Wednesday, 17 October 2018

012 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha biyu 012_

Gabatarwa; *UMMU SINAN*

*ABUBUWAN DA BASU HALATTA GA MAI AL'ADA;*

A wannan karon zamu lissafa abubuwan da basu halatta mace mai al'ada ta aikatasu ko a aikata mata, abubuwan sune kamar haka;

1⃣ *SALLAH;*
Baya halatta mai al'ada ta yi sallar
farilla ko nafila, idan kuma tayi, ta yi ba'a karba ba, sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta
kammala al'adar ba zata rama sallolin ba.

2⃣  *SAKI;*
Baya halatta matar da take al'ada a sake ta, wannan ya sabawa karantarwar
musulunci, saboda haka koda yana son ya sake ta to ya bari sai ta kammala al'ada kafin ya sadu da ita sai ya sake ta, amma idan ya sake ta tana jinin al'adar to sakin ya yi amma
za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai uku ba.

3⃣ *DAWAFI;*
Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin
Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsayuwar Arafah da
kwanan mina dana muzdalifa da jifa da
Labbaika, da daidai sauransu.

4⃣ *ZAMA A MASALLACI;*
  Mai al'adah ba zata zauna a cikin masallaci ba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu(SAI DA KWAKWARAN DALILI).

5⃣ *AZUMI;*
Baya halatta mai al'ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yi ba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta rama su.
  Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo,
amma dazaran ta zo to ba azumi.

6⃣ *TABA ALQUR'ANI;*
Mai al'ada bata taba ALQUR'ANI,
kasantuwar sa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.

7⃣ *KARATUN ALQUR'ANI;*
Mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duk da cewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karanta daga abunda ta haddace domin kada ta manta sabanin dauka.

8⃣ *SADUWA;*
Baya halatta saduwa da mace
a lokacin al'ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu
da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa Allah ba hasali ma ta yi biyayya ne ga reshi, baya halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai
al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al'adar ta dauke amma batayi wanka ba to bai halatta a sadu da ita ba. Ya
halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa a lokacin da take al'ada bayan ta yi
*kunzugu* in banda daga *cibiyarta* zuwa *gwiwarta*
wannan kam bai halatta ba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta
taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.

9⃣ *TABBATAR DA RASHIN TSARKI;*  Al'ada tana
tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.

🔟 *WAJABTA WANKA;*
  Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANI AKAN JININ BIKI(JININ HAIHUWA) INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

Monday, 15 October 2018

011 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na sha daya 011_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*


*ALAMOMIN DAUKEWAR JININ AL'ADA;*

Idan jinin al'ada ya dauke akwai wasu  alamomi da shari'ah ta sanya domin su zama manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, ga alamomin kamar haka:

1⃣ *BUSHEWAR GABA;*
Abunda ake nufi shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gaban ta, sannan ta fito dashi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata
al'adarta ta dauke.

2⃣ *FARAR KUMFA;* 

Wannan wani ruwa ne fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka karshen al'adar ta, ta sani ta kammala Al'adar ta.

Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba yin al'ada ba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki, ba sai ta jira farar kumfa ba, amma idan wacce ta saba gani ce sai ta ga bushewar gaba to malamai suka ce zata dan saurara kadan domin jiran farar kumfa, amma jinkirin ba zai kai
ga fitar zababbun lokutan sallah ba.

    A dunkule dai kowane daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu a lokaci
guda ba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai kiyi wankan tsarki domin ki cigaba da
ibada, domin idan ba kiyi wanka ba ko da jinin ya dauke mijin ki ba zai sadu da dake ba kuma baza kiyi  sallah ba, da dai sauransu.

Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga - diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jini ne, amma idan a karshen jini ne to wannan ba komai,
Ummu Adiyyah matar Manzon Allah  (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: *((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)).* [Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368 , Ibnu Majah Hadisi Na: 647,
Darimi Hadisi Na: 865].

Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar
asuba, amma ba'a ce ta tashi cikin dare ba domin ta duba.!!!

 

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ABUBUWAN DA BASU HALATTA GA MAI AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*

http://wa.me/+2349031666613

010 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na Goma 010_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*


*KARKASUWAR MATA GAME DA JININ AL'ADA:*
    Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; *WACCE TA FARA,* Kashi na biyu kuma; *WACCE TA SABA,* sannan sai kashi na uku; *MAI JUNA BIYU,*
mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka;
1⃣ *WACCE TA FARA;*
  Ita wacce ta fara al'ada ya zama shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwar ta, to abunda ke kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zai  dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha- biyar ba,(KAMAR YADDA BAYANI YA GABATA A RUBUTUKAN DA SUKA GABATA) idan ko ya wuce sha-biyar to abunda ya
doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'ada ba, kenan mafi yawan kwanakin da zata yi la'akari dasu sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama abunda ake kira
*(Isthala)* wato cuta sai a nemi magani, a karkashin wannan nake cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu mata su rika tuntubar su suna fahimtar da su
tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci yayi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka,ko makaman tan hakan Wanda wannan Na faruwa kwarai da gaske, wata babbar mace ce amma bata san menene jinin al'ada ba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganin shi,  kunga akwai hadari kwarai da gaske.

2⃣ *WACCE TA SABA:*
Abunda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku, a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai yayi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai a kira ta da sunan
wacce ta saba, domin ta saba akan kwanaki sanannu.
  Amma idan ta yi al'adar karo na farko
kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar
karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da
tsayayyun kwanaki.
  Ita wacce ta saba wato wacce take da
sanannun kwanakin al'ada to wadannan
kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada,
amma idan kwana kin suka cika al'adar kuma bata dauke ba sai ta kara kwanaki uku,haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki sha biyar su cika, misali idan al'adar ta kwanaki biyar ne sai kuma jinin bai dauke ba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan kwanaki takwas din sun zama sha-daya idan bai dauke ba sai ta kara uku sun zama sha-hudu idan bai dauke ba sai ta
kara kwana daya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai dauke ba domin kwanakin al'ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma
sun cika, abunda ya cigaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada ba,sunanshi jinincuta *(Istihala)*
  sai a nemi magani.  A dukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na
saurare sai ya dauke a kwana na daya cikin ukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

3⃣ *MAI JUNA BIYU(mai ciki);*  Galibin mata masu
juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga
al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita.
  Idan al'ada ta zowa mace mai juna-biyu, to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin
al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata
iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan
Kina da juna biyu kuma kika ga jini.

   *TANBIHI NA DAYA:*
   Idan mace jini yana mata wasa wato yazo yau ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abunda zata yi anan shine, ta tsaya ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki
domin da hakane zata cika kwanakin ta na al'ada, *MISALI,* kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki tara, wannan matar ita
ake kira *(Al-Mulaffiqa)* a larabcin mata masu
al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da
dawowarsa to na biyun zai zama sabon jini ne kenan, ba na da ne ya dawo ba.


ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN ALAMOMIN  DAUKEWAR JININ AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE:

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

009 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na Tara 009_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*TABBATUWAR JININ AL'ADA;*
     Shifa abinda ya
shafi jinin al'ada al'amari ne da Allah madaukain sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa:

```''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada,
Kace: Shidinnan cutane, ku nisanci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke), idan suka tsarkaka
(suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba
kuma yana son masu tsarkaka''.```
*[Bakara, ayata:222.]*

Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; ```(Wannan)
Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan
Adam''.```
> Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci
a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane
ya rike masa makoshi(makogaro) sai ya amayar da ganyen shi yasa maza basa yi.
   Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar.

Shifa jinin al'ada kada amanta jini ne da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu,
Allah madaukakin Sarki ya halicceshi domin ya zama abinci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da
mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sai Allah ya sanya shi ya zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga
mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada.

Idan kuma ta haihu sai Allah ya mayar dashi nono jaririn yana sha amatsayin abinci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata
da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya
kasance ba inda zaije(jinin al'adar) to shine sai ya taru a
mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko
bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan (kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah).

ZAMU TUQE A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANI AKAN KARKASUWAR MATA AKAN JININ AL'ADA INSHA ALLAHU

ALLAH YAYI MANA JAGORA

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE;

✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

008 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na takwas 008_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*

*MINENE MAFI QARANCIN JININ AL'ADA?*
   Malamai sun karawa juna sani
kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.

*MINENE MAFI YAWAN JININ AL'ADA?*
  Mafi yawan kwanakin jinin al'ada shine kwanaki goma sha-biyar, kenan idan ya
wuce haka to bai zama jinin al'ada ba muddin ba ciki take da shiba.

*MATA DANGANE DA JININ AL'ADA:*

  Anan ya kamata mu san cewa mata
suna da halaye biyar musamman idan muka yi
la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya
zo na al'ada ne ko bana al'ada bane, halayyar itace kamar haka:

1. *KASA DA SHEKARA TARA;*    Idan jini ya zowa
yarinyar da take kasa da shekara tara, to malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada bane, jinin ciwone sai a nemi magani.

2. *SHEKARA TARA ZUWA SAMA;*    Idan ya  zamana jinin ya zo ne
ga wacce ta cika she kara tara zuwa zamanta budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi
kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin na al'adane ko na ciwo.
Kada mu sha'afa
yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da
hutu da wahala suna tasiri a irin wannan wuri.
3. *BUDURCI ZUWA SHEKARA HAMSIN;* 
  Idan jini yazo
daga lokacin da ta zama budurwa zuwa shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun
tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.

4. *DAGA SHEKARA HAMSIN ZUWA SITTIN DA TARA(50-69);*
  Idan jini ya zowa mace a tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara
hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai sukace za'a tambayi kwararrun mata da likitoci domin sanin wannan jinin na ciwone ko na
al'ada.

5. *DAGA SHEKARA SABA'IN ZUWA SAMA;*
  Idan jini ya zo bayan mace ta cika
shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai sukace wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane.
Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce-hukunce akansu, kuma ana gini ne akan tsarin
kalandar musulunci, wadannan bayanai na karkasuwar mata har zuwa gida biyar kamar yadda ya gabata haka *MALAM ADAWY*
  ya kawo a cikin littafinsa *'Hashiyatul Adawi'*, Allah ya ji kansa da gafara.

  Ina Kara jaddada cewa yanayin abin ci da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri
matuka, dukkan abinda ba'a mahimta ba
dangane da yana yin zuwan jini ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi
tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi
bayani da cewa yanada alaka da hukunce
hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da
aka *SAKI* zata iya kammala idda a kasa da watanni uku.
Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shine zuwansa na farko sannan ya tabbata
cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga,
dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau
kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta mata lada idan kuma ta bari samari suna
jagwalgwalarta ita za'a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara yi mata rubutu, kenan har azumi idan ta sha sai ta ranka.


ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA INDA ZAMUYI BAYANIN TABBATUWAR JININ AL'ADA INSHA ALLAHU.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE;
✍ *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

007 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na bakwai 007_

Gabatarwa: *UMMU SINAN*



*HUKUNCIN JININ AL'ADA ( JININ HAILA)*

Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama
mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad s.a.w, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya.
   Bayan haka a yanzu kuma muna
daukene da abinda ya shafi jerin hukunce-hukuncen jinin al'ada wanda ake kira jinin haila,
da izinin Allah bayanshi za mu
kawo hukunce-hukuncen jinin biki (wato jinin
haihuwa).

*Muhimmanci:*   yana da matukar muhimmanci sanin hukunce hukunce jinin al'ada, muhimancin
bawai ya tsaya ga mata bane kadai, a'a har da maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada, misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko
dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta
bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a
sakinta ba kuma a saduwa da ita, sannan ga yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta
yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku
(al'ada uku) kafin ace ta kammala idda, sannan sai ai maganar sabon aure, to idan tana
al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan
sai bayan shekara daya da rabi za'a fara maganar aure, shi yasa muka ce sanin hukunce-hukuncen wannan jini ba wai ya rataya ga mata bane kadai har da maza.

*MINENE JININ AL'ADA:???*

    Jinin al'ada jinine da yake fita da karan kansa ta gaban macen da a
al'adance zata iya daukar ciki, ba tare da ya wuce
kwanaki goma sha-biyar ba.

Wannan shi ake nufi da jinin al'ada, da akace *'jinine da yake fita da kansa'* kenan idan ya
zamana ba da kansa ya fita ba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jini
ya balle mata to wannan bai zama jinin al'adaba.
   Da akace *Ta gaba*' kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al'adaba.
  Da akace *'Wacce a al'adance zata iya daukar ciki'* kenan idan ya fita daga wacce a al'adance ba zata iya daukar ciki ba sabo da
yarinta ko girma to wannan shima bai zama jinin al'adaba.

Amma da aka ce *'Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba'* kenan idan ya wuce kwanaki
sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba.

Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin
al'adaba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau kansu ba, za su yi sallah domin jinin ciwone sai a
nemi magani, Allah ya sawwaka.

ZAMU DAKATA A NAN SAI LOKACI NA GABA, INDA ZAMUYI BAYANIN MAFI QARANCIN JININ AL'ADA.

ALLAH YAYI MANA JAGORA.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE; *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy ( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

006 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN; *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na shida 006_

Gabatarwa: *UMMU SUNAN*

🔸 *DAGA CIKIN ABUBUWAN DAKE WAJABTA WANKA.*

1⃣  ```FITAR DA MINIYYI TA HANYAR SHA'AWA, A CIKIN BARCI KO A FARKE.```

2⃣ ```SADUWA DA IYALI(JIMA'I)```

3⃣ ```FITAR JININ HAILA(Al'ada) KO NA BIQI(Na haihuwa)```

4⃣ ```MUTUWA```

✍ *AL-ALLAMA SHEIKH MUHAMMAD BIN SALIH AL-UTHAIMIN*
(RAHIMAHULLAH) YAKE CEWA;

1⃣ *FITAR DA MANIYYI TA HANYAR SHA'AWA, A CIKIN BARCI KO A FARKE;* Duk Wanda ya fitar da maniyyi a cikin barci, wanka ya wajaba a gareshi, saboda Wanda yake barci yana mafarki, idan mafarkin yasa ya fitar da maniyyi, yana wajaba yayi wanka a kowane hali.

2⃣ *SADUWA(JIMA'I);*
    Idan miji ya sadu da matarshi, yana wajaba wanka a garesu, saboda boyuwar hashafa a cikin al'aurar matarshi, saboda fadar manzon Allah s.a.w cewa;

➡ << Ruwa daga ruwa suke>> Ma'ana: wanka yana wajaba a lokacin da namiji ko mace suka fitar da maniyyi.

➡<< Idan miji ya zauna tsakanin gabobinta guda hudu(matarsa) kuma yaji dadi da ita, wanka ya wajaba a garesu, koda basu fitar da komai ba, wannan matsalar(SADUWA BA TARE DA FITAR DA MANIYYI BA) da yawa daga cikin mutane suna jahiltar wannan hukuncin, ta inda wasu mazan suke amfani da yatsunsu a wajen saduwa da iyalansu ba tare da fitar da maniyyi ba sai suki yin wanka saboda jahilcin dake addabarsu, Malam yace wannan al'amari akwai hadari a cikinsa kwarai da gaske, abunda yake wajibi shine mutum yasan cewa idan ya sadu da iyalansa koda bai fitar da komai ba, wanka ya wajaba a garesu(mijin da matar).

3⃣ *FITAR JININ AL'ADA KO NA HAIHUWA;*
   Ita mace idan HAILA tazo mata sai ta dauke, yana wajaba tayi wanka, saboda fadar Allah S.W.T;
  "KU NISANCI MATA A LOKACIN DA SUKE HAILA, KADA KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI, IDAN SUNYI TSARKI TOH SAI KUZO MASU TA INDA ALLAH YA UMURCEKU, LALLAI ALLAH YANASON MASU TUBA, KUMA YANASON MASU TSARKAKEWA".
  Da fadar Manzon Allah s.a.w cewa; " MAI HAILA IDAN TA KARE KWANAKIN HAILARTA, DA MATA WADANDA SUKA HAIHU IDAN JINI YA DAUKE MUSU, NA GARESU SUYI WANKA."

  Siffar yadda ake wankan haila da na haihuwa kamar siffar yadda ake na janaba yake, sai dai wasu malaman sun so a wankan haila ko haihuwa ayi da ganyen magarya, saboda shi yafi a wurin tsafta da tsarki.

4⃣ *MUTUWA;* Dalili akan wankan gawa shine fadar Manzon Allah s.a.w cewa; "KU WANKE TA SAU UKU, KO SAU BIYAR KO SAU BAKWAI KO FIYE DA HAKA IDAN KUNGA YIYUWAR HAKAN.....HADITH

Da fadar Manzon Allah s.a.w cewa; " KU WANKE SHI DA RUWA, DA GANYEN MAGARYA, KU RUFESHI DA TUFAFINSA"...(mutumin da ya mutu a arfa a lokacin Manzon Allah s.a.w)

Sai Malamai sukace; Su wadanda suka mutu, wanka Na wajaba garesu, sai sai dai wajabcin yana hawa akan yan uwansu rayayyu, saboda shi Wanda ya mutu komi nashi ya yanke, bazai iya aikata komai ba, saboda haka yan uwansu dake raye su zasu yi musu wanka, kamar yadda Manzon Allah s.a.w ya umurta da yin haka.

▪_________________
◼ *Majmu'u fatawa warrasa'il Na Sheikh Muhammad bin Salih Al-uthaimin, Mujalladi Na sha daya, babin wanka.*

SAI WANI LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE; *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU~SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

005 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA GROUP DIN *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na biyar 005_

Gabatarwa: *UMMU-SINAN*

*ABUBUWAN DA RASHIN TSARKI YAKE HANA AIKATAWA;*

    kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki
wajibine, to mu sani idan mutum bashi da tsarki baya halatta a gareshi ya aikata wadannan abubuwan da zasu zo;

1. *SALLAH:*
    Baya halatta ga wanda bashi da tsarki yayi sallar nafila ko farillah.

2. *SUJJADAR TILAWA:*

  Wato sujjadar da mutum zai yi idan yana karatun Alkur'ani mai girma sai ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki, duk da cewa malamai sun karawa juna sani akan wannan.

3. *DAUKAR ALQUR'ANI MAI TSARKI:*
     Idan mutum
bashi da tsarki to sai yayi tsarki kafin ya taba wannan littafi mai tsarki.

Wannan shine abunda ya sawwaka insha Allahu.

*A GABA ZAMUYI BAYANI AKAN HUKUNCIN JININ AL'ADA INSHA ALLAHU*


WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE: *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

004 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA ZAUREN *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na hudu 004_

Gabatarwa: *UMMU-SINAN*

*CIGABA DA KAWO LADUBBAN ZAGAYAWA FITSARI KO BAYAN GIDA*

11. *KAUCEMA RAMI;*
    Ba'a yarda idan za ka yi fitsari ko bayan gida ka yi a rami ba sai dai idan
kai ka haka ramin, domin bakasan mike cikin ramin ba,
takan yiwu akwai mugun abu da zai iya cutar da kai.

12. *KAUCEMA WURAREN TSINUWA;*
    Wadannan wurare sune wuraren da mutane suke yawan
tsinema duk wanda ya yi musu bayan gida a wurin, wadannan wurare sune:
🔹 Inda mutane suke zama su huta, jikin bangone ko karkashin bishiya komadai inane.

🔹 Kan hanya: Akwai rashin mutunci mutum ya
zo kan hanya yayi bayan gida, wannan
dabi'a musulunci bai yarda da ita ba.

🔹 Mashayar ruwa: Hakanan baya cikin
karantarwar musulunci mutum ya zo inda al'umma suke diban ruwa rafi ne ko wani gulbi
ko gindin fanfo koma dai inane ya aikata wannan
ta'asa.
 
      Wadannan wurare uku musulunci ya
hana a aikata wannan danyan aiki a wurin, domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah ya tsaremu.

13 *NESA DA JAMA'AH;*
  Ana bukatar dukkan wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta
yadda ba za su ganshi ba kuma ba za su ji nishin shi ba, bai dace ace kana bayan
gida mutane suna ganinka ko suna jin nishinka ba,
ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka
boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba.
14 *KADA KA FUSKANCI ALKIBLA;*
    Wato inda
mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya
juya mata baya, wannan idan a dajine, amma
idan a gidane to da sauki babu laifi.

ZAMU TSAYA A NAN SAI LOKACI NA GABA ZAMU KAWO ABUBUWAN DA RASHIN TSARKI YAKE HANA AYI SU INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE: *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MAKUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

003 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE,  DAGA ZAUREN *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na uku 003_

Gabatarwa: *UMMU-SINAN*

*LADUBBAN ZAGAYAWA FITSARI KO BAYAN GIDA*

   Akwai tsari da ladubba da musulunci yake da su a lokacin da mutum ya ke niyyar kewayawa, wannan zai nuna maka cewa musulunci yayi bayani akan komai, daga cikin ladubban akwai;

1. *AMBATON SUNAN ALLAH*

  Ana bukatar kafin ka shiga ka ambaci sunan Allah domin ba'a ambaton Allah a makewayi, kuma ka nemi Allah ya tsareka da
sharrin aljanu, domin irin wadannan wurare
matattarace ta su, kafin ka shiga sai ka fadi:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ
ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ

Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina
neman tsarinka (Ka tsareni) daga sharrin aljanu maza da kuma aljanu mata. Idan kuma zaka fito sai kace:

ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ
ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ

Ma'ana: Ina neman gafarar Ka , Dukkan godiya
ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.

Ka sani ba'a shiga bayi da dukkan wani abu da yake dauke da sunan Allah.!!!

2 Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga, kafar dama kuma lokacin fita.

3 *AYI A TSUGUNNE;*  
kada mutum ya yi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitsarin ya fallatso masa,
sannan ba wanda zai ganshi, sai ya yi a tsaye.

4 *TABBATUWA A CIKIN SUTURA;*
   Ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye, sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga
suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar
wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko
unkula da wasu suke nunawa na bayyanar da
al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan
bai daceba, sai ka ji wani yace 'Ai duka
mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan
ba koyarwar musulunci bace, haka suma mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube
suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda, haka suma mata, wai sun dauka abinda yake
haramun shine namiji ya ga al'aurar mace ko mace ta ga al'aurar namiji, kai wani lokaci kana
tafiya a cikin mota sai kai arba da wani
gabjejen kato yana wanka a rafi, wani kuma a gefen titi ya kafe mashin ko ya aje kayan tallansa, duk wadannan ba kyawawan halaye
bane, mutum musulmi ya nisance su.

5 *MUTUM YAFI BADA KARFI A KAFARSA TA HAGU;*
Kenan abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da karfinsa a kan kafarsa ta hagu.

6 *YA BUDE TSAKANIN CINYOYINSA;*
  kenan kada ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai
fita, sannan idan ya mayar cikin wando sauran
ya gangaro, Allah ya sawake.

7  *NISANTAR INDA RUWA YAKE;*
  musulunci bai
yadda mutum ya yi fitsari ko bayan gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai haifar da cututtuka.

8 *ANA SO MUTUM YA RUFE KANSA;*
  Ana son wanda yake bayan gida ya rufe kansa a daidai lokacin da yake yi, domin koda wani ya yi kuskuren ganinsa to shi bai ganshi ba, abin zai zo da
sauki, amma ba zaka ji dadi ba kana bayan gida ka hada ido da wani, wanda zai iya zama
dalibinka ne ko suruki ko da..,'

9 *KADA AYI MAGANA;*
  An hana mutum yana bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai
dalili mai kwari, kamar ka ga makaho ya nufi
rijiya ko karamin yaro…'.

10 *KADA A TARI ISKA;*
An hana idan mutum zai yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari iska,
domin zai busowa jama'a warin bayan gidansa, kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska
take kadawa.
.............

ZAMU TSAYA A NAN SAI LOKACI NA GABA ZAMU KAWO MUKU SAURAN LADDUBBAN INSHA ALLAHU.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE: *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN;

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

002 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE, DAGA ZAUREN *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na biyu 002_

Gabatarwa: *UMMU-SINAN*

*HUKUNCIN TSARKI A MUSULUNCI*

     Tsarki wajibine, saboda haka
dukkan wanda dayan wadancan abubuwan da muka lissafa a rubutun daya gabata
suka same shi to dole yayi tsarki.

*ABUNDA AKE TSARKI DASHI:*  
   
   Abinda ake tsarki dashi a shari'ah shine ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, wannan shi ake kira Istinja'u .

Saidai idan mutum bai sami ruwan ba sai ya yi da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na
ukun ya fito a bushe ba wata laima shikenen, idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai
biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan kuma
ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan
ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan
hukunci shi ake kira Istijmari , ka samu ka hada duka a lokaci guda, misali idan ka yi bayan gida
sai kasa tsinke ko takarda mara rubutu sai ka share sannan sai ka biyo shi da ruwa. Kenan
ba'a tsarki da yawu (miyau).
Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da abinda ya fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a raba tsarki zuwa gida biyu:

(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin abinda ya fita daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari,
maziyyi…'.

(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake abinda ya taba jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko
wannensu baya yiwuwa saida ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.
Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin
girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:

(1) Babba wanda ake kira Hadasul Akbar:
Ankira shi babbane domin ba'a tsarkaka daga gareshi sai an yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko
saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki.

(2) Karami wanda ake kira Hadasul Asghar:
wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar
fitsari ko maziyyi.
Yadda ake yi: Da farko mutum ya wanke
hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai
wanke, domin hannun sa ya koshi da ruwa,
sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan
kuma sai ya fara wanke wurin bayan gida, ana bukatar mutum
ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman
idan maziyyi ne ya fita.

Insha Allahu zamu dakata anan sai wani lokaci Na gaba zamu tashi bayani akan LADUBBAN SHIGA BAYAN GIDA/MAKEWAYI(TOILET).



WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE: *Hashim Siraj Uba ats-tsamawy( _ABU-SINAN_ )*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN:

*MUKYAUTATA NIYYA*
http://wa.me/+2348064734911

*KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH*
http://wa.me/+2349031666613

001 MU KOYI IBADA A SAUKAKE

📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
MU KOYI IBADA A SAUKAKE,
DAGA ZAUREN *MUKYAUTATA NIYYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖

_Fitowa Na daya 001_

Gabatarwa: *UMMU-SINAN*

*MUKADDIMA*

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki Wanda ya wajabta mana tsarki, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w Wanda ya karantar damu yadda zamuyi tsarki.

_Bayan Haka;_
Insha Allahu kamar yadda muka alkawarta muku cewa zamu fara kawo muku karantarwa akan ibada da sauransu, yanzu zamu fara daga yau har zuwa lokacin da muke iyawa insha Allahu.
Mun tsara Abubuwan daki-daki, zamu fara da magana akan tsarki kafin sauran, zamuyi kokarin ganin kullum munyi sau daya, filin tambaya a bude yake insha Allahu.

*TSARKI DA YADDA AKE YINSA A MUSULUNCI*

*Shimfida:*  Mu sani ya 'yan-uwa masu albarka,
wannan addini na musulunci addinine da yake
cikakken addini ta kowane bangare, bai takaitu
ga alwala da sallah ba kawai, ya shafi kowane bangare na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya
zamantakewa, kasuwanci taimakon juna, tsare-
tsaren gudanarwa dadai sauransu.
A yanzu zamu kawo bayanai da suka shafi tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin tsarkin yake jawowa? Ya ladubban yin tsarkin
suke? Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran wadansu batutuwa da suke da alaka da wannan
maudu'i, da fatan Allah ya yi mana jagora ya
kuma fahimtar da mu.

*ABUBUWAN DA AKEWA TSARKI:*

Ana yin tsarki ne
daga dukkan abinda ya fito ta daya daga
mafita guda biyu ko ma ta duka inbanda hutu (tusa). Kenan ana yiwa fitsari, bayan gida maniyyi maziyyi jinin al'ada….tsarki, kawai dai idan mutum yana da alwala sai ya yi tusa to
alwalar kawai zai sake ba sai ya dauki buta ya yi tsarki ba.

Insha Allahu zamu dakata anan sai lokaci Na gaba.

WANDA YAYI BITAR RUBUTUN SHINE: *Hashim siraj uba ats-tsamawy(ABU-SINAN)*

DOMIN SHIGA GROUPS DIN:

*MUKYAUTATA NIYYA*
wa.me/+2348064734911

*KARATTUTUKAN MALUMAN SUNNAH*
wa.me/+2349031666613

Monday, 8 October 2018

SHAWARAR UMMU JURAIJ GA YAN UWA MATA

GAREMU MATA,SHAWARA CE KAWAI!!!.

Duba da yanda Allah ya halicce mu ,yasa nake ganin ya kamata mu Dan nutsu kadan mu gane muna da tawaya da kuma matsaloli a tare damu.
Duk inda aka duba koda Asibiti ko wurin magani za a tarar  mata munfi maza damuwa da kuma yawan lalurori.
Haka bangaren shedanci mata munfi yawa.
Sannan bangare tsafi da tsubbu mune a gaba.

Wani Malami Yace  "Idan Namiji ya zama Ustaz za a ga abin kamar wani abu gama gari,amma kafin mace ta zama ustaziya completely sai anci baqar wuya,zaka ganta dai kamar Ustaziya amma daga shedan ya Dan hura ta sai kaga ta zama wata qaramar shaidaniya ko 'Yar bori,amma Duk barnar 'ya mace indai akwai tsoron Allah a tare da ita da kuma ilimi kana fara Mata nasiha da wa'azi zata nutsu sa6anin wacce ta rasa wannan abubuwa guda 2,ita mace dole sai kayi haquri da wasu dabi ah NATA".Kuma na yarda da wannan maganar tasa,haka muke.

Hakan yasa naga ya kamata mudan riqe wannan domin samun nutsuwa a rayuwar mu ta yau da gobe,saboda yanda zamu ga mun zama abubuwan wasan  shaidanu,su shiga jikinmu sanda suka so su kuma fita sanda suka ga dama,Allah ya qare mu da lafiya baki daya.

Ki Tabbatar kina wadannan abubuwan koda kina da lalura ko baki da ita don Allah na roqeki.

*Karanta koda Rabin izu ne na Qur'ani kullum duk kasalarki ko simini 1 ki daure kiyi,a hankali zakiji kina qara yawan karatun idan kika saba,ko kinji kamar kin dauki dala da gwuron dutse idan za kiyi karatun ki fadawa zuciyar taki dole sai kinyi,don wata tace min " idan zata karanta Qur ani ji take kamar zata mutu".

*ki nemi (hisnul Muslim) Littafi ne,ki ajiye akusa dake ki duba a hankali akwai Azkar Wanda za kiyi da safe da kuma Wanda za kiyi da yamma,ko unguwa zaki je kidan  saka shi a jaka idan lokacin yi yayi ki dakko kiyi.

*Idan kika kama ruwa bayan fitsari ki Dan daure kiyi alwala ko ba ko da yaushe ba amma kidan dinga kokartawa kina yi.Zama da alwalan  yana da kyau koda kina Haidha kiyi.

*Yar uwa kina sallame sallar farilla ki karanta ayatul,kursiyyu,falaqi,Naasi,Qul huwal lahu(ikhlas)ko wacce 3,ki Dora da amanar rasul,barinma ki qara da subhanallahi 33,Alhamdulillah33,Allahu akbar33 ,ki yima Annabi (SAW)salati ,nan take zaki ji wani sanyi da nutsuwa aranki.

*Kin farka daga bacci kinyi Addu ah,zaki shiga ban daki kinyi addu'ah,zaki fito kinyi addu ah,zaki zauna kince Bismillah,zaki ci Abinci kinyi addu ah,kin gama ci kinyi Addu ah,zaki sanya tufafi koda bismillah kice,zaki cire Ki ambaci hakan,zaki fita daga gida kinyi addu ah,kin dawo zaki shiga gida kinyi addu ah,komai zaki yi na aiki ko baki iya addu arba,kawai ambaci "Bismillah".

*Ki Dan dinga zama kina Nazarin abubuwan da Ki kasan Haram ne ki kudirce fara ragewa,a hankali sai Allah ya dafa mana,kamar jin kada kada-kade,kallo mara amfani,sai fa muna ragewa Nasan muna son nishadi amma Reduction yayi a rayuwa,kamar zama ba dan kwali duk sai mun dinga kula ,Idan muna zaune bama komai muyi ta istigfari,hailala,salati da sauransu.

Guarantee na baki idan bakya yi ki fara daga yau zaki ji wani chanji na musamman acikin Duniyar ki.Allah yasa mu dace baki daya Ameen.

✍ummu juraij