Wednesday, 6 December 2017

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 005

*GORON SALLAH*1438/2017

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_*  *Malam Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na biyar(005)_

```√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA TAUHIDI.

‘Yan Shi’a mushrikai ne ta bangaren tauhidi
domin suna rokon Aliyu, da Hussaini da Zainab
da Fatima, dare da rana, lokacin tsanani da
jindadi. A wurin ‘Yan Shi’a ziyartar kabarin
Hussaini yana daga cikin manya-manyan
sabubban samun waraka daga rashin lafiya, da
wadatar arziki da samun taimako da biyan
bukata.
Babban malamin Shi’ar nan Jafar Ibn Muhammad
Kaulawaihi ya kawo a cikin littafinsa mai suna
“Kamilizziyarat” wato kammalallar ziyara
Babin da ke Magana akan ziyarar Hussaini kamar
ya ziyarci Allah a alarshin sa
Babin da ke Magana akan wanda ya ziyarci
Hussaini tana kore dukkan bakin ciki
Babin da ke Magana akan ziyartar Hussaini tana
dai-dai da aikin Hajji da Umra
‘Yan Shi’a sun kudurce cewa lallai ziyartar
kabarin Hussaini yafi tsayiwur Arfa falala kuma
lallai Allah yana kallon wadanda suka ziyarci
Hussaini kafin ya kalli wadanda suka tsaya a
Arfa. Haka nan kuma ‘Yan Shi’a sun kudurce
lallai limaman su sha biyu (12) daga cikin diyan
Aliyu ma’asumai ne kuma sunfi Annabawa da
Mala’iku falala, kuma basu mutuwa, kuma sun
san gaibu kuma su ke kula da halittun Allah gaba
daya.
Yazo acikin littafin su “Alkafi”
babi da ke Magana akan lallai limamai (12)
hasken Allah ne
Babi da ke Magana akan lallai limamai (12) sun
san abun daya kasance da abun da zai kasance
nan gaba, babu wani abu da ke boyuwa a kan su
Babban mawakin nan na Shi’a Aliyu Sulaiman
Almazidi Allabanani (Libenon) ya fadi a cikin
wakar sa yayin da ya ke yabon Aliyu
Baban Hassan kaine ainihin abun bauta, kuma
kaine ikon Allah baki daya
Ilimin ka ya kewaye dukkan gaibi, ko akwai wani
abu da zai boye maka?
Baban Hassan kaine mijin Batula, kuma kaine
abun bauta kuma kaine ma Manzon Allah
Kaine cikakken wata, kuma kaine ranar hankulla
mamallakin ubangiji kaine mai mulki
Zuwa gareka makomar komai take, kuma kaine
masanin abunda ke cikin zukata
Kaine mai tayar da wadanda ke cikin kabari,
kuma nassi ya nuna kai ne mai hukunci a ranar
kiyama
Kai ne mai-ji kuma mai gani, kai ne mai iko akan
dukkan komai
Badon kai ba da tauraro baiyi tafiya ba badon kai
ba da falaki bai zagayaba
Kai ne masanin dukkan sarari, kai ne magana da
Ahlulrakim
Ba don kai ba da Musa bai zama kalimi ba, tsarki
ya tabbata gareka da kai ne yayi Magana
Badon kai ba da Annabawa basu zamoba
Badon kai ba da Manzanni basu zamoba
Badon kai ba da alkalami bai rubuta a alloba
Badon kai ba da talikai basu zamoba, dukkan su
bayinka ne kuma mallakar kane.
Tambaya ita ce miya rage ma Allah idan har
Aliyu ya zama haka? Allah ya nisanta Aliyu ya
ksanace yana da siffa ta rububiyya. Wannan ita
ce tsantsar akidar Kiristoci ga Annabi Isah da
suka ce masa Allah, kaga wannan yayi dai-dai da
akidar Shi’a ga Aliyu (R).
ALLAH YA TABBATAR DAMU AKAN SUNNAH.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya(ABU SINAN)
08064734911```

No comments: