadansu
suke ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma
suka ce idan ya tabane domin ya ji dadi to ta
karye amma idan ba wai ya yi hakanne domin
ya ji dadi ba alwalarsa nanan, wannan maganar
kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai
sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al'aurarsa
ba kai tsayeba ko dai ta saman wando ko
saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa
nanan daram.
(4) Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi
mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji
ba alwalarsa ta karye, haka kuma al'amari yake
idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta
ji dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye,
malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu;
(a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji
dadin to alwalar ta karye.
(b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma
ya ji dadin to ta karye.
( c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji da
din ba to alwalar ta karye.
(d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma
bai ji dadinba to alwalarshi tanan daram.
Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya
kawosu. Mu sani wadannan bayanai sun shafi
macema idan ita ta yi.
Akwai wadansu da malamai suka karawa juna
sani akan suna karya alwala ko basa karyawa?,
wadannan kuma sune:
(5) Shakka Akan Hadasi: Idan mutum ya
tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokwanto
ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan bashi da
tabbas? Wasu malamai sukace; Ai da ya yi
kokwanto alwalarsa ta karye domin ba'a sallah
da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma
suke: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai
daga bayane yake shakka to ai shakka bata ture
abinda yake dahir, saboda haka sukace alwalar
nanan, Allah shine masani.
(6) Ridda: Shine mutum musulmi ya kafirta
(Allah Ya tsaremu). Wadansu malamai sukace
da zarar ya bar musulunci to da zarar alwalar ta
karye, wasu malaman kuma sukace; A'a, ai
ayyukansa da ya yi ba za su baciba sai in ya
mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na
cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga
wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi
yafi.
Alwala bata baci idan mutum ya yanke farce
(Kunba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko
anyi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko
kuma tuntube har jini ya fita duk alwala bat
abaci saboda wadannan, ko mace ta shafi
gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu
sunce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin
fitsari ko tusa ko bayan gida abinda musulunci
ya karantar shine mutum ya je ya biya wannan
bukatar ta shi tukunna, maimakon ya matse.
Kammalawa: Alwala tana da muhimmanci
matuka saboda haka a kiyayeta a san kuma
abinda yake warwareta, kuma wannan yake
nuna mana cewa tunda har alwala za'a ce
akwai abubuwan da suke warwareta dudda ga
laima a jikin mutum amma ace alwalarsa ta
warware to lalle yana da kyau musan kuma
abubuwan da suke warware musulunci domin
kullun mutum ya dinga ba addininsa kariya ta
yadda kada ya warware, Allah yak are mana
addinimmu, amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.

WANKAN TSARKI(JANABA)...

WANKAN TSARKI
(JANABA)...

Shinfida: Bayan da bayanai suka gabata akan
abinda ya shafi karamin hadasi wanda yake ya
takaitune ga tsarki da kuma alwala, sannan
bayanai suka zo akan abinda ya shafi kadan
daga cikin hukunce-hukuncen alwala, to a
yanzu za'a yi bayani ne akan abinda ya shafi
babban hadasi wanda yake bai tsaya ga tsarki
ko alwalaba a'a, shi tsarkinsa shine ayi wanka
shine an tsarkaka, wadannan abubuwa da suke
wajabta wanka suna da yawa za mu yi iya
kokari damin mu kawo su daki-daki, da fatan
Allah ya yi mana jagora, amin.
(1) Janaba: Janaba dayace daga cikin
abubuwan da suke wajanta wanka, wanda yake
hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar
haka:
(a) Fitar Mani: Idan maniyyi ya fita daga mace
ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin
wankan ya wajaba sai ya zama maniyyin ya
fitane ta hanyar jin dadi, kamar kallo ko wasa
ko tabe-tabe ko jingina…' amma idan ya fita ba
ta hanyar jin dadiba ya fitane ta hanyar wahala,
kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma
watar lantarki ta ja shi…' to wannan wanka bai
wajaba a kanshiba saida kawai ya yi alwala. Shi
wannan fitar maniyyi da ake Magana akan shi
ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana bacci,
idan ya fita ana farke shine ake maganar an ji
dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana
baccine to ba wata maganar jin dadi wanka ya
wajaba.
(b) Shigar Azzakari Cikin Farji: Idan kan kaciyar
namiji ya bace cikin gaban mace to wanka ya
wajaba. Anan ba'a maganar an fitar da mani ko
ba'a fitarba, da zarar hakan ya faru ko macen
ce ta fitar amma namijin bai fitarba ko kuma
namijin ne ya fitar amma macen bada fitar ba
ko ma dukansu basu fitarba wankadai ya
kamasu su duka, da wanda ya fitar da wanda
bai fitarba, tunda ba maganar fitarwa ake yi ba
maganar saduwace, amma inda wasa aka yi ba
saduwa ba to wanda ya fitar shi wanka ya
wajaba a kanshi.
Idan aka yi saduwa sannan aka kara yi to
idan an tashi wanka wanka guda kawai za'a yi,
koda an yi saduwar sau gomane sannan ake so
ayi wanka to wanka guda za'a yi ba wanka
goma ba.
Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so
ya jinkirta wankan janaba zuwa an jima to
abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala,
domin alwalar tana rage kaifin janaba, sannan
kuma tana kara kuzari lokacin da ake so akara
saduwar.
Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da
maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi kamar
yadda bayini ya gabata, to bayan ya yi wankan
sai kuma ya ga maniyyi ya zubo, to anan idan
wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan
maniyyin wani wankan ya kama shi, amma idan
janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo
yanzu to alwala kawai zai yi.
Abayan da suka gabata mun yi bayani na
babbancin maniyyi da kuma maziyyi, sannan
kuma da banbance-banbancen maniyyin mace
da na namiji. Sannan mu sani wadannan
bayanai sun shafi maza da mata, sannan kuma
ka'ida ta musulunci itace bayanin abubuwa a
yadda suke, domin kada a ga maganganun sun
yi tsauri, mahalline na bayanin hukunce-
hukunce.
Fitar maniyyi a farke ko ta hanyar nafarki,
kamar mutum ya yi mafarkin yana saduwa da
mace, ko mace ta yi mafarkin namiji yana
saduwa da ita to wannan al'amari yana tabbatar
da abubuwa kamar haka; abu na farko wannan
wanda ya fitar da maniyyin janaba ta hau
kanshi, abu na biyu; idan wannan shine fitar
maniyyinsa na farko to ya sani daga wannan
lokacin ya balaga, saboda haka hukunce-
hukuncen musulunci sun hau kanshi ko kanta.
Idan mutum ya yi mafarkin yana saduwa da
mace, ko mace ta yi mafarkin ana saduwa da
ita, sannan kuma ya farka bai ga maniyyi ba to
ba wata janaba akanshi, saboda haka ba zai
wanka ba kuma zai yi tsarkiba saboda hakan.
Wadannan kadan kenan daga cikin bayanan
da suka shafi janaba, kuma dole a tashi tsaye
domin a karantar da mutane, wani da ake
Magana da shi cewa yake yi shi bai san idan
mutum ya sadu da matarsa wai sai ya yi
wankaba, wai abinda ya dauka shine wanda ya
yi zina shine wanda zai yi wanka. Wannan
jahilci har ina!.
Abubuwan Da Janaba Ke Hanawa: Bai halatta
ga wanda yake da janaba ba ya shiga
masallaciba, ko kuma ya karanta Alkur'ani ba,
sai aya daya ko biyu domin neman tsari.
Mutumin da yasan ba zai iya taba rowan
sanyi ba to malamai sunce kada ya kusanci
iyalinsa sai ya tanadi abinda zai dumama rowan
dashi, kamar hita, risho ko itace…'.
(2) Daukewar Jinin Al'ada: Abu na biyu cikin
abubuwan da suke wajabta wanka shine
daukewar jinin al'ada, kenan idan jinin al'adar
mace ya dauke to abu na farko dake gabanta
shine wanka. Bayanai akan abinda ya shafi jinin
al'ada da hukunce-hukuncensa da alamar
daukewarshi da izinin Allah za su zo nan gaba,
mudai sani idan jinin al'ada ya dauke to dole
mace ta yi wanka, kuma zuwan jinin al'ada
lamace dake nuna wannan mai jinin ta balaga
musamman ace shine zuwansa na farko a
wurinta, bayanai dai za su zo da izinin Allah.
(3) Daukewar Jinin Biji: Wannan shine abu na
uku daga cikin abubuwan da suke wajabta
wanka, watau daukewar jinni haihuwa, da zarar
mace ta ga jinin haihuwa ya dauke mata ko da
ranar data haihune to wanka ya wajaba akanta
domin ta fara sallah, ba wanda yace sai mai
jego ta yi kwanaki arba'in kafin ta kama sallah,
shima bayai akan jinin biji zai zo da izimin mai
duka shine Allah, kawai mu sani anan daukewar
jinin haihuwa yana wajabta wanka.
(4) Mutuwa: Mutuwa tana wajabta a yiwa
wanda ya mutu wanka, shi kuma bayanai kan
abinda ya shafi wankan da yadda ake yinsa zai
zo ne alokacin da za'a kawo bayanai kan
jana'iza da izinin Allah, kuma Allah ya kaimu
lokacin, abinda ake so a fahimta anan shine
idan mutum ya mutu to dole ayi mishi wanka
sai dai idan shahidine da ya rasu a fagen fama.
(5) Musulunta: Wannan yana cikin abinda
malamai suka karawa juna sani, shin idan
wanda ba musulmiba ya musulunta wajibine sai
ya yi wanka? Wasu sukace wajibine domin
Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi- ya umarci wasu da suka
musulunta da su yi wanka, su kuma wadanda
sukace ba wajibi bane wankan sunce ba'a
ruwaito cewa Ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- ya umarci dukkan
wadanda suka musulunta da cewa kowa sai ya
yi wanka ba.
Kammalawa: A yanzudai munsan abubuwan
da idan yada daga cikinsu ya faru to wanka ya
wajaba, kuma mun sami takaitaccan bayani
akan abinda ya shafi janaba, kama daga
hanyoyin da ake samunta, bayanan da zasu zo
nan gaba za su kun yadda wankan tsarki yake,
wato wankan janaba da kuma na daukewar jinin
al'ada (haila) da bambance-bancen dake cikin
su, Allah ya kai mu lokacin da sauran kwana da
kuma imani.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.

ABUBUWA BAKWAI MASU HALAKARWA.

Abubuwa Bakwai Masu
Halakarwa(Yiwa Mace Mumina
Kazafi)...

Mace Mumina Kazafi : A yanzu za mu yi
ni akan abu na bakwai kuma na karshe cikin
uwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da
cin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa
abubuwan da suke halakar da wanda yake
uli dasu , wannan abu shine Yiwa Mace
ina Kazafi .
fi Shine: Jifan mutum da aikata alfasha ta
ko kore juna biyu ko ma Da ba tare da ya
r cikakkun shaiduba.
Alokacin da mutum ya jefa kanshi cikin irin
nnan halayya ta kazafi to lalle ya jefa
a cikin halayyar da take halakarwa, domin
kazafi ba karamin bala'ibane, alokacin da
m ai wance mazinaciyace ko ya yi lalata da
o wannan ciknnanata bana mijintabane ko
a/'yarta ai bana mijinta bane to lalle ya
no tsuliyar dodo dole ya kawo cikakkun
u na mutane hudu maza musulmai da zasu
shaida akan hakan, idan kuma mai kawo
uba ko ya kawo basu cikaba to kowanne
m gada cikinsu bulala tamanin (80) za'a yi
, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba
n.
Wannan shiri da musulunci yake dashi
ramin shiri bane domin kare mutunci, masu
agana na cewa mutunci madarane in ya
bai kwasuwa, addinin musulunci yana daga
manyan manufofinsa kare mutunci, wannan
musulunci ya dauki irin wannan mataki
mmamma 'ya mace, domin alokacin da aka
mata suna to gaba daya anbata mata
arta, shi yasa ayoyin da suka yi Magana
kazafi sun anbaci macece basu anbaci
jiba wannanko ba wai dan hukuncin ya sha
n bane a'a hukuncin iri dayane ga duk
a ya yi mace ko namiji kazafi, kuma bai iya
cikakkakun shaiduba, idan ko ya kawo
u da duk abinda Shara'a ke bukata suka
to baza'a kira wannan da sunan kazafiba.
Yiwa mace mumina kazafi bai halattaba
yana cikin abubuwan da suke halakarwa,
da haka dadin fira ko kiyayya kada ta dauki
m ya yiwa wata/wani kazafi ko yasa a yi.
in Da Suka Yi Magana Akan Kazafi: Idan ka
ka kalli ayoyin zaka gansu kashi ukune
duk suna cikin Suratun Nur.
i Na Farko: Ayata: 4-5, Allah Madaukakin
yana cewa: ''Wadanda suke jifan mata masu
nkai (da zina) sannan kuma basu kawo
u huduba to ku yi musu bulala tamanin (80),
kada ku sake karbar shaidarsu har abada,
waddan sune fasiakai. Saidai kawai wadanda
tuba bayan haka kuma suka kyautata to lalle
mai yawan gafarane kuma mai yawan jinkai .''
nan Allah madaukakin sarki ya bayyana
ncin duk mutumin da ya yiwa mace/namiji
fi kuma bai iya kawo shaidu huduba sai
ya bayyana hukuncin da za'a yi masa. Abu
rko bulala tamanin (80), abu na biyu ba za'a
karbar shaidarsaba har'abada, abu na uku
wannan mutumin fasikine. Sai idan ya tuba,
anne malamai suke maganar shin inya tuba
ci gaba da karbar shaidarsa kuma shikenan
a fasiki bane? Amma ko ya tuba sai an yi
i bulala tamanin.
i Na Biyu: Ayoyin da suka yi bayanin
idan da ya yiwa matarshi kazafi kuma bai
awo shaiduba to shi tsinuwa za su yi da
r ta shi, Allah Yana cewa:
''Wadanda kuma suke jifan matansu (da
kuma ya kasance basu da shaidu saidai
kansu, to shaidar dayansu (itace) Rantsuwa
da Allah lalle shi yana cikin masu gaskiya *
tsuwa) ta biyar tsinuwar Allah ta haukanshi in
asance cikin makaryata. * Kuma abinda zai
ayi mata azaba (haddi) shine ta yi Rantsuwa
da Allah cewar lalle shi (mijin) yana cikin
ryata *. (Rantsuwa) ta biyar lalle fushin Allah
bbata akanta in (mijin nata) ya kasance cikin
gaskiya'' Surartun Nur, ayata: 6-8.
Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin
miji ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya
shaidu huduba to 'Li'ani'' za su yi. Amma
anda ba miji bane to kodai ya kawo sahaidu
ne hudu maza musulmai ko kuma ayi mishi
a tamanin, ba maganar shi wanda aka yiwa
fi wai ya rantse idan ba haka bane, ko kuma
a ya yi kazafin cewa ya rantse duk babu
i shaidu ko bulala tamanin.
Kashi Na Uku: Ayoyin da suka yi Magana
kazafin da aka yiwa mata muminai masu
nkai natsattsu kammalallu to wadannan
yiwa irin wadannan matan kazafi tsine
aka yi duniya da lahira. Allah madaukakin
yana cewa:
''Lalle dukkanini wadanda ke jifan mata
kamun kai gafalallu (daga aikata dukkanin
ha) wadanda suke muminai to an tsine musu
niya da kuma lahira, kuma suna da azaba
irma* Aranar da harsunannu za su bada
a akansu da hannayansu da kuma
uwansu ta sanadiyyar abinda suka kasance
aikatawa* Awannan ranarce Allah zai cika
sakamakonsu na gaskiya, kuma zasu sani
Allah shi wanda yake mai gaskiya kuma mai
anar da abubuwa''. Suratun Nur, ayata: 23-25.
Wannan ya nuna mana shi karankanshi
fin ya kasu kashi-kashi, kashi na farko shine
gama garin mutane wadanda suke suna da
awan halaye da kuma wanda ba'a rasaba,
ka anbaci hukunci yi musu kazafi a kashin
, sai kuma wanda ya kasance tsakanin miji
ata. Sai wannan kashi na uku, wanda mutum
a mace/namiji mai kamun kai mai addini
ttse mumini kawai ya antayo ashar ya
a mata/mashi ya dinga fadan wasu
nganu wanda da za'a tara mishi arzikin
a domin ya kawo shaida akan haka ba zai
. Domin wani ya dauka irin halin da yake
i to kowa haka yake, to kaga bayan ya kasa
wadannan shaidu za'a yi masa hukuncin
fi anan duniya sanna kuma ya jira ranar
ama, domin Allah baya bari a taba bayinsa
warai, Ya Allah ka samu daga cikinsu, ka
u da sharrin masharranta ka tsaremu ka
mana imanimmu, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun bayananan
ayyana agaremu yadda musulunci ya dauki
nci da daraja da kima ya karewa kowa
ncinsa musamman 'ya mace, domin idan ba
ba sai kowa ya fadi abinda ya ga dama ko
hi ya fada yana ganin bai huce aci
shiba, amma idan yasan zai sha bulalane to
ya naba'a yasan me zai fada, sai yazama
are mutuncinsa dana zuriyarsa kamar yadda
re mutuncin wani dana ziriyarsa.
Annanne kuma muka zo karshen wannan
a wacce take dauke da sharhin wannan
i da Abu Hurairata ya ruwaito daga wurin
ikin Allah na wadannan abubuwa bakwai
halakarwa, lalle ma'aikin Allah ya isar da
anci kuma tsira da amincin Allah su tabbata
reshi, hakika ta'amuli da wadannan abubuwa
as yana halakarwa kuma wannan kowa ya
ya tabbatar wannan zai kara imanine bisa
i. Akaro na gaba zamu kawo bayanne kuma
nda zasu haskaka mana rayuwarmu da
inmu, Allah ya kaimu wannan lokacin ya
mu da imani, aimn.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.

NAJASA DA HUKUNCE HUKUNCETA A MUSULUNCI

NAJASA DA HUKUNCE-
HUKUNCENTA

Bayanda a darasin da ya gabata aka kawo
bayanai da suka shafi ruwa, a yanzu za'a kawo
abubuwan da ake yi da ruwan, akan haka za'a
fara da najasa da yadda ake gusar da ita da
ruwa da sauran hukunce hukuncen ita najasar,
Allah Ya yi mana jagora amin.
Abubuwan Da Suke Najasa:
Na farko: Fitsari. (Na mutum) Na babba ko na
karami na mace ko na namiji, ya fara cin abinci
ko bai faraba. Na biyu: Bayangida (Kashi na
mutum). Na uku: Mushe, shine abinda ya mutu
da karan kansa, ko aka yankashi ta hanyar da
bata musulunci ba. Na hudu: Nonon dabbar da
ta yi mushe. Na biyar: Nonon dabbar da aka
haramta cin ta, kamar nonon karya, ko alade ko
jaka...' Na shida: Fitsarin dabbar da aka
haramta cin ta, kamar fitsarin jaki, ko kare…' Na
bakwai: Kashin dukkanin dabbar da aka
harantata, kamar kashin alade (alhanzir), kashin
jaka/jaki..' Na takwas: Kashi da fitsari na
dukkanin dabbar da take cin najasa. Na tara:
Giya. Na goma: Jini, saboda haka bai halatta a
tari jinin da aka yanka dabba ba wai ace za'a
gasa shi ko a soya ko ayiwa dabbobi abinci da
shi ba domin najasa ne (in banda jinin da ake
samu a cikin dabba bayan anyankata wanda bai
fitaba, ai dakyar a rasa jini a cikin dabba). Na
sha-daya: Ruwan ciwo. Na sha-biyu: Maziyyi,
shi kuma ruwane da yake fari yana da laushi
yana fitane lokacin motsawar sha'awa ta mace
ko namiji ta hanyar wasa ko kallo ko nitsewa
cikin tunani, amma idan sha'awa ta kara
karkafafa to maniyyine ke fita, shi kuma
maniyyi ana jin fitarshi sabanin maziyyi, sannan
shi kuma maniyyi yana da kauri sabanin maziyyi
shi yana da laushine, bayanai za su zo akan shi
nan gaba kada idan Allah Ya yarda. Na sha-uku:
Wadiyyi, shi kuma ruwane fari yana kauri sau da
yawa yana fine akarshen fitsari, ta sanadiyyar
daukar kaya mai nauyi, ko matsanancin sanyi,
ko kullewar ciki. Na sha-hudu: Ragowar ruwa ko
aminci na dabbar da ba'a ci, kamar rowan da
jaki ya sha ya raje, in banda mage. Na goma
sha-biyar: Yawun kare da na alade, ko na
dukkan babbar da ta samu ta hanyar su. Na
goma sha-shida: Amai, alokacin da canza daga
yanayin abinci, kenan idan aka ci abin ci yanzu
sai kuma aka harar da shi wannan harawwar ba
najasa bace. Wadannan sune abubuwan da suke
najasa, amma akwai wadansu da malamai suka
karawa juna sani akansu kan najasa ne ko ba
najasa ne ba, kamar ragowar ruwa na wanda ba
musulmi bane ya sha, hakanan akan maniyyi.
Shidai Maniyyi na namiji: Ruwa ne da yake
fari maikauri yana tunkudar junansa alokacin da
zai fita, idan ka shinshina shi ya yi kama da
hudar dabino, kuma ya yi kusa da kanshin kulli,
amma idan ya bushe yana kasancewa kamar
karnin fasasshan kwai. Wannan shine galibin
yadda maniyyin namiji yake kasancewa, wani
lokacin ya kanzo sabanin wadannan bayanai da
suka gabata. Yana fitane lokacin matsananciyar
sha'awa ta sanadiyyar kallo ko wasa ko
matsanancin tunani ko lokacin saduwa. Shi
kuma Maniyyin mace, shi ma: Ruwane fatsi-fatsi
yana da laushi. Wannan ya tabbatar da cewa
mace ma tana da maniyyi kuma da shi ne da na
namiji Allah Yake halitta da su.
Wasu malamai sunce maniyyi najasa ne
domin yana fitane ta mafitar fitsari wanda yake
shi kuma fitsari najasane, wasu malaman kuma
sukace ba najasa bane domin da shi ne Allah
Ya halicci dan'adam kuma a cikinsu akwai
Annabawa da Manzanni, kenan ya za'a mutum
da Allah ya karramashi da yaukaka shi har ya
fitar da Annabawa da Manzanni ace kuma da
najasa aka yi shi??. Wadannan sune abubuwan
da suke najasa da kuma wadanda malamai suka
yi wa juna Karin fahimta.
Hukuncin Najasa:
Wajibine gusar da najasa daga jiki da tufafi da
wurin da za'a yi sallah, idan mutum yana da
ikon gusar da ita kuma yana sane bai gusar da
ita dinba ya yi sallah da ita to ba shi da sallah.
Addinin musulunci addinin tsaftane abinda
musulunci yake so shine akoda yaushe ka
sance cikin tsarki, mafificin tsarki kuma shi ne
tsarkin zuciya a kakkabeta daga barin shirka da
zalinci da hassada da munafunci da dukkan
wata mummunar dabi'a, idan aka samu tsarkin
zuciya kuma ga tsarkin tufafi da ganganjiki da
kuma mahalli to lalle wannan shi ke nuna
kammaluwar mutum.
Yadda Ake Gusar Da Najasa:
Idan ka ga inda najasar take a jikinka ko a
tufafinka to iya inda yake iya nan zaka kama ka
wanke, sabanin yadda wasu matan suke yi wai
dukkanin tufafin da tasa alokaci da take al'ada
to sai ta wanke su, kama daga dankwali da zani
da riga…' wannan musulunci bai zo da shi ba,
inda kwai kika ga jini iya nan kawai za ki
wanke. Idan kuma najasar ta rikice maka baka
ganta ba, amma ka tabbata akwaita ajikin
tufafin na ka shikenan sai ka wanke tufafin
gabadaya. Amma idan najasa ta fantsamo sai
kake kokwanton ta tabaka ko bata taba ka ba,
kuma kai baka ganta ba kuma ka duba mai
Ahlari yace sai ka yayyafa ruwa a wurin.
Amma kuma idan wani abu ya fallatso maka
sai kake kokwanto wannan abun najasane ko ba
najasa ba ne, to awannan lokaci ba wani
hukunci akanka, ba yayyafa ruwa ballantana
wankewa, domin mafiyawan abubuwa masu
tsarki ne, najasa kadanne shi yasa ake iya
lissafe su.
Idan inda najasar take kuma filine ko bango
ko wani dutse sai aka yi ruwan sama ko kuma
aka kwarara ruwa mai tsarki akai shikenen an
gusar da wannan najasar. Amma idan ta kasace
yawun karene wato karene ya baki a kwano ko
a kwarya to za'a zubar da abinda yake ciki
sannan a wanke sau bakwai sannan asa kasa a
daya daga cikin bakwai din. Amma najasar da
ba wannan ba sai a wanke ya wanku sabanin
yadda ake yi, da yaro ya yi fitsari sai ace wai
za'a yayyafa ruwa alhali wankewa akace a yi,
wani ruwamma da aka yayyafa kamar karawa
fitsarin yawa aka yi, Allah ya sawwake. Ya
zama wajibi a tshi tsaye a gusar da najasa a
tsaftace muhalli, musulmi ya kasance
tsaftattace tsafta cikon addini ai ta fi ace ita
ciko ce, ita sharadice sai mutum ya tsarkaka
daga wadannan najasar ibadar shi zata karbu.
Abubuwan Da Najasa Take Hanawa:
Anan za'a anbaci wadansu abubuwa ne da basu
halatta ga dukkan mara tsarki ya aikata su
saboda darajarsu da matsayinsu, kuma hadasin
babbane ko karami, wadannan abubuwa sune:
(1) Taba Alkur'ani: Bai halatta ga mara tsarki
ya taba Alkur'ani, har sai ya yi tsarki inda so
samune ma ya yi alwala musamman idan ya
kasance ba mai yawan daukan Alkur'ani bane.
(2) Sllah: Hakanan bai halatta ga mara tsaki ya
yi sallah ba farillace ko nafila, har sai ya
tsarkaka ya kuma yi alwala, kamar yadda
Ma'aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi- yace: '' Allah ba zai karbi sallar wanda
ya yi hadasiba har sai ya yi alwala'' Bukhari:135,
Muslim:225. Hakanan kuma ko da mutum yana
da tsarki amma tufafinsa ko wurin sallar baida
tsarki to delene ya tsarkake su kafin fara sallar,
saidai idan bai saniba ko ya manta cewa a
tufafinsa ko wurin da ya yi sallah akwai najasa
sai kuma da lokacin sallar ya fita sannan ya
gani ko ya tuna to anan ba komai sallar shi ta
yi.
(3) Tawafi: Kuma dukkan mutumin da bashi da
tsarki to bai halatta ya yi Tawafin Ka'aba ba,
daman kuma ananne kadai ake dawafi a sararin
duniyar nan.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka
gabata munsan abubuwan da suke najasa ta
yadda ko yanzu akace ka kawo biyar zaka iya
cikin gaggawa, da kuma hanyoyin da akebi
wurin gusar da wannan najasa, wanda yake
gusar da ita din wajibine domin munji abubuwan
da bai halatta mara tsarki ya yi ba, akaro na
gaba zamu kawo bayanai akan wadansu
abubuwa da ake ganinsu kamar najasane alhali
kuma ba najasa bane.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.