Wednesday, 6 December 2017

ZUMUNTA A MUSULUNCI

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*_TATTARAWA:_*

*MALAM SANI LIMAN (ABU HURAIRAH) TSAFE*

_Fitowa Na biyu(002)_

```Bisimillahir-rahmanir-raheem, Alhamdulillah, bayan bayanin da ya gabata na ABUBUWAN DA WANNAN RUBUTU ya kunsa, yanzu zamu fada cikin bayanin Abu na farko.

MECECE ZUMUNTA???

  Ibn athir yana cewa zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen SU koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka. A daya bangaren kuma, yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya.

DA WANE ABU AKE SADAR DA ZUMUNTA???

Ana sadar da zumunta da al'amura masu yawa kamar; Ziyartarsu, bibiyar halayensu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi(wato su yan uwan da ya kamata a sadar da zumunta garesu), sannan kuma ana Sadar da zumunta da bada sadaka ga fakirai daga cikin su da tausasama mawadatan su da girmama manyansu da kuma tausayama kananan su da masu rauninsu da yawan tambayar halin da suke ciki, ziyartar su da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.

    Mafi girman abunda ake sadar da zumunta dashi shine; mutum yayi kwadayin kiransu((yan uwansa) zuwa ga shiriya ya umurcesu da aiki mai kyau ya kuma hana su aikata miyagun ayyuka.

   Haka nan zumunta bata da wani kayyadadden lokaci da aka kayyade don sadar da ita. Duk abunda al'ada ingantatta ta tabbatar a matsayin Sada zumunta, ana daukarshi a matsayin haka. Haka kuma duk abunda al'ada ingantatta ta tabbatar a matsayin yanke zumunta to ana daukarshi a matsayin haka.

   Zumunta tana bambanta gwargwadon kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumuntar zuwa garesu, zumuncin da yake tsakanin uba da dansa ya sha bam-ban da Dan uwa na nesa.

   Bugu da kari, zumunta tana banbanta gwargwadon halayen da su wadanda za'a sadarmawa suke ciki, kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka kuma sadarwa ga babba ta banbanta da ta karami

    Haka nan sadar da zumunta yana banbanta ta fuskar bagire, Wanda yake zaune a cikin gari ya banbanta da Wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi da tambayar halinda yake ciki, da yimasa sallama ko aika mashi da sakonni.

Zamu tsaya a nan, sai wani lokaci idan Allah ya kaimu insha Allahu.

Allah ya bamu ikon sadar da zumunta gwargwadon iko Amiin.

A gaba zamuyi bayani akan FALALAR SADAR DA ZUMUNTA insha Allahu.

Allah yayi mana jagoranci.

Copyright©
MASJID ABU HURAIRAH TSAFE SOCIAL MEDIA```
+2348064734911

BIDI'AR SHAFAR FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'AH


BIDI'AR SHAFAR FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A🙏
Ibn Rushud yace: an tambayi imamu malik akan mutumin da yake shafar fuska da tafukansa yayin kammala addu'a bayan ya shinfida tafukan kafin hakan?sai imamu Malik yayi inkarin haka,yace bansan wannan ba. nace (Ibn Rushud) Malik (R)yayi inkarin shafar fuska da tafukan hannu bayan addu'a domin yana ganin yin haka badi'a ne, domin babu wani asar daga manzon Allah yake nuna halaccin hakan kuma ra'yi baida mashiga a cikin
📚(albayan wattahsil 49/18)
Imam Abu Daud yace:naji an tambayi imamu Ahmad akan mutumin da ya ke shafar fuskar sa da hannunsa bayan ya kammala wuturi? Sai ya ce "bantaba jin wannan ba" a wani lokacin ma cewa yayi "bantaba jin wani Abu game da shiba". Abu Daud yace banga imamu Ahmad yana aikata hakan ba(ma'ana:babu wani Abu da ya tabbata daga manzaon Allah akan yin haka, kuma babu wani daya daga cikin magabata da ya aikata  haka.
📚(masa'ilah 102).

SIFFOFIN MACE TA GARI

📜📜📜
SIFFOFIN MACE TAGARI📜📜📜
Shaikhul Islam Ibn Taimiyya yace"mace ta gari tana kasancewa tare da miji nagari tsawon shekaru masu yawa.
Ita ce jindadin sa Wanda manzon Allah(saw) ya fada a cikin hadithi yace"ita duniya wani Dan jindadi/amfani ne kuma mafi alkhairin amafani/jindadin ta ita ce mace mumina wadda idan ka kalle ta sai ta  burgeka, idan kabata  umarni sai ta yi maka da'a, idan kafita kabarta zata  kiyaye ka ga kanta(ba zata ci amarnarka ba).

Itace wadda manzon Allah yayi umarni da ita a cikin  zancen sa lokacin da muhajiruna suka tambaye shi:wace dukiya ya kamata murika? Sai yace: "harshe mai yawan ambaton Allah, da zuciya mai yawan godiya, da MACE TAGARI mai taimakon dayanku bisa imani"
(📚Timidhi ya Ruwaito shi saga Salim ibn Abilja'ad daga  Sauban).

Ita ce wadda kauna/soyayya da tausayi yake tabbata da ita kamar yanda Allah (SWT) ya fada a cikin Alqr'an, radadin rabuwa da ita yafi tsanani sama da na mutuwa,wani lakacin ma yafi tsanani sama da kariyar arziki, yafi tsanani sama da barin wurin zama(gida) musamman idan akwai alaqa a tsakanin su (zumunta) ko kuma suna da  'ya 'ya a tsakanin su wadan da rabuwar zata jefasu cikin yanayi na kunci da  tozarta da kuma  gurbacewar dabi'un  su"
(📚majmu'ul fatawa 35/299)

🕌🕌COMMITTEE FOR SOCIAL MEDIA MASJID ABU HURAIRA TSAFE ZAMFARA STATE (07039140450)

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 007

*GORON SALLAH*1438/2017

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_*  *Malam Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na takwas(008)_

``` √ AKIDATUL BADA’A.

Akidatul Bada’a rukuni ce daga cikin rukunnan
addinin Shi’a, akidatul bada’a tana nufin Allah
yana yin kuskure a cikin ayyukansa da
maganganunsa. Sai daga baya ya gano kuskure
ne, sai ya canza. Sun sanya ta a cikin rukunnan
addinin su domin su watsar da nassosa na
shari’ar musulunci da nuna duk abunda musulmi
ya yarda da shi to Allah ya canzashi bayan ya
gano kuskurene. A takaice dai a wajen su Allah
yana jahiltar wasu ayyuka da magan-ganunsa,
wanna akidar tana daga cikin mafi munin akidar
su domin suna nuna tozarci da kasawa da jahilci
ga Allah wadanda duk sunkoru ga reshi (SWT).
Shi kuma Mahadin sunnah, ingantacciyar ruwaya
ta zo game da shi cewa yana daga cikin tsatson
Hassan bin Aliyu
(R.A).
Daga karshe yaku bayin Allah, wannan yar
takaitattar nasiha ce da tayi bayani akan micece
Shi’a da miyagun akidunta saboda haka ne
malamai sun yi hukunci cewa ‘Yan Shi’a kafirai
ne, kuma zindikai ne.
Imamu Malik yace “Wanda yake zagin sahabban
Manzon Allah ba shi da rabon muslunci” (Wato
ba musulmi bane)
Imamu Ahmad bin Hambal yana cewa “ba’a
auren mata ‘Yan Shi’a, kuma ba’a cin yankansu
domin sunyi ridda sun bar musulunci. Kaga anan
Imamu Ahmad yana nufin idan har baya halatta a
auri diyan su mata to min babi aula kenan mu
musulmai baya halatta mu basu aure, duk da
cewa addinin muslunci ya halatta auren
ahlulkitabi, wannan yana nuna munin Shi’a sama
da Yahudu da Nasara.
Manufar wannan bayanin bayana nuna karanta
darajar Aliyu ko ahlulbaiti bane, lallai
ahlussunnah suna son Aliyu da ahlulbaiti da
sauran sahabbai. Shi’a ita ce kungiya mafi hadari
ga addinin muslunci, domin suna kashe musulmai
suna kyale masu bautar gumaka, suna zagin
Sahabbai amma a hakika Annabi suke zagi
Imamu San’ani yana cewa “al-ummar musulmi ta
hadu akan kafircin Shi’a Imamiyya
Sheikh bin Baz yace “Shi’a Rafida da kumaini
suna kan shirka babba
Sheikh Albani yace “Lallai abun da kumaini yake
kira akan shi na cewa sahabbai sun juyar da
Qur’ani wannan kafirci ne babu shakka
Don haka babu wadanda sukafi ahlussunnah son
ahlulbaiti da sauran sahabbai da magabata gaba
daya
Kamar yadda Imamu Shafii ya kawo a cikin
diwaninsa
Ya ku ahlulbait Rasulullah, lallai Allah ya farlanta
sonku kamar yadda ya saukar a cikin Qur’anin sa
Ya isheku girman alfahari duk wanda yayi salati
ga Manzon Allah bai sanya kuba to bashi da
salati.

DA WANNAN NE MUKA KAWO KARSHEN
WANNAN RUBUTU, MUNA GODIYA GA MASU
BIBIYARMU A KODA YAUSHE, ALLAH YA
AMFANAR DAMU DA ABUNDA MUKA KARANTA,
YA KARA TSAREMU DAGA MIYAGUN AKEEDU.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
08064734911```

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 006

*GORON SALLAH* 1438/2017

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_*  *Malam Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na shida(006)_

```√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA IMAMA.

Imama a wajen ‘Yan Shi’a tana dai-dai da
Annabawa a wajen musulmi, don haka ma suka
ce imamansu (12) ma’asumaine (Basu yin laifi)
“Yan Shi’a sun kudurce cewa lallai Imama baza
ta kasan ce ga kowaba sai ga Aliyu da diyan sa
(12) kuma sun sanya wannan a cikin rukunnan
imani suka ce duk wanda yayi kudurin Imama ba
ga Aliyu ko diyansa ba to ya kafirta kafirci mai
girma.
Hakika malaman sunnah sun hadu akan cewa
wadanda suka can-canta da halifanci bayan
Manzon Allah gasu kamar yanda suke a jere: -
Abubakar, Umar, Usman, sannan Aliyu, kuma
haka suke a wajen falala.
Ma’ana: Abubakar shine mafifici, sannan Umar,
sannan Usman, sannan Aliyu. Malaman suka ce
duk wanda yace Aliyu yafi Abubakar da Umar
falala to shi dan bidi’a ne.

√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA ILIMIN FIQIHU.
‘Yan Shi’a sun sabama ahlussunah dangane da
ilimin Fiqihu saboda basu karbar hadisai
ingantattu da sunnoni da aka ruwaito a cikin
littafan sunnah.
‘Yan Shi’a mabukata ne ta bangaren fahimtar
sunnah.
Sun kir-kiri bidi’o’i a cikin kiran sallah kamar
haka:
Suna karawa da Ash-hadu anna Aliyu
Waliyuullah, Madadin Ash-hadu anna
Muhammadarrasulullah
Sun kir-kiri bidi’o’i ta bangaren sallah kamar
haka:
Suna hada sallah ba tare da wani uzuriba
Basu yarda da sallar juma’a ba ko da a zahiri
anga sunayi.
Sun haramta cin zomo
Sun halatta auren mutu’a
Duk wadannan haramunne ga Ijma’in malamai.
ALLAH YA KARA TABBATAR DAMU AKAN
HANYA MADAIDAICIYA.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
08064734911```

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 005

*GORON SALLAH*1438/2017

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_*  *Malam Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na biyar(005)_

```√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA TAUHIDI.

‘Yan Shi’a mushrikai ne ta bangaren tauhidi
domin suna rokon Aliyu, da Hussaini da Zainab
da Fatima, dare da rana, lokacin tsanani da
jindadi. A wurin ‘Yan Shi’a ziyartar kabarin
Hussaini yana daga cikin manya-manyan
sabubban samun waraka daga rashin lafiya, da
wadatar arziki da samun taimako da biyan
bukata.
Babban malamin Shi’ar nan Jafar Ibn Muhammad
Kaulawaihi ya kawo a cikin littafinsa mai suna
“Kamilizziyarat” wato kammalallar ziyara
Babin da ke Magana akan ziyarar Hussaini kamar
ya ziyarci Allah a alarshin sa
Babin da ke Magana akan wanda ya ziyarci
Hussaini tana kore dukkan bakin ciki
Babin da ke Magana akan ziyartar Hussaini tana
dai-dai da aikin Hajji da Umra
‘Yan Shi’a sun kudurce cewa lallai ziyartar
kabarin Hussaini yafi tsayiwur Arfa falala kuma
lallai Allah yana kallon wadanda suka ziyarci
Hussaini kafin ya kalli wadanda suka tsaya a
Arfa. Haka nan kuma ‘Yan Shi’a sun kudurce
lallai limaman su sha biyu (12) daga cikin diyan
Aliyu ma’asumai ne kuma sunfi Annabawa da
Mala’iku falala, kuma basu mutuwa, kuma sun
san gaibu kuma su ke kula da halittun Allah gaba
daya.
Yazo acikin littafin su “Alkafi”
babi da ke Magana akan lallai limamai (12)
hasken Allah ne
Babi da ke Magana akan lallai limamai (12) sun
san abun daya kasance da abun da zai kasance
nan gaba, babu wani abu da ke boyuwa a kan su
Babban mawakin nan na Shi’a Aliyu Sulaiman
Almazidi Allabanani (Libenon) ya fadi a cikin
wakar sa yayin da ya ke yabon Aliyu
Baban Hassan kaine ainihin abun bauta, kuma
kaine ikon Allah baki daya
Ilimin ka ya kewaye dukkan gaibi, ko akwai wani
abu da zai boye maka?
Baban Hassan kaine mijin Batula, kuma kaine
abun bauta kuma kaine ma Manzon Allah
Kaine cikakken wata, kuma kaine ranar hankulla
mamallakin ubangiji kaine mai mulki
Zuwa gareka makomar komai take, kuma kaine
masanin abunda ke cikin zukata
Kaine mai tayar da wadanda ke cikin kabari,
kuma nassi ya nuna kai ne mai hukunci a ranar
kiyama
Kai ne mai-ji kuma mai gani, kai ne mai iko akan
dukkan komai
Badon kai ba da tauraro baiyi tafiya ba badon kai
ba da falaki bai zagayaba
Kai ne masanin dukkan sarari, kai ne magana da
Ahlulrakim
Ba don kai ba da Musa bai zama kalimi ba, tsarki
ya tabbata gareka da kai ne yayi Magana
Badon kai ba da Annabawa basu zamoba
Badon kai ba da Manzanni basu zamoba
Badon kai ba da alkalami bai rubuta a alloba
Badon kai ba da talikai basu zamoba, dukkan su
bayinka ne kuma mallakar kane.
Tambaya ita ce miya rage ma Allah idan har
Aliyu ya zama haka? Allah ya nisanta Aliyu ya
ksanace yana da siffa ta rububiyya. Wannan ita
ce tsantsar akidar Kiristoci ga Annabi Isah da
suka ce masa Allah, kaga wannan yayi dai-dai da
akidar Shi’a ga Aliyu (R).
ALLAH YA TABBATAR DAMU AKAN SUNNAH.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
08064734911```

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 004

*GORON SALLAH*1438/2017

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_* *Malam Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na Hudu(004)_

```√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA SUNNAH.
‘Yan Shi’a sune mafi jahiltar Hadisai da Sunnoni
da ruwayoyi daga Manzon Allah. Ba zaka samu a
cikin zancan su ba cewa daga Manzon Allah,
abun da zakaji kawai shine. Aliyu yace, ko Jafar
yace ko Hussaini yace mafi yawan ruwayoyin su
karya ce suka kirkira suka jingina ga Aliyu da
Ahlulbait musamman Ja’afarus-sadiq
‘Yan Shi’a basu yarda da littafin Bukhari, da
Muslim da sauran littafan Hadisan nan guda hudu
ba, suna cewa *kirkiren karya ne, kuma
tatsunniya ce a cikin su.
Suna da wani littafi wanda a wajen su yayi dai-
dai da bukhari da Muslim da sauran littafan
hadisi mai suna “Alkafi” wanda malamin su
Kulaini ya rubuta cike yake da karai-rayi da
tatsuniyoyi.

√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA SAHABBAI.
Sahabbai sune mafifitan halitta bayan Manzon
Allah (SAW). Allah (SWT) ya fada a cikin
littafinsa mai tsarki yana mai yabon su
“Muhammad Manzon Allah ne, kuma wadannan
da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai,
masu rahama ne a tsakanin su, kana ganin su
suna masu ruku’i masu sujada, suna neman
falala daga ubangijin su da yardarsa, alamarsu
tana a cikin fuskokin su daga kufar sujuda.
Wannan shine siffar su a cikin Attaura. Kuma
siffarsu a cikin Injila, itace kamar tsiron shuka
wanda ya fitar da reshen sa, sa’an nan ya
karfafa shi, yayi kauri, sa’annan ya dai-daita a
kan kafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu
shukar domin (Allah) ya fusatar da Kafirai game
da su, kuma Allah yayi alkawari ga wadanda
sukayi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai
daga cikin su da gafara da lada mai girma
(Suratul Fat’h – 29)
Duk wanda ya soki Sahabban Manzon Allah
hakika ya soki Manzon Allah domin zagin
Sahabbai gaba dayansu kafirci ne kuma ridda ne.
Kulaini ya fada a cikin littafin sa “Alkafi” cewa
“Lallai sahabbai gaba dayansu sunyi ridda bayan
rasuwar Manzon Allah in banda mutum ukku.
‘Yan Shi’a sunayin addu’a ta la’anci zuwaga
sahabban Manzon Allah a cikin salla, kamar
yanda Majiisi ya ambata a cikin littafinsa “Al-
anwar”. Suna cewa ‘Allah ka la’anci gumakan
Quraishawa guda biyu da makaryatansu guda
biyu da diyansu guda biyu’.
Gumakan sune Abubakar da Umar
Makaryatan sune Abubakar da Umar
Diyansu kuma sune Aisha da Hafsat
Kumaini (Batacce) ya fada a cikin littafinsa
“Hukumatil Islamiyya” cewa: Lallai Abubakar da
Umar fasikaine kuma wawaye ne.
Yan Shi’a suna da’awar cewa Usman munafukine,
Abubakar fasikine, Aisha mazinaciyace da dai
sauran miyagun maganganu da suka fada ga
sahabbai wanda da suna nan cike da littafan su.
ALLAH YA TABBATAR DAMU AKAN
INGANTACCIYAR AKEEDA.
ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU SINAN)
08064734911```